← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 152

Sashe 44

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da idanunsa suka sauk’a akan Jidda wadda yake ta faman nema tun d’azu ya samu ya d’an nutsu tukunna ya juyo ya d’anyi mata murmushi
kafin ya ce ”Really!
In ji wa?”
Ya fad’i hakan yana me maida kwayar idanunsa ga Jidda wadda ta had’e rai ta tamke fuska amman fa a chan k’asan ranta tsorone ya lullub’eta…dan tun d’azu ita kuma take ta k’ok’arin b’uya gudun kar su had’u, yanzu kam tana ganinsa gaba d’aya hankalinta ya tashi!
Sam bata son Yassir, dan idan akwai mutanen da bataso ta gani yanzu to Yassir ne sai su Yassira.
Muryarshi ta tsinkaya kawai yana cewa”Jidda mu je
Ko”
Ya fad’i hakan yana kallonta.

‘Dum!!!’
Haka k’irjinta ya bada kafin
a ranta tace
“Lalle wannan mutumin bashi da hankali…yanzu shi har yana tunanin zan iya tsayuwa a k’ark’ashin inuwa d’aya ma dashi bayan abunda yayi min ballantana har in bisa…
In bisa ya k’arasa rungumar da d’azu bai samu damar yi ba kenan…”

Yahanasu ce tace”Ai sun kira brother d’insu, zai zo ya d’auke su”
Sai da ya d’anyi shiruu kafin
yace”Am..siyan baki za su yi,
Yash yana k’asa, a yadda
na gansa d’innan na san idan ba su yi sauri sun sauk’a k’asan ba to za su yi loosing (rasa) kud’in siyan bakin…dan da kyar muka
tsaida shi da ni da Najeeb,
kema ku yi sauri ku wuce,
ku basa space, dan na lura a matse yake..”

Da sauri Yahanasu ta ce
“A’uzubillahi”
Sai kuma ta kai masa duka.

Kaucewa yayi yana dariya
Idanunsa suna akan Jidda wadda ta runtse idonta
da k’arfi tana mamakin rashin kunya da tsaurin ido irin
na wannan bawan Allah.

A hankali Munirat ta sunkuyar da kanta k’asa…a ranta tana aiyyana shin shawarar da ta yanke anya kuwa ta yiwa kanta da rayuwarta adalci kuwa.
So take yi kawai wani ya bata go ahead yace ta yiwa Yassir duk abunda yakeso amman daga Ummi har sister d’inta sun kora mata zazzafan warning akan Yassir sun ce ta rabu da shi, sun k’i ma su tsaya su saurareta kuma tun ganinsu tare da Ummi ta yi gaba d’aya sun k’i su sake da ita balle su ji cikinta sosai ta yadda za su fahimce ta…ita kuma gaskiya ba za ta iya rayuwa babu Yassir ba, ga shi ta lura ko ta kanta ma ya daina bi, ta san kuma yana samun guri a wajen Jidda shikenan tata ta zo k’arshee….
Ba ta Ankara ba kawai ta ji hawaye sun zubo mata, da sauri ta yi firgigit ta sake yin k’asa da kanta tukunna ta sa hannun ta goge, sai a sannan ta ji muryar
Yahanasu tana cewa”Munirat ko bacci kika fara ne daga sunkuyar da kan da kika yi yanzun nan?”

Sai da ta d’an gyara fuskarta
da style tukunna ta d’ago tana murmushi tace
“A’a”
Daga haka ta mik’e tsaye tana gyara mayafinta.

Shi Yassir harga Allah sai yanzu ma ya ganeta, shi fa idan ba ganinta ya yi ba wallahi mantawa yakeyi da ita.
Ya san sun had’a ido lokacin da ya shigo amman sam hankalinsa ba ya wajen shiyasa ma bai wani fahimci ita d’in ce ba…..
..
Aisha cewa ta yi ba zata je ba, haka itama Yahanasu..
sai da Yahanasun ta saka baki tukunna da kyar Jidda ta mik’e ta yarda za ta je…..

ba kad’an ba k’irjin Munirat ya dinga bugawa dan ba ita kad’ai ba Hatta su Aisha sai da suka lura da yadda Yasir ya ke bin Jidda da ido…..

