Sashe 126
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta tabbata Baba larai ta fice daga side d’inta gaba d’aya, tukunna ta fito daga cikin bedroom d’in nata!
kamar yadda ta yi zato ba ta tarar da Yahanasu ba, dan haka ta zauna ta yi shiruu ta shiga lissafin ta hanyar da za ta bi ta daidaita tsakaninta da Yahanasu….
Ta fi minti ashirin a zaune kafin su Yasira suka shigo a mugun hargitse, suna hangota suka kanta suna cewa
“ta zo
ta hana Baba Larai tafiya, ga ta chan ta had’a kayayyakin ta tsaff!tun d’azu suke rarrashinta amma ta kafe Akan Itafa sai ta tafi, kuma sai kuka take yi, dan Allah Mommyn ta zo su je ta tsayar da ita ta rarrasheta wataƙilan Daddy ko Hajiya mama ne suka yi mata wani abun…..”
Mik’ewa kawai Mommy ta yi, ta fad’a cikin bedroom d’inta ta kullo k’ofar!
wanda hakan ya sanya suka
fahimci matsalar daga wajenta ta taso kenan, dan haka kawai suka sauk’a da niyyar su je su ji da Baba larai first tukunna su dawo wajen Mommy su ji dalilin fad’an nasu….
sai dai suna sauk’a suka tarar da su Yasmeen suna shigowa cikin parlourn, a bakinsu suka ji ‘ai har ta riga ta tafi’
Cikin mayarda numfashi Yasmeen ta ɗaura da cewa “da Jaka ɗaya ma ta samu ta tafi, dan mun rik’e ragowar jakankunan nata mun hanata ita kuma ta tafi kawai ta bar mana su.
Mun so mu bita amma ba wani Napep d’in, dan itama sa’a kawai ta ci shiyasa ta samu sannan natan wanda ta ke cikin a baki baki ta zauna ta k’i bamu access bare mu shiga har aka ja aka yi gaba,
kuma na san kafin mu shigo mu d’au mota sun riga sun b’acewa ganinmu……”
Duk wannan dramar da ake yi su Daddy suna jin su suka manna musu hauka, daga k’arshema garden suka fice suka ci gaba da tattaunawarsu….Daddy ji yake kamar ya fi kowa farin ciki, a ransa kuwa addu’a yake yi ‘in shaa Allahu Baba larai ta tafi ta bar gidansa kenan har abada! next kuma Mommy ce!….’
Hajiya Mama ma ta ji dad’i da suka kirata suka sanar mata, tana fushi da su shiyasa yanzun ma kamar d’azu da suka kirata suka gaya mata zancen aure ba ta biye musu ba, kawai dai tace”a ci gaba da addu’a”
daga haka ta kashe wayar tana jin sanyi a ranta, in shaa Allah k’arshen Mommy ya zo
kenan, sannu a hankali za ta gani ne…..
Har yanzu mamakinsu take yi tana mamakin yadda ita kanta su Mommy suka goge mata hadda!!Amma ba komai, ai gashi nan sun fara gani tun yanzu, kad’an ma suka gani in shaa Allah.
A daren ranar Hajiya Mama ta bi jirgin k’arfe hud’u ta nufi Uk, duk da yadda abubuwan da suka wakana suka yi mata dad’i amma
tana so ta tafi…fushin da ta yi ɗin ta ga positive effects d’insa sosai a kan Daddy, dan haka ta yanke a kan gara ta tafin..za ta tafi ta je tai ta yi musu addu’a ‘Allah ya sa a dace, in shaa Allah Mommy ta kusa ganin k’arshen ta, kuma duk wasu abubuwa da ta rufe sai sun bankad’a a idanun kowa ya gani.’
Ya’isha ta fi kowa gigita da lamarin tafiyar Baba larai dan ta san Baba larai itace gatan su saboda yanzu haka ma aiki take yi mata a kan Siyama da Najeeb!!
Shikenan ta san ta shiga ukunta itakam yanzu..Yasira ma ta gigita sosai dan itama ta san Baba larai d’in dai itace gatan nasu, dan haka da daddare bayan ta bari Mommy ta d’an huce ta je ta sameta..
cikin son fahimtar da ita ta fara yi mata bayanin “illar tafiyar Baba larai a garesu, kuma ko ba komai bai kamata ace sun yi wa Baba larai haka ba! Ko me kuwa ta yi musu, ɓ ba ta chanchanci hakan daga garesu ba.”
Kamar Mommy ba za ta kulata ba, sai kuma Cikin nuna halin ko in kula ta ɗan nisa tukunna tace
“Yasira ba fa ni na cewa Larai ta tafi ba, ita da kanta ta yi zuciya ta ce za ta tafi, shiyasa ni kuma ban hana ta ba.
bayaga hakan abunda ta yi mini ma ya sanya dole in hukuntata in nuna mata iyakar ta, dan haka indai na Isa in fad’a miki ki ji to ki tsame hannunki sannan ki gayawa su Yusra suma duk su tsame hannayensu a lamuranta, ko waya bana so ku yi mata…
Allah na tuba idan banda failure (rashin nasara) ma me muke ta fuskanta! aikin nata yanzu duk ya daina ci!”
