Sashe 54
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin takaici yace
“Yassira gidanta fa kuka zo!
A gaban ta kuka gaida ni,
a matsayinta na matata ya kamata ace kun gaida ita ko da kuwa kun girmeta, idan ma kuma kuna ganin kun girmeta ɗin ai ko ‘Hi’ da ‘ya gida’ ya kamata ace kun ce mata.
Na ga take taken ku na lura fitina kuke nema da ita wanda ban san ribar ku a kan hakan ba, sarai na san abunda kukayi a gidansu, Daddy ne ya ja min burki shiyasa na d’aga muku k’afa ba dan haka ba Wallahi da sai kun gane kuranku!
Na yi masa alk’awarin ba zan yi muku komai ba akan wanchan abunda kuka yi ɗin amma hakan ba wai yana nufin zan zuba ido ku taka min Mata ba, dan haka be warned!…kin riga kin san wat i’m capable of ( me na kan iya aitawa,) but for now! (amma yanzun dai) kar ki bari in sauk’o in same ku a cikin gidan nan.”
Yana gama fad’in haka ya wuce ya barta anan a tsaye zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Ta so ta shiga d’akin Manubiya wanda yake a nan saman ta samu ko da ɗan style ne yadda dai
ba za a gane me ta yi a camera ba, ta ɗan zuba abunda Baba larai ta bata ta ce ‘ta zuba’, amman sai akayi rashin sa a ko taku biyu ba ta iya ta yi ba Manubiya ta hawo saman,
dan Yashjub yana tashi su Ya’isha suka fara yada mata da maganganu marasa dad’i! Saboda dama a wuya suke da ita! Ji sukeyi kamar su rufeta da duka.
Tana d’aga kanta, dayake dama ana iya hango parlourn saman daga nan k’asan ta ga Yashjub ya wuce ya sake hawa bene ya nufi d’akinsa Itakuma Yassira tana tsaye a nan parlourn, shiyasa ta mik’e da sauri ta wuce su ta nufi saman ba tare da ta ce musu uffan ko ta tsaya ɗaukar mayafinta ba ma, tsabar sauri.
Takaici da bak’in ciki da rashin jin dad’i duk sun kanainayeta a lokaci guda, zuwa yanzu ta riga
ta gama sanin Allah ya had’ata da dangin mijin da ba su san darajar d’an Adam ba sam, kuma ba sa k’aunarta.
Ita ko a labari bata tab’a jin labarin jahilan dangin miijin Irin nata ba.
Tana wannan tunanin ta hayo sama idanunta taff da kwallah,
Yassira ta ji motsinta tun daga stairs shiyasa ta juyo…….ta na juyowa kuwa dai dai ta gama hayowa ita kuma dan haka su ka yi ido biyu!!
Da sauri Manubiya ta d’auke kanta, dan sam bataso Yassirar ta ga idanunta, shiyasa tashi d’aya ta kauce ta nufi d’akinta ba tare da ta nuna ta ma ga Yasirar a wajen ba…
dai dai ta zo wucewa kenan kawai Yasira ta sha gabanta ta ja ta tsaya, lumshe idanu kawai Manubiya ta yi kafin ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tana mai k’ok’arin rik’e kanta dan tabbas in ta d’ago a yanzu da wannan temper da take ji ta na taso mata to ba Yaseera ba ko wacece sai ta d’auke ta da mari.
Sun kusan second ashirin a haka kafin Manubiya ta kauce ta chanja hanya amma sai Yasira ta sake shan gabanta ta tare mata hanya…a hankali Manubiya ta d’an d’ago still tana mai k’ok’arin danne zuciyarta tace”Anya ba daga gidan mahaukata kuka gudo ba kuwa?”.
Murmushi mai had’e da dariya Yassira ta yi kafin tace “eh to! amma tare da tsohon da ya d’aura miki aure muka gudo!
