← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 152

Sashe 89

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba su san waye ya gayawa su Yasira sun koma gidan ba, sai kawai ganinsu suka yi har da babbar jaka…Yasira da Yusra da Yadira, dan Yasmeen ma cewa ta yi ba za ta bi su ba wannan karon, tace ‘ita babu ruwanta, saboda zuwa yanzu da ta zauna ta yi lissafi ta fahimci tabbas idan ba su daina biyewa Baba larai ba to sai ta goge musu duk wani ilimin addini da suke da shi.’
Sosai kanta ya kasa ɗaukar yadda Yasira ta haƙiƙance tana gaya mata ‘wai ai da ma Baba larai ta duba ta gani Manubiya za ta taho da masifu a bayanta..ita za ta ga bayan Mommy, tou kuwa gashi alama sun fara nunawa, dan haka dole su tashi su tsaya…dama ai duk abunda Baba larai ta fad’a sai ya zama gaskiya.’
Bayan ba su san sakawa da suka yi a ransu ne ya sanya Allah ya barsu da halin su ba, shiyasa suke ta ganin masifun suna zuwar musu kamar yadda sukai zato! Dan idan ba hakan ba wacece Baba larai da har za a ce ‘duk abunda ta fad’a sai ya tabbata???…’.
Shiyasa Yasira tana gama zaiyyane mata itakuma tace ‘ita dai babu ruwanta,ba za ta hanasu ba, dan ta san ba za su hanu ba, idan kuma ta fad’a to ta san za ta samu matsala da Mommy, dan haka ba zata faɗa ba, amma kar su sake sakota a cikin zancensu….’

Shiyasa Yasirar ta kad’o kan Yadira da Yusra suka taho bayan Baba larai ta cika musu jakankuna da kayan barbad’e-barbad’e, dan tunda suka je asibiti aka ce an sallamesu ta fara harhad’awa.

Ba iyaka su Manubiya ba, hatta Yash ya fahimci kissa ce da k’arya su Yasira suka zo da ita wannan karon…dan yadda suka yi musu..suka wani chanja gaba d’aya tashi d’aya abun dole ya bawa duk wani mai hankali mamaki…hatta Yasira da murmushi ta gaida Manubiya sannan ta shiga tambayarta ya jiki, kamar za ta goyata har da zama a kusa da ita, tukunna tace”Mommy ce ta ce su zo
su tayata gyare-gyare.”

Shi dai Yash ba don kar ya ce su tafi abun ya zama case ba, da tuni ya sallame su! Dan gaba d’aya haka kurum hankalinsa bai kwanta da su ba.
Ya san watak’il idan Gwaggo ta zo za su tafi shiyasa yace bara ya je ya d’aukota, amma sai ya ga ko alamun gezau ba su yi ba ballantana a saka ran tafiya, shiyasa kawai ya fita yana jimami.

Bayan fitarsa sai wajen ya zama shiru, dan suma su Yasirar tun suna magana da suka ga su Siyama da Manubiyan sun k’i sakewa sai kawai suka d’aga k’afa suma suka yi shiru.
Suna a haka suna jimami Ya Nafi’u ya kira su Jidda yace”mutum biyu su fito a bar mutum d’aya a gidan, za su wuce gida su fara tartara kaya an sallami Baba..”

Siyama aka bar mata, Jidda da Muhsin kuma suka tafi, dan idan zai yiu a yau suke so su tashi daga gadon k’aya su koma sabon gidansu dake a gandun albasa wanda Yashjub ya basu.

Ba su yi ma tunanin za a sallami Baban yau ba, da tuni sun yi parking d’in.

Ita Aisha Mama Anty Umma da Inna ne suka tartare komai kafin dare sun kammala komai ya Nafi’u da Muhsin kuma su sakayi ta zirga zirgar kai kaya a motarsa da motar kai kaya.

Sai da suka gama kammala kai komai gidan tukunna suka d’auko Baba daga asibiti suka nufi tsohon gidan nasu dashi domin su je su yi wa su Uncle sallama saboda Baba dagewa ya yi yace”shi fa sai ya yi musu sallama.”
Suna zuwa Baba da Ya Nafi’u suka nufi wajen su Uncle d’in, Inna da su Mama kuma suka nufi wajen matayensu.…yunwa Jidda ta ke ji dan ba ta tsaya ta ci abinci sosai ba, shiyasa ta je kitchen ta d’aura ruwan zafi da niyyar ta je ta siyo milo da madara ta sha tea…
Sai da gabanta ya yanke ya fad’i sakamokon k’amshin turaren da hancinta ya fara jiyo mata,a take a ranta tace “nooo..it can’t be,ta ya ma zai shigo nan.”
daga haka ta mik’e bayan ta gama saita murhun ta juya za ta fita kawai ta ga mutum a tsaye kyam!…..
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”tace a fili, kafin ta d’an d’ago wayarta ta d’an haska dan ta samu ta tabbatarwa kanta da shi d’in ne…

Suna had’a ido ta fashe da kuka ta yi ƙasa da wayar sannan tace”dan girman Allah ka fita Ya Al’ameen kar ka janyo mana masifa”

