Sashe 26
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jinjina Kai kawai Kausar d’in take ta yi alamun fahimta,amma a ranta ta riga ta gama tsara ‘za ta bawa su Mommy second chance (dama ta biyu), za ta basu one month dukda tana jin kamar ba za ta iya bari a gaban idanunta Yash ya tare da wata ba amman za ta kwatanta fatanta shine Allah ya sa ta iya d’in.
In har wata ɗayan nan ya cika Manubiya ba ta bar gidan Yash ba to za ta bi ta ko wacce hanya ta fitar da ita, ko dai ta fitar da ita da ranta ko kuma a fitar da gawar ta…..
Kwanan Abhi shida a Uk ya dawo Nigeria…..jikin Na’ima da sauk’i Alhamdulillah ba ta samu buguwa ko wani serious internal injury ba ta dai karye a k’afa ta kurje a hannu. Kuma shima Alhamdulillah abun ya zo da sauk’i ga kuma kwararrun likitoci a kanta….Ummi ta so zuwa kafin biki ko da kwana d’aya ne ta yi ta juyo, Daddy ma da farko tashi d’aya ya amince yanata murna ya cewa Yash ya biya musu kud’in jirgi ita da Mommy su tafi su je su yi kwana d’aya su dawo, cikin murna Ummi ta ci gaba da shirye-shiryenta amman washegari da safe Daddy yana tashi ya ce babu inda za su je, da ta bishi d’aki domin ta sake rok’onshi ma sai ya rufeta da fad’a dan haka dolenta ta hak’ura ta fito ta kyaleshi, da daddare ta sanarwa mom sun fasa zuwa, wanda mom ɗin da hajiya maman ne ma suka d’an kwantar mata da hankali dan ba kad’an ba ranta ya b’aci.
Sosai Manubiya take karb’ar gyara dan mama da anty umma sun dage sosai, inna da Baba har ma da su Manubiyan sun ji dad’i kwarai akan yadda anty umma ta shigo jikinsu itama dan da ita ake yin komai na bikin, ta tsaya tsayin daka! Ko ba komak sunsan an samu nasara sab’anin da da kowa ta kansa kawai yake yi, kuma suna addu’ar Allah Ubangiji ya wayar da kan ragowar suma a samu a had’a kai a yi zumunci, dukda kuwa ba su hango alamar hakan daga garesu ba amman Allah suka ce!
dan duk yadda ake ta tururuwar shigowa ganin lefen Manu kaff cikin matan uncle da baba habu babu guda d’aya da ta lek’o, ko su ko y’ay’ansu.
Aisha da su Mama so sukayi sai washegari da safe idan aka d’aura aure tukunna su had’a da gadon da aka siya da su flask da kayan lefe su kai gidan
amarya, duk a lokaci d’aya. Amma yadda unguwar ta d’auka aketa zancen lefen da tsadar kayan da gwalagwalan ciki ne ya sanya suka yanke shawara…..Aisha ta kira Yahanasu ta zo a take suka kwashe lefen kaff da ragowar kayayyakin da za’a tafi da su suka kai gidan amarya dan ya fi security….gadon ma dan sun samu matsala ne amma da tuni ankai, 3 months ago suka je suka zab’a sai suka barshi a wajen, to shekaran jiya suna zuwa d’auka me wajen ya hau kame kame, wai su yi hak’uri an yi order wasu yau da daddare za su k’araso shiyasa last month da ya samu mai siya ya siyar tunda su sun ce ba yanzu za su ɗauka ba, amma kar su damu exactly irinsu d’aya kuma yau cikin dare kayan za su iso, su yi hak’uri su jira dan Allah……..
……Aisha tana dawowa daga gidan amarya ta haukacewa su Siyama…labarin gidan take basu tana maimaitawa amman gani take yi kamar ba za su tab’a fahimtar kyan gidan ba har sai sun gani a idanunsu, shiyasa daga k’arshe ta hak’ura ta yi musu iyaka bayanin da za ta iya ta mik’e ta fita ta barsu ta tafi gurin su anty umma waenda suke ta rabon abincin sadaka na walima dan basu yi taro ba iyaka girki aka yi mai uban yawa aka kai asibiti da gidan marayu yanzun kuma ake rabawa almajirai…
…Suna zaune su uku a d’aki jidda Siyama da Manubiya lokacin k’arfe biyar daidai na yamma kowa ya gaji da hada hada, Muhsin ya shigo ya cewa Manubiya “wai ta je kaka mallan yana kiranta.”
Dariya Siyama ta yi kafin tace”tsohon nan fa neman shiri yake yi, jiya Ina jinsa yana cewa Ya Musbah wai ‘yanayin tsarin bikin ya burgesa ai dama ba a so a yi ta kid’e kid’e a biki, albarkar ake kwashewa.’
Ko wa ya tambayesa oho.”
Murmushi Manubiya ta yi hakama Jidda daga haka Manubiyan ta mik’e ta gyara zaman 3D vail d’in da ta rufa akan tsaddaden lace d’in da ke a jikinta tace musu ”bara in je in dawo”
Tana fita Jidda ta kalli Siyama ta ce ”har yau kema ba ki ganshi ba?”
Jinjina Kai Siyama ta yi kafin ta ce ”kema kin cika damuwa wallahi, da kyar ma idan Muhsin d’in ba tsokanar ki yake yi ba, dan ni Wallahi ko kyallin Ya Yusuf ban gani a cikin gidan nan ba. Baya ga hakan idan ma ya dawo ɗin ai shi ya sani, ke ina ruwanki?”
