← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 152

Sashe 55

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba k’aramin tashi hankalin Ya Musbah ya yi ba, tashi d’aya ya shiga tunanin shin ‘tayaya k’anwarsa za ta yi rayuwa a tsakanin waennan Yaran….’

Tashin motocinsu ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka, a hankali ya Nafi’u ya matso kusa da shi ya d’an dafa shi dan shi dama tun ranar da aka kaita Aisha ta basa labarin iskancin da su Yassirar suka yi…
Sai da ya fesar da iska tukunna yace “InshaaAllah komai zai yi dai dai, ka kwantar da hankalinka”
Cikin rashin jin dad’i Ya Musbah yace “Nafi’u kaga d’aya daga cikin illolin yin aure ba tare da anyi kwakkwaran bincike ba ko?
Abunda na ke gudu kenan shi kuma Baba….”
Da sauri ya Nafi’u ya katse shi ta hanyar cewa “Karka ce haka! babu ruwan bincike da abunda Ubangiji ya riga ya tsara, kaidai kawai mu taya ta da addu’a”.

Lumshe idanuwa ya yi ya bud’e, daganan suka fara jidar kayan suna kaiwa bakin k’ofa,Siyama kuma ta fara kiran Manubiya a waya, dan ya Musbah yana zuwa yace “kar su shiga kai tsaye, su jira Yashjub ɗin ya zo ya shigar da su tukunna.”
..
Tun lokacin da Yassira ta wuce ita kuma ta shige d’akinta ta zauna ta fashe da wani irin kuka..
Zuwa yanzu ta riga ta gama amincewa ‘babu ta yadda za ayi su zauna lafiya ita da sisters d’in Yashjub, banda Yahanasu.’.
Wanann wacce irin k’addara ce!!
Ace wai k’annen mijinka ne za su fito k’iri k’iri su ce maka “ba sa sonka!!
Kuma sai sun aura masa y’ar uwar su!”
Shin tayaya za ta yi rayuwa a cikin su, taya y’ay’anta za su rayu a tsakanin su?……

Tana cikin wannan tunanin ta ji an bud’e k’ofar an shigo, dan haka ta yi saurin juyar da kanta gefe ta fara k’ok’arin share hawayenta.

Murmushi ya k’ak’alo shima dakyar, tukunna ya k’arasa inda take ya tsaya ya shiga k’are mata kallo..
kafin chan ya fesar da iska, ya zauna a gefen ta yana mai ruk’o ta izuwa jikinsa, cikin sigar rarraashi yace
“Wanne d’an gangancin ne ya tab’a mini matata? Ko Inna kike missing?”

Shiruu ta yi ba ta ce k’ala ba kuma bata daina sauk’e ajiyar zuciya akai akai ba.

Murmushi ya sake yi ya d’ago da fuskarta yana kallonta kafin ya ɗan girgiza mata kai alamun ‘ki daina kuka’ tukunna ya ce “i’m not suppose to make you cry…babu kuka ta silata, ki daina pls Baby ki yi hak’uri”

Girgiza kai kawai ta yi ta fara k’ok’arin mik’ewa…a hankali ya ruk’o ta yace “Ki yi hak’uri!ko..na baki hak’uri ai,next time idan sukazo za su yi miki magana,it’s only a matter of time (ba da daɗewa ba) za ku fahimci juna da su inshaaAllah…
Yanzun akwai abunda ya d’an faru ne….”

Ba tare da ta kalle sa ba kanta a k’asa tace “saboda ka ƙi yarda ka auri Kausar?”

Sai da gaban Yashjub ya yanke ya fad’i ba na wasa ba!
Dan sam bai yi tsammanin jin hakan daga gareta ba, bai so ace ta ji wannan maganar ba!Maganar da yake rok’on Allah Ubangiji kar ya tab’a nuna masa ranar tabbatuwar ta, ko da a cikin mafarki ne.
Besides waye ma ya gaya mata?, sannan ai shi ba saboda ya ƙi yarda ya auri Kausar bane ya sa su ke rikicin nan da su! yaushe ma aka tab’a maganar auren sa shi da Kausar??
Ya yi tambayar a cikin ransa.

