← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 152

Sashe 76

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karairaiyar da Ya’isha ta dinga yi da shishshige masa har zuwa lokacin da ya fita saida ya bawa Jidda kunya,shi kuma yanata basar da ita kamar bai ma san ta na yi ba.
Hakanan ya yi wa Manubiya ya jiki bayan ya ajjiye uban tulin laidojin hannusa ya juya ya yiwa su Innaa da Mommy Allah ya k’ara sauk’i ya fita.
Murmushi kawai Jidda ta yi a ranta tace”kina nan kina iyayi”
“Yana chan yana ziryar zuwa gadon k’aya ba a kula sa.”

A d’akin su Inna suka zo suka tarar da Ummi shiyasa Ummin ta mik’e ta fara haramar tafiya dan ta na so ta d’an basu guri kuma ta lura kamar akwai maganar da Innar ta ke so su yi saboda taga matar sai yawan yin shiru ta ke yi kamar tana ta tunani.
Ummi tana mik’ewa Yahanasu ma ta mik’e tace “Bara itama ta je ta d’an shirya tanada client da za su had’u in the next 2 hours”
Ta riga ta san Yashjub yananan ba inda zai je 24/7 shiyasa hankalinta kwance sukayi musu sallama ta bar su Mommy a d’akin suka tafi tare da Ummi wadda take ta addu’ar Allah ya sa su Mommy ma su yi kan gado su bar Manubiya da y’an uwanta su d’an keb’e, dan ta san rabon da su yi eyes to eyes tun kafin ta tafi honeymoon..

Ita kanta Manubiya so take ta keb’e da ahalin nata, dan ta lura ba iyaka Inna ba hatta Jidda kamar tanada damuwa
bayan ta Al’ameen wadda ta riga ta san ta da ita..
Sannan kwana biyu ba ta ji Ya Musbah ba, kuma ta kirasa a waya ko jiya ma bai d’auka ba! “anya kuwa lafiya??”
Ta yi wa kanta tambayar a cikin ranta.
Illai kuwa! wannan itace damuwar su Innar, saboda tun bayan sati 6 da suka wuce
da Baraka ta tare Abu bai yi dad’i ba…zuwa yanzu Inna ta fahimci ashe ladabin kura Baraka ta yi musu,
tunda gashi yanzu ta rabasu da Ya Musbah…
Tana tarewa ko sati ba ta yi ba tace “ita ta tsani unguwar”
Haka nan jikinsa yana rawa ya d’auki d’an kud’in da ya tara zai biya kud’in registration d’insa dan lokaci ya kusa cika
Suka tashi a unguwar suka kama wani gidan a Na’ibawa chan nesa da su Inna tsabar rashin adalci irin na Baraka.
Kuma ta hanasa fad’a musu sai a ranar da za a tashi d’in.

Da dafarko da suka tashi yana zuwa duk bayan kwana biyu a d’an mashin d’insa,sai ya dawo zuwa bayan sati d’aya tou tun daga nan basu sake saka shi a idanunsu ba, gashi kayan abincin su ya k’are. Jiya babu kalar kiran da Jidda ba ta yi masa a waya ba amma ya k’i d’auka….
Tabbas sai yanzu Innaa ta yi da na sanin barin shi ya dawo da Baraka
Dama baba yace mata “Indai Baraka ce tou kuwa za ta sha mamaki…”
Gashi kuwa k’iri k’iri ta rabata da d’anta kuma tunda ta dawo abu guda da inna ta fara fahimta shine Yaa Musbah mugun mugun tsoron ta yakeji.
Gashi ba a Isa a ce abunda ta yi bai kamata ba tashi d’aya zai hau kumbure kumbure…

Tun a kan issue na tashin su da Innaa ta so ta hana tashi d’aya ya nuna hakan fa ba zai yiu ba!.
Muhsin kuwa da ya yi alk’awarin d’auka ko kalar k’ofar gidansa na Na’ibawa har yau bai sani ba.

Ya Nafi’u kuwa ko waya basa yi,tun lokacin da ya dawo da Baraka dama ya fice a harkar sa, ko da ya zo tashin ma bai gaya masa ba dan ya san zai hana shi shima kuma ya Nafi’un har yau bai ce masa
‘Musbahu Ashe ka tashi ba,’
K’ark’ari ya kan je ya duba su Inna shi da Aisha da Khairat duk bayan kwana biyu, amma shi da Ya Musbah kam ko a waya sun daina gaisawa. Baba ne dama ya kamata ya tsawatar ya dawo da Abotar tasu to shi kuma Baba tun lokacin da Inna ta amince a dawo da Baraka tashi d’aya ba tare da ta shawarci kowa ba
Ya ce “case in dai na Musbahu da Baraka ne to ba zai bada shawarar komai ko ya ce zai saka Baki a kai ba…”
Gashi issue na Baba da su Baba Habu abun ba dad’i nan ma…Kaka mallan ma ya fara gulmace gulmace wai “Baba ya bi kud’i ya aurawa mai kud’i y’arsa amma gashi ya barsu a talauci har yau bai tab’a ganin an kawo ko kwayar shinkafa k’ofar gidan ba.!”

