Sashe 62
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da aka yi sallar isha tukunna Yashjub ya shiga ya gaida Inna.
Tsaraba ya so ya siya musu amman babu lokaci kuma ya lura kamar C I D aka turo Yadira dama shi kuma ba ya son case a halin yanzu, shiyasa sai da ya bari su Manubiya sun dawo daga wajen Aisha dai dai sun zo tafiya kenan tukunna ya damk’awa Muhsin kud’i yace da shi da Siyama da Jidda naira dubu hamsin hamsin….
Ya so ya basu wanda ya fi haka amman ya lura ba lalle su karb’a ba idan ya fi hakan
Dan dubu hamsin hamsin d’in ma sai da ya yi dagaske tukunna Muhsin ya k’arba musu…saboda shi Yaron kud’in ma tsoro suka basa gashi saida Yashjub d’in ya ga su Jiddan sun yi gaba su da Manubiya tukunna ya basa.
Har mota suka rakasu kuwa, Manubiya ta so ta shiga ta ga Mama amman sai Yashjub yace mata “ta bari taa ganta next time yanzu dare yayi, ya na so su yi sauri su je su had’a kayayyakin su saboda gobe siyayya za su yi na tafiya, jibi kuma 6 za su bar k’asar…”
Ba dan ta so ba ta bari akan za ta kira ta ta yi mata sallama, cikin share kwallarta ta shiga motar ta zauna dan tunda aka zo tafiya ta k’ank’ame Inna da kyar ta cika ta, su Jidda suka rakata har mota suka wuce.
Su Jidda sunso su yi maganar da suke son yi da Manu d’in..su samu su tambayeta menene matsalar ta, amman Yadira ta kafa ta tsare….da kyar aka ci sa’a ta gaida Inna, k’iri k’iri da aka zo yin alwallah ta k’i shiga toilet tace wa inna “idan suka k’arasa gida za ta yi”
Babu bak’ar magana babu rashin kunya amma yadda ta dinga wani d’ari d’ari tsaf kana gani ka san kyankyamin gidan take yi, kuma kamar gadin Manubiyan take yi tana nad’ar zance, dan idanuwanta kyar a kan kowa…
A b’angaren Yadira kuwa, tsoron Yash ne kawai ya hanata yi wa su Yasira videon d’akin…ashe daman a inda suka d’auki Manubiya ba nan ne asalin d’akin su ba ma,ashe dama Babanta gurgu ne??..
Shiyasa ta na zama ta zaro waya ta hau watsapp hatta kalar k’ofar band’akin su Manubiya da komai sai da ta zaiyyanewa su Yasira a group…..
….
Washegari da sassafe Ya Musbah ya gagara gane kansa, ko aiki ma ya kasa zuwa, ganin
yana neman mutuwa ne ya sa ya mik’e ya fad’a toilet ya yi wanka dama Muhsin ya dad’e da tafiya makaranta.
Da kyar ya samu ya kimtsa dan kamar muryar Baraka ya ke ji a duk wata kusurwa ta d’akin…a daddafe ya fito ya sakawa d’akin nasu key ya nufi
d’akin su Inna..
ya san Inna za ta ga kamar ya yi mata tsaurin ido, amma kuma hakan shine kad’ai zaɓinsa, bashi da wani zaɓin da ya wuce yin hakan…
A zaune ya sameta tana nad’e kayanta da na Baba, tana gyara musu wajen kayan..
dan Jidda ma bata nan ta tafi makaranta dan har sun koma, gaba d’aya tashi d’aya duk sai ya ji kunyar Innar ta rufe sa amman kuma sai ya kasa hana kansa abunda zuciyarsa ta ke so…….
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 25*
Ganin ya koma ya zauna ya yi shiru bayan sun gaisa ne ya sanya Inna ta ajjiye kayan dake hannunta, ta mik’e ta k’arasa inda yake ta zauna.
A hankali tace”Da!
