Sashe 42
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
….
Ko da su Yasira suka fito daga motocinsu babu wadda ta iya cewa k’ala har Baaba Larai, hakanan suka nufi cikin gidan kowa da abunda take sak’awa a cikin ranta…..ba k’aramin dad’i suka ji ba da suka hango Daddy zaune a main parlourn k’asa yana kallo, tashi d’aya Ya’isha ta k’ak’alo hawaye ta k’arfi da yaji, ganin haka ya sa su Yusra yin kalar tausayi suma.
Yanayin su kawai Daddy ya kalla ya fahimci akwai matsala, shiyasa ya kafe su da idanuwa har suka k’araso suka shiga gaishe sa!
Bai amsa gaisuwar tasu ba sai tambayarsu da ya shiga yi akan “mai ya faru?”.
nan kuwa suka zauna suka shirya masa k’arya da gaskiya…
A haka Mommy ta sauk’o ta samesu, ba k’aramin dad’i ta ji ba da ganin yadda Daddyn ya fusata matuk’a….ya na jinjina maganar tana kuma yi masa zafi…ta ya ana bikinka zakace ‘k’annenka kar su kai Amarya’ har da wani ‘kar suje masa gida’!. Tabbas da sake
dan ba zai yiu ba,dole ya san abunyi!, bai aurowa d’ansa wadda zata raba masa kan ya’ya ba wallahi…!
Hatta Baaba Larai zagewa ta yi suka yi ta shirya labarai ba kunya ba tsoron Allah dan ta san Daddy ba zai yi titsiye ya ce zai bi diddigi ba shiyasa suka shirga k’arya kala kala,
kuma duk a bayanin nasu suna yi ne akan wai rashin fahimta suka samu su da k’annen Amaryar shine Yashjub ya bi bayan k’annen Matarsa har ta kai sa ga hanasu zuwa kai amaryar.
Sai da suka tabbatar Daddy ya hau ya zauna daram! Tukunna
kowacce ta zame ta wuce
ciki.
Dukda bak’in cikin dake k’unshe a cikin zuk’atansu game da auran da Manubiya da Yashjub d’in kansa sai da suka ji kamar su taka rawa, dan a yadda suka ga yanayin mood d’in Daddy
sun san gobe akwai case!!!!
Direct d’akin Mommy Baaba Larai ta wuce, a tsaye ta same ta kamar yadda ta yi zato, dan ɗazu suna tsaka da magana ta yi excusing kanta ta hawo sama…
Baba Larai tana shigowa Mommyn ta k’arasa inda take tace”Ya ake ciki?”
Tiryan-tiryan Baba larai ta zaiyyano mata yadda suka yi na ƙoƙarin ganin sun yi ammman Yahanasu ta kafa ta tsare ta hana a yi komai….
Dab’ass!!!
Haka Mommy ta zauna akan gado ta yi shiru kawai dan ta ma rasa me zata ce.
Ajiyar zuciya Baaba Larai ta sauk’e kafin tace
“Ki yi hak’uri, wallahi d’azu shiyasa da suka zo chanja kaya na k’i yarda in shigo
saboda banaso in baki mugun labari….so na yi idan aka tafi kaita ko da ace ta riga ta shiga gidan ne in samu in yi dan da babu gara ba dad’i to sai kuma Yash d’in ya hanamu kai Amarya.
Amman kar ki damu, na hango mana wata hanyar da za mu iya bi cikin sauk’i mu yi nasara a kanta, shiyasa ma kika ga na hawo da kwarin guiwa ta.”
