Sashe 57
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin son sake kwantar mata da hankali ya d’ago da fuskarta yana mai kallon kwayar idanunta yace “Mannubiya ce kad’ai a cikin zuciyar Yashjub! Ba ki san yadda kika tare gaba da baya ba shiyasa kike wannan tunanin, amma inda ace kinsan yadda kikayi bake bake a cikin zuciyata to da ko ni da kaina idan nace miki zan k’ara aure ko zan kula wata na san ba za ki tab’a yarda ba…
I love you, only you, no one else!..
So idan ma akwai wani tunanin zan auri wata ko zan kula wata daban a ranki gara ma tun wuri ki cire
saboda wahalar min da zuciyarki kawai kike yi,
Iyaka abunda na sani shine ‘ke kaɗai ce tawa’
kuma na san su Daddy ba za su tab’a yi min auren dole ba.
Dan haka..pls Baby! ki daina b’ata ranki…um?!..”
Ya k’arashe maganar tasa cikin sa hannu ya janyo ta jikinsa sosai, kafin ya d’aura da cewa “ko amarci na ma ban fara ci ba har Amarya ta fara shiga damuwa ta fara fushi da ni, Pls ki daina, Plssssss”
ya fad’i hakan kamar zai fashe da kuka yana sake sakata a jikinsa.
Shiruu Manubiya ta yi, a ranta tace
“au bai ma fara cin amarcinba a hakan…”
Tana wannan tunanin ta ji yanayin nasa yana shirin sauyawa dan haka ta d’an yi y’ar dabara ta goce dakyar tukunna tace”Ya wuce fa!
Ni ba fushi na yi ba, kuma na daina kukan ai”
Cikin sake ruk’ota yana dariya dan ya fahimci zillewa ta ke son yi yace “ba wani nan!fushi kikayi mana bayan k’iri-k’iri d’azu aka yi denying d’ina kiss, yanzu kuma hug anjima kuma Allah kad’ai ya san mai za a hanani…”
Daga haka ya janyota ya fara aika mata da sak’onninsa ma su zafi da tsada……
Addua ta fara yi ‘Allah ya kawo mata ceto’ dan a yadda ta ji ya fara sakin layikan nan ta san k’aniyarta za ta ci.
Allah kuwa ya amsa adduar tata dan tashi d’aya wayarsa ta fara k’ara…sai da aka kira har sau biyu bai kula ba, jin kiran ya ƙi k’arewa ne ya sa yace”Ohh God!”
kafin dakyar ya samu ya sa hannu ya zaro wayar daga aljihu da niyyar kasheta gaba ɗaya amman sai idanuwansa suka hango masa sunan Mommy b’aro-b’aro…shi fa sai yanzu ma ya tuna da neman nasu da takeyi, wallahi shaf ya manta…sai da ta tsinke ta sake kira tukunna dakyar cikin k’ok’arin daidaita muryarsa ya d’auka ya ce”Mommy ga mu nan zuwa”
daga haka ya kashe wayar ya kalli Manu ya ce ”Bamu je ba, gashi Mommy har ta fara neman mu.
kece kika k’i ki warke da wuri shiyasa mukayi letti”
ya fad’i hakan yana dariya k’asa k’asa yana mai sake kissing d’inta tukunna ya mik’e da kyar….
Yasan idan suka zauna a d’aki d’aya suka ce za su shirya to ba za su yi sauri ba, gashi ya d’an jiyo fushi a muryar Mommy,
hakan ya sanya ya ce mata”ta shirya da wuri, bari shima ya je ya shirya”
Daga nan ya koma ya sake kissing nata kafin ya fice da sauri dan ji yakeyi kamar akwai wani magnet d’in da yake jansa zuwa gareta.
Yana fita ta sauk’e ajiyar zuciya, had’i da ta’a’uzi dan tashi d’aya ta ji wani tsananin kishi ya lullub’e ta sakamokon tunowa da ta yi ‘zata had’u da Kausar idan ta je gidan.’