Inna tana wannan tunanin Yashjub ya dawo d’akin yanata faman sussunkuyar da kai,
so yake ya tambayi Manubiya mai take so ta ci dan tun yoghurt d’in safe sai d’an malelen Mama da ta ci daga su bata sake cin komai ba gashi Doctor yace “ana so ta dinga cin abinci sosai saboda lafiyarta da lafiyar Babyn”…to kuma shi har ga Allah kunyar Inna yakeji
dan d’azu ma sai da Ummi ta sa ya ji kunya
Haka nan ta tisa shi a gaba tana tsokanar kalar zumud’in da yake ta yi a gaban su Innar…

Yana wannan tunanin ya ji wayarsa ta d’au k’ara, kamar ba zai d’auka ba dan da ya zaro bak’uwar number ya gani, sai kuma ya d’auka ya kara a kunnensa kafin yace ‘’Assalam alaikom,’’
A gigice ya ji wata murya kamar ta security d’insa yana cewa”Sir wuta!wuta!! ya kama a estate na kano ka zo
da wuri…….’’
Mutumin yana gama fad’in haka ya kashe wayar….
in banda hayaniya da k’arar y’an kwana kwana ba abunda Yash ya ji yana tashi daga background d’in.

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
ya shiga ambata a fili.

Da sauri Yasira ta matsa tace ‘’mai ya faru?’’

Cikin karkarwar murya da kyar ya kalleta yace
“Estate d’ina ne, ya kama da wuta’’

Salati gaba d’ayan su suka saka suka mik’e tsaye.

Cikin tsananin gigita Yasira tace “subahanallah!!
mu je mu je da sauri…”
Ta fad’i haka tana yin gaba.

Da sauri ya ruk’o Hannunta ya ce
‘’a’a, it’s not safe, kar ki damu zan je ni d’aya, zan kira Yassir a hanya sai mu had’u a chan. “

A hankali ta d’an dawo ta tsaya kafin tace “Allah zai mayar da alkhairi, inshaaAllah’’

Jinjina kai yayi yace”inshaaAllah”sannan yace”ku yi addu’a Allah ya sa Mutane ba su mutu ba!”

Jinjina kai ta yi itama, daga haka ya zare hannunsa a nata ya k’arasa inda Manubiya take zaune a kan gadon ya ce “bara in je ko?”
sai kuma ya d’an sunkuya yace
“Dan Allah kar ki d’aga hankalinki, ba zan jima ba zan dawo, okay?”

Ba ta san lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba, ita ya kamata ta rarrashe sa amman kalli shi yake rarrashin ta.
Da sauri ta sunkuyar da kanta tana jinjina kai…
Murmushi ya yi, daga haka ya yi sallama da su Innaa tukunna ya juya ya fita gaba d’aya suna jajanta masa tare da adduar alkhairi.

Yana fita ta sake sakin kukanta tana jin wani iri a cikin ranta

A hankali Innaa ta koma kusa da ita ta zauna ta shiga rarrashin ta tana bata baki,Mommy kuma ta shiga kiran Daddy domin ta sanar da shi halin da ake ciki.

Cikin rashin jin dad’i Ya’isha tace
“Ai dama matsalar had’a jini da mai farar k’afa kenan!
Dama ace a iyaka aure aka tsaya to da na san abun zai zo da sauk’i”.

Shiruu duk suka yi d’akin ya d’auki shiruu
Kafin Ya’isha ta sake cewa “Allah dai ya rufa asiri ya kuma tsayar a iya nan’’

Zuwa yanzu Manubiya ta ji ba za ta iya jurar cin fuska a gaban ahalin ta ba! Ashe dama jiya da suka dawo saboda a gaban Yashjub ne shiysa suka yi mata kissa kenan suke wani nan nan da ita…
Shiyasa kawai cikin wani irin fushin da ba ta san tana da shi ba ta mik’e ta cewa Inna “ta zo su tafi”

Cikin rashin jin dad’i Mommy tace “Kamar ya ku tafi?
Me kike nufi?
Idan tafiya kike son yi ai mu za mu tafi da ke ba Innaa kad’ai ba ko?”

“A’a inaga tana nufin za ta koma gidan ubanta ne!
Ai ta shafa farar k’afar tata yadda ya kamata shiyasa ta ga ya ci ace ta tafi…”
Cewar Ya’isha.

Ba k’aramin mamaki Innaa ta yi ba, ganin yadda ko gezau Mommy bata yi ba balle asa ran za ta cewa Ya’isha ta yi shiru wadda ta cigaba da fad’o zafafan maganganun kamar wata tab’ab’b’iya.

Cikin nutsuwa Innaa ta mayarda Manubiya ta zaunar da ita tace”kar in ji zance mara dad’i, ki zauna ki yi wa mijinki addu’a, ki jira dawowarsa”
tukunna ta kalli su Jidda wadda har ta fara kwallah tace mata ‘’ku tashi mu tafi’’
Sai da suka mik’e tukunna Innaa ta juya ta k’arasa inda Mommy take tace mata ‘’Hajiya mun tafi, Allah ya k’ara sauk’i’’
Daga haka ta fice ta na jin yadda kukan Manubiya yake dira a cikin zuciyarta kamar dalma…..

Sam ba haka Mommy ta so ba, so ta yi ace Manubiya ko k’anwarta ko Innar tasu wani ya biyewa Ya’isha, daga nan ayi kacha-kacha su yi zuciya su tafi da y’arsu ta yadda za ta raba auren ta kuma ga bayan cikin ta kowacce hanya hankali kwance…..
Yanzu haka ji take yi kamar zuciyarta za ta kama da wuta, ita kad’ai ta san halin da take a ciki tsakanin jiya da yau..shiyasa ko Baba larai ba ta gayawa ba ta taho asibitin dama opportunity irin wannan kawai take nema ta samu a yi ta ta k’are dan ta riga ta kai peak.Sai dai
Kash!Inna, ta lalata mata komai…

Su Inna suna fita, Yasira ta yi tsaki ta juya itama ta fita….
Daddy da Yassir ta fara kira suka yi magana tukunna ta kira wata k’awarta wadda bata dad’e da yin aureba a nan estate d’in Yashjub d’in suke haya, dan haka ta kirata domin ta ji ya abun yake, shin sun samu sun fita lafiya ko?.
Chapter 76 · 0% Book details