← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 152

Sashe 116

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka Kausar tace
“Eh ai dole ku ce in zauna…in zauna a ci gaba da aibanta ni sannan kowa yana jin haushina ana bi na da mugayen tunani da sharri!.
Haba Hajiya mama,
Ni ce ma na saka ku a cikin tashin hankali
Ba ku ba??
Ni na yi wa kaina cikin??”.

Cikin tsananin fushi Hajiya mama ta juyo tace”idan ba ki
rufe Baki kin daina zancen
ciki da ni ba sai na fasa miki Bakin wallahi!
Shegiyar Yarinya mara kunya
kawai!.”

Fashewa Kausar ta kuma yi da wani sabon kuka
kafin tace”Eh tabbas kam!!na ji na kuma yarda ni shegiya ce
amman kuma yanzu ai ga shege zan haifa muku!jikanki!.”

Duk yadda Hajiya mama ta so daurewa kasawa ta yi sai da ta juyo a fusace ta kifawa Kausar mari!

Da kyar Yassir wanda suka yi da ita akan za su yi pretending kmr yana fushi da ita na y’an kwanaki,ya iya danne kansa.

Cikin fushi Hajiya mama tace
“Like I said, ki koma ciki
kafin zuwa gobe in gama tunani”.

Cikin kuka Kausar tace
“Ni kuma na k’i yarda in k’ara kwana d’aya a cikin gidan nan!.
Haba mana! wai shin maraici da rashin uba hauka ne??
shikenan sai a dakeni a hanani kuka?
ce muku akayi Inada burin in haifi shege??.

Bari ki ji in gaya muku
last miscarriage d’ina
Likita ya tabbatar mini in har na sake samun wani fitar cikin to mahaifata ba za ta sake rik’e ciki na tsawon wata hud’u ba! meaning ba zan sake haihuwa ba!.
Tun daga ranar na riga na yanke na kuma gama tsara rayuwata da
yadda zan kula da kaina da yadda zan yi aurena in haihu sai dai kash!!!tashi d’aya bagatatan Yashjub ya tarwatsa mini tsari da duk wani abun da na shirya.

Amma dukda haka kaff cikinku babu wanda ya duba yadda akayi raping d’ina (aka yi mini fyaɗe) haushina ma ake ji da hantarata da kyarata saboda bani da kowa ba ni da gata ko??.

Kowa in banda cin fuska ba abunda yake mini a cikin gidan nan!! safe da dare, dan haka na gama tsarawa zan tafi kuma
rest assure idan na fita kowa sai ya san abunda ya faru dan babu wanda zan b’oyewa, wallahi kowa sai ya san wannan d’an na Yash ne!
Daganan kuma ba za ku sake ganina ba
Ni ko d’ana.
Tunda dama abunda kikeso kenan, na yarda zanyi rayuwata ni kad’ai tunda dama bani da kowa”.

Da sauri Mommy ta matsa inda take ta rungumeta cikin
kuka tace
“Kausar kina da ni mana.
Kinada ni ga kuma y’an uwanki,
Kinada gata mana Kausar.”

“Kar ki yi mini haka Mommy,
kar ki kashe mini guiwa!
Ki ci gaba da fushi da ni kawai kamar yadda kika d’auka da
farko, hakan zai fiye miki.”

Zuwa yanzu kowa ya hallara har Yashjub wanda Daddy ya kira yace ya zo yana son ganin sa kafin Kausar ta fara dramar tata.

Tabbas Mommy tana son Kausar da gaske shiyasa ta sake fashewa da kuka cikin
kukan tace
“Ke nake gani na ke jin sauk’in rashin y’ar uwata Kausar, idan kika tafi kika barmu ni da Larai
kin san ba ki yi mana adalci ba.
Haba Kausar, ya za ki yiwa uwar da ba ta san komai ba sai k’aunarki haka??”

