Sashe 24
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata dad’e da sauk’a ƙasan ba su Mommyn ma suka sauk’o,
gaba d’ayansu a shirye tsaf! Suna yak’e.
Tashi d’aya idanun Ya’isha suka sauk’a akan sir Najeeb, yana tsaye shi da wani driver suna gyara d’aurin carpet…..ya yi kyau ya yi fresh abunshi kud’i sun sake zama daram..har ga Allah dama chan ita tana son Ya Najeeb, kawai dai tana ja mishi aji ne saboda ita ta san tana da mutunci da daraja dan haka duk wanda zai sameta to sai ta wana shi! Saboda ba za ta taɓa bari a same ta a b’agas ba.…amma tunda ta lura kamar Najeeb d’in yana shirin sub’uce mata ta yi sauri ta gyara ta daina duk wasu halaye da ta san tana masa marasa kyau, sai dai kuma gani take kamar ta makaro dan ta fahimci sam sam kamar ba ta gabansa kamar ya daina sonta, ko dan ya ga yanzu ya yi kud’i sosai ne maybe shiyasa yake ganin kamar ya fi k’arfinta….amma inshaaAllah za ta sake gyara komai, za ta zage dantse za ta yi duk abunda yake so dan ita kanta ba ta san tana mahaukacin son shi kamar haka ba sai yanzu da ta ga yana shirin sub’uce mata….
Tana cikin wannan tunanin ya matso suka gaisa da Mommy, da su Yasmeen kafin ya juya ya cewa Hajiya Mama “zai jira su a mota”
daganan ya sa Kai ya fice daga cikin parlourn ba tare da ya kalli ko da inda take ne ba.
Yasmeen ji ta yi kamar ta rufeta da duka, idan shi bai kulata ba ai ita kamata ya yi ta gaidashi, shiyasa ta juya da niyyar ce mata “ta bishi motar” amman sai mom ta katsesu ta hanyar matsowa ta fara
nuna musu zabgegiyar sark’ar gold da bangles d’in da aka kawo yanzu…sark’ar Hajiya Mama ce ta bada as gift daga b’angarenta ita kuma mom d’in bangles d’in ne ta bada.
Shiyasa Yasmeen ta ja Bakinta ta yi shiru da niyyar in sun keb’ance za ta yi wa Ya’ishar magana, dan ya kamata ta kama Najeeb da kyau tun kafin ya sub’uce mata.
Saida suka yi da gaske tukunna Yasira ta d’anyi
murmushi ta karb’a ta shiga yabawa, yayinda Hajiya Mama ta yi shiruu kawai ta zuba musu ido ita da Ummi………
Tun safe yau Kausar bata lek’o ba, ko breakfast ba ta yi ba, jira take ta ga ko wani a cikin su Yassira zai lek’ota amman gashi har kusan yamma babu wanda ya lek’ota.
Bak’in ciki, tashin hankali, fargaba, k’unci da yunwa ne suka tuso ta a gaba, ganin tana shirin sumewa a d’akin ne yasanya kawai ta mik’e ta fita dan kanta.
Hankalinta bai sake tashi ba sai da ta sauk’a k’asan, ta ga uban lefen da aka had’a sannan ta ci karo da sark’ar da ta gani a Hannnu Yassira da bangles wanda tun kafin ta k’arasa sauk’k’owa ta fahimci d’anyen gold ne.
Babu wanda ta kula, babu wanda ya kula ta. Haka nan ta wuce kitchen tana ganin dishi-dishi, ta d’auki abunda za ta d’auka ta zo ta wuce da sauri ta haye sama.
Tab’e Baki kawai Hajiya Mama ta yi, ta d’auke Kai dan kai tsaye ta hango baƙin ciki da tashin hankali a idanun Kausar, kamar yadda tun ɗazun ta ke hangowa a Idanun Mommy da su Baba Larai!