Anyways
Dama idanunki kawai na ke so in gani, saboda ina so in ga gwargwadon ƙarfin jarumtarki, kuma na riga naa gani..dan yadda idanuwanki suka cicciko ɗinnan ya tabbatar mini da cewa ‘u are weak!’(‘ke mai rauni ce’)!! Hakan ya sanya a take a yanzu wallahi har kin bani tausayi, saboda bakiga komai ba! there is a lot coming your way(dan abubuwa masu yawa su na nan tafe zuwa gareki)…”
Sai kuma ta kalleta sama da
k’asa tukunna tace
“Da ni da y’an uwana ba ma yin ki!ba ma sonki, ba ma k’aunarki!
Kausar ita mukeso ta auri d’an uwanmu amma kika shiga kika fita, amma dukda haka kar ki yi zaton kin ci riba, dan wallahi idan sama da k’asa za su had’e sai Kausar ta auri Yashjub!!!.
Mark my words
(Ki rubuta ki ajjiye).”
Tana gama fad’in haka ta wuce fuuu cikin tsananin takaici da bak’in ciki….dukda maganganun da ta gayawa Manubiya sun d’an rage mata takaici, amma ji takeyi kamar ta mutu…wai ace yau itace ta zo gidan Yayanta a karo na farko amman ya koreta!!! Saboda ba ta gaida matarsa ba. Gashi ba ta zuba maganin da ta ci burin zubawan ba, kuma Yash yace su tafi! Sannan ta tabbatar ko da ace su Mommy sun shiga maganar an samu an sasanta ta zo gidan gobe to ko dai ya ƙi sake musu, ko kuma ma ya sake ce musu su tafi gaba d’aya!.
Ga kuma takaici da tsantsar tsanar Manubiya da ta ke ji tana ratsa ta…ta ya ma Yashjub zai kalle ta ya ce ta gaida wannan Yarinyar, saboda Allah idan shi ya zubar da kansa ya watsar da ajinsa ya aureta ya zubar da mutuncinsa, ai bai kamata ya yi tsammanin hakan daga garesu suma..bai kamata ya sa ran za su zubar da class ɗinsu a wajenta ba suma…
Duk lalacewa dole ita Manubiyan ce ya kamata ta gaida su after all ta auri Yayansu!!! an rufa mata asiri!! ta shigo cikin family dinsu y’ar talakawa da ita.!!
Amman ace ba ta san na gaba da ita ba!! Haba, -abun sam ba tsari….wato daman zaman da ta yi da kuma tare k’ofar da ta yi tun farkon zuwan nasu jira takeyi su gaishe ta kennan!!
shi
kuma Yash ya biye mata da ya ke bai san darajar su ba…saboda giyar amarci tana d’ibaar sa shine zai ci musu tuwo aka a gabanta ya wulakanta su saboda ita…..
Waennan tunane tunanen ne suka sa duk dauriyar Yassira ta kasa daurewa, dama har yau akwai takaicin dukan da Daddy yayi mata saboda su, shiysa ta na sauk’a k’asan da suka had’a ido da su Yasmeen kawai sai ta fara sakin hawaye…..
Gabad’ayansu kanta suka nufa suka shiga tambayar ta “mai ya faru?”
Dakyar ta iya controlling kanta tace musu “Ku d’auko handbags d’inku mu tafi”
K’asa k’asa da murya Yasmeen tayi kafin tace
“Kin zuba, har kin gama?”
Girgiza kai kawai ta yi kafin ta sake ce musu “ku taho mu tafi!”
Cikin rashin jin dad’i Yasmeen tace “Kamar ya mu tafi? Ba tare da mun yi abunda ya kawo mu ba?”
Ahankali Kausar wadda ta fi kowa nad’ar takaici ta d’an dafa Yasmeen d’in tukunna tace “mu je kawai, ma dawo wata rana”
Saida Yasmeen ta kalli Yassira tuukunna Yassirar tace mata “ku taho mu tafi kafin ya sak’k’o”
Cikin fushi Ya’isha tace
“Ba dai shi ya ce mu tafi ba??”
