Sashe 152
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Siyama ce mai Yaro d’aya, saboda sai da ta haihu tukunna ta durfafi karatu, shiyasa suka tsayar akan ‘sai ta gama karatun tukunna sai ta d’aura haihuwar daga inda ta tsaya’.
Sosai suma suke zaune lafiya, dan shima Najeeb mijin marainiya ne, ma sha Allah.
Mijin Yahansu Kamal yanzu shine governor na Jahar Kano state, dan shekara d’aya asalin governor d’in ya yi ya yi ya rasu, shi ya maye gurbinsa aka basa ruk’on kwarya da aka zo zab’e kuma jama a suka sake zabaar sa.
Yasmeen ta yi aure.
Munirat ma ta auri Alhaji bashir (asalin saurayinta)matarsa ta rasu ata sanadiyyyar ciwonta da ya motsa mata haka kurum..ta yi jinyar sati biyu Allah ya karb’i ranta. Ko da ya dawo yace zai auri Munirat su Ummi basu b’oye masa komai ba, amma sai ya ce ‘ya ji ya gani, ai k’addara tana kan kowa kuma har Yaron ma zai rik’e..’
Aikuwa ya rik’e amana, dan shekara ta hud’u kenan suke a ciki amma bai tab’a nuna mata rashin mutunci ko
gori ko banbanci a kan d’anta ba.
sosai ya had’a da Yaron nata (ɗan gidan Yassir), da wanda ta Haifa masa, da y’ay’ansa na wajen uwargidansa marigayiya yake kula da su tsakani da Allah, itama kuma Munirat ta rik’e masa Ƴaƴa bilhakk’i da gaskiya….
Yadira da Junior sun koma Uk da zama, d’ansu d’aya yanzu take da cikin na biyu, suma zamansu Alhamdulillah.
Hajiya Mama kam k’iri k’iri Ummi da Mama sun yi wa Mom wayo dan sunce suma ta bari su samu nasu ladan.
Za ku sha mamaki idan na ce muku Abbakar Yusra ya aura!
Wanda itance ta ce ta ji ta gani duk duniya ita shi take so…da farko farko ma b’oyewa ta yi, sai da ta ga k’aunarsa ta na shirin yi mata illah tukunna ta fito ta fad’a…da farko su Manu k’in yarda suka yi, amma da suka ga k’anwar tasu ta mato da yawa kuma Abbakar ya yi nadama sai kawai suka nemi zab’in Allah, ai kuwa tunda aka fara maganar har aka d’aura aure komai sumul…yanzu haka Shekarar su biyu da aure suna zaune a garin Abuja inda yake aiki d’ansu d’aya mai sunan Daddy.
Muhsin ma yana Abuja yana karantar English a nile university, level 1.
Yasira ce dai Allah ya d’aura mata jinkirin aure dan sai yanzu ne tukunna Allah ya fito mata da miji alhaji isma’il matansa biyu itace ta uku…yanzu haka an saka rana wata uku….
An yankewa Mommy hukuncin d’aurin rai da rai….
Na
kisan da suka saka aka yiwa mallan lawal..
mutuwar Ya’isha, da kuma d’an Khadija (Amarya) na farko wanda ita da Baba Larai suka dinga d’ura mata magani har sai da suka kashe tun a ciki.
Dama tun kafin y’an sanda su tafi da ita ta daina gani…Shekarar ta d’aya a prison kuma mugayen prisoners suka jefa mata bonk gado na k’arfe a k’afafuwanta, ba a bata kulawa da wuri ba
har sai da k’afafun suka rub’e!!
hakanan tana ji tana gani daga ƙarshe sai yankewa aka yi..kuma har yau an gagara a samu yadda aka yi akai mata transfer zuwa gidan gajiyayyun, hakanan take fama a prison ba ido ba k’afa.
Ƴaƴan Manubiya da Yashjub uku..ta farkon mace takwarar Hajiya Mama ‘Yahanasu’ suna ce mata Noor, sai maza guda biyu masu sunan Baba da Najeeb,
Yaran Masu tsananin shiga rai, kamannin Manu duk suke d’aukowa gasu da k’ok’ari da wayo tubarkallah.
