Sashe 81
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Duk yadda Yassir ya so ya jira ya d’an saisaita kansa kafin ya fuskanci Kausar kasawa ya yi…ba ya so ya tunkare ta yanzu dan tabbas zai iya illatata amma kuma zuciya da bak’in cikin rashin samun nasarar kashe Yashjub da kuma kishi ne suka k’i su barshi ya iya jira d’in, dan haka kawai ya nufi gida gadan-gadan.
A b’angaren Kausar kuwa!!
A mugun rikice ta shiga gidan itama
sakamokon wani amai mai k’arfi da ya hanata sukuni yake ta faman yunk’uro mata…ta na shiga d’akinta kuwa ya taho da mugun k’arfi..
Da gudu ta nufi toilet amman tun kafin ta k’arasa ta fara sakinshi.
Ta jima tana yi kafin ta samu ya d’an sarara mata, ta shiga mayarda numfashi…
Yanayin k’arnin aman ne ya firgitata ya tsoratata..dan haka ta na haki ta shiga hargitsa toilet ɗin a gigice tana neman pts, a lokaci guda kuma tana tana addu’a.
Da ikon Allah kuwa ta samu,
dan haka ba ta yi wata wata ba ta auna kanta.
Bata iya ajjiyewa lokaci ya cika ba, hakanan ta shiga safa da marwa a cikin band’akin da abun riƙe a Hannunta idanunta kyam a kai, gaba d’aya ta hargitse ta ma rasa tunanin me za ta yi…tunda take ba ta tab’a
jin tsoron shigar ciki da fargaba da tashin hankali kamar na yau ba!.
Aikuwa tashi d’aya ta fara ganin alamun positive…kafin ma ya gama tabbatar mata da hakan ta fashe da wani irin kuka ta durk’ushe a wajen, tana kallon yadda abun yake yi mata nuni da tana d’auke da ciki ne.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
ta shiga maimaitawa a cikin zuciyarta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita…..
Ganin kuka ba zai fishsheta ba ne ya sanya ta share hawayenta ta mik’e jikinta yana wani irin karkarwa ta ajjiye abun ta shiga lissafin neman mafita……
Tashi d’aya kwakwalwarta ta d’auki chaji, dan haka ta fito ta nufi side d’in Mommy jikinta har yana wani Irin karkarwa.
Su Mommy suna isa gida ta wuce sama d’akinta, Baba larai tana ganin haka ta bita da sauri…
Sai da ta kai k’ofar d’akinta tukunna ta lura da Baba larai dan haka tace “larai ki je kawai ina buk’atar sarari..”
Daga haka ta bud’e ta shiga tana k’ok’arin rufowa Baba larai ta sa hannu ta tare k’ofar ta shiga ta rufo, Mommyn tana shirin yin magana ta ji Baba larai tana cewa”Khadija zama na a cikin gidan na ya k’are, dan haka na zo ne in yi miki sallama, sannan in gaya miki abunda ya faru da kuma taimakon da na yi miki d’azu wanda ya taso na gaggawa.
Daga nan ni kam yanzu ba sai anjima ba zan tafi!”.
Runtse idanuwa Mommy ta yi, kafin ta bud’e tace”dan Allah Larai ki barni in huta tukunna, za mu yi magana anjima..”
Cikin tarar numfashinta Baaba Larai tace “Au wai a tunaninki barazana ce nake yi?…wallahi wallahi na gama sakawa a raina Khadija barin gidan nan zan yi!..
Dan ba zan zauna rashin hak’uri da rashin lissafinki ya kaini prison ba!.
Bari ki ji abunda ba ki sani ba d’azu kuna fita na ji Daddy yana waya, ko kin san wanene ya kirasa?”
Kallonta Mommy ta yi tukunna tace”A’a”
Sai da Baba larai ta sake ce mata “kin san wa ya kirasa?”Mommyn tace “a’a”
suka yi haka har sau uku tukunna Baba larai tace”Mallan lawal!”
Wani kalar mahaukacin bugawa k’irjin Mommy ya yi, kafin cikin in Ina ta ce ”mme yya ce mmasaa??”.
“Cewa ya yi yana son magana da shi inaga, dan ji na yi Daddyn yana cewa
‘mallan lawal dama kana raye Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’ sai kuma ya fara basa hak’uri kafin na ji ya yi shiruuu yana sauraronsa sai
kuma yace ‘na godewa Allah, nauyi d’aya ya sauk’a a kaina, mallan lawal amma ba za ka iya gaya mini ta waya ba dole sai na zo??’
Daganan na ga ya fice compound ya nufi parking lot, to inaga case d’in Yashjub ne ya tsayar da shi wanda ba dan haka ba da tuni yanzu haka ma yana garin Garin Mallan……”
Cikin takaici Baba larai ta d’aura da cewa“wallahi Khadija in da ace ba ki tsaya dawo mana da aiki baya ba da tuni ba mu zo nan ba!