Shiruu yayi ya sake fad’awaduniyar tunani….
sai yanzu kansa ya d’au chaji! wato hatta su Yasira sun san zancen maganar Kausar tana son shi kenan , kuma sun so ya aureta ne, abunda shi da kansa bai sani ba….shiyasa kenan suke fushi suke wannan haukar. To amma Mommy ma a bayansu take itama ba ta son aurensa da Manu! Ba ta son farin cikin sa kenan?! Ita da y’an uwansa duk so suka yi su manna masa Kausar saboda basu damu da farin cikinsa ba ko ya abun yake ne???….
Tashi d’aya ya ji kansa ya d’aure……

Ajiyar zuciya ta sauk’e ganin yadda yayi shiruu ya sha jinin jikinsa, a hankali tace “Ba ka tab’a ce min Kausar family d’inka sukeso ka aura ba. ko a ranar da muka fara had’uwa da ita cemin ka yi she’s just a sister”

Ahankali ya fesar da numfashi, ya kamo hannayenta tukunna yace”Wallahi Allah nima yau na fara jin zancen nan
Wai ‘Kausar family d’ina suke so na aura!’
ban san maganar ba,
In da na sani kin san da zan fad’a miki,but a Ina kika ji zancen?”

Girgiza kai tayi tace “Shikenan”
daga haka ta fara k’ok’arin barin wajen!
A ranta kuma tana mamakin yadda still yake k’ok’arin b’oye mata zancen bayan ga mamaki nan k’arara a kwance a kan fuskarsa wanda hakan yake tabbatar mata da ya san da maganar.

A b’angaren Yashjub kuwa
mamaki yakeyi…shi dai ya san ya ji lokacin da Kausar tace tana son shi, ya san kuma dama Mommy za ta iya goya mata baya, amma bai san abun ya kai har haka ba, kuma harda su Yassira ma sun san maganar kuma suna so ya aureta ne bayan sun san ita d’in budurwar Yassir ce….
To me yake faruwa ne a cikin gidan nasu wanda shi bai sani ba?, dan ko Manubiya bata gaya masa ba ya fahimci a zuwan su na yau ne aka samu wata ta gaya mata wannan maganar domin a shiga tsakanin ta da shi!
Me yasa su Yassira za su zama haka ne!
Wannan wacce
iriyar halayya ce suka k’irk’iro da ita sabuwa…..

Ji yayi kawai ta bud’e k’ofar ta fita, har ga Allah har ta miƙe ta isa ga ƙofa ta fice duk bai san lokacin ba…tana fita wayarta ta d’auki k’ara, dan haka ta d’auka ta kara a kunnenta…
Bama ta iya ganin sunan mai kiranba sai da Siyama ta fara magana tukunna ta fahimci ita ce me kiran, shiyasa ta yi iyakar bakin k’ok’arinta ta tsayar da hawayen ta d’an share, tukunna ta sauk’a k’asan da sauri dan ta ji kamar Yashjub d’in zai fito ita kuma har ga Allah a yanzu dai ko fuskarsa bata k’aunar gani!
Zuciyarta ta gama aminta da cewa ‘ya san da zancen Kausar amman ya k’i gaya mata’
dan haka tashi d’aya ta yi concluding akan shima yana son Kausar d’in wataƙila dai akawai wani abu da yake b’oyewa amman dai yanada niyyar auren Kausar duba da yadda ya yi shiruu ya gagara cewa komai.

Wani irin mahaukacin tafarfasa zuciyarta takeyi, ita kanta ba ta san ta na son Yashjub kuma tana kishin sa irin haka ba sai yanzu da ta ji maganar aure na shi da wata
sannan kuma yanayin martanin da ya bata na maganar da kame kamen da ya hau yi mata duk bayan ya ji maganar sun tabbatr mata akwai zancen b’oye mata kawai yayi.