Wata nannauyar ajiyar zuciya Jidda ta sauk’e kafin ta ce ”ba wasa Muhsin yake yi ba, d’azunnan na ji inna tana gayawa Baba wai ya bita har d’akin ummanku yayi mata murnar warkewarta da Allah ya sanya alkhairi.”
Ahankali ta sauk’e numfashi kafin ta ci gaba da cewa “Siyama Ya Yusuf ba alkhairi bane ba, Ina tuna yadda ya tsundumamu a bala’i kwanakin baya, shiyasa kika ga duk na tsure, kuma inajin tsoro kar Baba ya aura masa ni…”
Da sauri Siyama ta katse ta ta hanyar cewa ”a’uzubillahi, Jidda dan Allah kar ma ki fad’a wani ya ji, inshaaAllah Ya Yusuf ba shine Mijinki ba, sannan ki kwantar da hankalinki da yardar Allah ba abunda ya Isa ya yi muku”.
Shiruu kawai Jidda ta yi, dan ita gaba d’aya kwana biyun nan sai a hankali, tunda Muhsin ya ce mata ya ga Ya Yusuf shikenan gaba d’aya hankalinta ya yi masifar tashi, jiya kuma tsautsayi ya sanya ta ta shigo d’akin lokacin mama tana ciki suna waya da Al’ameen, kuma wayar maman irin me muryar nan ce shiyasa ta jiyo dadd’ad’ar muryarsa rad’au…after abunda Ammi ta yi musu da kuma yadda shi kansa Al’ameen d’in
ya yi watsi da ita sam bata yi tunanin za ta ji haka dangane da shi ba! Dan tun a jiyan da ta ji muryarsa suna waya da Mama shikenan komai nata ya tsaya chak!
Llissafinta, wayonta fushin da tayi da shi da komai tashi d’aya duk ya tsaya chak, ta ji ita kawai all she needs and want is him!him alone nothing more(abin da take buƙata kuma ta ke so shine ‘shi’, shi kaɗai kawai, ba wani abun ba)
Tun jiya take k’okarin ta yi controlling kanta ta b’intike tunanin Al’ameen a ranta amma ta gagara, shiyasa tashi d’aya tausayi da haushin kanta suka lullub’eta, ga kuma fargabar had’uwarta da ya Yusuf….
Tunanin nan da take yi ne ya janyo har ba ta san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.
Da sauri Siyama ta matso ta dafa ta ta ce ”subahanallah, Jidda lafiya kuwa,wai duk akan Yusuf d’in dai??”
Girgiza Kai Jidda ta yi, cikin son ragewa kanta damuwa ta ce ”Siyama Ya Al’ameen bai kyauta min ba, ki duba ki ga yadda ya watsar da al’amurana, da ya san ya daina sona ai kamata ya yi ya fito fili ya gaya min ba wai ya share ni ba, ba abunda ya fi b’ata min rai irin yadda ya san ya bani waya kuma na san ya kira ya ji shiru a kwanakin baya, amma bai damu ya nemi sanin mai ya faru ko ya bincikoni ta wata hanyar ba sannan kuma har yau bayan na yi welcome back kusan watanni biyar bai damu ya sake kira ya ji ko na kunna layin ba, bai damu ya san me ya faru ba…bama ya nema na tunda ga layin ai a kunne yanzu amma ko alamun kiransa ban taɓa gani ba…bai damu ya san shin Ina raye ko bana raye ba sam shi ba damuwarsa bane..”
Kukan da ya taho mata ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana,
shiruu Siyama ta yi tana jiyo tsananin k’auna da son Al’ameen k’arara a cikin zantukan Jidda, dan haka a hankali ta shiga rarrashinta dan ta ma rasa ta Ina za ta fara nuna mata ‘hakan fa ba daidai bane ba!”.
Sun jima Siyama tana aikin rarraashi kafin dakyar tukunna aka samu Jidda ta yi shiru.
Siyama tanaso Jidda ta d’an huce kafin su yi maganar Al’ameen, shiyasa ba ta sake yin maganar ba,instead sai ce mata ta yi”am…ni kam Jidda ko kin san abunda yake damun Ya Musbah?
Naga gaba d’aya ya chanza tun watanni uku ko ma ince hud’u baya, gaba d’aya na lura a fusace yake kuma kamar haushin kowa yake ji,ko dai matarsa yak….”
Cikin katseta Jidda ta ce ”tab! Allah ya kiyaye”
Dariya Siyama ta yi kafin ta ce ”kar dai ki yi halin dangin Miji, indai har yanzu yana son abarsa a ganina gara kawai ku bashi shawara ya dawo da itan…”
“Hmm”
kawai Jidda tace, daga nan bata sake cewa komai ba, dan ta san inda ace ita kanta Siyama ta san me Baraka ta yi da ko zancen ta ba za ta sake yi ba….
Manubiya tana zuwa wajen Kaka Mallan ya karb’eta Hannu bibbiyu, abunda bai tab’a yi ba, tunda Manubiya take bata tab’a sanin cewa kaka mallam yana da wannan hankalin kuma ya san me yake yi ba sai yau!
Dan nasiha yayi mata mai ma’ana da tsananin ratsa jiki har sai da ya sakata kuka…..
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 14*
Manubiya tana zuwa wajen Kaka Mallan ya karb’eta Hannu bibbiyu, abunda bai tab’a yi ba, tunda Manubiya take bata tab’a sanin cewa kaka mallam yana da wannan hankalin kuma ya san me yake yi ba sau yau
Dan nasiha yayi mata mai ma’ana da tsananin ratsa jiki har sai da ya sakata kuka….. kafin ya sallameta yanata saka mata albarka.