← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 152

Sashe 43

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan karon murmushi ya ga ta d’an yi…tabbas idan ba ta yi da gaske ba to mutumin nan ba barinta zai yi ba gashi kuma akwai wani abun game da shi wanda ta san idan har ba ta yak’i ta kuma fatattaki tunaninsa da shi kansa daga rayuwarta ba
tou tabbas akwai matsala…tana tsoron kar ta je ta jangwalowa kanta abunda ba za ta iya ba, dan haka ta d’ago ta kallesa kafin tace”Bana kishinka! Kamar yadda na faɗa make ban ma sanka ba ballantana har in shak’u da kai
wanda shak’uwar ce za ta janyo abunda zai sanya in yi kishin naka, kawai dalilin da ya sanya ka ga Ina guje maka yanzun shine har ga Allah...ka yi haƙuri da zan gaya maka hakan ƙiri ƙiri...amma sam ba na shiri da Abota, ni ko kirki ma ba na yarda in yi da Namiji irinka.”

Shiruu ya d’an yi kafin yace “Namiji irina?,menene ni d’in??”.

Itan ma sai da ta d’an yi shiru tukunna tace”Masu two timing! (Soyayya da mutum biyu a lokaci ɗaya), waenda a fuskar duniya ake yi musu kallon mayaudara!”.

Kamar zai fashe da kuka yace
“Siyama ni ba mayaudari bane ba, can you pls allow me to explain myself(dan Allah ki bani dama in yi miki bayani mana)”.

Cikin katse shi kanta tsaye tace
“A yadda ka karb’i numberna, da kuma yadda kake treating d’ina yau tun safe har daren nan, da ni da kai duk mun san inda zancenka zai sauk’a, bayan kuma ka riga ka san kana da wadda za ka aura, wadda kake so itama take sonka.
Menene hakan kake shirin yi mini idan ba yaudara ba?

Ko mata biyu za ka aura a lokaci daya?
besides na san ma itan za ka aura tunda itace dai dai da kai, ni kawai a side kake da shirin ajjiyeni ka b’ata mini lokaci”

Da sauri ya ce “idan za a bani zab’i ke zan zab’a, ke kad’ai!”

Da sauri ta d’aga masa hannu tace “Plss…dan Allah, banaso in ci gaba da gaya maka maganganu masu zafi
saboda dukda abunda ka yi
min still Ina ganin girmanka sosai….
Na cire kunya na cire komai na gaya maka abunda yake raina da abunda na fahimta a kanka
Wanda na tabbata hakan shine gaskiyar lamarin, dan haka
dan Allah inaso ka fita hanya ta kwata-kwata.
Bana son case da su Ya’isha,
ba wai tsoron ta nakeji ba amman duk inda na kai ga iya fad’a ba zan had’a kaina fad’a da Mutanen da basusan darajar d’an Adam daidai da kwayar zarra ba.
Dan haka dan Allah
For the last time…
Ka fita a hanya ta,
sannan ka bud’e min k’ofa in fita.”

Shiruu kawai ya yi ya tsura mata ido…bai ma san me zai ce ba!
Dan bai san ta Ina zai fara fita a hanyar tata ba, shi da yake son shiga cikin rayuwarta amma gashi tashi d’aya ita kuma ta ce masa ya fita a hanyarta ma gaba d’aya!! Wanda hakan shine abu na ƙarshe da zai iya yi arayuwarsa, dan shi kansa ya san ba zai iya rabuwa da ita ba, ya tabbatar da hakan…
Ba ta san yadda ya dinga fama da soyayyar ta sama da wata uku ba ne shiyasa har ta ke iya gaya masa hakan…

Ba zai iya yi mata ma alk’awarin fita a hanyarta ko rabuwa da ita ba dan ya san ko ya yi alk’awarin to ba za ya cika ba.

Ahankali cikin son ta fahimce sa yace “Siyama ba zan iya rabuwa da ke ba, ki yi hak’uri ki fahimce ni ki bani dama, ba zan tab’a yaudararki ko in cutar da ke ta ko wacce hanya ba, na yi alƙawari!”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “me ye tsakanin ka da ita,
Ya’isha? Ka gaya min gaskiya kawai!
dan Allah”

Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya ce
“She s my girlfriend(budurwata ce)”.

Yadda kalmar
‘She’s my girlfriend’
ta daki k’irjinta
Ita kanta sai da ta yi mamaki.
Da kyar ta iya cewa “kuma har yanzu kuna tare ko?”

Still sai da ya d’an runtse idanunsa na y’an sakanni
tukunna ya bud’e yace
“Eh! Amma Siyama wallahi ke
nakeso, kuma ba wai haɗa ku biyun nake shirin yi ba, very soon ita ɗin zan yi mata bayani ta yadda za ta fahimce ni cikin sauk’i, zan rabu da ita InshaaAllah…
Ni da ke
haɗi ne daga Allah, ki d’an ba ni lokaci, zan yi mata bayanin komai….”

Da mamaki Siyama ta tsaya kawai tana kallonsa kafin da kyar tace
“Ka na ji da fahimtar abunda ka ke faɗa min kuwa?”
Bata jira ta ji abunda zai ce ba ta d’aura da cewa”za ka rabu da ita saboda ni??”

Da sauri yace”Yeah” sai kuma ya sake cewa”tun ba yau ba Ina…”
Girgiza kai kawai ta yi cikin katse sa tace”pls………”sai kuma ta runtse idanunta kafin ta kama handle d’in k’ofar tace “zan fita!”