Ba ta jira jin me zata ce ba ta d’aura da cewa
“Yanzunnan yanayi da mood d’in da Daddy ya shiga daga jin bayanin su Yassira ya sanya na fahimci idan akace Yashjub da Matarsa su dawo cikin gidannan da gudu zai yarda…Daddy yana son Yash matuk’a na san dan babu yadda zai yi ne shiyasa tun farko ya barsa ya je ya tare a wani waje daban, amman in ta shine bai k’i su zauna a nan a bangaren Yashjub d’in ba kusa da shi tunda akwai space……yanzu a yadda na lura da shi ya fusata sosai ɗinnan iyakar abunda kawai ya kamata mu yi shine mu kuma d’aura sa akan ‘idan ya yi sake to Manubiya da y’an uwanta za su kwace masa d’a!’,
ke kuma sai ki tado da maganar dawowar ta su nan, daganan inshaaAllah za ki ga yadda al’amari zai chanja, ni kuma daga nan zan karb’i aikin kuma muddin ta dawo nan d’in wannan karon kam InshaaAllah bazamu samu failure ba. Dan zaman ta a kusa da mu kamar k’arshen ta ne, tunda kinga ga ni!
sannan ga Yaran nan waenda na san ko ba komai takurawa da baƙin cikinsu kaɗai ya isa ya korata…
Sannan kinga duk wani abun da ba mu samu mun yi na yau ɗin a chan gidan nashi ba sai mu yi a nan inda zata zaunan, kafin ta taren. dukda dai na yau ɗin ya fi tunda shi aka fi buƙata a yi a yau(ranar shigowarta gidansa ta farko) amma da babu gara ba daɗi, sai a jarraba a gani..”
Ita dai Momy da “to” kawai ta bi Baaba larai da , dan ba kad’an ba ta ji haushi kuma ta tsorata da ta ji tace “ba su yi komai ba”
a ganinta tunda har basu yi d’in ba kuma ga abunda ita kanta baba larai d’in ta fad’a da farko akan abun to fa babu wani abu da zasu yi daga baya wanda zai yi tasirin da za su samu nasarar cire Manubiya a gidan….da sauri ta kawar da tunanin gudun ma kar tunaninta ya tabbata dan idan ya tabbata bata san kuma ya zata yi ba….cikin son bawa kanta kwarin guiwa ta d’aura gaba d’aya hope d’inta akan zancen dawowar Manubiya da Yash ɗin kusa da su. Sannan tana addu’ar Allah ya sa abunda su ka yi ya zauna a jikin Yash, Allah kuma ya sa ya riƙesa har su dawo gidan nata da zama dan yadda ake ɗokin amarcin nan dukda Baaba Larai ta tabbatar mata amma tana tsoron kar su je Manubiya ta samu ciki kafin ta dawo cikin gidan da zama...dan muddin suka dawo kusa da su ɗin to kamar yadda Baba Larai ta ce komai zai zo musu da sauƙi ne, shiyasa damuwarta ta fi ta’allaƙa akan kafin su zo kusan, dan zamansu su biyu a chan ango da Amarya abun da kamar wuya ace ba za su yi komai ba!…..
Tana cikin wannan tunanin ta ji Baaba larai tace”sai kuma maganar Yahanasu itama ya kamata asake..”
Dasauri Mommy ta katseta ta hanyar cewa “Larai mu bar maganar Yahanasu tukunna”
Cikin tarar numfashi ta Baba larai tace”She is out of control…
Yahanasun da na sani ko
shegen duka su Yassira suka yi wa Manubiya bai kamata ace ta yi magana ba, kar fa Yarinyar nan ta zo ta yi b’aramb’atama wata rana.!”
Kallon da taga Mommy tana yi mata ne yasa ta had’iye maganar ta ta kasa ci gaba da cewa komai.
Ahankali Mommy tace
“Dan girman Allah ki yi min uzuri akan case d’in Yahanasu Larai, ko me za ta yi kiyi min alk’awarin za ki tsaya akai mu gyara b’arnar da ta yi kawai,
dan abunda kike tunani bazan iya sake bada goyon baya akai ba…na ga illar hakan!.
