← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 152

Sashe 94

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsabar tashin hankali sumewa ta yi,ruwan da Mommy ta shek’a mata ne ya sa ta farka a gigice!!! chan ta hango Daddy ya nufo ta gadan gadan da wuk’a a hannunsa kafin ta yi wata wata har ya Burma mata a ciki………
Sama sama ta ke jin Mommy tana kuka tana rok’on Daddy tana cewa”kar ka yi haka Daddy,Ubangiji kad’ai ne ya Isa ya yanke hukunci, kar ka yi abunda zaka kai kanka prison, ka bud’e musu su fito dan girman Allah…..”
K’aurin wuta ta fara ji kafin hayak’i dga haka ta ga wuta tana ci wanda hakan ya tabbatar mata tabbas Daddy wuta ya cinna musu.
Kamar d’azu yanzun ma ba ta yi yunk’urin yin komai ba dan ba za ta iyaba gashi jikinta ba kwari,ba ma ta gani sosai ga tashin hankali..ko yatsarta ba ta iya d’agawa.

…..Ba ta san Ina Mallan lawal ya yi ba ita dai ta ji an d’auke ta sannan muryar wani yana cewa”ta nan za ku bi”
Wanda har gobe ta kasa tantance muryar mutumin ballantana ta yanke hukunci.

A cikin wani d’an madaidaicin gida ta farka ta ganta, ana yi mata k’arin ruwa, ga likita a gefenta da mallan lawal.

Rufar mata suka yi suna tambayar ta ya jikinta, itakam bak’in ciki da tsananin tashin hankalin da take a ciki ma bai barta ta ko kallesu ba…duddubata likitan ya yi ya cewa mallan lawal “idan wani abun ya tashi ya nemesa” daga haka ya yi musu sallama da Allah ya k’ara sauk’i ya fice.
Yana fita mallan lawal ya gyara zama ya fara magana”Khadija ki yi hak’uri dan girman Allah..wallahi sharrin shaid’an ne, amma inaso ki san cewa babu abunda ya shiga tsakaninmu dan ko da na yunk’ura kasa aikata komai na yi a gareki….na san kin tsaneni ba kya son jin ko murya ta ma shiyasa na zab’i in yi nesa da ke daga yau har abada.
Ga gida nan ki zauna a ciki kar ki tambayeni a ina na samu kud’in kawai inaso ki san wannan gidan naki ne, ga takardun nan a cikin wachchar drawer!ki yi hak’uri ki yi hak’uri ki yafe mini dan girman Allah”.
Yana gama fad’in haka ya mik’e yace mata”a cikin garin Abuja muke ba a kano ba.”
Daga haka ya sa kai ya fita.

Sai da ta tabbatar da ya yi nisa tukunna ta mik’e tsaye..d’inki ne a cikinta amma kawai tsintar kanta ta yi da fara takawa a hankali a hankali a haka har ta fice daga d’akin ta fice daga cikin gidan gaba d’aya,ta ya ma za ta fara zama a gidan da lawal ya ajjiyeta?! ba zai yiu ba!.
Dare ya yi a lokacin gashi unguwar shiruu babu ma mutane sosai…..
Tafiya kawai take yi ba ta san ina za ta je ba, ba kuma ta san abunda ya kamata ta yi ba…wani ikon Allah zuwa yanzu ta nemi zafin da cikin nata yake yi ta rasa, amma kuma ko ba ta kalla ba ta san d’inkin ya warware dan tana jin yadda jini yake bin jikinta…ta lura da yadda wata mota take ta binta a hankali, sai da aka yi kusan tafiyar minti ashirin da mutumin ya ga ba ta da niyyar tsayawa gashi sai faman zubda jini take yi tukunna yayi parking motar a daidai gabanta ya fito yana k’are mata kallo.

Sai a lokacin wata juwwa ta kwasheta ta tafi ta zube a wajen.