Ahankali ya yi taku d’aya ya matso gareta muryarsa har tana d’an karkarwa yace”D’azu na ji Mama tana gayawa Ammi cewa za ku tashi…”

Cikin sharar hawaye tace”eh,mun ma tashi..dan Allah ka fita…”

A hankali yace”Jidda ni da ke fa?ba za ma ki tsaya ki ji uzuri na ba?tun safe nake ta faman zirya Ina lek’en gidan nan Jidda duk dan saboda ke amma kora ta ma kike yi?”
Bai jira jin amsarta ba yace”a lokacin da na tafi,wallahi wallahi tun a kwana biyu da na kirawo wayarki na ji ba kya amsawa na had’o kayana na biyo jirgi na sauk’a a garin Abuja, inaga cousin d’ina da muka tafi tare da shi ne ya kirawo su Ammi yace musu na taho dan flight d’ina yana shirin boardn zuwa Kano Mahaifina ya kira ni yace idan na zo sai ya tsine mini tunda bani da hankali. Kalar fad’an da ya shiga yi min a wanchan lokacin ni kaina na san akwai abunda Ammi ta gaya masa mai muni shiyasa ya yi fushi sosai ya ji haushi dan ko fad’a bai cika yi mini ba.A wanchan lokacin babu yadda ban yi da shi ba amma ya k’i saurarona, yace in juya in koma. Tun daga ranar ya daina kulani, ya yi fushi da ni, yace kuma wallahi idan ya ji labarin na zo Nigeria ba tare da na gama abunda ya tura ni in yi ba sai ya bani mamaki, yace kuma ko waya na yi miki bai yafe ba. Sai da na dawo tukunna a cikin maganarsa na fahimci ashe Ammi ce ta ce masa saboda ke na rubuta letter na bar course d’in da ya tura ni in yi saboda kince ‘Baba zai aurar da ke a Yusuf idan ban dawo an yi auren da ni ba’.

Jidda Course d’in duk yawansa na san ba zai kai wata hud’u ba wanda da ni kwata kwata ban ma san zai kai yawan hakan ba dan na yi tunanin 4 weeks ne sai da na je tukunna na gani, amma da naduba sai naga ai wata huɗun shima ba wani lokaci mai tsayi bane shiyasa na hak’ura na yi masa biyayya na bari akan idan na dawo sai a yi komai, amma ko a wanchan lokacin ɗin ma sai da na saka mai gadin mu ya sa mini ido gudun kar Ina chan Ina shirya ta yadda zan shayo kan iyayena ke kuma a aura miki Yusuf.”

Shiruu ya yi kafin ya d’aura da cewa”wannan shine abunda ya faru Jidda shiysa kika ji ni shiru, na san waye mahaifina yana son duk abunda nake so kuma zai tsaya mini a kai, amma muddin na yi masa taurin kai to na san tsaf za a samu matsala, kuma na san halinsa da bin diddigi yadda yace ‘kar in kiraki’ wallahi da ace na kiraki to sai ya sani, ni na san waye shi. na san kuma ya yi hakan ne saboda ya ga shin zan yi masa biyayya ko akasin hakan.”
Cikin sake yin taku d’aya zuwa gareta yace”I love you!always and forever, ba zan iya hak’ura dake ba Jidda, gara ma tun wuri ki yi saurin karb’ar uzuri na ki yafe mini mu fara nemawa kan mu mafita!”

Shiruu ta yi a ranta ta ji matuk’ar sanyi da dad’i da ta ji ba banzatar da ita ya yi ba, a fili kuma sai tace”Ya Al’ameen ni kam na dad’e da hak’ura da kai,ka duba fa ka ga Mahaifinka ma ba so yake yi ba tunda shi ne yace kar ka ki…”
Cikin tarar nufashinta yace”noo Jidda wallahi ba da ke ya ke fushin ba da ni yake yi, kuma na san da ace ya ji batun aurenku da Yusuf ya taso to da zai yi wani abun …
A ranar da zan tafi, a airport na yi masa bayanin komai na ce masa Ammi ba ta so, shi da kansa a wanchan lokacin ya tabbatar mini da cewa ‘inshaaAllah ina dawowa za a yi auren mu, kuma kafin ma in dawo za a yi tambaya, batun Ammi kuma kar in damu ya san yadda zai yi da ita, ba matsala inshaaAllah. Amma shi abunda ya ke so dani a lokacin shine in yi k’ok’ari in maida hankali a kan abunda na je yi saboda saboda course ɗin yanada matuƙar mahimmanci wa business ɗinmu!’
Shiyasa da ya ji na shallake sa, na bar ma makarantar shi kuma ya ji haushi ya yi mini haka, amma wallahi ko yanzu Mahaifina a shirye yake ya d’aura mana aure ko a yau!ita ma Ammi ta amince kuma wannan karon da gaske, saboda halin da na shiga ta tsorata ta yi nadama ta gaskiya ba kamar wanchan lokacin ba da ni kaina ban san linke ni ta yi a baibai ba”.
Chapter 89 · 0% Book details