Sashe 21
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yash ba k’aramin shock ya shiga ba dan yana shiga parlourn Mommy ta rufesa da fad’a, kamar za ta had’iyi harshe! Abunda ba ta tab’a kwatantawa ba kenan, babu abunda ya fi b’atawa Yash rai kamar akan abunda take yin fad’an, in da ma wani abunne ya faru recently har ta kai ta ga yin fad’an to da dasauk’i amman fa tana fad’an ne akan wai ‘lokacin da za’a d’aga auren sa ba a yi mata magnar ba, ba’a tuntub’eta ba, sai ji ta yi kawai an d’aga.
Kuma wai Manubiya ba ta kiranta ta gaida ita amma tana ji suna yawan yin waya da Yahanasu har ma da Ummi…idan so yake ta yafesa a cikin y’ay’anta ne to kawai ya fito ya fad’a, dan abunda ya ke yi mata ya isheta,in ba rashin sanin ciwon kai da wulak’anci ba ta ya zai dinga fifita kishiyarta da y’ar kishiyarta sama da ita a rayuwarsa???….”
Yash ya so ya yi mata bayani ta fahimta, sannan ya bata hak’uri amma yadda ta k’i sauraronsa da kuma yadda ya fahimci kamar ma Baki take shirin yi masa ne ya sanya shi kawai ya fice ta k’ofar baya ya bar mata parlourn, zuciyarsa tana wani irin tafarfasa.
Sam ya rasa dalilin da ya sanya Mommy take bak’in ciki da farin cikinsa.
Bai nufi side d’insa ba direct mota ya nufa ya shiga ya kunna ya fice daga mansion d’in gaba d’aya, ya nufi gidansu Manubiya.
Yana yin parking a k’ofar gidan ya ji zuciyarsa tana yin sanyi ahankali ahankali, rabonsa da ita tun last month dan wannan karon da yaje uk ya dad’e sosai shiyasa yake ji kamar ya yi shekara uku bai ganta ba, suna waya da chatting har ma da video call kullum amman yayi mugun mugun missing d’inta……
Tana zaune suna hira, ita da mai gyaran jikinta da su Siyama a parlourn su Siyama ta ga kiran sa, murmushi ta yi tana wani Irin blushing kafin ta yi picking, a hankali ta ji ya ce ”surprise!ina waje”
Kad’an ya rage ba ta tsala
Ihun murna ba, da kyar ta iya cewa “ok” tukunna ta katse kiran ta kalli Siyama ta cw ”yana waje” ta fad’i hakan fuskarta tana baiyyana tsananin farin cikin da take a ciki.
Dariya Jidda ta yi kafin ta ce ”Allah adda idan aka zo kaiki kika yi mana kuka kowa ya san kukan murna ne,”
Dariya duk suka saka wanda hakan ya sa Manubiya ta d’an nutsu ta bar zumud’in rufa mayafin da take yi, kafin ta kalli Jidda ta galla mata harara tukunna ta kalli mai gyaran jikin ta ce ”an gama?”
Murmushi matar ta yi kafin ta mik’e ta shiga harhad’a kayayyakin ta tace “ai ko ba’a gama ba jeki kawai”
Dariya sosai suka yi kafin Siyama ta ce ”ki shigo da shi nan, bari mu tartare”
“To” kawai tace, daga haka ta sa kai ta fice.
Tunda ta taho ya kafeta da idanu, har sai da yasa ta ji kamar ta nutse dan yau kalar kallon nasa na daban ne….a b’angaren Yash kuwa har wani jiri-jiri ya fara ji tsab’ar kasalar da ta rufar masa tashi guda!
Ya san yana son Manubiya so mai tsanani na tsanakani da Allah amma tunda yake bai tab’a jin kalar sha’awar ta da yake ji a yanzu ba, ya na ji from time to time ba wai ba ya ji ba amman abun na yau ya girmama, dan har wani ciwon ciki ne ya ziyarcesa tashi d’aya…..ta yi wani kyau ta yi fresh kamar wata y’ar baby, har wani murmurewa ya ga ta sake yi gwanin ban sha’awa.
Cikin d’an turo Baki ta ce ”ni dai ka daina kallona”
Murmushi ya yi ya bi Bakin da ake turo masa da kallo wanda yakenan kamar na y’ar jinjira ma’abociyar tsotso, kafin da kyar ya d’an k’ura wa fuskarta ido tukunna ya ce ”gani na yi kin sake zama baby, y’ar babyn Yashjub”
A hankali ta sunkuyar da kanta tana murmushi k’asa-k’asa kafin ta ce” kaima ka k’ara kyau sosai”
dan Itanma tunda ta fito ta lura da haske da kyan da ya k’ara….wani irin blushing Yash ya shiga zubawa kamar mai tallar makilin, kafin da kyar ya samu ya tsayar da murmushin tukunna ya amsa gaisuwa da ya hanyar da take yi masa.
Daga nan ta yi masa iso zuwa parlourn su Siyama wanda har sun gyara tsaf sun kunna turaren wuta…..Tabbas Yash da Manu sun yi missing juna dan sai da suka kashe sama da awa uku ba tare da sun ma sani ba, dukda kuwa Yash dauriya ce kawai yake yi dan yau kam shi kanshi mamakin kansa yake yi saboda bai tab’a jin desire irin wannan ba, ga kuma ciwon ciki, amman kuma ba ya so ya tafi so yake kawai ya yi ta kallonta…
Da kyar dai, yana jin kamar kar ya tafi, ya yi mata sallama dan Najeeb yana chan yana ta jiransa.