Babu Yadda Yassir ɗin bai yi ba akan a barsa ya ga fuskar amarya a cewarsa “ai shima zai iya yaye lullub’in tunda k’anin ango ai ango ne”amman k’iri k’iri Yahanasu ta hanasa….haka nan yana ji yana gani ya hak’ura suka fita,ya so ya ga fuskarta sosai wallahi dama yanzu ne chance d’insa na yau dan ya san Yash ba zai tab’a yarda ya rakosa ba.

Yassir ya so ya d’an wanke kansa a wajen Jidda amma sam ta k’i ta basa damar ya yi mata magana ma, haka nan ta mak’ale a tsakiyar su Siyama har suka sauk’a.

A k’ofar parlourn chan k’asa dama Najeeb ya tsayar da Yashjub k’iri
k’iri ya hanasa shigowa ko cikin parlourn ya ce “wallahi yau sai yayi al’ada”
gashi ya tusa shi a gaba da tsiya da zolaya…tun Yashjub yana fushi wai ko Najeeb d’in zai hak’ura har ya hak’ura ya d’an fara dariya kad’an-kad’an.

A haka su Siyama suka sauk’o suka samesu, sai da ya hangesu tukunna ya bar Yashjub ya shigo ya zauna…

Shiruuu parlourn ya d’auka bayan duk sun zauna, su
Siyama basu tab’a sanin ma yadda ake siyan baki ba,
Munirat kuma tana d’an shakkar Yashjub sannann ga tunanin Yassir shiyasa ta yi shiru.

Tashi d’aya suka fahimci bama su iya siyan bakin ba shiyasa kawai Yassir ya fara dariya k’asa-k’asa

Ganin za a rainasu ya sa Siyama ta yi k’arfin halin cewa
“Siyan baki za mu yi”

Murmushi duk sukayi kafin
Najeeb yace “Ai ba ku za ku yi siyan bakin ba mu ne za mu yi,ko??”
Yayi mata tambayar yana murmushi

Nan ma duk shiru sukayi dan dama itace me d’an bakin to kuma Najeeb ya sako Baki shiyasa itanma sai ta ja tayi gumm!

Ganin suna b’ata masa lokaci ne ya sanya Yashjub dag’owa ya kalli Munirat yace”Munira bani acc number d’inki”

Dariya sosai Najeeb da Yassir sukayi.

Cikin nutsuwa ta karanto account number
Yashjub yana shirin turawa
Najeeb ya ce masa “wait mana!ba kaara?bari inyi ai wannan
aikin mu ne ba naka ba..”

Dama Munirat ta yi expecting kud’i masu nauyi amman bata yi tunanin har 1.5M ba.

Murmushi tayi tace sun gode daganan ta mik’e tace “bara muje mu sauk’o da amaryar, da sauri Yashjub yace
“Wacce amaryar kenan?”
ya fad’i hakan yana gyara zama
sannan ya d’an had’e fuska.

Nan ma dariya suka yi hadda Siyama kafin Najeeb yace
“Kwantar da hankalinka muma mun gaji, tafiya zamu yi, muje mu huta”
sai kuma ya kallesu yace “ku saukk’o mu tafi.”
“To”kawai Munirat tace daganan suka nufi sama gaba d’ayansu.
……
Nasiha sosai
Aisha da Yahanasu sukayi mata, bayan fitar su Munirat, har sai da suka taso mata da tsumin kukanta, sannan Yahanasu ta yi welcoming d’inta warmly into their family.

Dare ya yi sosai, sun san idan aka tsaya sallama shima wani b’ata lokacin ne, shiyasa iya su biyun suka yi mata sallama, suka d’aukarwa su Jidda jakankunan su…
Da kyar kuwa ta saki Hannun Yahanasu dan sai yanzu wani tsoro da fargaba suka rufeta, gashi haka kurum sam sai ta ji bata so a tafi a barta ita kad’ai…..

