← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 152

Sashe 80

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiruu ya yi ya d’an k’ura mata ido……ya san idan ya zurfafa zancen itama za ta fara zargin abunda yake zargi, sannan hankalinta zai tashi kamar yadda nasa ma yake a tashe wataƙilan ma fiye da nasa d’in, shiyasa ya sauk’e ajiyar zuciya yace”Allah ya tsayar a iya ka hakan…”
Ahankali tace “ameen” hankalinta duk a tashe.

Cikin ruk’ota izuwa jikinsa yace”sannan kar ki damu saboda businesses d’ina have been successful, kuma tun farkon shekarar nan har kawo yanzu inaga na samu abunda zan iya gina estate d’in ma biyar!! a iyaka ribar shekarar nan kawai. ban saka komai a raina ba na karb’i k’addara.
Kuma ko da ace ban samu income da ci gaba a business d’ina ba to banga dalilin da zai sanya in ji takaici ko in shiga damuwa saboda na rasa estate ba.
Ubangiji na ya yi mini ni’imomi masu tarin yawa a wannan shekarar…kinga na farko ya bani ke, har da k’aruwa gashi mun samu,sannan abubuwa na da businessess d’ina sai bunk’asa su ke daɗa yi!..
kina ganin dan estate guda d’aya ya k’one zan ji haushi? Ai ya bani abunda ya fi estates dubu ma Baby tunda ya bani ke”.

A hankali Manubiya ta sake shigewa Jikinsa ta kwantar da kanta a kan k’irjinsa, ta yi shiruuuu.
A karo na biyu, ta ji ya sake cewa “ki yi hak’uri a kan abunda Mommy ta yi miki, dan Allah’’

Ahankali tace ‘’ba komai fa, iyaye basa laifi, sannan kai a matsayin ka na Mijina ka daina bani hak’uri, ka fi k’arfin haka a waje na.”

Shiruu duk su biyun sukayi kowa da abunda yake tunani..

“Dan Allah ka kaini in ga Baba’’
Muryar Manubiya ta katse masa rikitaccen tunanin da yake yi.
Shiru ya yi kawai bai ce komai ba, dama wallahi ba dan Mommy ta tambaya ba to da ba zai fad’a mata ba! Dan
Su kansu su Innaa cewa suka yi kar ya gaya mata saboda kar ta d’aga hankalinta.
Muryar ta ce ta sake katse masa tunani jin tana cewa
‘’Dan Allah” a hankali kamar za ta fashe da kuka.

Numfashi ya fesar kafin ya sake rungumeta da kyau yace’’ok zan kai ki amma wataƙila sai zuwa gobe, saboda kinga kema baki da lafiya…yanzu bara in kira Doctor ya fara duba mini ku tukunna kin ji ko,
ki kira su a waya kar ki sa damuwa zai samu sauk’i inshaaAllah….’’.

Sai da ya lallab’a ta sosai tukunna da kyar ta hak’ura a kan goben za ta je, dan haka ta d’au waya ta shiga kiran su, ya ji sun yi magana da Jidda da Inna har ma da Siyama amma bai ji sun yi magana da Ya Musbah wanda tunda ya je gidan kafin su tafi kai Baba asibiti ake ta kiran sa yana cewa”gashinan zuwa”. Ba.
shiruu ya yi sai da ya gama had’a one plus one tukunna ya kalli
Manu yace mata “Musbah bai je bane??har yanzu?”.
Diriricewa ya ga ta d’an yi dan ita kanta lamarin na Ya Musbahu ya fara d’aure mata Kai, dan a bayanin Jidda ta fahimci su hud’u ne kawai a wajen Baban yanzu haka gashi idan ta kira sa a waya ba ya d’auka.

Dukda shima yana fama da tasa damuwar amma haka ya daure ya danne tasa cikin nutsuwarsa ya sake ce mata “akwai wani abun ne?is there anything I can do to help
(Akwai wani abun da zan iya taimakawa da shi?)
saboda jinin Baba fa ya hau ne sosai”.

Tashi d’aya tun kafin ya gama rufe bakinsa ta fashe da kuka,
cikin kukan tace “dan Allah ka kai ni in gansa”

Numfashi ya fesar yace”to bari in kira Doctor ya zo ya duba min ku,tukunna sai in ga ko zai iya barin ki ki fita yanzun”
Daga haka ya mik’e ya fice yana ganin dishi-dishi tsabar tension…

Yana fita ta kira Jidda shi kuma ya na fita Ya Nafi’u ya kira dan tabbas ya lura family d’in Manu suna cikin damuwa…
Da farko Ya Nafi’un b’oye masa yayi, sai da Yashjub d’in ya nace tukunna ya zaiyyane masa komai halin da ake ciki, halin Baraka da yadda ta janye Ya musbah da kuma yadda y’an uwan Baba suka sako shi a gaba..ba su ajjiye wayar ba sai da suka yi wa tufkar hanci daganan suka yiwa juna sallama bayan Ya Nafi’u ya yi wa Yashjub alk’awarin zai sanya Baki ya lallab’a su Baba su yarda su k’arbi gidan da Yashjub d’in ya basu su koma..

Ba k’aramin rarrashi likitan ya yi wa Yashjub ba da ya ji batun Manu har ta suma amma ba su sani ba, ya san ba laifin sa bane ko na nurses tunda sun gama yi mata allurai kuma ita da Mijinta suka barsu a d’akin sannan da aka zo fita ba a kira kowa ba amma hakanan ya yi ta bawa Yash d’in hak’uri dan ya lura ransa a b’ace yake.