A ganina Yahanasu k’aramin alhaki ce a halin yanzu da ke kanki kin san idan ba mu tsayawa kanmu ba komai mai iya faruwa ne, dan haka mu ajjiye batun Yahanasu a gefe mu maida hankali akan abubuwa da su ka fi mahimmanci….”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin ta mike tsaye
tukunna ahankali tace “inshaaAllah, duk yadda ki ka ce…sai da safe.”………
…..
Motar Najeeb ce ta k’arshe
shiyasa basu samu damar yin parking a cikin gidan ba, sai
a waje a bakin titi.
Yana sane ya k’i bud’e side d’in Siyama, ita kanta ta fahimci shine ya k’i bud’e mata dan tare suka fara kokawar bud’ewa ita da su Jidda
amman duk na su ya bud’u nata kuma shiru.
Ganin tana ta bawa kanta wahala ne ya sa ta hak’ura
da niyyar Jidda na fita itama za ta bi bayanta ta fice.
Munira ce ta fara fita
ta ce ”mun gode”
Da murmushi ya amsata dan ba k’aramin farin ciki yake ciki ba..dramar Siyama burgesa takeyi..yadda ta had’e rai ta chuno Baki abun ba k’aramin dad’i yake yi masa ba.
Jidda tana sauk’e k’afafunta k’asa ta juyo ahankali cikin nutsuwar ta tace masa”Mun gode” daga haka ta sauk’a a motar. Ganin Siyama har ta matso tsakiya yasa ya yi
sauri ya juya ya sa Hannunsa ya janyo murfin motar yana me cewa “Ba komai Jidda”
Yana dariya k’asa-k’asa yana kallon Siyaman, bayan ya tabbatar ya sake saka lock a duk k’ofofin.
B’ata rai ta yi sosai kafin tace
“Zan fita”.
Murmushi ya yi tukunna yace
“Ashe Inada aiki a gabana sosai ni ban saniba, dan handling Mace mai kishi
Is not an easy task(ba ƙaramin aiki bane ba)”.
Da sauri ta d’ago ta kalle shi,
sai kuma ta kau da kanta kawai.
Ganin ta ƙi cewa komai ne ya sanya ya ce “Amman naki kishin yayi tsauri sosai, ya yi yawa, dan Allah a d’an rage, atleast a bani dama in yi bayanin da zai wanke ni”.
Cikin tarar numfashinsa tace
“Ni fa ba kishi nake yi ba, bayaga hakan ma yaushe har na sanka….yau kad’ai fa na sanka ta ya zan yi
kishi??
Infact babu wani abu a tsakanin mu ai! Kuma na riga na sani
Ya’isha girlfrnd d’inka ce
Ita za ka aura kowa ya sani…bai
shafe ni ba sannan ba komai
dan ka yi hugging d’inta saboda ba hurumina bane ba
tsakanin ku ne ku da Ubangijinku. dan haka pls dan Allah ka daina cewa ina kishi saboda babu komai tsakanina da Kai sai mutuncin da muka yi a iyaka yau!.
Babu ruwana da alaƙar ku Kai da Ya’isha!.
Bud’e mini k’ofa in fita
Pls.”
Ta fad’i hakan tana mai sake matsawa kusa da jikin k’ofar dan ta samu ya d’auke Hannunsa yanzu.
Ya d’an ji zafin yadda ta ce”ba ta kishinsa, amman sai ya kawar yace
“Okay!In yi miki tambaya guda d’aya, za ki amsamin?”
Kamar ba za ta ce wani abun ba sai kuma ta d’aga masa kanta alamun ‘yes’
ba tare da ta kalleshi ba.
Sai da ya sake juyowa ya fuskanceta sosai kafin yace
“D’azu, you were nice to me(kin yi min kirki),amman tunda kika ganni da Ya isha ki kalleni ma aiki ne a wajenki, kuma it’s obvious haushina kike ji, shin ta ya zaki yi min bayanin hakan ba a matsayin kishi ba?.”