Sashe 73
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin son fahimtar da ita Yusra ma tace
‘’Yasmeen tunda har ga abunda Mommy tace miki ki yi kawai mana, kin fi ta sanin daidai ne?’’
Ahankali Yassira wadda tun d’azu ba ta yi magana ba, ta fesar da iska kafin ta kalli Yasmeen ta ce ‘’ki rubuta, za mu je mu siyo yanzu ni da Ya’isha…abun da Babba ya hango k’arami bai Isa ya hanga ba’’
Cikin rashin jin dad’i Yasmeen d’in tace
‘’Wai me yasa baza ‘a samu mutum d’aya a cikin ku wadda za ta kalli issue d’innan daga point of direction d’ina ba! A samu wata ta kalli al’amarin nan ta fuskar yadda na ke kalla, pls??”
Wani wawan tsaki Ya’isha ta ja kafin tace
“Ai dama na riga na sani, na san sai kin yi taurin kan naki da kika saba!
Yasira kawai ki zo mu je zan yi
browsing mu siyo kuma wallahi idan muka kawo dole sai kin yi
dan babu wanda kika Isa ki gwadawa taurin kai anan!.’’
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice fuuuu zuciyarta kamar ta b’ullo waje.
Still cikin son fahimtar da su Yasmeen tace
‘’in da ace mun san zamu aikata haka to da bamu barta har ta rayu dashi a wata k’asa daban ba,
Infact da bamu barta ma ta shigo gidan ba.”
Cikin tarar numfashinta Baba larai tace
“Yasmeen ke shaida ce wanne irin abu ne ba a yi ba amman sai da ta shigo ɗin!
Y’an uwanki da mahaifiyarku sun fi ki gaskiya fa….”
Cikin katseta Yasmeen d’in tace”to Baaba sai ku duba ku ga yadda akayi ta fama d’in amma sai da auren nan ya d’auru, shin ba za ku yi lissafin watak’il wannan cikin shine rabon da ke a tsakanin su wanda Ubangiji ya k’addara sai sun yi auren kuma sai ya zo duniya ba??ba za ku yi tunanin mai za ta kasance da mu idan muka dage muka ce sai cikin ya fita ba??”
Shiruu kawai Baba Larai ta yi tana kallon ta.
Ahankali Yasira wadda itama tun farko tsarin bai yi mata ba tace
‘’Yasmeen ki yi abunda ake so, ki yi kawai!! A iyaka sanina Mommy ta fi ki sanin duk waennan abubuwan dan haka dole akwai abunda ta hango.
sannan kuma inaso ki sani duk yadda za ki so Yashjub bai kai ga yadda ita za ta so shi da shi da abunda zai Haifa ba, dan haka tunda har kika ji tace haka akwai dalili Babba!
We re supposed to stick together
(Kamata ya yi ace mun kasance tsintsiya maɗaurinmu ɗaya)
Yasmeen, kar kanmu ya fara rabuwa tun a nan!
mun fi ki yawa dan haka Ina shawartarki da ki yi hak’uri ki yi abunda kowa anan yake so ayi.’’
Shiruu d’akin ya d’auka kafin chan Yasmeen ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ahankali tace”okay!bara in rubbuto”
daga haka ta juya ta fita.
Ahankali Yasira ta fesar da iska…ta rasa ganin ta inda abunda suke shirin aikatawa ya kasance daidai ya kuma dace ace sun yi!
Tabbas itama a cikin zuciyarta a bayan Yasmeen take d’ari-bisa-d’ari
Amman kuma akwai abunda Mommy ta hango tabbas!
wannan shine dalilinta na bin bayan Mommyn dan ta san in dai Mommy za ta iya cewa a kashe d’an d’an cikinta
to tabbas lamarin Yashjub da Manubiya ya wuce tunanin su,ya fi k’arfin iyakar abunda ta gaya musu suka sani.
………..
Bayan kamar 40 minutes,
Su Yashjub suna zaune har da Yahanasu wadda ta kawowa Mannubiya tea take sha, suka ji ana knocking.
