Sashe 97
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A b’angaren Baraka da Ya Musbah kuwa, tunda ta ji labarin tashi tashin ma zama gida d’aya da su Inna tace ‘ba ta san zance ba!’
gashi kuma tun a ranar aka basu notice akace ‘su tashi daga wannan gidan da suke a ciki, a cikin sati ɗaya, mai gidan ya siyarwa wani…’
Sai da aka yi fad’a da ita a k’ofar gida ta inda ta haƙiƙance akan
”ai ba a tab’a bada notice d’in da ba na shekara d’aya ba!
dan haka ko ubanwa ya siyarwa gidan wannan tsakaninsu shi da sabon mai Gida ne!
ita kam ba za ta tashi ba har sai ta cinye shekara d’ayar ta!
sannan ba za ta karb’i refund ba.’
Da kyar aka rabata da mutumin, dan shima d’an a yi ne, shiyasa ya biye ta suka dinga hayya-hayya, sai da ta koma ciki tukunna mutumin ya bawa Ya Musbah kud’in hayarsa wanda ya biya, ya sake bashi hak’uri, ya ce ”ya taimaka su nemi gida su tashi, ga kud’insa nan complete ma ya bayar”.
Ya Musbah dama yana so ya ci gaba da makarantar da ya soma, kuma har ga Allah zuwa yanzu yana son zama a kusa da su Baba sosai sosai, shiyasa shi abun ma dad’i ya yi masa dan haka ya karb’a yace”ba komai za su tashi a cikin sati ɗayan kamar yadda ya buƙata”
Yana shiga gidan da ya so ya yi mata bayani sai abu ya rinchaɓe a tsakaninsu! Dan sam ta k’i fahimtarsa ƙarshe ma ta rufesa da fad’a, a ranar dai ba su yi bacci ba, dan kwana ta yi tana bala’i kuma ta tabbbatar masa da ‘babu inda za ta je…..’
Shi dai ya Musbah a hankali a hankali ya dinga kwasar kayansa, da nashi da na mai sunan Baba suna kaiwa sabon Gida, sannan ya je ya biya kud’in registration d’insa ya ci gaba da zuwa makarantarsa…ranar da sati d’aya ya cika ya zo ya yi mata sallama yace”za su tafi shi da mai sunan Baba”.
Da kyar Baraka ta fita daga shock d’in Musbahu wanda tana tunanin ta riga ta saka a kwalba bai Isa ya yi mata hakan ba…a take ta fahimci akwai matsala, shiysa ta danne zuciyarta kawai dan ta san dole sai ta sake sabon shiri kenan kuma a yadda ya botsare mata ɗinnan idan ta ce za ta yi turjiya to kanta za ta jawa shiyasa kawai ta ce “ba komai, ya jira ta itama za ta bishi…..”
Sai washegari aka gama kwashe kaya….a plan d’in Baraka idan ta je sai ta yi abunda shi da kansa zai ce su bar gidan kuma sai ta had’a sa da su Inna wannan karon ta kissa asiri da komai za ta had’a…sai dai kuma tunda ta je ta ga danƙareran gida a take a ranta ta ce ‘ba ta ga ta tashi ba!!’
ta san kuma fitar da su Inna a gidan aiki ne ko da zai yiu to ba yanzu ba….gashi ya Musbah gaba d’aya ya juya mata baya, aikin ma ya daina tasiri a kansa Kwata Kwata ba ya sauraronta ba ya jin maganarta, dan yanzu ma k’iri k’iri so take ya d’aga katanga a tsakaninsu da su Innar ya fitar musu da gate d’insu a daban, tama ce ita da kanta za ta bayarda kud’in amma yace”ba ta Isa ba!
“Idan kuma ta sake yi mishi wannan maganar shirmen wallahi sai ranta ya yi masifar b’aci”
Shiyasa gaba d’aya hankalinta yake a masifar tashe, ta sake dagewa!! gidan kullum idan aka shiga in banda k’aurin hayaki mara dad’i babu abunda yake tashi, dan haka suma su Inna suka sake dagewa da rok’on Allah.
Jiya da daddare Hajiya Mama da Junior suka zo….Shiyasa yau da safe su Manu suke ta shiri akan za su je.
Ana ganinta an san ta ci kuka, dan fuskarta duk ta kumbura, shiysa tunda su Yusra suka ganta a haka farin cikin su ya nunku ya gagara b’oyuwa har sai da ta d’an lura..a b’angarenta kuwa fad’a suka yi ita da Yash jiya abunda bai tab’a shiga tsakaninsu ba kenan!
Tun bayan sati biyu da ya nemeta ta k’i bashi had’in kai ta fara kuka shikenan bai sake neman wani abu a wajen ta ba,abun ya yi mata matuk’ar ciwo dan a tunaninta sun wuce haka ita da shi, ba ta tab’a zaton zai yi irin wannan fushin da ita har haka ba! mutumin da a ko da yaushe ya ke cewa”Manubiya ba ta laifi a wajen Yash,he loves her morethan life itself, ba zai sakata a damuwa ba”amma shine wai zai yi irin wannan fushin da ita!
Ba wai fushi na k’in magana ba dan suna wasa suna dariya yana kula da ita yadda ya kamata, kawai dai ko hannunta ya daina rik’ewa…..
Dama da haushin hakan a ranta yau kuma k’iri k’iri da ta yi masa maganar makaranta ba kunya ba tsoron Allah yace”ba za ta ci gaba ba!”