Na ce ba zan yi maka magana ba nima, amma kuma na ga abun naka kullum k’aruwa yake yi.
Jiya dai Baba ya ce mini yana tunanin matsala kuka samu kai da Nafi’u kwana biyu, duba da yadda kukayi jiya kai da shi a gabanmu, sai dai kuma ni ina kokwanto.
Dan haka inaso Musbahu ya gaya mini meye ne yake damunsa kwana biyun nan?
Ko ya fara b’oyewa Innarsa abu ne bata sani ba?”.
A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa kafin yace
‘’Inna kunyar ki nake ji, shiyasa kika ga na kasa gaya miki,”
da sauri ta kamo fuskar tasa da hannu biyu ta d’ago da shi kafin tace”kunya ta kuma Musbahu?
Ni ce ma kenan silar damuwar taka?.
Gaya mini kar ka d’auki lokaci, Ina sauraron ka, ka gayamin ko ma menene yanzunnan.’’
Ahankali ya Musbah ya kama hannayen nata duka biyu, yana jin wani nauyinta da kunyar ta,
tukunna da kyar kamar wanda dama chan jira yakeyi a tambayesa yace
“Idan na ce inaso in dawo da Baraka Inna za ki iya yafe mini?’’
Ya fad’i hakan kwayar idanunsa suna kallon k’asa.
Ahankali ta zame Hannunta daga fuskarsa ta kawar da kanta gefe.
Da sauri yace
‘’ki yi hak’uri, inshaaAllah ba zan sake yin maganar ba‘’
A hankali ba tare da ta kallesa ba tace
‘’Musbahu mai ka d’auke ni?”
Da sauri ya sake cewa
‘’Ki yi hak’uri Inna, inshaaAllah ba zan sake yin maganar ba har abada, dan Allah ki yi hak’uri’’
Ya fad’i hakan yana mai k’ok’orin mik’ewa.
A hankali ta ruk’o hannunsa ta juyo da fuskarta, ta kalle shi kafin tace‘’Ba ka bani amsata ba!.
Mai ka d’auke ni?”
Ganin ya yi shiru ya sunkuyar da kansa k’asa ne ya sa tace”A tunanin ka idan uwar Mijin Jidda ko Manubiya ta bayar da gudunmawa wajen kashe musu aure murus zan ji dad’i?.
Sannan kana tunanin dama chan Ina farin ciki ne saboda ka hukunta Baraka a ta dalilina?
Bari kaji..Baraka ta yi mini k’ololuwar rashin mutunci, amman a ko da yaushe idan na tuna da mai sunan baba na tuna cewa a ta dalilina iyayensa suka rabu gaba d’aya sai in ji babu dad’i.
Dukda na ji dad’i kuma ka zame mini abun alfahari Musbahu saboda yadda ka nuna b’acin ranka a lokacin da aka wulak’anta ni, na ji dad’i! Na ji dad’i matuk’a! kuma har gobe Ina sanya maka albarka amma kuma idan ka ce za ka dawo da matarka ba zan ji haushi ba, dan Babban burina a yanzu shine in ga kai da k’annenka zaune lafiya a gidajenku..”
Hawayen farin ciki da k’aunar mahaifiyar tasa ne suka shiga sintiri a kan fuskarsa, bai san lokacin da ya rungumeta ba ya ce ”Amman Innaa sai nake gani kamar ban kyauta miki ba…”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta saki murmushi ta d’ago ta kallesa tace
‘’ka dawo da ita, na san yanzu ta kusan fita daga idda ma ko?”
Ba ta jira jin amsar tasa ba ta d’aura da cewa”ni kaina ba son zaman nan naka nake yi a d’aki gabjeje da kai ba.
Ka dawo da ita, ku koma gidanku ku ci gaba da rayuwar ku, Allah ya yi maka albarka.”
Tana gama fad’in haka ta mik’e ta fice daga d’akin ta nufi kitchen bayan ta d’auki mayafinta.
