← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 152

Sashe 9

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘’Tam’’
Jidda ta ce, daganan suka juya suka nufi sofa ita da Siyama suka zauna.

Shi kuma ya zauna a gefen Yash kan gadon.

Manubiya ya sake kalla ya ce
‘’Amaryarmu ba za ki zauna ba ke??’’

Da sauri Yashjub ya juya ya na mishi wani irin kallo!
Dan haka Najeeb ɗin yayi dariya, kafin ya ce masa
‘’Sorry!’’
sai kuma ya kalli Manu ya ce ‘’Amaryar Yashjub shi kad’ai! Ki taimaka ki zauna’’

A hankali ta juya da niyyar zuwa inda su Jidda suke, amman sai
ya sa Ƙafa a daidai inda za ta bi ta wuce….
Dukda k’afar ba ta wani kafeta sosai ba amma ta fahimci sarai abunda yake nufi!
Zuwa yanzu ta riga ta san halin Yash, ta san ba k’aramin abu bane a wajensa yanzunnan sai ya ja mata ta ji kunya a gaban su Jidda muddin ta k’i yin abunda yake so,
shiyasa kawai sai ta nemi waje ta zauna a kujerar mai jinya,
tana mamakin shi a d’ayan b’angare na zuciyarta kuma
tana mamakin Sir Najeeb shima!
Mutumin da a da ko kallon kirki baya yi mata, daga ɓaɓɓata fuska sai ciccin magani kullum,
amman yanzu wai shine haka kamar zai goyata.

D’an zungurin Yash Sir Najeeb d’in ya yi ganin yadda yake ta kallon Manu,
ƙasa-k’asa yace masa’’kar ka
cinye ta da ido mana..’’

Dariya Yash d’in ya yi shima k’asa-k’asa, kafin kawai ya d’auke kansa daga kan Manubiya ya maida kan Najeeb ɗin sannan ya ce ’’wanne munafurcin Yasmeen ta shirga maka ɗazu?”

Shiruu Najeeb ya yi yana kallonshi, kafin ya mik’e tsaye sannan ya ce ‘’za mu yi magana da kai anjima”
sai kuma ya kalli Manu ya ce ’’bari in bawa bak’inmu ruwa’’…
…tun lokacin da su Siyama suka koma chan gefe suka zauna, yake ta so ta juyo ya sake kallonta amman ta ƙi!…
Suna zaune abunsu hankalinsu na ga wayar Siyaman……ya san hakan bai dace ba, bai kamata ba! Sannan ko a ta b’angaren sa shima sam two-timing (soyayya da Mata biyu a lokaci guda) baya a tsarinsa, daɗin-daɗawa kuma ga Yashjub a wajen, dan haka abun zai yi kamar cin fuska sannan ya san yana yin wani abun Yash d’in zai gano sa!!!
Shiyasa tun d’azu yake ta tausar kansa amman duk yadda ya so sam ya gagara hak’ura, a yanzu so yake ko ƙaƙa ya ɗan sake kallon Fuskarta….dan haka ya yanke shawarar kai musu ruwa….. bai damu ba dan ya zama waiter (hadiminsu), in dai har hakan zai bashi damar ya kalli fuskarta a karo na biyu.

Muryar Manubiya ce ta katseshi jin tana cewa ‘’Laa,a’a fa, yanzu ma za mu tafi, su Baba kawai muke jira’’

Da sauri Yash ya kalleta ya ce
‘’Nooo! Dan Allah ki kirasa ki ce ya zauna a gida, ba sai ya zo ba, ai na warke.’’
Sai kuma ya juya ya kalli Najeeb
ya ce ’’ka ga abunda ka janyo ko??’’

Murmushi Najeeb ya yi kafin yace ‘’Sorry’
tukunna ya kalli Manubiya ya ce ‘’ki kirasa ki ce ba sai ya zo ba’’.

Da sauri ta d’ago ta kalli Sir Najeeb d’in ta ce ’’Allah in ma nace kar ya zo fad’a zai yi min, ya riga ya gama shiryawa akan zai zo d’in.’’