Sai da ta yi kwana huɗu tukunna aka samu ta farfad’o da mugun kyar.

A asibiti ta bud’e ido ta ganta,wannan mutumin da ya tsinceta ne yake sanar da ita cewar”kwananta hud’u da kyar aka samu ta farfad’o a ranar.”
Babu yadda bai yi da ita akan ta gaya masa inda family d’inta suke ba amma ta k’i magana..ganin kamar ba ta ji kuma ba ta magana ne ya sanya ya hak’ura ya rabu da ita ya had’a ta da nurses ya biya kud’in komai yace “idan akwai emergency a kirasa”daga haka ya tafi.

Duk yadda ya so ya manta da al’amuranta sam sai ya gagara,gaba d’aya tausayinta ya hana sa sukuni lamarinta ya tsaya masa a rai..ya san tabbas tanada buk’atar taimako.
Ba a yi sati uku da rasuwar k’anwar sa ba, wadda su ka yi wa aure suka kai garin jos!! ashe mijin ba zaman adalci yake yi da ita ba, k’arshe sai ciwon zuciya ne ya kasheta…..
Mahaifiyarsu ta rasu kuma su biyu ne kad’ai shiyasa har gobe yake blaming kansa dan in da ace yana yawan zuwa dubo ta kuma ya saka idanu a kanta to da hakan ba ta faru ba.

Sai da ya tabbatar ta warware ta fita a shock,na kusan wata ɗaya tukunna ya koma,a lokacin ta warke amma wani ikon Allah damuwa ko kad’an ba ta barta ba asalima kuka ya je shi ya tarda ita ta na yi.
Ya kad’u sosai da lamarinta dan haka bayan sun gaisa ya amsa godiyar da ta yi masa da kulawa ya zauna ya shiga tambayarta “menene matsalarta har haka?,kar ta damu ta d’aukesa a matsayin yayanta ta fad’a masa komai.”
Sau uku tana bud’e baki da niyyar bashi tarihinta amma tana fara cewa”Mijina ne…”
Sai kuka ya ci k’arfinta……
Zuwa yanzu ya fahinci inda gundarin matsalar take shiyasa kawai ya ce “ta yi shiru…..ta yi hak’uri, ko ma me ya yi mata ta yi hak’uri Allah zai saka mata.”

Sai da ya tabbata ta d’an nutsu tukunna yace”akwai wanda take so ta kira a cikin y’an uwanta?”
Ba b’oye b’oye tace masa ”ba ta da kowa”

Jinjina kai ya yi yana mai jin tsananin tausayinta,haka kurum take tuno masa da marigayiya k’anwarsa tun ba ma da ya ji itama sunanta Khadijah kamar k’anwar tasa ba.Ya jima yana nazari kafin yace”kina buk’atar ganin shi Mijin naki ne?a nem…”
Tun kafin ya rufe bakinsa tace”A’a”
Dan ba wai iyaka Lawal da ya k’ulla mata sharri take jin haushi ba har da Imam wanda ya yarda ya aminta ta aikata abunda aka nunawa idanunsa bayaga haka kuma ya hari rayuwarta.

“In kai ki Gidana za ki taya matata zama?,Dr ya ce mini a yau zai sallameki inshaaAllah”
Muryarsa ta katse mata tunani.
….Da farko k’in amincewa ta yi tace”ya barta a asibitin ko kuma ya barta ta tafi kawai za ta san abunyi.”Shi kuma ya k’i, dan a yadda take da damuwar nan idan ba ta samu wani da zai yi mata gata ya tsaya a kanta ba tabbas akwai matsala, shi kuma haka kurum ya ji yana so ya taimake ta, kuma yana so ya yi making up to negligence d’in da ya yi (biya bashin sakacin da ya yi) wa sister d’insa, shiysa ya nace ya k’i barinta har sai da ta amince ta bisa suka tafi gidan nasa.

