← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 152

Sashe 27

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar yadda ta fita ta bar su Jidda a zaune haka ta shigo ta same su, sallama kawai ta yi suka amsa daga haka ta nemi guri ta zauna, suna ganin idanunta suka fahimci kuka ta yi….sun san idan suka fara bata hak’uri sake b’arkewa za ta yi da wani kukan shiyasa suka ja bakunansu suka yi shiru, amma dukda haka ba su tsira ba dan kamar wadda aka daka hakanan ta fashe musu da kuka tashi d’aya. Wanda hakan ya yi dai-dai da shigowar su Aisha da anty umma da Mama da inna cikin d’akin….

A hankali Aisha ta zauna a kusa da ita, ta kamo Hannayenta tukunna ta ce ”haba mana Manu, kanki fa zai yi ciwo, ki yi hak’uri haka nan mana, ke ki godewa Allah ma a garin za ‘a ajjiyeki waenda ake d’aukar su a kai su wani garin daban su kuma su ce me??”

Cikin karb’ar zancen anty umma ta ce ”wasu ma k’asar gaba d’aya ake bari da su, kuma haka suke zuwa su zauna su rayu, ke kam gidanki ko da k’afa idan Mutum ya zage tsaf zai je, ki yi hak’uri ki yi shiru karki ja wa kanki zazzab’i.
dama indai sunan ki Mace to wannan rana tana jiranki……

mu kanmu sai hankalinmu ya fi kwanciya idan muka kai ki d’akinki gobe inshaaAllah, fatanmu shine ki yi biyayya ki nuna cewa mun baki tarbiyya mai kyau.”

Kamar zuga Manubiya sukeyi haka ta sake fashewa da kuka, shiyasa suka hak’ura suka kyaleta…
anty umma suka fita ita da inna dan su ci gaba da shirye-shiryen gobe, Mama kuma Ammi ta kirata tace “ta zo ta taya ta girki tana da bak’on cikin dare, yau.”

Suna fita d’akin ya rage daga Manubiya sai Aisha
Siyama da Jidda…
Sai da Aisha ta lallab’a Manu aka samu ta yi shiru da kyar, tukunnan ta bud’e mata abunda ta shigo mata da shi
a flask ta bata ta ce “ta ci.”

Har ga Allah kayan nan sun fara Isar Manu dan wani irin ciwon mara take yi amma ta san ba ta Isa ta cewa Aishar A’a ba shiyasa ta hak’ura da kyar ta danna tana ji kamar za ta yi amai, marar ta kamar za ta fashe.

Ahankali ahanakali Aisha ta samu ta d’an kwantar mata da hankali tukunna Manubiya ta d’an sake…..ana fara kiraye-kirayen sallar magrib kiran wayar Yash ya shigo wayarta, ta yi mamakin ganin kiransa a dai-dai lokacin sallah amma sai ta d’auka cikin sanyin murya ta gaidashi,
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ”lafiya
Alhamdulillah”
Kafin ya d’aura da cewa “yau na shiga busy ban samu na dame ki da kira ba,”

Murmushi kawai ya ji ta yi a hankali

Shiruu ya yi kamar mai nazartar wani abun kafin ya ce “wa ya saka min ke kuka??.
Fad’a aka ta yi miki ko?”

A hankali ta sake yin murmushi kawai. Numfashi ya sauk’e kafin ya ce ”Aikuwa yanzun za’a sake yi mana wani, dan na san nasiha Baba zai yi mana, ya kirani akan yana buk’atar ganin mu a tare.
Ina ma unguwar ya ce bayan magrib zai ganmu.”

Maganar sa ce ta katse jin ana shirin shiga sallah, shiyasa ya yi mata sallama ya ce ta zama
ready suna idar da sallah Baba zai gansu.

Sallah ta fara yi, tukunna su Aisha suka taimaka mata ta chanza kaya zuwa super(exclusive)black colour d’inkin riga da zani, da ash chantily vail mai kyau, kauri da tsada!.

D’aurin gaba ta yi irin kalar wanda ake yayi, ta rufa mayafin nata har ka, kana ganinta ka ga amarya dan ta fito rass da ita kamar ka sace ta ka gudu saboda tsabar tsananin kyau da haiba.
Tana cikin gyara sakun d’an kunnen ta Ya Musbah ya lek’o ya ce ta zo su je ita ake jira.

Sai da ya kaita k’ofar parlourn su Siyama tukunna ya juya…ya so ya shiga ciki shima amma sai ya zab’i ya koma masallaci domin ya samu su rik’e Kaka Mallan a chan, dan tunda ya ga Yash ya zo gaba d’aya hankalinsa ya tashi!!! Dan haka sun san indai ya shigo cikin gidan to sai ya je inda yake, su kuma ba sa so ya je gudun kar ya kwafsa, shiyasa da shi da ya Nafi’u suke ta jan sa da zance tunda yanzu yana kula su yana ji da su….dan su samu su yi buying time ma (su jaa lokaci saboda) su Baba..