..
Cikin nutsuwa tana ta korar shed’an a hankali ta shiga shiryawa…wanka ta fara yi tukunna ta fara d’auko kayan da za ta saka.
A ganinta gidan surukai za ta je, shiyasa ta yanke shawarar saka kayan da suka yi mata a cikin lefe dan ta san in suka ga ta saka za su ji dad’i kwarai.
Wata dandatsetsiyar atamfar exclusive ta saka, kalar royal blue da ratsi ratsin silver da red, an zuba mata d’inkin riga da skirt na zamani waenda sukayi asalin amsarta…ita kanta ta san d’inkin ya fito da ita ras , matsalar ta d’aya yadda d’inkin ya matseta gashi kusan rabin k’irjinta duk a waje, sannan skirt d’inma ya kamata, ga waist d’in ya fito sosai shima…d’inkin ya fito da surar jikinta gaba d’aya.
dama tun jiya da ta zo zab’ar kaya ta lura da yanayin d’unkunan..gaba d’aya sun yi fitting dayawa, dan haka ta yanke akan gaskiya idan ta samu lokaci zata ce su mayar musu a dan bud’a mata dan ba zai yiu a kashe uban kud’i ba kuma a yi mata d’inkunan da ranta bai so ba….
Dama tanada abun d’auri na ture kaga tsiya, dan haka ta d’auko ta saka a cikin dankwalin nata ta ajjiye, kafin ta koma gaban madubin ta d’auka powder ta shafa ta saka eye liner ta d’auko lipstick ta shafawa labb’anta.
Ita kanta ta san tayi kyau, irin sosai d’innan..murmushi ne ya sub’uce mata ta san Ya Yash yana shigowa zai hau mita yace ‘mugunta ta had’a masa, saboda ta san ba zama za su yi a gidan ba shiyasa ta chab’a wannan uwar kwalliyar.’
A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya tana jin tsantsar k’aunar mijin nata tana sake shiga jikinta tana ratsa ko’ina.
Tana tunanin shi tana murmushi a haka ta shiga tufke gashin kanta a ta baya chan k’asa ta kanainaye sa ta saka d’an siririn ribbom black gudun kar ya sunce, daga nan ta d’auko dannkwalin da ta saka abun daurin a cikin ta d’aura sa perfectly.
Saida ta san yadda ta yi ta b’oye uban tulin gashin nata da ya fito ta k’asan d’aurin, tukunna ta tafi closet ta bud’e wardrobe ta zaro mayafi, jaka da takalmi, kafin ta d’auko iyaka y’an kunne zobe da agogo kawai dan ba ta cika son sark’a da awarwaraye ba.Y’an kunnenta,zobe agogo da Mayafinta silver yayinda jaka da takalminta suka kasance red colour.
Tana shirin yafa mayafi ya turo k’ofar ya shigo..dama k’ofar take facing dan a kan gadon nata ta jere jaka da mayafin nata.
Saida numfashin Yashjub yayi sama ya dawo bai san lokacin da a fili yace”MashaaAllah,Ubangiji mai halitta.”ba.
Kamar had’in baki shima sanye yake da kaftan blue nasa da farar hula da farin takalmin da agogo,wanda hakan ya yi kamar anko sukayi.
Ahankali ya taka ya shigo cikin d’akin idanunsa a kanta.
Gaba da’ya Manubiya sai ta diririce sakamokon kallon da ta ga yana yi mata…so take ta ware mayafin ma ta rufa amman sai ta kasa.
Murmushi yayi kafin ya maida k’ofar ya rufe ahankali ya k’arasa inda take, still idanunsa suna a kanta.