Daga haka ya shige toilet ya barta a tsaye kuma ko da ya fito ya ga tana kuka bai tsaya ya rarrasheta ba a maimakon rarrashin shima sai ya had’e fuska tamau! ya ci gaba da shirinsa ko a jikinsa…hakanan yana ganinta har ta gama kukan ta ta sauk’a k’asa had’a breakfast bai ce mata komai ba.
A b’angaren Yash kuwa..dalilin da ya sa ya d’aga mata k’afa kwana biyu ba ya so ya cika naci ne ya je garin hakan ya fara fita a ranta, shiysa ya hak’ura akan har sai yaga ta shirya masa tukunna…..sannan yana so ya yi k’ok’ari ya ga ya kawar da duk wani abunda zai sa ya yi zarginta ko ya ji haushinta.
A yadda ya ji tana waya dole ko ma waye ya dasa mata ayar tambaya amma shi kuma k’ok’ari yake yi ya goge zargi ya bawa hakan kyakkyawar manufa…
Ya san dole idan ta koma makaranta ya san hankalinsa ba zai taɓa kwanciya ba tunda ga issue a tsakaninsu dama basu gama sorting out ba!(basu gama sasantawa ba!).shi kuma ba ya son irin hakan a tsakanin shi da ita.
sannan ga ciki a jikinta da ake buk’atar ace ta huta,shiysa yanzu da ta yi masa maganar yace mata”A’a”kuma ya had’e rai.
Sannan har ga Allah ya na kishi shiyasa ya ga dacewar gara kawai ta yi online…
Kukan ta ya tab’a shi sosai amma ya san idan ba hakan ya yi mata ba, to ba za ta hak’ura ba!.
Har ta kai masa breakfast ya ci ya fita,sam fuskarsa babu walwala.
Sai wajajen 11 bayan sun gama girki Yasira ta ja su ta kai su gidan ita kuma ta wuce office wanda da so ta yi yau ta zauna a gidan itama amma sai Daddy ya kirata.
Shiruuu gidan ba kowa suka tarar, dan haka su Manubiya suka ajjiye flask d’in girkin da suka yo, suka nufi sama side d’in Mommy.
kamar ko da yaushe, ita da Baba larai sai Ya’isha suka tadda a parlourn nata..zuwan Hajiya Mama babu notice ya d’aga musu hankali matuk’a, ga kuma Daddy wanda yake bin diddigin Mommy kamar ba gobe…
Ba yabo ba fallasa suka gaisa, kafin Mommy ta kalli Yadira tace”ta raka Manubiya wajen Hajiya Mama su gaisa.”
Suna fita ko tambayar ta su Mommyn ba su yi ba, Yusra tace”yanzu haka ma cikinta ciwo yake yi,ba ta dai fad’a ba amma tun safe take rik’e ciki idan ya murd’a har sai ta durk’usa”
“MashaaAllah,Alhamdulillah!!”
Baba larai tace cike da farin ciki,kafin ta d’aura da cewa”tunda na ga matar nan da safe hankalina ya tashi, dan na san tsaf za ta iya cewa ku dawo gida..”
With full confidence Yusra tace”ai aikin gama ya riga ya gama yanzu kam..dan duk wani ruwa nata muna sakawa a ciki ita kuma tass take shanyewa.. yau sati biyu ta shanye sachet biyu fa!.
Ragowar abubuwan ne dai da na toilet da na d’aki duk ba mu samu damar yi ba ai dama na gaya miki..saboda ya Yash ko k’afar benen sa bai bamu fuskar mu tab’a ba, k’iri k’iri ma yace mana ‘ko ba ya nan kar mu shigar musu d’aki.’
Na abinci ita kuma ba ta yarda da mu ba! dan ko girkin mu ba ta ci, kuma tana yawan addu’o’i dan haka na san turaren shima ko ta shak’a ba lalle ace ya yi wani tasiri ba, dukda dai na lura kwana biyu rikici suke yi amma gaskiya ba lalle abubuwan namu bane, dan ba ta cin duk wani abu da muka bata…wataƙilan wata rigimar tasu ce daban.”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”Allah ya shige mana gaba,tunda har suka fara rikici su kad’ai ai sun sauk’ak’a mana kinga….sannan ba komai dan ba ku samu kun yi waenchan d’in ba indai komai ya tafi yadda muke so, to maganin da kuka saka da chatting d’in ma kaɗai sun ishi komai.
Yanzu Ya’isha ki kirawo Abbakar kice masa zai iya tunkarar Yashjub a yau!”
Shiruu Ya’isha ta yi kafin tace”amma bai yi wuri ba?”
Murmushi Baba larai ta yi tukunna tace”kina ji fa Yusra tace ta fara ciwon ciki!ai yanzu shine lokacin da ya fi dacewa, dan tunda ta fara ciwon cikin nan ba za ta kai jibi da shi a jikinta ba.”
“Tam shikenan,bari in kirasa…”
Daga haka ta d’au waya ta kirasa….a gaban su suka tattauna kafin daga baya suka yi sallama,zuciyar kowa fesss!!!.
Sosai Manubiya ta ji dad’in ganin Hajiya Mama, haka itama Hajiya Maman…bayan gaishe gaishe Hajiya Mama ta bata tsarabar da ta yo musu ita da Yash, ita kuma ta karb’a tana ta murna da godiya.
Dai dai nan Ummi ta shigo dan haka suka zauna su uku gwanjn ban sha’awa suka hau hira bayan Ummi da Manubiya sun gaisa.