Da sauri yace “You ask for the truth(ke kika nemi jin gaskiya) shiyas…”

Bud’e idanunta ta yi kamar zata fashe da kuka tace
“Ka bud’e min k’ofa in fita! Wai ta ya kake tunanin zan iya yarda da kai..in yi trusting d’inka?
ka bar wata saboda ni!
Ka ga kenan in ka had’u da wata a gaba nima ka rabu da ni saboda ita ban Isa in ce zan ji haushi ba!”

“Ba haka bane, abun namu akwai sarƙaƙiya a cikinsa ne, its complicated, ki fahimceni dan Allah”

Cikin takaici ta kallesa sosai tace
“Ta yaya ya ke da Sarƙaƙiyar??
Complicated how?”

Tashi d’aya zuwa yanzu Najeeb ya fahimci ya riga da ya jagula komai da hannunsa, ga shi ya lura Siyaman ta zuciya sosai dan idanunta da kan hancinta sun d’an yi jaa! shiyasa kawai ahankali ya sa hannu a gefen seat d’inshi ya bud’e mata motar, yana shirin
ce mata ‘ya bud’e’ kawai
ya ga ta bud’e ta fice da sauri dan yana dannawa ta gane ya bud’e ne.
A ranta tace “baka da abun fad’a ai dole ka bud’e min.
Mayaudari kawai…….”

Juyawa kawai ya yi ya jingina a jikin kujerar da yake zaune a kai ya yi shiruuu….idan akwai abu ɗaya wanda ya ke da tabbaci akai to shine ‘ba zai tab’a iya hak’ura da Siyama ba’
Ko menene zai faru sai dai ya faru amman Siyama tashi ce da izinin Allah. Kawai dai kamar yadda ta fad’a anya ba zai zalinci Ya’isha ba idan ya yi hakan? Ga shi shi harga Allah
ba zai tab’a iya auren mata biyu ba, tsarinsa na mace d’aya ne tun farko, bayaga haka a yadda yakejin soyayya da k’aunar Siyama 95% da kuma yadda yakejin na Ya’isha da bai wuce 5% ba ya san idan ya had’asu su biyu a matsayin matansa to tabbas akwai matsala dan ya san ba zai tab’a kwatanta adalci ba.
Ko a lokacin da yake tare da Ya’isha shi dai ya san yana sonta amman bai san zafin so
da asalin mene shi so d’in ba ma
sai a kan Siyama…..

Kaff y’an kawo amarya babu wanda bai shiga shock ba! Dan tun daga gate da compound suka fara ganin ikon Allah….an san dama Mijin yana da kud’i duba da yanayin kud’in
da aka bayar lokacin da aka zo saka rana da kuma lefe
amman sam ba su yi tunanin ya kai har ba, dan a kaff cikin su 5% ne kawai suka tab’a sanin akwai Irin gine ginen nan ma a Nigeria, ga furnitures kamar ba za a mutu ba!Tabbas Manubiya ta dandalo arzik’in,
dan a kaff area d’insu babu y’ar da ta tab’a dandalo kalarsa….Ah lalle kam dole dangin miji su ce ta durk’usa uwarta kuma ta amince, yo idan sune ko kwanciya akace y’arsu ta yi ai sai ta yi wallahi, Irin wannan aljannar duniya haka gida kamar ba a Africa ba…..
Haka nan dai suka dinga mamaki da zancen zuci
waenda kuma ba za su iya dannewa ba suka koma gefe aka shiga tattaunawa……..

Tun case d’in Baraka da Ya Musbah su Maman Abbakar ba kula su Manubiya sukeyi ba
sai yau!
Yadda Maman Baraka ta ga Manubiya ta samu duniya ne ya sa hankalinta ya sake tashi ta kuma bada goyon baya akan y’arta ta koma gidan Ya Musbah dan ko banza yanzu kam Musbahu ba shi da nauyi a kansa dan ta san duk Manubiya za ta d’ebe komai, wataƙila suma su samu su dandala……

Ba a fara barin gidan Manubiya ba sai wajajen 11
na dare…shima kuma sai da
Yash ya kira Najeeb yace
“Idan bai zo sun fara kwasar jama’a suna maidawa gida ba to wallahi zai shiga gidan da kansa ya ce musu ‘dare yayi”’

Najeeb ya san tsaff Yash ɗin zai iya aikata hakan, shiyasa ya mik’e ya dauk’i makullin motarsa ya fice,
gaba d’aya gab’ob’in jikinsa na masa ciwo, ga tension da tunanin ta Ina zai fara da Siyama da Ya’isha dan gaba d’aya kansa ya d’aure….
….
Zuwa yanzu gidan ba kowa daga Manubiya, Jidda, Yahanasu sai Aisha, Siyama da Munirat….Su Najeeb sun tafi kai wasu a cikin Mutanen su dawo.
A tunanin su su ne za su d’auki su Siyama ma su maida su gida, nan kuwa ba su san tuni su Siyaman
sun cewa su ya Nafi’u idan sun gama za su yi musu magana, ba.

Suna zaune gaba d’ayansu
sukaji kamar an shigo parlourn bedroom d’inta, dan haka da sauri Yahanasu ta lek’a..
dariya ta yi kafin ta ce ”Au Yassir!Asahe kai ne, ai na yi tunani angon ne”

Bai damu da yadda ta tsaya ta tare k’ofar d’akin ba, haka ya kutsa ya fara k’ok’arin shigewa, ganin kamar zai shige jikinta ne yasa ta d’an matsa tana cewa ”babu kyau fa shiga d’akin Amarya”.
Chapter 43 · 0% Book details