Ya Musbah bai tashi a wajen ba sai da ya maida Baraka,
Cikin tsananin jin dad’i ya mik’e ya fice…wajenta ya fara zuwa ya sanar mata ta yi masa iso cikin gidansu ya sanar da Mamanta, aka kira kawunta a waya dake ba a garin yake ba shima aka sanar masa…tukunna ya wuce aiki daga baya, suna ta murna shi da Baraka.
Sai dare tukunna Innaa ta samu Baba ta gaya masa yadda sukayi da Ya Musbah.
Dama ta san zai yi fad’a shiyasa ta bari sai daren..ai
kuwa ta sha fad’a, dan rabon da Baba ya yi mata irin haka har ta manta.
Jidda kanta ba ta ji dad’i ba
dan ita har ga Allah a tunanin ta Baraka ta tafi kenan..wacce iriyar zuciya ce da Inna haka?
Ta ya za ki bayar da goyon baya d’anki ya dawo da matar da ta yi miki wannaann kalar wulak’ancin….
Kuma ta san Innar ta san Baba ba zai yarda ba shiyasa ta k’i tsayawa a yi shawara da shi ta yanke hukuncin ita kad’ai.
A b’angaren Baba kuwa….ya san idan har zama bai k’are ba to ko yankasu Baraka take yi a da! sai ta dawo.
Dan haka dama shi basa da ma burin raba aurenta da Musbahu murus! rabuwa ta har abada, kuma shi ba wai yanaso ta dawo baneba, kawai dai a nasa b’angaren duk abunda Allah ya tsara tou zai yi maraba da shi…Kawai shi babban abunda ya b’ata masa rai shine yadda aka dawo da ita da wurwuri ba tare da ta gama gane mutuncin iyayensa ba,
dan yanzu ba ta horu ba, ya tabbatar ko da gidan gyaran Hali aka kaita bai ci ace ta yi hankali a cikin wata uku da y’an kwanaki ba.
Saboda Allah tsabar rashin lissafi ace wai duk kalar tujarar da Baraka ta yi amman Musbah ya maido da ita ko idda ba ta fita ba sai kace ƴar gwal!.
Ba kalar fad’an da Baba bai yi ba, daga k’arshe ma kawai ya mik’e zai fita dan takaici yasa yake ji ba zai iya ci gaba da zama a cikin d’akin ba.
Yana Isa bakin k’ofa ya ci karo da Ya Musbah da mai sunan baba. Bai gama k’are musu kallo ba ya ga Baraka a bayan su…da farko so ya yi kawai ya zagayeta ya wuce amman kuma sai ya koma ya nemi guri ya zauna..
To dai Allah kad’ai ya san kalar turare da rubutun da Baraka ta yi sannan ta sha kafin ta zo ɗin dan tashi d’aya zuciyar Baba, Inna da Jidda har ma da Muhsin wanda shigowarsa kenan daga d’akinsu ta yi sanyi.
Har k’asa da durk’usa ta bawa Inna hak’uri tana kuka tana cewa sharrrin shaid’an ne
haka shima ma Baba ta basa hak’uri.
Har Jidda sai da ta bawa hak’uri Akan abubuwan da ta yiyyi.
Daganan d’akin ya d’auki shiru
kafin Baba ya kalli Ya Musbahu yace “ka riga ka maida ita ko?”
Jinjina Kai ya yi alamun ‘eh’
ya na mai jin kunya da nauyin Baba.
Ajiyar zuciya Baba ya sauk’e kafin ya ce”Sai ku tare da wuri,
Allah ya so naga gidan naka babu kowa a ciki”
Daga haka ya fara k’ok’arin fita.
Kamar Ya Musbah ba zai ce komai ba sai kuma ya d’an yi gyaran murya yace
“Wai da sai nan da sati biyu tukunna, dan itama ta samu ta bayar da kayayyakinta gyara nima kuma akwai y’an gyare gyaren da zan yi a gidan.”