Na gaya miki Yarinyar nan barinta tare da Yashjub masifa ne a gareki amma kin k’i ki bada goyon baya a samu a fitar da ita daga rayuwar tasa cikin sauk’i, yanzu ai ga irinta nan! Idan kika ga yadda hankalin Daddy ya tashi gaba ɗayansa ya rud’e lokacin da ya ji mallan lawal yana a raye, za ki yi mamaki…kin san yanzu zai fara wasu wasin mutuwar Khadijah itama ai ko?”
A mugun rikice Mommy tace”larai shiyasa tun a lokacin na ce a kashe su, kika ce A’a za ki san yadda za ki yi dasu, yanzu ga irinta nan ai”
sai kuma ta fashe da kuka cikin gunjin kuka tace”wannan duk ba laifin kowa bane laifin Manubiya ne, ita ce wallahi, tunda ta zo shikenan ta lalatamin komai, larai na gaji kashe Yarinyar nan zan yi wallahi kuma ba ki isa ki hanani ba…”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”ba za a yi haka da ni ba, in da ace zan barki ki kashe rai da tuni mun yi tun a kan Khadija..hak’uri za ki yi ki kwantar da hankalinki ki danne zuciyarki tukunna ki ci riba, dan ni dai ba zan tab’a gajiya da gaya muku da ke da su Yassira ba saboda haƙurin ne kad’ai mafita”.
Cikin wani irin kuka Mommy tace “Larai yanzu to
ba Manubiyan ba, shi mallan lawal d’in larai mun bashi dama ta biyu amma kinga yanaso ya tona mana asiri, na rok’e ki da girman Allah ki taimaka mini ki rufa mana asiri a kawo k’arshen sa, dan wallahi na san gaskiyar lamari zai fad’awa Daddy idan har suka had’u dan in ba hakan ba menene zai sa yace yana son ganinsa?…”
Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace”kar ki damu..
Daddy yana fita na kira mutumin da muka ce ya saka mana ido a kansa, ashe ciwon hanta ne ya ke damunsa likita yace masa ba shi da sauran lokaci shiyasa yake neman Daddyn, saboda ya samu ya gaya masa gaskiya.”
Numfashi ta fesar kafin ta ci gaba da cewa”tunda dama mutuwa zai yi shiyasa kawai na cewa mutumin ya k’ara masa gudu, mu kuma za mu bashi naira miliyan d’aya…..to dai a halin yanzu Ina tabbatar miki mallan lawal ya tafi kai balance, dan mutumin a lokacin ce mini ya yi a take zai aiwatar da aikin saboda gidan dama ba kowa, shi mallan lawal d’in ne kawai a zaune a gidan da shi da jikarsa wadda take jinyar sa to alokacin ya ga itama ta fita ta nufi kasuwa……
yanzu miliyan d’ayan za a tura masa, dan naga ya kirani d’azu Ina asibiti shiyasa ban d’auka ba.! Muna tura masa ni kuma zan kama gabana dan ba zan zauna ki ci gaba da lalata m….”
Cikin Jin dad’in maganganunta Mommy ta rungume Baba larai, wanda hakan ne ya sa ta kasa k’arasa abunda take cewa, wani kuka Mommy ta fashe dashi tana cewa”na gode Larai na gode sosai, ki bani accnt number miliyan biyu ma zan bashi wallahi….sannan zan gyara wallahi zan yi yadda kike so, dan Allah kar ki sake cewa za ki tafi.”
Da kyar Mommy ta lallab’a Baba larai ta hak’ura da tafiya, daganan suka kira mutumin ya shaida musu cewa”Mallan lawal yana ma shirin shiga k’asa a halin yanzu dan wanka ma ake yi masa.”
Naira miliyan biyu Mommy ta tura masa a take, daga nan ta nutsu tana sauraron hud’ubar Baba larai.
Da sallama Yasira ta turo k’ofar d’akin ta shigo, kafin ta k’araso ta zo ta tsaya a gabansu.
Kallonta kawai Baba larai ta yi ta maida hankalinta ga Mommy kafin tace”a baya da kika iya kwantar da Kai wacce kalar riba ce ba ki ci ba?yanzu kuwa kinga ai komai lalace miki yake yi saboda rashin tunani da lissafin da kika bawa ragamar rayuwarki,kuma bari ki ji ba ni da tantama a yau Yash ya dasa ayar tambaya a kanki wallahi, saboda abunda kika yiwa Manubiya a gaban kowa ya na nuni ne da kin tsaneta dama tun asalin farko, wanda hakan zai sanya ya fahimci dama chan pretending kike yi kuma bakin ku d’aya ke da su Yasira duk ba son matarsa kuke yi ba!
Dan haka yanzu ko ciwon yatsa Manubiya ta yi Ina mai baki tabbacin Yashjub ke zai zarga, tunda dama ba wata shak’uwa ce a tsakaninku ba balle ya ki zarginku, kuma ko su Yasira sun je gidan ido zai sanya musu ya dinga d’arr d’arr da su ta yadda ba su isa yin komai ba, shikenan kina ji kina gani Manubiya zama daram!
Hakanan abubuwa za su yi ta faruwa da mu, tunda kink’i ki bada goyon baya mu samu a yi abunda za ta tafi.
Shiysa na yanke shawarar in tartara ya nawa ya nawa in kama gabana tun kafin bomaboman da za su iya hallaka ni su fara fashewa.”