Aisha ma har da y’ar kwallar ta, haka nan tana hawaye tana waving d’inta har suka fice suka rufe mata k’ofar d’akin nata, dai-dai su Jidda sun k’arasa hawowa dan haka suka yi sauri suka basu jakankunan su, suka ce su wuce gudun kar ma ta ji muryoyinsu ta ce za ta fito……..

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 20*

Tun lokacin da aka faara siyan baki dama Siyama ta turawa Ya Musbah message, shiyasa dai dai sun hau sama kenan Ya Nafi’u ya kira Aisha ya ce “su sauk’kk’o sun zo”
Sun so yi wa Manubiya sallama amman Aisha ta hanasu ta damk’a musu jakunkunan su tace su tafi…hakanan suka je suka yiwa Yash sallama tare da fatan alkhairi suka wuce.

Yahanasu ce ta d’auki Munirat a motarta dan ita bata fito da tata ba,suma suka wuce….Yassir ma sallama kawai ya yi masa ya wuce.

Najeeb ne sai da ya d’an tsaya ya yi masa y’ar guntuwar nasihar rik’e alkawari da amana kafin shima ya yi masa sallama ya wuce Yash d’in yana ta godiya.

Sai da ya ga fitar Najeeb d’in tukunna ya k’arasa cikin motarsa ya dauki duk abubuwan da ya sissiya ya wuce cikin gidan, yana shiga ya maida main door d’in ya rufe yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya…kamar a mafarki haka yake ji wai yau shine Angon Manubiya!
Alhamdulillah
Alhamdulillah
ya yi ta maimaitawa, kafin ya saita gabas ya durk’usa ya sanya goshinsa a k’asa ya yi godiya ma Ubangiji
Subahanahu wata a la!.

Kitchen ya nufa, ya harhad’a komai, da decorations d’in, tukunna ya fito ya nufi sama.

Sai da ya fara duba d’ayan d’akin tukunna ya lek’a d’akin gym d’insa, dan dama ya san wataƙila anan su Aisha za su ce za su jera kayan gadon da suka nace sai sun yi…ai kuwa yana bud’ewa ya hango ta zaune a kan gadon wanda aka shimfid’awa wani had’add’en bedsheet mai tafe da wani k’ayataccen quilt da pillows farare tas tas, masu tsananin kyau da d’aukar hankali.

Ba kad’an ba ya ga d’akin ya yi masa wani irin masifaffen kyau, sannan tashi d’aya ya ji wani irin sanyi da annashuwa sun lullub’esa. gadon tun a kallo ɗaya ake fahimtar ba mai tsada bane ba amman kasancewarta a ciki ya sanya ya ga gaba d’aya kaff gidan babu wajen da ya kai ya wannan a kyau da bashi peace of mind(kwanciyar hankali)…

Sallama ya yi mata, kafin ahankali ya fara takawa zuwa inda take…

Tun kafin ya kaiga k’arasawa gareta ya fara jiyo sheshshek’ar kukan ta…..

Ba ita ba, hatta shi zuwa wannan lokacin yanayi na bugun zuciyarsa ya tsananta…itakam dama tun lokacin da ya rufe k’ofar falon ta fara jin inama akwai inda za ta je ta b’uya!….

Yadda yake takawa zuwa inda take haka take jin takun nasa kamar a kan k’irjinta yakeyinsa….

Sai da ya ƙarasa dai dai kanta tukunna ya ja ya tsaya kafin a hankali ya durk’usa a gabanta, sannan ya saka hannu ya yaye hular alkyabbar.

Shiruu kawai ta yi ta lumshe idanunta tare da damk’e hannuwanta guri d’aya wanda hakan ya sake bawa hawayenta damar sauk’a akan kumatunta…

ajiyar zuciya ya sauk’e yana mai jin takaicin su Yassira yana sake lullub’esa, dan ya tabbata har da bak’in cikin abunda sukayi mata ne yasanya tsadadden hawayenta k’in daina zuba.
ba zai yi mata maganar ba, dan ba zai sako ta a ciki ba amman idonsa idon su Yassira gobe tabbas sai ya ci uban su!.
Chapter 44 · 0% Book details