Ita fa wani lokacin har tsoro bayan mamaki Mommy take bata, anya kuwa Mutum ce wannan Matar?
wacce iriyar muguwar zuciya gareta haka? Ta ya k’iri-k’iri za ta k’i auren d’anta?
Kalli yanzu Allah kad’ai ya san mai da mai ta rad’awa su Yasira dan suma kaff d’insu da ganinsu an san yak’e ne kawai sukeyi amman babu mai son wannan auren.
Kausar tana shiga d’akinta ta fashe da wani irin kuka….
Wato dai auren Yashjub za’ayi a cikin gidan nan, sannan a gaban idanunta kuma no body is willing to do anything about it(babu wanda ya ke ƙoƙarin yin wani abu game da hakan)….
Shin wai Mommy bata san idan ta bari aka d’aura auren nan tsaf za ta iya mutuwa bane ko yaya?!
Tabbas zuwa yanzu ta yarda ta amince cewa ‘ita kaɗai ce kawai, bata da kowa!’.
Inda ace Yasira ce ko d’aya a cikin ya’ya’n Mommy ta san da tuni an nemi mafita amman da yake itace yau an fi sama da watanni nawa kullum ce mata akeyi ta yi hak’uri za’a san abun yi, yau gashi har za akai lefe bata ga alamar tab’arb’arewar komai ba k’arshema sun b’ige da bin bayan d’an uwansu, sannan
shima Yashjub d’in ta lura kamar ma rura wutar tsanar ta aka kuma yi a cikin zuciyarsa,
ga kuma d’an kad’afe ‘Yassir’ wanda gaba d’aya ya hanata sakat, ko numfashi in yananan da kyar take shak’a, dan ma ta samu ta yi masa wayo yanzu yana zuwa office yana d’an aiki ba laifi a cewarta “ya dage saboda shima aga ya zama serious, kuma sai ya na da isassun kuɗaɗe ne tukunna zai iya yin destroying sannan ya yi galaba akan duk wani maƙiyinsa, tunda yanzu komai na kud’i ne”
To dai an ci sa’a yana zuwa office d’in yanzu, ba dan haka ba ta san da tuni kullum yana nanik’e da ita.
Kuma ta lura kamar su Yassirar sun d’an fara jin haushinta akan Yassir d’in saboda suna gani kamar tana yi wa ɗan uwansu wasa da hankali
tunda duk sunsan ba ta son shi amma kuma gashi ta ƙi rabuwa da shi, wataƙila ma shiyasa suka k’i taimakon ta suka barta ita kad’ai kowa ya kyaleta take ta fama da tashin hankali dare da rana……
Wani sabon kukan ne ya kuma kufce mata, bayan ta gama waennan saƙe-saƙen, tashi d’aya ta fara ganin duhu-duhu kafin daga k’arshe ganinta jinta da k’arfin jikinta ya tsaya chak, komai ya d’auke, daga haka ta tafi luuu ta zube a wajen kamar matacciya….
Duk yadda Mommy ta so ta d’an rabu da Kausar ko da na kwana biyu ne sam sai ta ji ta kasa, dan tunda taga yanayinta ta gaza hak’uri, kuma a yadda ta ga fuskar Kausar d’in ta kumbura ta yi jaa ta san akwai matsala, dan haka ta mik’e ta bi bayanta domin ta je ta rarrasheta ta kuma sake bata hope….
Wata razananniyar k’ara Mommy ta saka daga shiga d’akin Kausar d’in, sakamakon hangota da tayi wanwar a k’asa a zube.
A gigice ta fita ta tsaya a dai-dai k’afar bene ta shiga rambad’awa su Yassira kira, dama suna hanya dan tunda suka jiyo ihunta Yassirar ta mik’awa mom sark’ar Hannunta suka nufi saman gaba d’ayansu.
Har Ummi za ta bisu dan bata san menene ba, sai kuma kawai ta rabu da su dan ta lura kwana biyun nan wuyar ta su ga babu idon Hajiya mama kiri k’iri suke sauk’e mata maganganu!harare harare!da tsuka kamar masu jiran ta biyesu su dambatu.