Dama ba so yake yi ta fita d’in ba, aikuwa likitan yana zuwa da ya duba ta yace”ba zai yiu ta fita yau ba gaskiya jikinta ba kwari”…

Hakanan da kyar ya samu ya sake lallab’ata ta hak’ura dan jikinta duk ya yi sanyi daga wayar data gama yi da Jidda yanzu
Saboda Jiddan ta gaya mata komai itama…….

Yahanasu Yash ya kira ta zo
ta zauna da Manubiya yayinda shi kuma ya nufi estate d’innasa….

Sai da ya je Estate d’in nasa tukunna ya ga abunda ya faru da b’arnar da aka yi, tashi d’aya zuciyarsa ta aminta da zargin da yake ta yi tun d’azu ‘tabbas kashesa ake so a yi’ shi aka so a akashe da basaja sai Ubangiji ya kub’utar da shi kuma wannan aikin na jikinsa ne yake yi, da kunce masa tayar mota da aka yi da incidence d’in dole sai na jikinsa wanda kuma ya san shige da ficen sa ne zai iya yi, to amma wanene mai wannan aika aikar???
Dan zuwa yanzu ya fahimci ba Kausar bace ba, wannan aikin sai dai aikin gayya ko kuma kwararren tantiri tunda har da y’an fashi a lamarin…gabansa ne ya yanke ya fad’i a tashi d’aya ya yi istighfari da ta’auzi dan kamar yadda d’azu kwakwalwarsa ta basa ‘Mommy ce ta turo Yasmeen ta yi wa Manubiya allura,’
hakanan yanzu ma lissafinsa ya basa’ita da Kausar maybe da ko Yasira ne suka yi wannan aika aikar, dan aikin ya wuce b’arnar mace d’aya’
Cikin runtse idanunsa ya shiga kokawa da zuciya da kwakwalwarsa dan sam bai ga ta inda mutuwarsa za ta zamo riba wa Mommy ba….ta ya ma zai yi tunanin hakan ita fa ta haifesa.
Still shi da kansa a cikin zuciyarsa yace”amma fa some facts cannot be denied(ammafa wasu abubuwan a baiyyane su ke kuma ba zaa iya chanja su ba),…
a iyaka d’azu kad’ai ya fahimci kamar ba ta tab’a shiga fushi irin na yau ba, ta ya za ace d’anki ya kusan mutuwa amma da kika gansa ya dawo lafiya lau bai ji kwarzane kwata kwata, ace ba ki yi
farinciki ba maimakon farin cikin ma sai fushi da bak’in ciki…kamar irin tana fushin ganin plan d’insu bai ci bane shiysa ta fusata ta kasa controlling kanta…..amma mai yasa?
Mai yasa suke son kashe sa, me za su cimma ta hanyar hakan?
A take zuciyarsa ta shiga aiyyana masa tana yi masa flashing yadda ‘ba sa son Manubiya!’
To kenan za su kashe sa saboda sun kasa raba sa da Manubiya kenan? Da sauri ya bawa kansa amsa ta hanyar cewa”noo, hakan sam bai bada maana ba!.”
Bai san lokacin da hawaye suka shiga ziraro masa ba, yana mai jin wani irin yanayi na tashin hankali da bak’in ciki da rud’ani, a ransa ya ce”Mommy ba za ta iya kashe ni ba amma duk wata alama tana mini nuni ne da tsaf za ta iya aikata hakan….tun ba yau ba na san ba ta sona, sannan tunda na d’auko maganar aure abubuwa suke ta sake tab’arb’arewa, ga kuma abunda ta yi yau.”
Rud’ani rikici da kuma rashin sanin gaskiyar lamari ne suka sanya ya runtse idanuwansa da mugun k’arfi, still a cikin ransa yace “akwai wani abun da ya kamata ace na sani…akwai abunda ban gani ba kuma ban sani ba!to amma what is it(menene shi ɗin)????”.
Ya yi wa kansa tambayar ba tare da ya san mai basa amsar ba!.
dan tabbas a yanayin yadda ya ke ganin abubuwa to dole dole tsakaninsa da mommy ba complete bane ba, akwai wani abun da bai sani ba, wanda sai ya samu ya sani ɗin ne tukunna in ya haɗa komai da ke faruwa a tsakanin shi da ita zai yi makin sense, ya san a take zai bada cikakkiyar ma’ana….

Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e ya dafa shi ganin yana hawaye sannan ya runtse idanuwa yace”Yash sai hak’uri fa!na san me kake tunani, amma ka kwantar da hankalinka ka ci gaba da addu’a, bawa bai Isa ya yi wa bawa abunda Ubangijinsa bai yi ba”

A hankali ya bud’e idanunsa da suka koma kamar garwashin wuta, ya zuba su a kan Najeeb.

Jinjina kai Najeeb ya yi ya ce ”yeah, tun akan incident na hatsarin motar da ku ka yi kwanaki na fahimci akwai wanda yake harin rayuwarka, kawai na yi shiru ne saboda na ga kaima ka sani amma ba ka son tada maganar, yanzu kuma duba da yadda motarka tana shigowa suma suka baiyyana suka rufe gate suka fara kashe mutumin suka kunna wuta, ya sanya na sake tabbatarwa…amma kar ka damu, a hankali zan taimaka maka za mu yi bincike ko dan rayukan mutane kusan d’ari da aka b’atar inshaaAllah za a kama ko ma waye me aikata wannan mummunan aikin…”

A hankali jikin Yashjub ya fara karkarwa, duk yadda ya so hana kansa yin kuka sai da hawaye suka balle masa sosai..yanzu a ta dalilin sa aka kashe duk waennan Mutanen….ta ya zai taɓa iya yafewa kansa??
Ga kuma zargin Mommy da yake yi wanda ya sake hautsina sa…
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 30*
Chapter 80 · 0% Book details