Dafe Kai Najeeb ya yi, yad’an fesar da iska, kafin ya zaro waya ya ce ’’okay, bari ni
in gwada yi masa magana’’
Yana gama fad’in haka ya koma chan gefe kare da waya a kunne.

Shiruu suka yi kafin chan Yashjub ya ce ’’yanzu duk za ku saka ni jin kunya wallahi.
Allah yasa ya hak’ura da zuwan’’

Shiruu Manu ta yi kawai ta sunkuyar da kanta k’asa.

A take kuwa ya turo Baki, ya b’ata rai tukunna ya ce ’’yanzunnan a
gaban idona kika gama kallon ido da fuskar Najeeb, ni kuma kin wani sunkuyar da Kai k’asa’’.

Tana shirin yin magana
Sir Najeeb ya dawo ya ce
‘’ai suna bakin gate ma’’

‘’Innalillahi!
Najeeb ka kashe ni’’
Yash ya fad’a, kafin ya mik’e tsaye kawai ya na zabgawa Najeeb d’in wata uwar harara.

Bai dad’e da mik’ewan ba,
su Baba suka k’araso….
Shi da mai sunan baba da Ya Nafi’u da Ya Musbah da Muhsin waenda suka had’u da su a hanya…

Ba k’aramin dad’i Manubiya ta ji ba ganin yadda Yash ya gaida Baba cikin tsananin girmamawa.

Da kulawa Baba
ya amsa yana mai tambayarsa ‘ya jiki, daganan ya yi mishi jaje
da adduar Allah ya kare gaba
kafin ya masa gaisuwa.’

Daga haka, suka gaisa da su Musbah suma suka yi masa
kamar yadda Baba ya masa.

Yash ya dad’e bai had’u da Yaron da ya shiga ransa tashi d’aya kamar Muhsin ba.. ɗan
sukuti da shi so chubby, gashi fari tass kalar ajebo no 1
Dan sam babu wanda zai kalli Muhsin ya yi zaton ya taso a wahala. Yanayin round face d’in shi irin na Manubiya, ga
Yaron da ladabi dan sai da ya d’an durk’usa tukunna ya gaida shi..
tashi d’aya Yash ya fara addu’ar Allah yasa Manu ta Haifa masa irin wannan, wai!! Ranar bai san ya zai ji ba, zai iya bada komai nasa dan ya samu ya ga wannan rana……

Har kanshi Yash ya d’an shafa yana tsokanarshi da d’an auta,
aka yi dariya, mai sunan Baba shima yanata tsalle tsallen shi…
Sosai Yaran suka burge Yashjub kwarai, dan yana matuk’ar son Yara.

Manubiya ce ta bawa Baba kujera, ya zauna, ita kuma ta ja su Muhsin suka koma wajen su Jidda, su ya Musbah suka tsaya a tsaye.

Sun d’an jima suna alhini
kafin Baba ya sanar da Yashjub d’in ‘ai Daddy ma ya kirasa….
Daddyn ya ce yana so za su zo ayi tambaya da abubuwan al’ada,
sannan ya ce d’aurin auren nan da kwana goma za ayi inshaaAllah…in an gama daidaita komai.
Hallau Daddyn ya ce d’an uwanshi kawai yake jira, za su taho daga uk yau
Gobe inshaaAllah idan sun ƙaraso za su zo tare’’.

Tsananin murna da kunya ne suka sanya Yash kasa cewa komai, ya sunkuyar da kanshi kawai, ya kasa had’a ido da Baba.
Sir Najeeb ne ya ce “Allah ya nuna mana, Allah ya tabbatar da alkhairi yasa za ‘ayi da mu’’.
A tare gaba d’ayansu suka ce ‘’Ameen’’ har Yashjub, daganan Baba yace
“Allah ya ci gaba da kareka, Allah ya k’ara sauk’i, na ji dad’in ganin jikin naka haka, da aka ce ka yi hatsari na firgita sosai, amma ganin ka haka ya kwantar min da hankali.
Allah ya k’ara lafiya,
Allah ya ji k’an driver d’inka
Ya ci gaba da tsare ka a duk inda kake’’.

