Sashe 34
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A b’angaren Siyama kuwa ba wai jan aji bane kawai ita bata so ta zak’e da shi dayawa ne,
har ga Allah ba ta so ta saki jiki dashi gudun kar ta je ta fara sonshi
A samu matsala.
Suna tafe kuwa Ya’isha ta kira shi, sarai ta lura da yadda ya yi da farko kamar irin baya so ya amsa a gabanta d’in nan.
Sai da Ya’ishan ta sake kira tukunna ya d’auka ko tsayawa jin me zata ce bai yi ba ya ce ”ina driving, zan kiraki”
Ba ta ji me akace daga d’ayan b’angaren ba sai ji ta yi shi ya ce ”Nndc quarters! Da sunan layi da number gida…..”
Yana gama fad’in haka yayi sauri ya kashe.
Ba ta san wacece ta kirasa ba amman tabbas ta sake yin dana sanin basa numberta da ta yi. Ba ta yi mamakin yadda ya ci gaba da flirting yana mata hira ba dan ta riga ta san halin maza, shiyasa kawai ta dinga binsa da “um,um um…”
A haka suka tsaya suka d’auki
gado da ragowar kayan kitchen aka had’a su da manyan motocin d’aukar kaya da masu kafi
suka wuce.
Sun d’anyi tafiya mai nisa kafin suka k’arasa gidan Yashjub
dake a unguwar sharad’a nndc quarters..dank’areren gida mai hawa biyu!
Tun daga waje suka fara kallon aljannar duniya,tun kafin a shiga ciki kuwa suka fara ganin ikon Allah dan gate d’in gidan ma……
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 17*
Da remote aka bud’e musu.
Gaba d’aya motocin harda na kaya ciki suka shige dan atleast compound d’in gidan zai ci motoci sama da bakwai ma.
Sai da suka gama shiga tukunna gate man d’in ya rufe musu daga nan inda yake sannan ya ajjiye abun ban ruwan da yake yi wa flowers, ya tunkarosu
dan tuni daman ya san da zuwan nasu…
Basu kai ga fara fitowa ba suka ga ya koma da sauri ya d’an lek’a tukunna ya d’anna wani abu a jikin gate d’in ya bud’u.
A tunanin su ma Yash ne, shiyasa basu juya dubawa ba.
Aisha ce kawai ta fito dan
Yassir yana ganin Jidda tana shirin fita ya ce mata”please wait”.
Ganin masu kaya sun fara k’ok’arin sauk’ewa sannan
motoci har uku sun shigo
ne ya sanya Najeeb ya ce ‘bara suma su fita,’
sam bai lura
da motocin da kalar su ba, kawai shi dai ya san an shigo.
Bai bud’e side d’in Siyama ba….kamar d’azu yanzu ma sai da ya zagayo sannan ya bud’e mata da kansa.
Cikin rashin jin dad’i dan ita
har ga Allah bata so ta ce ”ka daina, ba na jin dad’i”
Murfin motar ya rik’e yana kallonta kafin ya ce ”dan ma ban nemo red carpet na shimfid’a miki daga nan har bakin k’ofar entrance d’in ba?!…”
Ya fad’i hakan yana kallon ta yana murmushi, a ransa
yana mamakin yadda ya koma…dan gaba d’aya ya nemi
jan aji!muzurai!da duk wani class d’insa ya rasa.”
Ba ta sake tanka shi ba, sai
matan da suka fara fitowa daga motocin ta d’an kalla…ta gane Yasmeen dan sun had’u a asibiti shiyasa tashi d’aya ta fahimci dangin Yash ne.
Ganin inda take kallo ne yasanya Najeeb d’in shima ya d’an juya….
…Ya san dama ko ba yau ba dole za ta ta sani, amman dukda haka sai da ya d’an ji wani iri, kuma yana juyawa da Ya’ishar suka fara had’a ido….
D’auke Kai ya yi, ya juyo ya kalli Siyama ya ce “Bismillah”
ya yi maganar fuskarsa
ba yabo ba fallasa.
Fitowa ta yi, shi kuma ya maida k’ofar ya rufe mata.
Zuwa wannan lokacin Siyama ta fahimci wani abun tsakanin sa da Ya’isha sakamokon kalar kallon da ta ga Ya’ishan tana ta yi mata har ana yi mata magana ma bata sani ba.
Sai da Yassira ta ce mata “keee!”da d’an k’arfi, tukunna Ya’isha ta samu ta d’auke dubanta daga kan su sir Najeeb idanunta suna masu
ciccikowa da hawaye.
Da sauri Yasmeen ta matso ta tsaya a gabanta ta d’an kareta daga Najeeb d’in tukunna ta ce ”ba ce miki mukayi karma ki kallesu ba?amma kalli yadda kike..….”
Shiruu Yasmeen d’in ta yi sakamokon hawayen da ta gani taff a idanun Ya’ishan suna shirin zubawa…ta san in har tace wani abun ko kuma tace za ta rarrasheta to fa hawayen nan da suka cika suka yi mak’il sai sun fito duba da yadda idanunta suka cika taff sannan sukayi jaaa!hatta farar fuskarta ta yi jaa itama…
Hakan ya sa Yasmeen d’in ta yi shiru, kafin kuma kawai ta jaa hannunta da sauri suka nufi k’ofar parlourn.
Suna zuwa suka tura k’ofar……
Allah ya so su akwai masu goge goge a ciki so k’ofar already a bud’e take. Ba ta
tsaya da ita a parlourn, ko sama ba dan hanyar saman shima akwai masu guga har biyu haka ma cikin parlourn, kuma ta san kafin su Isa kukan zai iya kufcewa Ya’isha shiyasa ta nufi d’akin da ta gani anan k’asan da ita.
