Sashe 133
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin kuka Ya’isha ta tari numfashin Mommyn itama tace “Daddy ka yi hak’uri akan komai, dan Allah.
Sannan ka duba yadda fa ka ke yiwa Mommy!!!
Ka sanyata ta durk’usa haka a gaban kowa!!
A gani na kamar yadda ranka ya b’aci muma namu fa zai b’aci idan ka tab’a mana mahaifiya!”
Cikin tsawa junior yace mata”bar nan kafin na yi ball da ke!!
Manya suna magana kina saka musu baki daɗin daɗawa kuma ‘rude tone’!!”
Harara ta zabga masa wanda hakan ya sanya ya mik’e ya nufota gadan-gadan, cikin bashi kwarin guiwa Hajiya mama tace”kana zuwa ka rufeta da duka kar ka raga mata!!”
Ganin yadda ya taho kuma ta san tsaf zai aikata ne ya sanya ta mik’e ta bar wajen da gudu ta haye sama tana sharar hawaye.”
Tsaki Hajiya Mama ta yi tace”marar kunyar banza”
Sai kuma ta kalli ragowar tace”duk wadda na sake jin muryarta a cikin ku za ta sha mamaki.”
Yayinda Daddy ya had’iye wani abu mai d’aci a mak’oshinsa, da kyar ya juya kawai ya k’arasa ya d’auki wayarsa ya fara k’ok’arin playing video d’in, da sauri Abhi yace”ka yi hak’uri ba sai kowa ya ji ya gani ba”
Cikin fushi Daddy yace”tabbas Abhi ya kamata kowa ya ji ya gani sabida idan ba haka ba wannan makirar matar sai ta k’unsa k’iyayyata a zuk’atan dukkannin jama’ar gidan nan,,dan cewa za ta yi Yassir bai yi mini komai ba hakanan na koresa, kalli fa kukan kissa da kisisinar da take yi bayan itace silar komai!
Muguwar zuciyarta da gurb’atacciyar tarbiyyar ta su suka janyo komai dan haka kawai ka bari kowa ya ji ya gani.”
Daga haka ya wuce ya k’arasa inda take ya cilla mata wayar yace”bud’e ki kalla ,kalla ki ga abunda rashin tarbiyyar da kika yiwa y’ay’ana ya janyo mana!!
Ki duba kiga abunda Yassir ya aikata a d’an uwansa…..”
Tarin da ya sark’afe sa ne ya sanya ya gagara ci gaba da magana…
Da sauri Abhi da Hajiya Mama suka k’arasa inda yake suka ruk’osa suka kaisa kan kujera suka zaunar, Junior ya yi saurin matso masa ruwa daga dispenser ya kawo….
Shiruu parlourn ya d’auka in banda sheshshek’ar kukan Mommy da na su Yassira ba ka jin komai!!.
Mommy ce take kallon video d’in amma iyaka voice d’in Yassir da bayanansa sun fahimtar da kowa na wajen abunda ke faruwa!!!
A tare Yasmeen da Yadira suka mik’e suka bar wajen suna wani irin kuka kamar ransu zai fita, dan ba ma su san abun cewa ba.
Da kyar aka samu Daddy ya dawo dai dai, tarin ya d’an lafa…cikin gajiya da komai ya d’ago ya kalli Hajiya mama yace
“ki gafarceni Hajiya mama, ba zan iya ci gaba da zama da matar nan k’ark’ashin inuwa d’aya ba!”
Gaba d’aya a tare Yasira
Yusra da Mommy k’irjinsu ya yi wani irin mahaukacin bugawa..Ummi kuwa ta san me Daddy zai yi dan ya dad’e da gaya mata matsayin Mommy a cikin gidan, dan haka ta mik’e da sauri ta wuce sama…..
Har ga Allah Junior ya ji dad’in abunda ya faru da Yassir, amma kuma sam bai ji dad’in abunda yake da shirin faruwa da Mommy ba shiyasa ya ce”Daddy koma me Mommy ta yi ka yi hak’uri…”
Cikin tarar numfashinsa yace”Junior ba ka san me ta yi ba!!!”
A hankali yace”Daddy ta ci albarkacin y’ay’anta!!!”
Girgiza Kai kawai Daddy ya yi yace”not anymore!!!”
Daga haka ya kalli Mommy yace”shekaru 32 kina zaluntata Khadija..na san nima wasu lokutan na kan sab’a miki ta hanyar nuna soyayyar wata fiye da taki, ko kuma nuna halin ko in kula da nake yi a kanki, amma Khadija wannan ma duk laifin ki ne! Saboda kin san ba na sonki ba na k’aunarki amma haka kika tilasta mini zama da ke…tsakanina da ke wata shari’ar sai a lahira, dan wallahi ko da zunubin tarbiyyar Yarana da kika lalata aka barki ya isheki!!
Duk wata cutarwa da kika yi mini da su Ubangiji zai saka mana!!.
A alamarin Khadija
Sam ban kama ki da komai ba! Tabbas kin yi k’ok’ari wajen kare kanki, amma na san komai laifinki ne, kuma shima zaki had’u da Ubangiji zai yi mana hisabi mu uku ya bi mata hakkinta wanda a ko da yaushe idan na tuna hankalina tashi yake yi matuk’a, amma dole na san sai na fuskanci Ubagiji da wannan tarin zunubin da kika yaudareni kika sanya na aikata …..”
