← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 152

Sashe 37

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiruuu Yassira ta d’an yi sai kuma ta kawar da ƙoƙarin fahimtar maganar da Yahanasun ta gama gaya mata yanzun, kafin
ta matsa kusa da ita
ta ce
“Mecece matsalar ki?
me kikeso ki yi proving?
A tunaninki ni da Hannuna zan cutar da d’an uwana ne ko me kike zato?
Dan tsaf na fahimceki, na kuma gano abunda kikeyi wanda har ya kai ga kina k’ok’arin saka zarginmu a idanun waennan k’azaman Mutanen!
So kike ki nuna musu wani abu akan mu ko me?.

Na san ba uwa d’aya ce ta haifemu ba amman dukda hakan ke ɗin y’ar uwata ce kuma na san matsayinki a wajenna shiyasa kika ga Ina binki a sannu…
amman fa Yahansu karki kuskura ki kai ni bango!! Kar ki bari mu fara yaƙi da ni da ke a cikin gidan Imam kura dan wallahi in kika ja hakan ta faru to ba za ki ji dad’i ba!…
Dan na lura kwana biyun nan
wani gigi kike ji, kina ƙetare iyakar ki!!!.
Tsabar rainin hankali ɗazu in tanbayeki kwatancen gida ki ce baki sani ba sannan kuma ko kunya ma bakiji ba mun had’u da ke kinsan mun gane k’arya kika yi mana amman shine zaki zo da wani sabon shirme?

Amma, daga wannan ba za ki sake ba! Saboda lokaci ya yi da za ki koma matsayarki! Dan na lura ƴanci bai kamace ki ba..”

Murmushin takaici Yahanasu ta yi kafin tace”Madallah! Da kyau, hakan ya yi kyau!….
Gara da kika fito k’iri-k’iri kika gaya min komai, na ji dad’i.

Sai dai inaso ki san cewa nima fa na san kaina, kuma zan iya tsare jikina da ayoyin Ubangiji, dan haka
ko me kike tunanin yi a banza ne”

Da fushi sosai Yassira ta ce
“me kike nufi? wa ma ya
damu da wata ke ballantana ya miki wani abun, bayaga hakan ma me kika maida Mutane?”

Dariya sosai Yahanasun ta yi sannan ta ce “dad’ina da ke Yassira har gobe ba ki iya magana ba….kina nan da rashin iya sakaya maganar nan naki har gobe bai chanza ba.
Na san kin san me nake nufi dan haka mu rufe chapter kawai.

Inaso kawai ki san cewa ‘ba zan tab’a bari ku zalinci Manubiya ba..’
and kamar yadda kika tuhume ni ba zan ɓoye miki ba! eh, hakan ne, saboda maganar gaskiya ban yarda da ku bane
shiyasa na yi duk abunda nayi,
kuma kar ki sha mamaki idan aka kawo Manubiya in zaunar da ita in zaiyyane mata su waye ku! Saboda
gudun kar ku yi mata shigo shigo ba zurfi, dan an yi min ban ji dad’i ba shiyasa ba zan bada k’ofa ayiwa wata ba!
Hatta su Ummi lokaci kawai nake jira, sannan akwai abunda nake dubawa shiyasa kawai nake ɗaga muku ƙafa amma dukda hakan akwai ranar da zan yi wa kowaccenku zazzagar kwanyo, har a gaban Daddy, dan wallahi ba wai ke kad’ai ba hatta Mommy ba
tsoron ta nakeji ba yanzu! Kuma za ki tabbatar da hakan soon”

Cikin fushi Yassira ta d’aga Hannu za ta kifa mata mari, da sauri Yahanasun ta rik’e Hannun tukunna tace “Wannan zamanin ya riga ya wuce Yassira, na wuce haka daga gareki
har abada wallahi, sannan Ina so ki san kun yi kuskure!
Tara abokanan adawa da yawa shi yake janyo Mutum k’asa wanwar, kinga ga ni ga Ummi sannan ga Manubiya
kuma dukkan mu babu yadda kuka isa ku yi damu wallahi, ban san wanne dukan za ku fara
karewa ba dan tabbas kun d’aukarwa kanku dala babu ganmo….