Cikin mamaki da tsanannin rashin jin dad’in abunda Momyn ta yi ta kuma fad’a yanzu Yasirar tace”idan na fahimceki Mommy ‘a yanzu dai Baba larai ba ta da wani amfani a gareki shiyasa kika b’ige da cewa kinaso ki hukuntata ne’,
saboda na san inda ace a lokacin da Baba larai take ganiyar taimaka miki komai yake tafiya daidai ne to da ko me ta aikata a gareki ba za ki tab’a barinta ta tafi ba, me ye ne ma ta aikata miki yanzun da ya yi zafi har haka???”
Yasira ta yi mata tambayar cikin b’acin rai.
Mik’ewa tsaye Mommy ta yi, ta nuna mata k’ofa tukunna tace”get out Yasira, tun kafin ranki ya b’aci!!!”
Za ta yi magana ta kuma daka mata tsawa tace “get out nace!!!”
Juyawa kawai Yasira ta yi ta fita ranta a b’ace da takaicin Mommy! dan ita a rayuwarta ba ta son mutum mai use and dump!!
kawai idan ana tare to duk daɗi duk wuya duk tsanani kawai a kasance a taren har abada! kuma a taimaki juna. amma ita Mommy bayaga use and dump d’inma da ta yi wa Baba Larai,
tun ba yau ba ta lura da Mommy kanta kawai ta sani, using d’insu take yi…..gaba ɗayansu amfani da su kawai ta ke yi.
…
Sai da aka yi kwana biyu tukunna Mommy ta je d’akin Yahanasu, dan ta san zuwa lokacin ta d’an huce.
A zaune ta sameta suna waya da Yashjub, tana ganin ta shigo ta yi sauri ta kashe ta ajjiye wayar, ba tare da ta kalletaba ta ce”bacci zan yi”
A hankali Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya, ta nemi guri ta zauna a kusa da ita ta kamo hannuwanta.
Kawar da kai Yahanasu ta yi,tsabar takaici da bak’in ciki ba ta san lokacin da hawaye suka shiga sintiri a kan fuskarta ba.
A hankali tace”na san na yi miki laifi Yaha amma ba laifi na bane ba completely.
Na shirya gaya miki komai in gyara tsakanina da ke amma da Larai ta fahimci hakan gudun kar asirinmu ya tonu sai ta je ta yi abunda ta yi ta kawar da tunanin ki daga gabana wanda ba dan hakan ba Yaha da ba zan tab’a bari mu kawo war haka a hakan ba!
Amma yanzu komai zai gyaru Yaha, saboda ke da kuma na fahimci Larai ta saka na cuce ki yanzu haka ba ta cikin gidan nan tun jiya saboda ke y’ata.
Na san abunda na ke roƙo a wajenki mai nauyi ne sannan za ki ga ya yi yawa dan ni kaina na san its alot to ask for amma dan Allah ki dubi uwar da aka shiga tsakaninki da ita ba tare da saninta ba, ki yi mini adalci ki bani chance ki bani dama Yahanasu….”
Mik’ewa da sauri Yahanasu ta yi, tace”dan girman Allah ki fita!ba na buk’atar gyaruwar komai a tsakanina da ke Mommy, kawai ki bari mu k’arashe rayuwarmu a haka!
Me ye ne ma ya rage??
You’ve missed out all the important stages na rayuwata(kin riga kin yi watsi da duk wasu matakai masu matuƙar mahimmanci na rayuwartawa)..da na fi buk’atar ki, dan haka yanzu ban ga amfanin ki gyara komai ba wallahi.
ba na buƙatarki a rayuwata, na riga na san ba kya so na ba kya k’aunata kin yi amfani da ni saboda ki samu abunda kikeso which u do, dan haka na rok’eki da girman Allah kar ki nemi ki ja ni a jiki saboda ba zan janyu zuwa jikinki ba.
Dan haka kawai ki yi harkar ki nima in yi tawa harkar, ba zan tona miki asiriba saboda saɓanin ke ni idan na yi Abu yana damuna kuma na san duk lalacewa ke ɗin mahaifiyata ce dan haka muddin na bada gudummawa ko na zamo silar tafiyar ki prison to na san abun sai ya dameni har k’arshen rayuwata, shiyasa kawai na zuba miki ido na ke jira Ubangiji ya yi ikonsa a kanki.
amma fa muddin ba ki daina yi wa Yash barazana kina threatening ɗinsa da tsinuwa ba! Wallahi kamar yadda na gaya miki shekaran jiya tabbas zan fad’a masa ba ke ce kika haifesa ba!
Saboda kamar yadda na san guilty conscious zai addabeni idan na fad’i abubuwan da kika yi aka hukuntaki haka zalika guilty conscious zai addabeni idan na bari bak’in cikin ki ya kashe Yashjub, dan haka ki daina threatening d’insa!!!
daga nan ni da ke mu ci gaba da mu’amala da juna kamar yadda muke yi kafin ki san na san ni ƴarki ce, iyakacin abunda nake buk’ata kenan daga gareki ba wai sulhu da fahimtar juna ba!
Kin riga kin cuceni wata shari’ar sai a lahira,Mommy ba wai iyaka hakki na ba wallahi ko da Hakkin Mama khadija kad’ai aka barki ke da Mallan lawal da Baba larai ya isheku…..”