Har mota ta raka sa, yana ta zuzuta yadda ta yi kyau dan ba kad’an ba ta tafi da imaninsa…..itan ma santin kyan da ya k’ara take ta yi a cikin zuciyarta, a haka suka rabu kowa yana muradin d’an uwansa.
Bai yi tunanin za su yi dare shi da Najeeb ba, dan har sha biyu na dare ba su samu sun kammala abubuwan da suka tisa a gaba ba.
Sai da yaje mota domin d’aukar wasu abubuwa tukunna ya ga wayarsa tana haske dan haka ya yi saurin d’auka ya k’ara a kunnensa…
Yana d’agawa ya ji muryar Daddy ya ce ”come home yanzu, Hajiya mama tana nemanka ta d’agawa kowa hankali”.
“Okay tam”
Kawai yace, daganan Daddy ya katse kiran, sai a sannan Yash d’in ya lura da uban jerin misscalls d’in da aka jera masa…..
ajjiye wayar ya yi, ya je ya cewa Najeeb zai tafi sukayi sallama, tukunna ya nufi gida.
Yana zuwa, bai tsaya ma yin tunani ba saboda kar ya ji ba zai iya shiga ba dan har ga Allah ba ya son had’uwar sa da Mommy gudun kar ta kuma yi masa abunda ta yi d’azu…wayoyinsa kawai ya d’auka ya zuba su a aljihu, daga haka ya rufe motar ya nufi cikin gidan.
Tun kafin ya shiga cikin main parlourn ya fara jiyo hayaniyar Hajiya Mama, tashi d’aya ya fahimci ita da Mommy ne sakamakon yadda ya ji tana
magana cikin fad’a da rashin kara sannan tone d’inta very rude!.
“Ai dama ba ki gaji arzik’i da ɗa’a ba, wallahi yadda na ga ba ki wani damu ba na san kece kika b’ata masa rai ya
bar gidan nan bani da tantama.
Dama ta ya za ki so ya yi aure ya tara iyali ba tare da kin riga kin mallakesa ba!
Ƴaƴa dai Allah ya baki amma wallahi ko Akuya ta fi ki sanin ciwon ƴaƴanta!
ke kuwa kanki kawai kika sani, burinki kawai ke kanki kad’ai sam baki damu da farin cikin su ba.
To bari ki ji, wallahi tun wuri ki san yadda kika yi ya dawo gida idan ba haka ba kema sai kin bar gidan nan!Yau zan nuna miki cewa ba fa surk’ullenki da munafurce munafurcenki ne suka sanya na barki cikin gidan ɗana ba”
A hankali ya ji Daddy yace “Mama ba fa inda Yash ya je,
maybe aiki ne ya rik’e shi..”
Cikin tsawa Hajiya Maaman ta ce ”shiyasa sometimes (wasu lokutan) nake jin kamar in rufeka da duka! Ai ko ba’a fad’a ba na riga na sani, jikina ya bani, gashi kuma ba ya d’aukar waya, amman sai wani ce min kake yi aiki ne ya rik’esa, wanne irin aiki ne zai hanasa d’aukar waya??”
Ba ta jira jin amsar sa ba ta ce ”kuma Yadira ta ce min fita yayi ranshi a mugun b’ace”
cikin fushi ta juya ta nuna Mommy tace “Kuma na san wanann makirar ita ta janyo fad’a da shi, ba ni da tantama!!
Ita ta b’ata mishi rai, ita za ta yi abunda zai fasa auren. dama tun farko ita ta hanashi yin budurwa. Wallahi Khadijah ki ji tsoron had’uwar ki da Ubangiji!
son zuciyarki yayi yawa, kwata-kwata ba ki da tunani da lissafi mai kyau!”
Wani irin kuka Mommy ta fashe da shi wanda ya sa su Yassira suka k’arasa inda take itada Yasmeen suka rufar mata, suka shiga bata hak’uri, fuskokinsu
tamau! Alamun sun ji haushin abunda Hajiya maman take yi.
Itakam ko a kwalar rigar ta, haka nan ta ci gaba da tsigale Mommy tass.
A haka Yashjub ya yi sallama ya shigo ya samesu, da da farko so yayi ya juya dan wallahi kansa har ya fara ciwo amman kawai sai ya dake ya shigo.
Dasauri kowa ya d’ago ya na kallonshi, Hajiya mama kuma ta nufeshi cikin takun ta na tsoffi da d’an sauri tana zuwa
ta rungumeshi, sai kuma ta d’ago tana kallonshi kafin ta ce “Karka b’oye min komai, mai ta yi maka? Me ta ce maka? matsala take shirin kunnowa ko? So take ka fasa auren na sani.”
Ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin yace “idan akwai wanda zai kunno matsala a aurena ai ke ce, tunda gashi yanzu ma abunda kike yi na san duk kishi ne ya rufe miki ido kike k’ok’arin ki tada husuma tun kafin kishiyar taki ta zo”
Dariya Yadira da Munirat suka yi, kafin Ummi ta d’an matsa kusa da su ahankali cikin ladabi ta ce “Hajiya mama mun gaya miki tun d’azu, babu komai InshaaAllah.
Yadira kuma zolayar ki kawai take yi wataƙilan kawai so take ta ja ki da magana”