Kin d’aukarwa kanki aiki mai tsananin wahala, kin jefa kanki a masifa, sannan kin biyewa son zuciyar da ba inda zai kaiki sai garin dana sani”
Cikin sauk’e ajiyar zuciya ta ci gaba da cewa “Inama ace za ki san kuma za ki ga abunda na sani, to da kin gane wacece Mommy, da kin daina biye mata.
Gaba dayanmu mu
ukun ba abun tsana bane a wajen ki, ni y’ar uwarki ce!
Manubiya matar wanki!
Ummi kuma Matar Daddy ce,
masoyiyar mahaifinki ba abar gaba bace a gareki.
Zan so ki gane sannan ki fahimci cewa Mommy amfani kawai take yi da ku domin cimma manufarta..using d’inku kawai takeyi amman na san ba za ku fahimci hakan ba!.

Kamar yadda na faɗa miki tun farko
‘kina rayuwa ne cikin ruɗi!, akwai abubuwa da yawa da ya kamata ace kin sani.”

“Mommyn tawa ce take using d’ina? Tabbas yau na sake tabbatar da ke ɗin mahaukaciya ce, bari ki ji!!!
Mahaifiyar da ta tsugunna ta haifeni idan tana da dama ko mosquito ba za ta tab’a bari ya cijeni ba.
Ni ba mahaukaciya ce Irin ki ba, na san menene dai dai
nasan menene ba dai dai ba, babu wanda yake using ɗina ko tunzurani, komai in kinga na yi to na san me nake yi kuma gaban kaina ne…”

Shiruu kawai Yahanasu ta yi tana la’akari da yadda maganganunta suka tab’a Yasirar……tashi d’aya mood d’in Yahanasun sai ya chanza, da kyar ta iya hana kanta kuka, ahankali ta kalli Yasira sosai kafin ta ce “ki yarda da ni in na ce miki ‘Mommy za ta iya aikata abinda ya fi using d’inki ma Yasira’.”

Wani irin yanayi Yassira ta ji ta shiga daga kallon idanuwan Yahanasu, da sauri tq kauda kanta gefe ta yi shiruu, na y’an sakanni…da kyar ta fatattaki tausayin Yahanasu tare da mugun tunanin da take k’ok’arin dasa mata a rai!
Ta juya fuuu ta fita da sauri.
Tabbas sun yi sake kam
d’an hakkin da ka raina….
gashi har tana yi mata barazana….
Yahanasunda a da idan ta saka mata kara bata Isa ta tsallaka ba amman wai yau itace take fad’a mata maganganu har haka!
Ba laifin kowa bane laifin
Mommy ne wadda ta fara taka musu burki a kan Yahanasun, a tunanin Mommy Yahanasu ba ta Isa yin komai ba, to gashi yanzu ta zame musu problem.
…
Babu yadda ba su yi ba, amman duk ta inda suka zaga gidan a cike yake taff.
Baaba Larai kamar ta d’aura Hannu aka ta fashe da ihu!!! Haka nan tanaji tana gani ta hak’ura da abubuwan da suka zo da su za su yi, ko d’aya cikin kwalayen flask d’in da suka shirya a kan za su saka turaren a ciki su je su jere ya gama su tafi da shi
fasawa sukayi dan zuwa wannan lokacin ba damar yin wannan basajar, saboda Yasira ta yi mata signal d’in Yahanasu
sannan ga dangin amarya
sun kunna nasu ba zai yiu su suna dangin ango su zo su hau kunne kunne ba suma, bayaga hakan ma ko mahaukaci Idan ya ji warin ya san ba turare bane suka kunna…….Yayyafe yayyafen da suka shirya yi shima ko Ina mutane……

