Sashe 6
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Girgiza Kai kawai Ya Musbah ya yi, wanda hakan ya sanya ta d’an lura da zumud’in nata dan haka ta fara kame-kame..ta hau wasa da bakin hannun hijab d’inta. Jidda ma dariya ta yi
kafin ta kalli Baba ta ce
“Baba dan Allah bara in kira Siyama sai mu je tare”
Kamar Baban zai hanata,
sai kuma ya kawar da wannan tunanin, dan a ganinshi ai babu mahaifiyar Siyama a cikin case din..
iyakar da aka yi
‘ tsakanin shi da su Uncle da Baba Habu ne’
shiyasa ya ce mata ‘’to’’ kawai.
…
Sai da suka tabbatar su Innar basa buk’atar komai tukunna suka yi musu sallama suka fice.
Suna fita kuwa Baba ya matsa kusa da Inna saboda dama akwai maganar da yake so ya d’an tattauna da ita akan auren Manubiya kafin su ya Nafi’u su k’araso, suma su tafi….
Da kyar Manubiya ta rarrashi kanta, ta hana kanta kuka a cikin adaidaita sahu…
A ranta ta shiga aiyyanawa
‘kullum shi yake kiranta, da ta ga bai kira ta ba jiyan kamata ya yi ace ita ta nemesa…
Allah dai yasa bai karyeba, Allah yasa bai ji wani mummunan rauni ba!
Allah yasa babu abunda ya samu Yashjub…’
In kuma ta tuno ance ‘driver d’in shi har ya rasu ma’ sai ta ji
gaba daya hankalinta ya sake tashi.
Tsararren private hospital ne mai kyau sosai da had’uwa, sai da suka fad’i sunan shi da number d’akin da yake a ciki
a reception d’in tukunna aka raka su har bakin k’ofar d’akin.
Suna tsayawa a bakin k’ofar d’akin, su Jidda suka tuna ba su siyo kayan dubiyar da Baba ya ce a siya ba, dan haka suka juya da sauri ba tare da sun cewa kowa komai ba!
saboda a yadda Ya Musbah yake a fusace kwana biyun nan sun san in suka ce ‘sun manta!’ sam ba zai yi la’akari da ‘har da shi aka yi mantuwar ba’
zai rufe ido ne ya ci k’aniyar su.
Suna juyawa ya lura dan haka ya juya shima ya bi su da sauri bayan ya cewa Manubiya
“ta shiga suna zuwa’’.
Muhsin ma bin bayan Ya Musbah ya yi dan a yadda ya ga duk sun fita da sauri ya d’auka wani abun ne ya faru…
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 04*
Ji ta yi kamar itama ta juya, dan tashi d’aya ta ji k’irjinta ya fara bugawa..
Da kyar ta samu ta d’aga Hannunta ta d’an yi
knocking a hankali.
Sam bai kawo itace ba dukda kuwa yadda ya ji yanayinsa ya ɗan chanza saboda shi dai ya san bai gaya mata ba.
Jin an sake yin knocking a karo na biyu ne ya sanya shi cewa
“Yea, come in..’’
Ya fad’i
hakan, a ransa kuma yana tunanin wataƙila ko sir Najeeb ne ya dawo ko kuma finally Likitan ne ya zo domin ya sallameshi daga wannan kurkukun…
A hankali ta murd’a handle d’in, ta shiga.
Yana kwance a gefen Hannun damansa mara ciwon, ya d’an
d’ago Hannun, ya na amfani da shi ta hanyar daddana computer da ke akan bedside d’in jikin gadon.
Tana shigowa ya d’ago ya kalle ta, bai san lokacin da ya tashi ya zauna ba, sai kuma ya mik’e tsaye gaba d’ayansa, ya
nufe ta.
Da farko ya d’auka gizo take yi masa, sai da ya je daff da ita tukunna ya tabbatar ita d’in ce.