Saida ya gama k’are mata kallo tukunna ya sa hannu ya karb’i mayafin sannan ya zagaya ta bayanta ya tsaya tukunna ya ware mayafin gaba d’aya ya rufa mata shi a saman kanta, gefe da gefen kuma ya zagaya dashi ya rufe mata gaba d’aya jikinta dashi wanda hakan ya basa damar yin hugging d’in ta!
A tare shi da ita suka sauk’e ajiyar zuciya kamar ta saani dama aikuwa ta ji yace
“Wannan dai tsokanata akayi, amman kar ki damu, zan fanshe idan muka dawo”.
Daga haka ya manna mata wani dogon peck a kumatunta, kafin yayi saurin cikata dakyar, yana mai sauk’e ajiyar zuciya.
Jakarta ya d’auka, daganan ya ruk’o hannunta suka fita tare gwanin ban sha’awa.
Wani Irin shauk’i da so ne suke jan Yashjub game da ita, ji yakeyi kamar ya had’iye ta ya kora da ruwa ko ya samu sauk’in abunda yake ji.
Gaba d’aya robobin kayan zak’in garar Manubiya tace su tafi da shi a su Mommy, ita za ta raba har su sai ta basu nasu haka akeyi.
Sai da ya bud’e mata mota ya sakata a ciki tukunna ya kira masu gadi suka kwasa suka sanya a boot da seat d’in baya sannan ya shiga motar ya ajjiye Jakarta da yake rik’e da ita, ya zauna tukunna ya kunna mai gadi ya bud’e musu suka fice.
Har suka k’arasa gidan Daddy yana rik’e da hannunta..da hannu d’aya yayi tuk’in sai dai in zai chanja gear ne ya ke d’an cikata yana chanjawa kuwa ya ke sake ruk’ota kamar wani zai kwace masa ita ne.
Haka kurum suna zuwa bakin gate d’in gidan da taga ya danna horn ta ji gabanta ya yanke ya fad’i sosai..da kuma ta tuna su Yassira da Kausar sai ta ji ranta ya b’aci…..salati ta shiga yi a cikin zuciyarta, da ikon Allah sai ta ji fad’uwar gaban da b’acin ran suna raguwa.
Tunda suka shigo gidan ta shiga alajabi da mamakin tsantsar girman gidan, ita
tana ganin gidanta Babba ashe ga mansion anan!
MashaaAllah masu kud’i suna hutawa..tashi d’aya ta fara addu’ar ‘Allah itama ya bata ikon fara aiki, ya bata kud’i, ta samu ta siyawa su Baba gida ko d’an flat ne suma su ji dad’in rayuwa.’
A parking space sukayi parking, kafin ya kashe motar ya d’auki jakarta ya fita da niyyar zagayawa ya bud’e mata…
da sauri ta juya ta bud’e ta fito da kanta kafin ma ya zagayo.
B’ata rai ya yi sosai kafin
yace”Why?!”
Murmushi kawai ta yi tace “yi hkr”….
Da kyar ya d’an saki fuska ganin ta masa kalar tausayi tukunna suka wuce suka nufi main parlour.
A bakin k’ofar shiga suka ci karo da Yassir wanda ya zo shiga shima..bai dad’e da dawowa daga office bama jakarsa kawai ya ajjiye a side d’insa ya zo da niyyar ganin Kausar dan kwana biyu karantarta kawai yake yi…ya fi
minti d’aya tunda ya hangosu har suka k’araso suka tsaya yana k’are musu kallo yanajin yadda zuciyarsa take wani irin tafarfasa!
A ransa yana aiyyana”how can Yashjub be this lucky….ta ya
zai fi sa sa’a ata ko wanne b’angare ata ko wanne fanni
na rayuwa!….”
Da mamaki Yashjub yake kallosa yana la’akari da yadda idanuwansa suke sauya kala dan lokaci guda yaga sun fara rinewa suna chanzaa kala zuwa jajajaja…
Babban abunda ya b’ata masa rai game da Yassir d’in shine yadda ya kafe Manubiya da idanuwa ko kiftawa ba ya yi.