Dakyar Yassira ta lallab’a Baaba Larai had’e da d’an fad’a
tukunna ta hak’ura amman da cewa ta yi ”sai ta yi a gabansu bata damuba”
Ita dai yassira tsoro takeji da kyar dama ta yarda ta biyo su gidan tun farko….
bata nuna bane amman maganganun Yahanasu sun ratsata, ga kuma abunda Ya’isha tace mata sir Najeeb yace kuma ta san tsaf zai iya bada sheda in Yahanasu ta je ta fad’i wani abun akansu….ita tsoronta kar su je su sake lalata relationship d’insu da d’an uwansu shiyasa ta yi dagaske suka tarkata suka yi gaba
bayan sun gama kushe gadon Manubiya a gaban su Jidda…..

Yasmeen harda cewa “Irin gadon matar mai gadin su ne
exactly.
Itakam dan Allah anjima a rufe d’akin in an kawo amarya, dan wanann abun kunya ne ba kad’an ba”

Yadira ma y’ar k’arama da ita
amman harda ita a masu cewa
“Ita Wallahi da ta ji anata jeere jere ta d’auka za ta zo ta ga wani abun kirki, ita wallahi
gadon ma tsoro yake bata…”

Ba wanda yace musu uffan,
amman Ummi ta gama shirya gayawa Daddy idan ta koma
dukda basa magana
amman zata kulashi saboda Manubiyan ko da ace zai ji haushin tane, saboda ba za ta
zuba ido su tisa y’ar mutane a gaba ba, dan a yadda
taga take taken su indai aka barsu to akwai kallo.

A b’angaren Jidda kuwa, zuwa wannan lokacin wallahi ji take kamar ta hana Manubiya tarewa da wannan Mutumin, kamar ta wargaza auren ma gabad’aya haka ta ke ji, saboda waenan mutanen.
ta san yanzu ta makaro
shiyasa kawai ta yi shiru ta dinga ajiyar zuciya
tanaji kamar za ta fashe.

Haka ma Siyama, ga takaicin Najeeb ga kuma takaicin dangin mijin Manubiya…anya akwai haske a lamarin nan kuwa!
dan ita ko a wasa bata tab’a jin labarin jahilan dangin miji Irin waennan ba…..
K’iri k’iri suke yin abunsu babu b’oye b’oye ko kauda kai, babu kissa ballantan kawaici….

A yadda
suka dinga gaya musu zafafan maganganu babu control
wallahi da waensu aka samu
da sai an dambatu!
kawai dai sun samu masu kauda kai ne da gudun magana shiyasa suka kyalesu.
A haka ma basu ga matsugunnin su ba kenan, shiyasa daga Jidda har Siyaman suke ta addu’ar ’Allah yasa banda su za a zo d’aukar amarya.’
Bawai dan suna jin kunyar gidan nasu bane ‘A’a’! Kawai dai ba sa so su zo su yi musu shirme a gaban Mutane ne.

Suna wucewa Ummi ta yi musu sallama bayan ta ajjiye ragowar frames d’in da ta zo da su tace “za ta je ta d’auki k’awarta, sai sun had’u a wajen d’aukar amarya.”

Munirat dama tashi d’aya ta ce mata ”ta tafi kawai, sa had’u a wajen d’aukar amaryar”

Ummi tana wucewa suma suka fara shirin tafiya…

Aisha da Yahanasu za su zauna a gidan har a kawo amarya, Siyama kuma za su wuce gida wajen Manubiya dan an santa ba k’awaye gareta ba so tana buk’atar su.

Jidda ba ta son shiga motar Yassir Siyama ma ta nace itama ba zata shiga motar Najeeb ba.
Allah ya so Siyama Najeeb ya tafi gida yin wanka dan an kusa tafiya d’auko amarya, Yassir ma ya d’an fita shiyasa suka yi wayo suka ce “ba za su iya jira har su dawo ba babu time za a b’ata lokaci, gashi akwai vail d’in manubiya a wajen Siyama kuma yanzu ta kirata tace tanaa buk’ata zata chanja kaya…”
Chapter 37 · 0% Book details