← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 152

Sashe 113

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K’arni da wari ne ya daki hancinansu wanda hakan ya sa suka fara waiwaye..ba abunda Yashjub ya tsana irin amai shiyasa idanunsa suna kaiwa kan aman ya fara kwala kiran mai aikinsu..Tana chan ciki shiyasa sai da ta d’an d’auki lokaci tukunna suka fito tare itada gwaggwo.
Aman ya nuna musu sai a sannan tukunna hankalinsa ya kai kan Kausar wadda ke tsugunne a wajajen ita da Yassira tana hawaye.

Gabansa ne ya ji yayi wani irin mahaukacin bugawa..Adduarsa d’aya Allah ya sa ba Kausar bace ta yi wannan aman!
Ba ya buk’atar Kausar ta yi koda ciwon Kai ne bayan abunda ya faru tsakanin su!..
Dama yayi tunanin hakan
tun a ranar amma gudun janyowa Kai tashin hankali da masifa ne yasa kawai ya banzatar da tunanin ya kawar da shi ta k’arfi da yaji.
Yana wannan tunanin k’irjinsa yana wani irin bugawa
Junior ya shigo rik’e da first aid box.

Ahankali Daddy da Abhi
suka k’arasa inda suke,suna shirin yiwa Hajiya mama magana tace”Na kiraku saboda wani case daban, amma yanzu bari mu fara yin wanda yake a gabanmu emergency!!!……Y’ar ruk’on gidanka!
Ciki ne da ita a karo na
na tabbatar ita kanta ba ta san adadin ba.
Su Khadijah na san watak’il duk sun san da zaman cikin dan ana cewa a yi mata test
suka gigice.
Wai har ni suka fara k’ok’arin yi wa wayo tsabar raini.
Anyways Junior!!”
Ta fad’i hakan tana kallonsa kafin ta d’aura da cewa”
Ga first aid box!
Ga kausar!!
Ga ciki!!!
Ga jini a jikinta da za a d’auka
a gwada.
Banaso inji kowa yace Uffan!!
har sai an gama test d’innan.

Tunda Yashjub yake a rayuwarsa bai tab’a jin mutum yana tsaye kyam amma ji da ganinsa sun d’auke ba lokacin guda tsabar fargaba sai yau!…da kyar ya samu ya fara gani
amman fa dukda haka dishi dishi ya ke ganin.!
Shi da kansa ya yiwa Kausar iyakar fita k’asar waje anyhow lokacin da ya dawo! har passport d’inta ya kwace, da kyar aka samu ya bata..
Gashi ta nuna kuma tace
bata son Yassir, dukda ya fahimci kamar ba su rabu duka ba amma ya san ba za ta kula shi ba, bayaga haka ma in ba ma ta dalilin ciwon nan ba ya san ba sa fita tare, shi da kansa ya tabbatar da hakan
kuma ba ta zuwa side d’insa….
sannan ko su suka kawo Iskanci duniya ya san ba za su
yadda su yi wani abun anan
sama inda d’akinta yake daff da na su Mommy sannan a tsakiyar su Yadira ba…..

Durk’usawa Junior ya yi!
Abunka da consultant..
Idanuwanta, tafin hannnunta
da bayan kunnenta sai k’eyarta kawai ya duba ya tabbatar da tana d’auke da ciki.
Sai yanzu ya fahimci komai tun daga kan abunda ya faru 2 weeks ago zuwa message d’in da Yassir ya yi masa yanzun daga fitarsa kafin ya shigo..
a tak’aice dai Yassir ya dirk’a mata ciki kuma suna so su ce na Yashjub ne tunda A message d’in Yassir cewa ya yi ya ce cikin 2 weeks ne exact!.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Junior ya shiga ambata a cikin ransa, saboda ya san tsaf Yassir zai yi abunda yace masa zai yi a cikin message d’in muddin ya k’i bin umarnin sa, shi kuma ba ya so a had’a Kai da shi a cuci Yashjub.