A hankali ya sa Hannu ya tura k’ofar da ta bari a bud’e tukunna ya ce ’’ya aka yi ki ka sani?’’
Sai a lokacin ta samu ta d’an daidaita numfashi ta, kamar za ta fashe masa da kuka ta ce ’’Mai yasa ba ka gaya min ba??’’
Murmushi ya yi tukunna ya ce
‘’Sorry’’
A hankali ta kalli Hannun, kafin ta d’ago tace masa ’’ mai ya sami Hannun?’’
Dukda yadda ta ji dad’in ganinsa garau a kan k’afafunsa, amma sai da ta shiga tashin hankali daga ganin yadda aka d’aure Hannun nasa.
Yashjub kuwa yadda ta nuna damuwarta garesa abun ba k’aramin dad’i ya yi masa ba, Shiyasa ma ya gagara bata amsa hakanan kawai ya tsaya ya kafeta da idanu yanata zuba mata wani kalar sihirtaccen murmushi.
Kallon sa ta yi taga yadda yake kallonta yana murmushi shiyasa gaba d’aya sai ta jita a takure dan haka sai ta hau wasa da y’an yatsun Hannunta.
Y’ar siririyar dariya Yashjub ya yi kafin ya ce ‘’mu je ki zauna mana’’ daga haka ya d’an matsa ya bata hanya yana mai jin wani farin cikin da ya dad’e bai tsinci kansa a ciki ba.
Ji ta yi kamar ta ce masa ‘a’a bara su Jidda su shigo tukunna’ ko kuma ma kawai su yi sallama ta juya tunda ai ta ga jikin nasa, ita sai yanzu ma lissafinta yake bata yadda ta burkice da kuma yadda ta shigo tsulum ba tare da ta yi kawaicin jiran su Ya Musbah su dawo ba, dan kamata ya yi ace ta jira su ko kuma a d’azun kafin duk su tafi da ko Hannun Muhsin ne ta dan rik’e ta hana shi bin Ya Musbah sun shigo tare….
shikenan yanzu ta san za su ga rashin kararta, in ba da kyar ba ma sun riga sun gano sirrin da ke cikin zuciyarta, shikenan ta tonawa kanta asiri da kanta…
Wallahi ita gaba d’aya hankalinta gaba yayi ne d’azun, shiyasa kwata-kwata bata yi waennan tunanin ba….
So take ta juya kawai ta tafi,
amman kuma still tana so ta ga yanayin jikin nasa, sannan ta ji ya akayi hakan ta faru…tana so ta duba shi sosai. Shiyasa duk yadda ta so sam sai ta kasa tafiya.
D’agowa ta yi ta d’an saci kallonsa…still itan yake kallo yana murmushi, shiyasa ta d’an d’auke idanunta kafin ta wuce ciki ta isa kan kujerar mai jinya ta zauna.
Dariya ya yi kafin ya juya shima ya k’arasa bakin gadon ya zauna, sannan ya ce ‘’Tabbas Likita ya na shigowa zai sallameni, dan yadda kika zauna anan kujerar za ki yi jinya ta! na san ko mintuna uku ba zan k’ara ba zan warke.’’
Sake yin k’asa ta yi da kanta kawai, tana sauraronsa…ita ba abun ta tashi ta koma chan gefe kan sofa d’in da ke cikin d’akin ba dan tunaninta a lokacin da ta kalli sofar ‘kar ta je ta zauna tunda guda d’aya ce shima Yash d’in yace zai zauna akai’ shiyasa ta yo nan tou gashi nan d’in ma ba ta tsira ba, ba ta tab’a jinta un comfortable (ba a sake ba) sosai dashi kamar yau ba!
Dan a kusa da ita sosai ya zauna.
A b’angaren Yash kuwa, so yake ma ta d’an d’ago amma ta k’i, k’arshema gani ya yi ta d’an muskuta ta ja baya ita da kujerar tata sannan ta sake sunkuyar da kanta.