Hawaye ita ma Kausar d’in ta share tace
“Mommy na san kina sona,
amman anzo gab’ar da a cikin gidan nan nan da y’an kwanaki dole ki zab’a Ni ko d’aya a cikin y’ay’anki kuma na san dole Yashjub da farin cikin sa da rufin asirinsa za ki zab’a tunda ba zai tab’a yarda a haifi cikin nan ba saboda abubuwa dayawa ni kuma saboda mahaifata da aka ce za ta lalace in na kuma zubar da ciki
Wallahi ko sama da k’asa za ta had’e ba zan zubar ba!.
Besides in banda gori da masifa da bak’ak’en maganganu babu abunda nake janyo miki a cikin gidan nan fa!
Na gode da yadda kika tsaya tsayin daka akaina, kika bani gata amma lokaci yayi da ya kamata nima in tsayawa kaina,
shekaru na sun ja
Uwa ce ni dan haka zan iya kulawa da kaina and move on…..”

Gaba d’aya har Yadira kan Kausar suka rufa suka shiga lallab’ata amma ta birkice furr ta dage akan “itafa sai ta bar gidan” su kansu sun tsorata da Lamarin nata ballantana su Daddy.

Ba abunda yafi daga musu hankali Irin yadda ta rantse ta sake rantsewa akan idan
ta sa k’afa ta fice ba wanda zai
sake ganinta ko ita ko d’an da za ta haifa tunda babu wanda yake buk’atar su.

Tsaki Hajiya mama ta yi tace”ai sai ku yi”
Daganan ta juya ta wuce ta nufi d’akinta ta shige ta banko k’ofar da k’arfi.

Sai a lokacin Abhi ya matsa
kusa da ita yace”Kausar ki je d’akinki ki zauna..zuwa nan da
2 hours zan neme ki. Daganan in kin ji hukuncin da na yanke still bai yi miki ba, sai ki tafi babu wanda zai tsayar da ke.”

“Kausar plss..ki sauraremu
mana,
b’acin rai da zuciya ba abunda yake janyowa sai da na sani!.”
Cewar Ya’isha.
“Fushi ne mukayi dake na y’an lokuta, amma yanzu komai ya wuce..kar ki yi punishing d’inmu ta hanyar rabuwa da mu na har abada.
Muna k’aunarki, ke d’in y’ar uwarmu ce, jininmu ce!.”
Cewar Yasira

Shiruuu kowa ya yi,
kafin Kausar ta juya kawai
ta wuce ta koma ciki ba tare da ta kalli kowa ba, ranta fess!!…
Ba abunda ya fi yi mata dad’i irin zuwan Yashjub, kuma ta tabbata maganganunta sun yi tasiri a kansa duba da yadda ta ga ya tsaya yayi shiruuu
a stairs d’in ya ma kasa k’arasowa saman.

Tana shiga ta rufo k’ofarta da sauri ganin su Yasira sun biyota suna shirin shigowa suma.

Dama Mommy bataso ayi abunda ta shirya ta kuma gama tsarawa a gaban Hjiya mama dan ta san idan sama da k’asa za su had’e ba za ta tab’a yarda ba
Shiysa ta yi godiya ga Allah da ta ga tunda ta shiga ciki bata sake ko lek’owa ba.

Daddy Abhi sai Yashjub wanda Abhi ya k’arasa ya ja hannnunsa ne suka nufi saman,dan haka da sauri jikinta har yana rawa ta bi bayansu.

Suna shiga parlourn Daddy itama ta kutso
Kai bakinta d’auke da sallama.

A fusace Daddy ya juyo yace”the last time da kika hawo mini side d’ina me na ce miki???”