D’ansa d’aya mai suna Al’ameen da matarsa suna ce mata Ammi, dan shima mai gidan sunan mahaifiyar sa ne da matar tasa.
Dama tun farko Ammi ta fara nuna kishi da Khadija dan ce mata ya yi y’ar uwarsa ce cousin za ta zauna da su. Daga baya kuwa da ya fad’a mata gaskiya dan shi bayason b’oye b’oye,da kuma itama y’an uwanta suka zugata shikenan ta fara hauka!……har ta yi haukar ta kuwa ta saduda babu wanda ya biyeta,ita da kanta ta zauna ta yi lissafi mai kyau ta nemi gafarar mijinta da khadija aka zauna lafiya, dan a lokacin sun kusan shekaru shidda tare shiyasa lissafinta ya bata inda ace fa aurenta zai yi tou da tuni ya aura.Kuma yadda Khadija take kula mata da Al’ameen ko ita ba ta kula da shi..mai d’a wawa!ta haka Khadija ta siye zuciyar Ammi gaba d’aya.

A kwana a tashi zama ya dawo da su Kano.Sai a lokacin Khadija ta gaya musu tana da y’a Yahanasu.
Addu’ar ta d’aya Allah ya sa ba a chanja musu makarantar da ta san an fara saka su ita da Yashjub tun farko ba,dan haka suka tambayi baban Al’ameen suka tafi ita da Ammi.
Ba su sha wahala ba dan tashi d’aya matar ta shaida ta ta amsheta hannu bibbiyu har da hawayenta tana cewa”ai ce musu aka yi ta rasu,amma ta je gida an ganta?ko dai nan wajen Yahanasu ta taho direct??ta je su ganta suma hankalinsu ya kwanta waye waye…”
Ita dai Khadija ce mata ta yi tou kafin tace”a kawo mata Yahanasu da Yashjub.”

‘Yashjub ai ya dad’e da komawa Uk,amma Yahanasu dai tana nan,da tare take ma da siblings d’inta, to yanzu bamu da nursery section sakamokon gobarar da muka yi shine aka chanja musu school.”
Matar ta faiyyace mata hakan tana mai fita domin ta je ta taho mata da Yaha.

Sai da Khadija ta yi kuka,saboda da kyar Yahanasu ta shaida ta.
Tana murna tana kuka kamar ranta zai fita haka ta mak’alk’ale y’ar tata.

Hatta Ammi da mai makarantar sai da suka yi kuka..

Tun daga ranar duk ran Jumaah kafin su d’auki Al’ameen a school sai sun biya sun ga Yahanasu,Yarinyar ta shak’u da mahaifiyarta sosai zuwa yanzu….Khadija Ammi da Baban Al’ameen suna shiryen shiryen zuwa su je a yi magana ta fahimtar juna a samu Imam ya bawa Khadija Yahansu kwasam rannan sun je mai makarantar tace “Mahaifin Yahanasu yace idan ta sake barinta ta shiga makarantar sai ya k’ulle ta!.
Dan Allah dan Annabi ta yi hak’uri ta tafi kuma yace idan har ta sake zuwa kusa da y’ar sa wallahi kowa sai ya ji kansu kuma kowa sai ya ji abunda ta aikata har ita y’ar tata”…

….Babu kalar tambayar da su Ammi ba su yi mata ba a kan ta yi musu k’arin bayani amma ta k’i cewa komai,Baban Al’ameen da har yana shirin shiga kotu a samu a kwato mata y’arta amma ta hana ta kuma rok’esu akan kar su sake yin maganar a bari ya wuce kawai…Zuwa wannan lokacin sun riga sun san Khadija sun san ba muguwa bace ba kuma ba ta da wani mummunan hali,shiyasa ba su dasa ayar tambaya a kanta game da hakan ba kuma suka bar maganar ya wuce kamar yadda ta rok’a ta buk’ata.
Chapter 94 · 0% Book details