D’agowa ya yi a hankali ya kalli Yassir d’in wanda shima shi d’in yake kallo,bai gama nazartar sign d’in da Yassir d’in yake yi masa ta ido ba ya ji Hajiya Mama tace”ya dai???”

Tabbas Yassir ya ji masifar dad’i da farko da ya ji ance Junior ne zai yi test d’in amma
kuma yanayin sa yanzu sai ya fara bashi tsoro ya shiga tantama a kan ‘anya kuwa zai yi yadda yace masa ya yi???’

Numfashi Junior ya fesar
kafin ya kalli Hajiya mama
Yace “Bara inyi confirming..”

“Ciki ne ko?”
Tayi mishi tambayar tana matsowa kusa da su kafin ta
kalli Kausar wadda itan ma Junior take kallo tana yi masa sign ta ce”Wallahi yau sai..”

Cikin katseta Junior yace
“Ban tabbatar ba tukunna, bara mu yi test dai.”

Flat Junior ya ce Kausar ta kwanta ya d’auki wani abu ya d’aura mata a kan mararta sannan ya ɗauko y’ar k’aramar allura ya huda tomb d’inta ya d’auki drop d’in jininta a kan PT.

Sunayen Allah kawai Yashjub yake karantowa dukda sanyin standin Ac guda hud’u da
suke kewaye da makeken parlourn hakan bai hanasa
jik’ewa da gumi ba.

Ahankali Daddy wanda shi kansa ya sha jinin jikinsa ya juya ya kalli Yashjub..Hatta Abhi sai da ya ji tausayin Yash wanda unlike (saɓanin) Hajiya Mama shi Daddy ya riga ya gaya masa komai, sun san ba da sanin shi hakan ta faru ba, kuma sun san tsanar da yake yiwa Kausar shiyasa gaba d’aya tausayin sa ya lullub’esu. So suke yi su ce wani abu a samu a fasa wannan gwajin
Amman suna tsoron Hajiya mama kuma ko da ace sun hana d’in in dai akwai ciki kuma na Yashjub ne tou fa dole za a gani kuma za a fahimta sooner or later.

Wayar Junior ce tayi k’ara, bai kula ba saboda ya riga ya san Yassir ne…
Tashi d’aya pT d’in ya nuna Kausar tanada ciki kuma yadda result d’in ya fito da wuri hakan ya sa ya fahimci cikin ya dad’e a jikinta.

Abunda ya ke gwadawa a cikin nata yakeso ya samu ya k’arasa, dan yana so ya tabbatar sannan ya ga ko zai iya kintata adadin kwanakin cikin….

Kamar ance ya d’ago hakanan ya sake d’agowa, suna had’a ido da Yassir ya kallesa ya nuna masa aljihunsa inda wayarsa take da sauri.