Itama ta kammala karatunta ta yi masters yanzu haka PhD takeyi kuma tana lecturing a buk…..
A ko da yaushe idan Manubiya ta zauna ta kalli rayuwarta sai ta yi kwallah….Duniya rawar y’an mata…
Kasancewarta y’ar talaka, talakan ma maskini hakan bai hana Ubangiji yin ikon sa a kanta ba, dan gashi abunda mutane wasu suke gani impossible(kamar ba zai yiu ba) ita ya faru a kanta, kuma tana rayuwa a cikinsa…ta samu miji mai masifar sonta wanda sam ba class d’insu d’aya ita da shi ba! Ta aura, kuma ya sota yana kan sonta tsakaninsa da Allah
Tabbas komai yayi farko zai yi k’arshe, farkon rayuwarta da kuma kusa da tsakiyar rayuwarta (lokacin da su mommy suka sakota a gaba kowacce hanya ta kulle) inda ace wani zai ce mata za ta ji wannan dad’in da take ciki sannan za ta samu wannan kwanciyar hankalin, a gaba, to da ba zata tab’a yarda ba..amma with faith haƙuri da kuma addu’a everything find its place perfectly… addu’a ita ce makamin mumini dan tabbas in da Rabbana komai ma ba wahala.
Mugu ba shi da riba, musamman ma mugun da yake zalinci yake cin riba baya tuba kullum ribar kawai yake gani!
Tabbas irin su waennan sun fi kowa wulak’anta daga k’arshe, sannan kuma azabar su ta fi tsanani ranar gobe k’iyama.
A ko da yaushe idan mutum ya yi hak’uri ya dogara da Allah Tabbas komai mai wucewa ne kuma komai akwai lokacin sa.
A bangaren Yashjub shima babu abunda zai ce sai Alhamdulillah!!
Ga matarso Allah ya basa, ga Ƴaƴa
Alhamdulillah, ga Mahaifiya ta gari, ga mahaifi mai k’aunarsa, ga y’an uwa masu sonsa, sannan ga arzik’i dukiya farin ciki da jin dad’i da tsantsar kwanciyar hankali duk ya samu yana kuma kan samu ta koina!!
Tabbas a ko da yaushe bashi da kalmar da ta fi dacewa yacewa Ubangiji sai ‘ALHAMDULILLAH!!!!!.’
Alhamdulillah!Alhamdulillah!!
Na godewa Allah da ya bani ikon kammala littafina mai taken suna’MANNUBIYA’.
Kuskuren da na yi a ciki Allah Ubangiji ka yafe mini, darussan da suke a ciki Ubangiji ka sa mu amfana.
GODIYA TA MUSAMMAN GA
Nazeefa Sabo Nashe.
Da
Maryam Bulama.
Ba zan tab’a mantawa da ku ba,alkhairin Ubangiji ya isar muku a duk inda kuke.
JINJINA da GODIYA mai tarin yawa zuwa ga mutanena
Oum Zahra
Maman Aliyu
Fauziyya Gwandu
Hannah OC
Binta Muhammad
Yumin Aliyu
Shamsiyya wada
Sadiya Ka’oje
Ummi Muhammad
Indo Aysha
Fati Abbas
Kudra
Maman Hafeez
Zahra Auwal
Iymert
Habiba Idris
Salmerh
Maryam Mustapha
Hannah collection
Mrs MB
Sadiya
Oumhanan
Da duk wani member na group d’in MANNUBIYA group one and two..ba zan tab’a mantawa da ku ba,ba ni da bakin gode muku sai addu’a wallahi!na gode na gode sosai Allah ya bar zumunci ya kuma kare mini ku kullum da ko da yaushe!na gode kwarai!!
Ina muku fatan alkhairi.
FATAN ALKHAIRI ga
duk wani fans ɗina a duk inda suke, Alkahirin Allah ya isar muku, ina godiya kwarai da addu’o’inku da kulawa…
Taku har kullum
Humayrah Bulama.