Cikin tsananin jin dad’i Yash ya ce ’’Ameen ya rabbi, na gode sosai Baba’’

Daga haka suka mik’e suka yi masa sallama, suka tafi, Yash yana ji kamar ya janyo Manubiya ya rik’eta ta ci gaba da zama tare da shi…..

Ba su dad’e da tafiya ba Likita ya shigo, yana shigowa kuwa Yash ya fara masa mita yana cewa
‘shi dai a sallameshi’,
dariya likitan ya yi kafin yace “ai na riga na sallameka, Yasmeen har ta kira su Daddy ma.
allura na zo in yi maka, ga kuma takardun sallama nan (discharge papers) ka yi signing, sai ka dinga zuwa follow up kuma akai-akai’’

Sai a sannan Yash ya yi murmushi a ranshi ya ce ‘Alhamdulillah’’
Dan kamar a k’an k’aya haka yake jinsa.

Sai da aka yi masa allura, Likita ya sake duba Hannun tukunna Yash ya yi signing papers ya yi wa likitan godiya daga haka Likitan ya fita.

Likitan, bai jima da fita ba ya sake aiko wata nurse da sabbin magunguna…
Karɓa kawai Yash d’in ya yi, ya d’an dudduba, kafin ya ajjiye a gefe ya ci gaba da zaman jiran su Daddy.

Yana nan zaune boredom(zaman shiru) ya ishe sa, dan haka ya mik’e ya fita domin ya shak’i fresh air, kafin a zo d’aukar sa.

Yana fita wajen, motar Yassir ta danno kai, dama Yashjub ya san wataƙila Daddy Yassir d’in zai turo dan yanzu a kaff gidan
kusan shine kad’ai yake zaman banza, a yanzu. A take tausayin k’anin nasa ya lullub’e shi,
sam ba shi da wani abun yi,
gashi shekarunshi sun kusan kaiwa talatin amma ba shi da wata hanyar samu mai k’arfi, shares d’in shi (kasonsa) na companyn Daddy kawai garesa, wanda a ko da yaushe yake adduar Allah ya taushi zuciyar Daddy ya sa ya k’arawa Yassir wani abun….

Dan a ganinshi ya kamata a k’ara mishi, saboda ko ba komai ma bai kamata ace yana Naamiji wanda daga yanzu zuwa ko wanne lokaci zai fara tara iyali amman ace shares d’insa ya kasance dai-dai da na mata ba, kuma kullum yana zaman banza.
Ya san komai da ya ke faruwa da Yassir ɗin laifin shi Yassir ɗinne tunda ko company d’insa ma da hannunsa ya lalata…..baya san zuwa aiki wani lokacin sai 11 zai ci uban kwalliya ya je, kuma
ko cikakkun awanni biyu ba zai yi a cikin building ɗin ba, haka nan zai fita ya shiga gari….

Amman koma dai yaya ne, haka za su dage, su ci gaba da taimakon sa dan Hannunka ba ya tab’a rub’ewa, ka yanke ka yar.

Yana cikin wannan tunanin Yassir ya yi parking a gaban shi, ya fito ya zagayo a ranshi ya ce ’’Mutumin da ya kamata in je kai ziyara kabarinsa, shine na zo d’auka daga asibitin zan maidashi gida garau!
Anyways, na riga na tanadar maka babban shirin da ya fi na baya..”

Dakyar ya k’ak’alo wani d’an guntun murmushin yaƙe
Ya ce ’’hi’’

Murmushi shima Yash d’in yayi, ya ce
‘’Follow me(biyo ni)’’
daganan ya juya.

Binsa Yassir ya yi kamar yadda ya buk’ata, suna zuwa cikin d’akin, Yashjub ya k’arasa ya d’auko
takardun da suke cikin jakar computer d’in shi, da wani a cikin k’aramin envelope, ya
dawo nan kan sofa inda Yassir yake wanda ya nemi waje ya zauna kawai yana binshi da ido .

A tsaye ya tsaya ya mik’a masa takardun, sai da yace
“ungo mana’’
Tukunna Yassir ya janye idanuwanshi a cikin na Yashjub, ya maida kan takardun kafin ya sa Hannu ya karb’a, sannan ya fara duddubawa.
Chapter 9 · 0% Book details