Suna shiga suka rufo k’ofar tukunna Yasmeen ta cika mata Hannu….ko magana Yasmeen ba ta yi ba Ya’isha ta fashe da kuka, da sauri Yasmeen ta toshe mata Baki, tana yi tana
dan kallon k’ofa cikin yin k’asa da murya tace”so kike a jiyo ki?
wanne Irin rashin lissafi ne wannan?
ce miki akayi wani abun ne a tsakanin su? ki tsaya ki tabbatr mana!.”
Ingije Hannun Yasmeen Ya’isha ta yi kafin ta ce ”Haba Yasmeen! Yanzu ke ba ki fahimci komai ba? ba ki ga yadda yake murmushi yana kallon ta ba?
da kansshi fa ya bud’e mata mota ta fito kuma ya mayar ya rufe, abunda bai tab’a gigin yi mini ba kenan.
Sannan ki duba ki ga ya ganni fa mun had’a ido da shi amman bai zo inda nake ba, ko sake kallon inda nake ma fa bai yi ba…..”
Kukan da ya taho mata ne ya sa ta kasa ci gaba da magana dan haka ta yi shiru da magaar ta ci gaba da kukanta.
Cikin d’an fad’a fad’a
Yasmeen tace “Yanzu kuka za ki tsaya kinayi ko tunani mai kyau??kalle ki yadda kika koma a cikin y’an sakannni
saboda shi!!
wanda hakan yana nuni ne da tsananin son da kike yi masa, dan haka sai ki tashi ki nemi mafita tun kafin dare yai miki, ba wai ki tsaya kina kuka ba.
Sannan kar ki bari su ga kukan ki! ballantana su rainaki.
Tun farko kuma ai ke kika yi wasa da damarki, abunda naketa gayawa Yadira akan Junior kenan amman sam ta k’i fahimtata..
Haka kuke! Sai kun shure abu da k’afa kuma sai ku dawo kuna rarumowa da Hannu.!
Kuma Ya’isha har yanzu fa ba kya lallab’a Najeeb ba kya yi masa yadda ya kamata…a yanzu duba da yadda Najeeb ya yi kud’i haka sosai dole fa sai da tarairaiya kwantar da kai lallami da rarrashi, dole sai kin bi ta koina kin mamaye kin rik’esa da kyau! kin ajjiye kishi da girmankai a gefe dan wallahi one mistake (kuskure ɗaya) idan kikayi to tashi d’aya zai cika wandonsa da iska sai dai labarin wani ba shi ba. A da ma ya aka k’are y’an mata sun yi masa chaaa! ballantana yanzu.”
Cikin kuka kamar za ta shid’e Ya’ishan ta ce ”Yasmeen shekaran jiya fa da kuka ce idan ya zo in je in basa hak’uri wallahi da na je har k’asa na durk’usa na bashi hak’urin!
Shin, Har ya ya kamata in lallaɓa shi bayaga hakan? Wacce kalar biyayya da kwantar da kai ne a sama da hakan???
How much more good can i possibly be?”
Ya’isha ta yi mata tambayar tana kuka sosai.”
Tausayinta ne ya rufe Yasmeen,
shiyasa ta ma kasa ci gaba da magana, ahankali ta sa Hannu ta rungomota…ita kanta ta jijjiga da lamarin, babu abunda ya fi d’aga mata hankali kamar yarinyar.
Itama Ya’ishan haka dan dukda ta san tana da kyau amman fa ta san ba ta Isa ta tsaya ta ce za ta kara da Yarinyar da ta gani yanzu a fannin kyau ba.
(Ba za a kira Siyama doguwa chan ba sannan ba gajeriya ba ce, tanada haske sosai itama
sai dai yanayin hasken ta ba kalar na Jidda bane dan ita ba fara bace fat! Ta fi kama da kalar ruwa biyu, waenda su ka yi haɗin nasu da turawa.
Kamar yadda fuskarta take round haka idanuwanta suke suma, ba manya chan bane ba kuma ba k’anana ba y’an madaidaita sannan farare k’al waenda sukayi daidai da yanayin tsarin fuskarta mai ɗauke da cikar gashin gira
Pointed nose, da ƴan madaidaitan lips ɗinta masu tudu waenda suka haɗa ɗan ƙaramin Bakinta.
Bata da jiki sosai amman kamar su Jidda itama tanada structure (ƙira) mai kyau tubarkallah………)
…..
Su Ya’isha suna wucewa,
Jidda ta fito daga motar Yassir ranta a b’ace.
Inda Aisha take ta k’arasa ta tsaya, bayan ta karb’i d’ayan flask d’in da aka mik’o mata daga motar kayan, dama flask biyu ne kawai a cikin kayan sai
robar turare.
Dan haka Aisha ta d’au k’aramin flask da robar ita kuma Jidda ta d’auki babban mai d’an girma.
Ganin su Yassira ma duk sun fito ne yasa Aisha ta ce ”inaga dangin angon ne, dan ga wata mai kama da Yashjub d’in, ku taho mu je a gaisa sai mu wuce ciki gaba d’aya a tare.”
Dai-dai nan Siyama wadda ta samu ta zillewa sir Najeeb da kyar ta k’araso wajen. Tana shirin yin magana ta ji shi a bayanta ashe tare suke tafe ita bama ta sani sani ba, cikin nutsuwa ta ji yana cewa Aisha “ga sisters d’in Yash da aunty d’insu, mu je ku gaisa dasu”
“Ok”Aisha ta ce daga haka ya wuce gaba suka bi sa a baya.
Kamar Siyama za ta tambayi Jidda mai ya b’ata mata rai har haka sai kuma kawai ta kyaleta tana mamakin abunda ya sake fusatata daga shigowarsu cikin gidan.