Sunkuyar da kai Junior yayi yana jin yadda k’irjinsa yake bugawa, ba ya so ya d’aurawa Yashjub laifin da ba nasa ba sannan ba ya so asirinsa ya tuno dan ya san muddin Yassir ya nunawa Daddy da Yadira da su Hajiya Mama video d’in nan to Yadira ba za ta tab’a yarda ta auresa ba, su Abhi kuma bayanta za su bi ga kuma kunyar da zai kwasa……sannan idan aka yi rashin sa’a videon ya zaga duniya to fa da shi da Yarinyar sunansu ya ɓaci kenan har gaban abada….
Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya zaro wayarsa a aljihu..tashi d’aya gabansa ya yanke ya yi wani irin mahaukacin fad’uwa sakamokon video d’in da ya ga Yassir ya turo masa, a ƙasan videon ya rubata ”incase idan kana tantama, kamar yadda na turo maka ɗinnan to hakanan zan turawa duk wani wanda yake a family ɗinmu..”
Ko bud’ewa bai yi ba dan ya riga ya gani kuma ya san shine…ya san videon farin sani tun a school yanzu ma da ya zo nigeria Yassir ɗin ya sake nuna masa lokacin da suka yi faɗa…
da sauri ya kashe wayar yana wani irin haki ya mayar cikin aljihu.
“Me kake yi da waya ne haka junior?abun bai yi ba?”
Muryar Hajiya Mama ta katse sa.
Cikin d’an diriricewa ya d’ago ya kalleta yace “time nake dubawa”
Daga haka ya mayar da kallonsa ga abunda ya d’aura a kan cikin nata ya d’an yi shiruu kafin ya sa hannu ya d’auke dan ya kammalu, daga haka ya mik’e tsaye…
……
Tsayawa ya yi ya k’urawa abun ido kamar mai son fahimtar wani abu nan kuwa ba su san tunani yake yi ba.Ya riga ya fahimci abun ta inda yake nuni da cikin jikin Kausar zai iya wuce watanni biyu a jikinta…
Gashi shi kuma ance yace cikin satinsa biyu idan kuma ba haka ba to ya san me zai biyo baya!
Zuwa yanzu tabbas bai san abun yi ba.
“Junior ka yi shiru ka k’ank’ame abubuwa ba ka fad’i sakamako ba.”
Muryar Hajiya mama ta katse masa lissafi.

Ahankali ya d’ago ya kalli kowa
kafin yace
“She’s pregnant!(ciki ne da ita)”.

“Yauwwwa!!ai dama na sani”
Hajiya mama ta fad’i hakan cikin tsananin b’acin rai yayinda gaba d’aya parlourn akace”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
kamar an yi rasuwa,
Har su gwaggwo waenda suka lab’e a bakin corridor d’insu chan gefe.

Wani irin karkarwa jikin Yashjub ya fara yi..
Tunda ya shigo ya ma kasa k’arasawa cikin parlourn, ganin yana shirin zubewa ya sa ya ja kujerar dining ya zauna ya dafe kansa.
Yana sake karanto sunayen Ubangiji.
A ranshi yana “Ya Allah ka san yadda na ke k’in Yarinyar nan,
ka san yadda na tsani zina, Ya Allah ka sa ba zan haifi shege ba Ya Allah ka kawo mini sauk’i da mafita.
Ya Allah Ina son Manubiya ban san ta ina zan fara yi mata bayani in fara bata hak’uri wannan karon ba..Ya Allah ka sa wannan cikin ba nawa bane ba.”
Dan har yanzu bai cire hope ba!
Tunda ta tabbata ciki ne da kausar to yanzu yake son sanin sanin adadin kwanakin cikin…

Kamar Daddy ya san meye a ransa hakanan shi da Abhi suka matso kusa da Junior, Abhi ya d’an juyo da shi a hankali, gaban Daddy yana fad’uwa dan bai san ta ina zai fara had’a jini da Kausar ba..yana murna Yassir ya tsallake rijiya da baya yanzu kuma ace innocent Yashjub d’insa ne a ruwa…tausayinsa ya ke ji matuk’a dan tun d’azu ya lura da halin da ya shiga…
Ahankali ya kalli Junior yace
“Zaka iya aunawa?,kwanakin?”
Dan a yanzu bashi da wani burin da ya wuce ya ji ance cikin nan ya fi sati biyu…

Sai da Junior ya juya ya kalli Yassir wanda ya ke yi masa wani kalar ɓoyayyen murmushi, Dan tunda ya tura masa last message da video ya lura tarkonsa ya kama kurciya..
Had’e fuska Junior ya yi ransa a b’ace hankalinsa a tashe ya kalli su Daddy yace”Eh amfanin abun nan da na d’aura mata ma a cikin nata kenan,new invention ne(kwanan nan aka ƙirƙirosa)….”

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 37*

Gyaran muryar da Yassir ya yi ne ya sanya Junior ya yi shiru ya juya ya kallesa….signal ya yi masa kawai ya nuna masa Yadira da ido, daga haka ya sunkuyar da kansa bai sake yin komai ba.
Chapter 113 · 0% Book details