Kukan da ya kufce masa ne ya sanya ya gagara cewa komai kafin da kyar ya samu ya ci gaba da cewa”zamu had’u da ke a lahira!!! Amma for now Khadija a halin yanzu bana k’aunar in sake jin ko da labarinki ne dan haka ki bi Yassir ku b’ace mini daga gani, har gaban abada ba na so in sake jin ko da muryoyinku ne!!!!!”
Tabbas wannan itace rana mafi muni a rayuwar Mommy…wani irin kuka take yi tana janyo numfashinta da mugun kyar….duhu-duhu kawai take gani!!
tabbas ta san Idan ta biyewa Daddy tsaff zai sake ta a take a yanzu shiyasa ta yanke shawarar tafiya kamar yadda ya buk’ata tun kafin ta b’intike igiyoyin aurenta ta je ta tonawa kanta asiri ta tarwatsa kanta….gara ta samu ta je ta yi sabon shiri a samu ya biyota ya rarrasheta ya d’aukota da kansa ya dawo da ita gidan, daga nan kuma sai ta san abunyi saboda ta riga ta san ba kowa bace silar wannan bala’in da take a ciki face Manubiya, dan haka dama ta gama tsarawa tunda ta k’i fita daga rayuwar Yashjub gara kawai su mutu tare cikin gaggawa……tun kafin su zamo ajalinta…..
Tana cikin wannan tunanin kamar a mafarki ta ji muryar Daddy yana cewa”kwanaki da kika tarwatsa auren Yassir da Kausar na sake ki!!
Da na fahimci abunda kika koyawa y’ay’ana kika turasu suka je suka aikata a gidan Yashjub shima a take a wannan lokacin na sake sakinki!!!
Kuma na san baki manta da sakin farko ba.. dan haka yanzu ni da ke babu maganar aure har abada!.”
…..Da farko duhu Mommy ta gani ya mamaye ganinta, sai kuma ta daina ji gaba d’aya kafin ta ji k’afafunta da hannunwanta da duk wani sassa na jikinta kamar ma babushi!! Daga ƙarshe kuma ta tafi luuuuu ta zube a wajen sumammiya.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 42*
Gaba d’aya Yaran kanta suka nufa har Junior, babu kalar ruwan da ba su yayyafa mata sun shafa mata ba amma ko gezau!
Dan haka Yasira ta kalli Junior hankali a masifar tashe tace”Junior taya ni mu d’auketa mu kai ta sama, sai in kira Dr…”
Ko gama rufe bakinta ba ta yi ba Daddy yace”amma ba ku ji abunda na fad’a ba ne?!!
Wanne saman za a kai ta?”
Cikin tsananin mamaki Yasira ta d’an cika Mommyn ta d’ago tana kallonsa idanunta jazir tace”Daddy suma fa ta yi?a hakan still baka hak’ura ba, so kake ta fitar maka daga gida?
Atleast ka tsaya a samu ta dawo cikin haiyyacinta mana, inyaso sai a yi komai, dan girman Allah.”
Hajiya Mama ta so ta saka musu baki tun d’azu, amma kuma sai ta ga wannan hukuncin Daddy ya kamata a barwa ya yanke, ita dai ta basa shawara ne, dan haka kawai sai ta ja bakinta ta yi shiru.
Cikin d’aci Daddy yace”Yasira ban bawa kowa ikon ya hau mini da ita sama ba, sannan iyaka mintuna biyar na bayar a fitar mini da ita daga cikin gidana!”.
Sosai zuciyar Yasira ta hau tafarfasa ta fusata sosai, dan a ganinta duk lalacewa dai ai ko dan darajarsu bai kamata ace ya kori Mommy ba daɗin daɗawa kalli fa halin da take a ciki amma dukda hakan ya dage kawai shi a fitar masa da ita daga cikin gida kamar wata annoba!!
Idan ta gaskiya za a bi ai ba ita ta sanya Yassir ya yiwa Yashjub abunda ya yi ba!…..
Cikin sharar hawaye ta mik’e zuciyarta a iyaka wuya tace”Daddy muddin fa Mommy
ta fita to muma binta za mu yi tabbas!!!”
Cikin matsowa kusa da shi ta ci gaba da cewa ”shin ka shiryama rasa mu muma akan dai ka tsaya a yi magana a yi sulhu??”
Shiruu ya yi kamar ba zai ce komai ba (dama wannan shine abunda shi da Hajiya mama suke gudu!!!)
kafin chan ya d’ago ya kalleta, yace mata”time d’in da na baku ku fitar da ita ya kusan cika…Yasira nan gidan ku ne dan haka feel free ki zab’i wajen Mahaifiyarki sannan ki dawo nan a duk lokacin da kika ga dama, babu wanda zai dakatar da ke.
Iyaka abunda na sani, na kuma tsaya akai shine a yau a yanzu sai Khadija ta bar cikin gidana! ta bar rayuwata, bari na har abada!!!!.”
Wani irin kuka Yasira ta fashe da shi, ta juya ta fita daga parlourn gaba d’aya rai a b’ace sannan hankali a masifar tashe…….
Tana fita Daddy ma ya sa Hannu ya share hawayen da ya zubo masa, tukunna ya wuce sama da sauri…..
Ba tare da ɓata lokaci ba Hajiya mama ta bisa…..
A tsaye ta same shi yanata faman safa da marwa, yana ganinta ta shigo ya k’arasa gareta ya rungumeta ya fashe da wani irin kuka, cikin kukan ya shiga cewa ”ki yi hak’uri, na gagara ci gaba da jurar ganin Khadija a cikin gidana da kuma rayuwata gashi kuwa abunda kike gudu ɗin shi zai faru da ni ‘za ta rabani da y’ay’ana Maamaa’!”.