Kafin ta k’arasa k’asan har ta fara haki, tsabar yadda k’irjinta da zuciyarta suke lugude
ga kuma sauk’an stairs.

A bud’e ta hango k’ofar dan haka ta tsaya ta ɗauki mayafinta wanda ta bari akan kujerar ɗazu, ta rufa, tukunna ta ƙarasa da d’an sauri sakamokon fara hango ahalinta da ta yi..dan chan ta hango Muhsin yana fama da roba sai k’ok’arin d’auka yake yi.

Da sauri ta k’arasa, ta na fita sukayi karo da su jidda dan haka ta fad’a jikinsu cikin murna da kewar su.
Sai da ta yi da gaske tukunna ta samu ta hana kanta kuka,
dan ganin su ɗin da tayi ba kad’an ba yasa ta sake zama emotional(sake jin zuciyarta ta yi rauni).

Murmushi kawai suke ta zubawa suna kallon ta tana faman bin su ɗaya bayan ɗaya tana rungume su har Ya Musbah, Ya Nafi’u ne kawai batayi hugging ba..
Daga nan ta fara jan hannun Jidda tana cewa”su shigo”
ba tare da ta kalli kowa ba, dan sai yanzu ta tuna yadda ta sauk’o ba tare da ta wanke fuskar ta ba…ta san tabbas idan suka yi mata kyakkyawan kallon kurilla to tsaf za su fahimci kuka takeyi, sai dai kuma abunda ba ta sani ba shine tana fitowa duk suka lura da hakan.

Ya Musbah ne ya tsaida ita ta hanyar cewa”ki bari ya zo ya shigar damu mana”

Dariya Siyama tayi
kafin tace “Allah ya Musbah ka iya abun dariya,”
Sai kuma ta kalli Manu tace
“Tun d’azu fa shi ya tsayar da mu, akan wai ala dole sai Ya Yash ya ce masa ya shiga tukunna zai shiga.”

Ahankali ta juyo tace
“Dan Allah ku shigo mana”.
Yana shirin yin magana Yashjub d’in ya k’araso shima yana d’an murmushi yace “bismillah, amma dai next time ba sai na ce ka shigo ba gaskiya”.
Duk murmushi sukayi banda Ya Musbah wanda hankalin sa ya tashi da ganin yanayin Manubiya, dan ya tabbatar da kuka ta yi, kukan ma bana wasa ba dan gashi hatta kan hancinta yayi ja!……

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 23*

Ahankali ta juyo tace
“Dan Allah ku shigo mana”.
Yana shirin yin magana Yashjub d’in ya k’araso shima yana d’an murmushi yace “bismillah, amma dai next time ba sai na ce ka shigo ba gaskiya”.

Duk murmushi sukayi banda Ya Musbah wanda hankalinsa ya tashi da ganin yanayin Manubiya, dan ya tabbatar da kuka ta yi, kukan ma ba na wasa ba tunda gashi hatta kan hancinta yayi ja!……

Anan parlourn k’asan suka nemi guri suka zazzauna,
tukunna su Jidda suka shiga gaida Yashjub cikin girmamawa da mutuntawa.

Da kulawa ya amsa yana tsokanar Muhsin da d’an lukuti,
kafin ya amsa gaisuwar Aisha da y’arta daganan suka gaisa cikin mutunta juna shi da su Ya Musbah.

Yunk’urawa Manubiya ta yi tace “bara na kawo muku ruwa” da sauri Ya Musbah yace “A’a sauri fa mukeyi”

Aisha ce ta kalli Yashjub tace
“ga gara nan mun kawo, da kayan zak’i.
Allah ya sanya alkhairi, ya baku zaman lafiya.”

Murmushi Yashjub yayi kafin yace”kun dage dai Aisha, har da wannan wahalar itama?. Wannan fa duk bidi’a ne”
Sai kuma ya ce “An gode!
Haka ake cewa ko?”
Ya yi musu tambayar yana kallonsu.
Chapter 55 · 0% Book details