A zaune suke akan carpet su biyu suna magana, Yashjub sai wani sussunkuyar da Kai yake yi, amman ta na yin sallama bai san lokacin da ya d’ago ya kafeta da idanuwa ba…
Har ta k’araso ta zauna bai daina kallonta ba sai da ta ce ”ina wuni tukunna ya yi snapping out (ya ɗan dawo dai-dai) da kyar ya ce “lafiya”
daga haka ya sunkuyar da kan nashi k’asa yana mai jin wani yalwataccen farin ciki yana ratsasa ta koina…..

…Nutsatsiyar nasiha Baba ya yi wa Yashjub da Manubiya tare da fatan alkhairi da sanya Albarka,
Daga nan ya bawa Yash d’in amanar Manubiya……

Hatta Yash jikinsa sai da ya yi wani irin sanyi, Manubiya kam tun lokacin da Baba ya fara magana ta fara kuka.

Sosai kukan nata da nasihar Baba suka taru suka kashewa Yash jiki, shiyasa ya gagara d’agowa yana jin kamar shima ya fashe da kukan.

Sai da aka kiran sallar isha tukunna Baba ya sallameta shi kuma suka wuce masallaci shi da Yash.

Tana shiga d’akin nasu Aisha ta dafe Kai ta ce “shikenan an dawo mana da aiki sabo”

Murmushi su Inna da Siyama suka yi, daga haka suka ci gaba da had’a jakar takeaway d’in da za a raba gobe inshaaAllah a wajen d’aurin aure.

Kamar d’azu, yanzun ma
Aisha ce ta yi ta aikin rarrashi, musamman ma da ta tab’a jikin Manu d’in ta ji zafi rad’au, nan take hankalinta ya sake tashi……

Da kyar kuwa Manubiya ta samu ta yi sallah, dan tashi d’aya zazzab’i da ciwon Kai suka yi mata rufdugu, shiyasa Aisha ta ja ta zuwa d’akin su Ya Musbah, ta bata magani ta sha tukunna ta ce “ta kwanta anan”dan d’akin nasu ya cika da makwaftan da suka lek’o taya su aiki.

Ba ta dad’e da kwanciya ba, bacci ya yi awon gaba da ita dan har da maganin bacci Aisha ta had’a mata da shi, ai kuwa kasancewarta a gajiye kwana biyu ya sanya nan da nan baccin ya d’auke ta.

Ko da Yash ya kira Aisha ce ta d’auka, yana ji Aishar tace ta yi bacci ya ce “Alhamdulillah”
dama aikin rarrashi ya so ya yi kafin ya wuce amma tunda har an lallab’ata ta yi bacci shikenan, dan haka ya yi wa Aishar sallama da godiya, daga haka ya kashe wayar ya wuce bayan yayi sallama da su Baba da Kaka Mallan………

*Washegari*
A d’akin Ya Musbah Aisha Manubiya da khairat suka kwana, dan tunda Manu ta kwanta sai kiran sallar asubah ne ya farkar da ita, Aisha bata so ta tasheta shiyasa ta cewa su Ya Nafi’u su tafi da shi da su Muhsin da Ya Musbah kawai dan yau d’akin nasu is occupied.

Tana farkawa ta hango Aisha a kan darduma tana nafila, dan haka itama ta mik’e ta fad’a toilet…ta kama ruwa ta yo alwallah bayan ta d’auraye Bakinta da iyaka makilin d’in da yake available a cikin banɗakin tukunna ta fito tana jin yadda Jikinta yake yi mata ciwo, dan ba ta saba kwana da manyan kaya ba.

Har ta fito Aisha ba ta Ida ba…

darduma itama ta nema ta shimfid’a a gefen Aishar, sannan ta tada ik’ama domin gabatar da nafila….ta na idarwa aka kira assalatu dan haka ta mik’e ta gabatar da sallar asubah….
Sai da suka kammala Azkar tukunna suka gaisa ita da Aisha, ta bata wayarta..miscalls d’in Yash ta gani na jiya kafin Aisha ta d’auka sai wanda ya kirata around sha biyu na dare da kuma yanzu da asubah.

Sai da ta fara cire wayar a silent tukunna ta kira sa…ringing uku ta yi ta kashe dan ta san ko ta bari ya kai k’arshe ba d’auka zai yi ba.

Ko gama haske wayar ba ta yi ba ya biyo kiran, sai da ta d’an d’auki lokaci dai-dai wayar tana shirin tsinkewa tukunna ta amsa.

Murmushi ya yi kafin ya ce ”sai an ja min aji tukunna za’a d’auka? Kar ki damu gobe by this time (iwar haka) na san babu maganar jan aji ko kunya a tsakanin mu dan tuni zan yi fata-fata da su.”

Da sauri cikin san kawar da zancen tace”Ina kwana”
Ta fad’i hakan a ranta tana mamakin Yash! Wanda a da kamar ba ya magana amma ta lura tun lokacin da aurensu ya matso ya zama mai surutu, kuma ko wacce iriyar magana in ta zo Bakinsa juye mata ita yake yi, gaba d’aya ya daina jin kunyar ta.”

Ta na cikin wannan tunanin ta ji ya ce ”lafiya Alhamdulillah, matar Yash in the next (nan da) 5 hours!7 minutes!37seconds inshaaAllah.”
Chapter 27 · 0% Book details