Bata rai Yassira ta yi kafin tace
“Shikenan! Ni dai kunga tafiya ta…idan ya sak’k’o ya same ku babu ruwana”
Ta fad’i hakan tana mai yin gaba ta nufi k’ofa.
Cikin tarar numfashinta Ya’isha ta ce”Ai kuwa yau sai dai ya kashe ni wallahi amma babu dalilin da zai sanya in fita a cikin gidan nan!aikin banza ku kuke jin tsoronsa…za a ga ikon Allah yau a cikin gidan nan!”
A hankali Yasmeen wadda itama jikinta yayi sanyi ta matsa ta shiga bawa Ya’isha baki.
Itakam Kausar juyawa kawai ta yi, ta bi bayan Yassira suka nufi k’ofa, dan tunda uwarta ta kawota duniya ba ‘a tab’a yi mata disgi irin wannan ba!
Yashjub bai aureta ba!
sannan tunda ta shigo ko kallonta baiyi ba!
kuma saboda ba ta gaida matarsa ba yace
su fitar masa daga gida.!…
Dakyar da mugun kyar Yasmeen ta lallab’a Ya’isha,
tukunna ta yarda za ta tafi.
Su Yassira suna bakin k’ofar dan a yadda sukaga Ya’isha ta burkice sun san idan har Yashjub ya sak’k’o ya tadda ita to fa ba za su k’are ta sauk’i ba.
Tana zuwa ta wucesu, ita ta bud’e k’ofar da k’arfi dan a wuya take,
tana bud’ewa suka yi ido biyu da Siyama wadda ta d’aga hannun ta da niyyar yin knocking…tun jiya take kiran Najeeb a waya amman ya’ki ya d’aga kuma bata da tantama saboda wannan shegiyar Yarinyar ne.
Hannun Siyaman wanda ta dunk’ule da niyyar yin knocking d’in Yaisha ta bi da kallo, tukunna ta kalli fuskarta tace “Er mallan Shehu bell ake dannawa ba kwankwasawa ake yi ba!”
Murmushi kawai Siyama tayi, kafin ta matsa gefe ta tsaya ta hard’e hannuwanta akan kirjinta, kawai.
Zuwa yanzu Ya’isha ta fara bawa Yassira haushi, dan ta ga alamun ta rantse sai ta janyo abunda ransu zai kuma b’aci!
dan haka ta yi gaba kawai ta fice ta barta a wajen, hakama su Yasmeen suka wuce aka barta daga ita sai Yadira.
Ya’isha so tayi ta hana su Siyama shiga, dan ba zai yiu ita ta gidan yayanta amma ace bata samu zama ba wasu kuma su zo su shige a gaban
idanunta!
amma kuma ganin da ta yi su Yasmeen duk sun watse sun barta ne ya sanya kawai sai itama ta watsawa Siyama tsaki ta wuce tana jin tsanar Yarinyar tana ratsata!ji takeyi kamqr ta koma ta yi mata illa.
A harabar gidan suka tarar da Aisha ita da su Ya Musbah da ya Nafi’u sunata faman sauk’e kayan gara daga motar ya Nafi’u da d’ayar y’ar k’urk’urar da suka zo da ita.
Takaicine ya sa tunda su Yassira suka yi musu kallo d’aya ba su yarda sun maimaita na biyu ba….tsabar tsiya kalli kayan garar da aka kawo gidan d’an uwansu kamar an rok’o!
A haka wai amma har wani so yake a gaida ita!
Inaa da sake wallahi…
dama sunsan ba za su barta ta rayu a cikin gidan ba, amman dukda haka dole ta gane kuranta ta san matsayinta kafin ta fita a gidan, dan ruwa ba sa’an kwando bane ba.
Dama tunda suka tunkarosu
Aisha tacewa su Ya Nafi’u ‘kar ma su kula su, kar su ce musu komai, basu da mutunci.’
Haka kuwa suka zo suka wuce bayan sun sake tamke fuska tamau kamar ba su tab’a dariya ba.