Suna shiga d’akin suma duk suka
gigice, suka rufu akan Kausar…
Sai da Yasmeen ta tabbatar musu da ‘tana da rai’ tukunna hankulansu suka ɗan kwanta.
Sai dai kuma babu kalar dabarun da Yasmeen d’in ba ta yi mata ba amman ta ƙi yin koda motsi ne, dan haka suka kinkimeta suka sauk’o k’asa domin kaita asibiti.
A nan k’asan suka tarar da kusan kaff masu aiki da masu gadin gidan suna ta jidar akwatunan suna kaiwa cikin motocin da suke nan jere a compound d’in gidan.
A kan doguwar kujera suka shimfid’e Kausar kafin
Yassira ta k’arasa kusa da main driver d’in gidan ta ce ”Baba Sani, yi maza ka fito da babbar mota, za mu fita gaba
d’ayanmu, Kausar ba lafiya”.
Shiruu ya yi, dan tuni babbar motar a cike take! Dan a cikinta ne ma aka jiide gaba ɗaya kayan su shinkafa carpet da tabarma da su randa….
Yana cikin tunanin mai zai ce mata ta daka masa wata uwar tsawa ta hanyar cewa “Ina maka magana ka yi shiru, ba ka ganin Kausar a kwance kamar gawa ne??..”
Cikin tarar numfashinta Hajiya mama tace “and so what?? (To sai me??) idan Kausar tana kwance kamar gawa?.
Ai ita dama haka take, indai
aka zo abun farin ciki na ni da d’ana har ku kanku ma tou sai ta b’ata.
Maganar auren Yashjub kuwa, idan a rami ake dannata wallahi sai an yi kuma sai mun yi farin ciki!.
Ita ta sani, ta yi ta kwanciya karta tashi daga nan har abada”.
Ahankali Ummi ta matso ta ce ”. Maama…...”
Cikin katseta Hajiya Mama ta ce ”Saddik’a kar ki wani damu, makirci ne, so sukeyi a fasa auren Yashjub!.
ni na gaya maki muna fita Kausar za ta mik’e, dan lafiyarta k’alau! Na riga na san duk acting ne takeyi”
Tana gama fad’in haka ta kalli mom da Yahanasu da Ummin ta ce musu “let’s go( mu tafi)”
Tunda iya su ne yanzu za su tafi, Munirat ba ta nan yayarta ta yi kira yau ta tashi bata da lafiya sosai shine ta d’an je ta dubota ta dawo.
Basu bar muusu driver ko d’aya ba, gashi Hajiya Mama ta sanya su Yassira sun rarraba makullayen motocinsu a drebobin da za su kaisu tun d’azu.
Dan tashi d’aya ta fahimci basa san zuwa da motocin su
shiyasa ta karb’e tun da wuri dan so take ayi convoy.
Haka su Hajiya mama suka jera convoy d’in nan kuwa dan kaff motocin gidan sai da suka kwashe iya na Daddy Yassir Yashjub ne kawai babu suma kuma dan sun fita a ciki ne.
Motar Ya’isha kuma ta samu matsala balle su Mommyn su fita a ciki,gasu da uban yawa…..
Suna fita Mommy ta fashe da kuka tace “Baba Larai na ce miki dama ba zan iya tolerating (jurar) matar nan ba, kalli wulakanci da rashin tausayi da isa da mallaka a cikin gidana?!!”
Shiruu duk sukayi zuciyar kowa a wuya, da kyar Yassira ta share kwallar da ta zubo mata, ta wuce ta nufi dak’in Kausar…da kyar kuwa ta ga makullin motar Kausar d’in dan haka ta d’auko ta fito aka samu aka tafi kaita Asibiti daga Mommy sai Yassira da Yasmeen wadda ta zauna da Kausar d’in a baya dan motar ba za ta ishe su su duka ba…..