Sai da Yashjub ya kalli wayarsa ya ga likitan bai kira sa ba, tukunna ya kalli Yahanasu yace “ta bud’e, maybe su Mommy ne”
Ai kuwa tana bud’ewa suka yi
Ido biyu da Yasira Yasmeen da Ya’isha.
Ba musu ta matsa musu suka shigo..sai da suka fara yi wa Manubiya ya jiki tukunna Yasmeen tace “Mommy ce tace in zo in duba ta”
Cikin tarar numfashinta Yahanasu tace
“Ai Likita yana hanya”
Murmushi Yasira ta yi, ta matsa kusa da Yashjub da Mannubiya waenda suke zaune a bakin gadon tace’’Manu, ya akayi kika bari ya kira Dr bayan gamu da soon to be consultant a gida?.
Yasmeen matso ki duba ta, Mommy tana jira, ta ce in ta kama sai a wuce asibiti.
Gaba d’aya hankalinta har mu duk a tashe yake…aman da ta yi ai dole a dubata da wurwuri ta yadda in ma k’arin ruwa ne ya kamata sai a yi mata, dan na san she’s weak(ba ƙarfi a jikinta)”
Shiruu Yashjub ya yi, kafin chan ya d’ago ya cewa Yasmeen d’in “matso mana, mai kike jira?”
Sai kuma ya kalli Ya’isha yace
‘’ki je ki cewa Mommy jikin nata fa da sauk’i, ta kwantar da hankalinta”.
Murmushi duk suka yi banda Yahanasu wadda gaba d’aya hankalinta yake a tashe!
Har ga Allah ta gama shiryawa akan ko da ace cikin ne to za ta san yadda za ta yi ta lallab’a Yashjub su b’oye har sai ya d’an yi kwari tukunna a fad’a,
amma gashi yanzu su ne ma za su fara sani!
Sannan yadda suka dad’e a saman nan ba su sauk’k’o ba bata da tantama plan suka gama had’awa….
Tana wannan tunanin ta ga Yasmeen ta matsa kusa da su ta shiga duba Mannubiya…dama har da abun auna hawan jinin ta ta taho da ragowar abubuwanta…
Duk wani gwajin da ya kamata sai da Yasmeen ta yi mata.
….Tun a kan pulse d’in Mannubiya Yasmeen ta jiyo alamun ciki ga kuma ragowar gwaje-gwajen da ta yi mata waenda suma suke nuni da hakan,
shiyasa tashi d’aya gabanta ya yanke ya shiga fad’uwa dan ba ta san ya za ta yi ba, sannan ba ta san ma ta Ina za ta fara ba…
Cike da murmushi da tsantsar farin cikin da ya baiyyana a iyaka kan fuskarta Yasira ta matso ta ce ‘’good news ko? pls tell me I’m about to become an aunt(dan Allah yi maza ki sanar mini cewa na kusan zama anty).’’
Ta k’arashe maganar tata da y’ar guntuwar dariya kwance a kan fuskarta.
Murmushi Yashjub ma ya yi, yana jira kawai ya ji ance masa Mannubiya na d’auke da ciki ne, amma maimakon hakan sai kunnuwansa suka jiyo masa muryar Yasmeen d’in tana cewa
“A’a gaskiya, ba ciki bane ba, dan in da ace shine to da zan ji yanayin pulse d’inta ma ya d’an chanja, sannan ragowar gwaje-gwajen da na yi mata suma duk ba su yi detecting pregnancy ba, inaga gajiya ne da fever…
Amma yanzu abu na farko da ya kamata.. bari in fara yi mata allurar tsaida aman nan, saboda da na duba idonta gaskiya she’s very weak sannan bp da ruwan jikinta ma duk suna nuna za ta iya faɗuwa daga yanzu zuwa ko wanne lokaci….!”