‘’Inaa Yarinya ba za mu yi haka dake ba wallahi’’ Yash ya fad’i hakan a cikin zuciyarshi, a fili kuma sai yace “Auch’’
Da d’an k’arfi.
Da sauri ta mik’e tsaye ta d’an matsa inda yake, kafin ta ce
“menene, me ya faru? Hannun dai?’’
Ta jero masa tambayoyin a gigice saboda yadda ta ga
yana yi kamar irin azabar nan yake sha.
Kamar zai yi kuka ya ce ’’zafi sosai, har cikin zuciyata’’.
Ai kuwa babu shiri ta yunk’ura ta ce ’’Bara in kira Doctor’’
Ta fad’i hakan tana shirin juyawa.
Da sauri ya mik’e ya tare ta ta hanyar tsayawa a gabanta, tukunna ya ce ’’in kikayi murmushi ma kad’ai ya wadatar, zai daina, dama kyaliyar da kika yi min ne ya sanya Hannun ya fara wani irin azababben zugi’’
Shiruu ta yi da farko, sai kuma ta d’ago ta kalleshi, murmushi ta ga yana yi mata, suna had’a ido ya d’aga mata gira d’aya….
Ɓata rai ta yi, sai kuma ta
maida kanta ƙasa a ranta ta ce
‘’lalle wannan Mutumin, da alama garau yake, kawai tab’ara ce yake ji da ita’’.
Murmushi ya yi, kafin ya d’an matso kusa da ita a hankali ya d’an lek’a fuskarta, ya langab’ar da Kai sannan ya ce ’’kuma wai a haka an ƙi ace mun ana sona’’
Ji ta yi kamar ta nitse cikin k’asa, dan haka ta juya da sauri ta bashi baya tana jin yadda yanayin bugun zuciyarta ya sauya lokaci guda.
A hankali ya d’an sake taku d’aya izuwa gareta ya tsaya a dai-dai bayanta tukunna ya ce ’’Manu plsss, jan ajin nan ya fara cutar da ni, ki fad’a min wani abun mai dad’i mana, ko so kike in yi miki kuka tukunna???’’
Shiru ta yi kawai ta kasa cewa komai, dan zuwa wannan lokacin bugun da k’irjinta yake yi ba na wasa bane ba, ba ta jin kalmar ‘A’
za ta iya fitowa daga gareta.
Jin da ya yi ta yi shiru yasa ya ɗan sake matsawa kad’an a hankali dai-dai saitin kunnenta ya ce ‘’dan Allah ki ce kina so na…plss Baby!….’’
Inaa….she can’t take this anymore
(Ba za ta iya ci gaba da jurar wannan abun ba)!
Dan haka da sauri ta d’an yi gaba kad’an, kafin ta juyo da niyyar fita.. wanda ta yi hakan ne gudun karma ta juyo tashi d’aya ta je ta afka jikinsa. Amman ta na juyowa sai ta ga ba hanya dan gefenta fridge ne, d’ayan gefen gado, bayanta kujera, gabanta kuma shi…
Da sauri ta sunkuyar da kanta dan wani irin kallo ta ga yana yi mata, ba ta gama dawowa dai-dai ba ta ga kamar ma tunkarota yakeyi, dan haka ta yi sauri ta d’ago ta ce ’’Allah ya k’ara sauk’i, Allah ya ji k’an driver d’in ka ya sa ya huta, z z an wuce ggi d a….’’ta fad’i hakan cikin in inaa
Tsayawa ya yi chak, kafin ya ce ’’Saboda na ce ki ce kina sona shine za ki gudu??
Haba mana Baby, aure fa za mu yi amman har yanzu ban san matsayi na ba, kuma daga na yi magana sai a fara gudu na…’’
Juyar da kanta ta yi gefe,
tukunna ta girgiza masa kai alamun ‘’A’a’’ kawai.