Cikin in Ina tace”Haba Daddy, meeting fa za a yi wanda ya shafi rayuwar d’aana, dole za ka ganni a nan mana sabo…”
Cikin katseta da b’acin rai sosai yace”za ki b’ace mini daga gani ko sai na yi ball da ke??”
Hawaye ne suka b’alle mata kamar an kunna famfo..
Cikin son tura mata wani bak’in cikin ya matso kusa da ita yace”da ke da frame ba ku da maraba a cikin gidan nan, bi ma’ana sai dai a kalle ki ki kalli mutum shi kenan amfanin ki!.

Daga yau! ko da wasa na ganki a wajen da ake magana mai amfani da mahimmanci wadda ta shafi ni ko y’ay’ana Wallahi ranki sai ya yi masifar b’aci, bana buk’atar ki a cikin komai nawa! ko yunk’uri kika yi na son shiga cikin maganata ko ta yarana wallahi bak’anta mini rai kike yi.!
Tsabar tsaurin ido ko Ummi wadda na damu da ita ba ki ganta a nan ba amma ke k’ok’ari kike yi ki shigo!….”

Da mugun sauri Mommy ta juya tana hawaye kamar ruwan fanfo, bibbiyu haka ta sauk’a daga stairs d’in ta nufi side d’inta inda ta bar Baba Larai tana mai had’a hanya….

Tana shiga ta tarar da su ita da su Yasira…
Ganin yanayinta ne ya sake d’aga musu hankali, dan haka suka rufar mata da tambayar “mai ya faru?”.
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 38*

Tana shiga ta tarar da ita da su Yasira…
Ganin yanayinta ne ya sake d’aga musu hankali, dan haka suka rufar mata da tambayar “mai ya faru?”.

Ba ta b’oye musu ba, dan zuwa yanzu tana so ta gogawa Daddyn bak’in jini a idanun ƴaƴan nasa ta yadda za su tsaya mata su bi bayanta a kan komai.
Dan haka ta zage ta kwashe Komi ta sanar da su, tana kuka abun tausayi..wanda hakan ya sa Yadira da Yusra fashewa da kuka suma…
Yasmeen kam ta d’an ji babu dad’i tunda uwa uwace, sai dai kuma har ga Allah ita ba ta ji haushin Daddy ba,Yasira da Ya’isha ne suka fi kowa fusata, Ya’isha har da cewa “ai da ba ta fito ba!” Lokacin da ya ce ta fito d’in.

Sosai suka rarrashi mahaifiyar tasu, wadda hakan da suka yi ya sa ta d’an ji sanyi, daga nan ta kalli Baba larai tace mata “suna sama suna meeting Larai, kin san me ya kamata ki yi a halin yanzu ko?”

“Dalla dalla ma kuwa!”
Baba Larai tace,daga haka ta mik’e ta fice, Ya’isha da Yasira suka bi ta, Yusra da Yadira kuma suka zauna suka ci gaba da rarrashin Mommy yayinda Yasmeen ta fice ta basu guri,dan tunda Mommy ta fara magana da Baba Larai ta fahimci me su ke shirin yi…ba ta againsting wai Kausar ta auri Yash, kawai ita Asiri ta tsafin nan nasu ne ba ta so, sannan makircin su har ga Allah ya yi yawa, gashi ba ta Isa ta ce komai ba.

Mommy tana fita Yassir ya shigo…kwata-kwata ya kasa
gane kan dalilin wannan dramar da Kausar ta gabatar, zai je ya sameta su keb’e su yi magana ya tambayeta dalili amma for now tun kafin iyayensa su yanke wata muguwar shawarar da zata tarwatsa shi gara ya zo ya fito kawai ya gaya musu shi zai aureta…a yanzu babu lokacin pretending ko acting domin a yadda abubuwa suka gudana da abunda tayi ya san tsaf su Daddy za su ce Yashjub ya d’auki responsibility d’in cikin da ya yi wa Kausar ko dan kar sunan family ya lalace.

Ba su kai ga fara magana ba shima Junior wanda sai yanzu ya dawo daga had’o results ya hawo saman ya shigo cikin parlourn.
Chapter 116 · 0% Book details