Gaba d’ayansu jikinsu sanyi ya yi musamman ma Yashjub wanda ya gama kwallafa rai ya gama yarda akan kawai cikin ne, ganin yadda Mannubiyan ta yi ne ya sa cikin son bata kwarin guiwa ya samu dakyar ya aro jarumta yace
“ok, dama nima na yi tunanin gajiyar ce, a ina za’a siyo allurar?
A samu a yi mata da wuri, a samu ta d’an ci wani abun ta kwanta ko?”
Cikin tarar numfashinsa Yahanasu tace‘’Ina ga gara dai a jira Doctor d’in ya zo shima ya dubata tunda kaga shi Babba ne!
sai a san da me da me ya kamata a bata.”
Da sauri Yasira tace ‘’ba ki ji abunda itama Yasmeen d’in tace ba?
Iyaka allurar tsaida amai za ta yi mata saboda itace emergency ana buk’atar a tsayar da gaggawa.’’
Cikin katseta Yahanasu tace’’Yasira allurar tsaida amai fa tanada k’arfi sosai! ki bari a yi kwak’kwaran bincike kafin a fara d’irka mata abubuwa’’
Murmushi Yasmeen ta yi sannan tace
“Na yi duk gwaje-gwaje fa!
In da ace akwai ciki ko na sati d’aya ne to da zan gani zan kuma fahimta, kar ki manta Gynea na yi specializing a.
Also allurar da zan yi mata yanzu ba ta da wani k’arfi iyaka tsayar da aman za ta yi.’’
Zuwa yanzu ran Yahanasu ya b’aci, kuma ta sake tabbatarwa akwai abunda suka shirya dan haka tace
‘’Ai nima ba cewa na yi ciki ba, cewa na yi ki tsaya dai a yi kwakkwaran bincike, dan wannan gwajin da kika yi bai kai ace ya yi detecting komai b..’’
A hankali cikin katseta Yashjub yace
‘’Yaha Mommy ce ta aiko su kar k….’’
Juyawa kawai ya ga Yahanasun ta yi ta fice daga d’akin da alamun ranta ya b’aci.
Shiruu kawai Yashjub ya yi,
sam bai ji dad’in abunda ya yi mata ba, amma kuma ba ya so Mommy ta yi fushi..
Shiyasa ya bari akan idan su
Yasmeen d’in sun gama zai je ya bata hak’uri, gara ace ita ta yi fushi ta bar case d’in akan su Yasmeen su je su gayawa Mommy ta ga kamar ya sace mata guiwa ne daganan ta yi fushi.
Tunda sun ce ita ta turo su, kuma ta na chan hankalinta a tashe, to ya san idan ya hana su bazata ji dad’i ba…
Gara Yahanasu ya san ita za ta fahimcesa idan ya je ya bata hak’uri zuwa anjima…
Iyakar abunda ya sani ya ke kuma da yaƙini akai shine ‘su Yasmeen ba za su tab’a yi masa k’arya ba, kuma ba za su cutar da shi ko Mannubiya ba…’
dan ko kwanaki da aka yi ta case yanzu ya fahimci saboda Kausar suka yi ta abubuwa amma yanzu gashi da ya dage da addu’a ai sun shiryu sun dawo saiti dan yadda suke yiwa Manubiya tun zuwansu ɗinnan har kawo yanzu ya ji dad’i kwarai ya fahimci suna sonta yanzu….shiyasa har ga Allah tunda suka ce ‘babu ciki’ shi kuma ya yarda, kuma ba ya so ma wani likitan ya zo ya kuma duba ta ya ce ‘babu cikin’ saboda shi kad’ai ya san kalar disappointment d’in da ya ji a lokacin da Yasmeen tace ‘babu cikin’….
ya san kuma a b’angaren Manubiya itama hakan ne…..
Da waya Yasmeen ta kira Yusra tace ‘’dan Allah ta duba cikin bed side d’inta na left, akwai wata green Leda ta d’auko ta kawo mata…
Allurar tsayar da amai ne a ciki da su paracetamol”.