← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 152

Sashe 20

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiyasa murna a wajen su har kasa b’oyuwa ta yi, tun daga kan Baba Larai har izuwa kan Yadira, kowaccensu idan aka kalla tashi d’aya za a san tana cikin tsananin farin ciki wanda hakan ba k’aramin sake ingiza Hajiya Mama ya yi ba, dan tabbas ta sake tabbatar da cewa ‘dukkansu ba son auren suke yi ba.’

A b’angaren su Manubiya kuma kaka mallan ne yaketa b’ab’atun sa shi kad’ai, duk inda ya zauna ya tashi sai ya sanar ‘ai an fasa auren Manubiya!!’….a cewarsa ‘’babu wani d’agawa da akayi, Yaron ne ya fasa, saboda ya gama lalubeta, dan kusan kullum sai ya zo ya d’auketa sun fita kuma basa dawowa sai dare…tun Mutanen layi basa biyeshi har aka fara ƙus-ƙus dan in ya zauna har rantsuwa yake yi yana cewa
“Yaron nan fa ba zai auri Manu ba, tunda ta kasa rik’e kanta ta bi kud’i ta bashi abunda dama ya kawo sa wajenta, dan wallahi akwai ranar da a gaban idanunsa suka dawo da daddare har da Muhsin amman sai aka cewa Muhsin d’in ya fita, shi da driver, su kuma suka zauna a bayan mota wallahi wallahi sun fi awa uku a cikin motar kuma motar har motsi yaga tanayi…shikam daga k’arshe ma hak’ura ya yi ya shige ciki bai san lokacin da suka gama ta shigo gida ba.”

Duk wannan gulmace-gulmacen da gutsiri tsoman da yake yi, hakan ba ta ishe sa ba sai da ya sa aka kira masa Ya Musbah takanas yace masa”ai ga irinta nan, ranar a masallaci sune har da yi masa rashin mutunci saboda yaga y’ar uwarsa ta shiga daula, to ga irinta nan ai tun kafin a je koina saboda abunda suka yi masa ne ya sa aka fasa auren, waye waye..”
Hakanan dai ya yi ta b’ab’atun sa, uffan! Ya Musbah bai ce da shi ba har ya yi ya gama, sai da ya dasa aya tukunna Ya Musbah ya mik’e ya ce ”Allah bamu alkhairi”
daga haka ya sa kai ya fice.
…
Bayan sati d’aya da d’aga bikin Yashjub ya zo yi mata sallama. A cikin sati d’ayan nan zazzab’i sosai yake yi, shiyasa ko iya fita ma bayayi balle ya je wajenta, sai dai kullum suna waya.

Ko da ya zo a waje ya tsaya ta fito, tashi d’aya hankalinta ya yi tsananin tashi dan ba kad’an ba ya rame sosai, ashe shiyasa
kullum take jin muryarsa wani iri idan kuma ta tambayesa sai yace mata”ba komai.”

Cikin tsananin mutuwar jiki ta k’arasa ta gaida shi, da kyar ya iya amsawa har da d’an k’ak’alo murmushi duk dan kar ta gane.

Cikin rashin jin dad’i ta ce ”ba ka da lafiya ne?”

Murmushi ya yi kafin ya girgiza mata kai kawai, ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ”gobe da asuba za mu tafi,”
Sai da ya sake fesar da numfashi tukunna ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce ”ni kam har ga Allah na fara da na sanin amince musu da na yi, kawai inaga gara a d’aura mu wuce tare, na so in same su da maganar amman sai na ga gara in fara yi miki maganar in ji ta Bakinki, amma duk da haka dan Allah baby kar kice A’a, kawai kema ki amince a d’aura a yau dan hakan nake so”
Ya k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.

Da kyar Manu ta iya danne kukan da ya taho mata, ta d’ago idanunta waeda suka cika taff da kwallah ta ce ”na san ba za ka ji dad’in abinda zan fad’a maka ba amma hakan shine daidai….ana barin halak ko dan kunya, kai fa da kanka ka ce min kawaici da alkunya ne suka sanya ka amince da buk’atar su, yanzu kuma kawai sai ka zubar ka je ka samesu ka ce ka chanja shawara?
Kuma kowa gani zai yi saboda ka zo ka yi magana da ni ne”

Cikin sanyin murya ya ce ”baby gani nake yi kamar idan aka d’aga wani abun zai iya…”

Cikin katsesa ta ce ”duk abunda ka ga ya faru to muk’addari ne daga Ubangiji, wayonmu ko saurin mu bai Isa ya k’ara ko ya rage lokacin da Ubangiji ya riga ya tsara za’ayi ba….dan Allah inaso kamar yadda ka ji kunyar su ka yi kawaici a farko to yanzun ma ka zauna akan bakarka, ka yi musu biyayya, baka san dad’in da hakan zai sanya su ji ba. amman yanzu idan ka bijire, to kowa rashin hak’uri da karar mu zai gani,kuma hakan ne.
Dan haka gara kawai mu yi musu biyayya, mu yi hak’uri mu mik’awa Ubangiji komai, inshaaAllah za mu dace”

Ganin yadda ya yi shiruu ya kasa cewa komai sannan idanunsa suka yi jajir yasanya manubiya ta kawar da kunya direct daga cikin zuciyarta tace masa ”inshaaAllah, i’ll forever be yours, no matter what(duk rintsi, ni taka ce, har abada)”

Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, dan ba kad’an ba kalamanta sun yi tasiri a kansa.

Cikin tsareta da lumsassun idanunsa waenda suka k’ank’ance suka yi jaa ya ce ”promise??( kin yi alƙawari?)

Ahankali tace”I promise(na yi alƙawari)”

Lumshe idanunsa ya yi wanda hakan ya bawa kwallar da yake ta k’ok’arin rik’ewa damar zubowa, da sauri Manubiya ta kauda kanta ta sunkuyar k’asa dan tashi d’aya itama ta ji tata kwallar tana shirin zubowa.

A hankali ya share idanunsa, ya d’an ja hanci kafin ya ce ”3 weeks (sati uku) zan yi in dawo, na san kuma zan koma follow up kamar sau biyu haka kafin auren namu”
Cikin yin k’asa da murya ya ce ”zan yi missing ɗinki sosai, take care of yourself ( ki kula da kanki), ki dinga rik’e wayarki a ko da yaushe pls”

Ahankali ta d’ago ta kallesa tace “inshaaAllah”

Cikin wata kalar kasalalliyar murya ta ji ya ce ”I love you, always and forever”

Ahankali ta sunkuyar da kanta k’asa duk yadda ta so ci gaba da rik’e kwallar kasawa ta yi dan tashi d’aya suka zubo mata, gudun kar ya gane yasanya ta sa hannu ta goge a hankali tukunna itama ta ce ”I love you too”

Murmushi ya yi, daga haka yace”see you in three weeks time..”

Ahankali ta d’ago ta ce”bye”

Kamar baya so haka ya yi Waving nata, tukunna shima ya ce ”bye”

Daganan ta yi sauri ta juya ta shige cikin gidan dan tabbas Idan ta ci gaba da tsayawa a gabansa tou za ta yi kukan ne mai yawa ba d’an kad’an ba ma.

Ai kuwa tana shiga, ta nemi waje ta zauna a kan d’an dakalin hanyar d’akinsu ta saki kukan ta…..ta yi k’ok’ari ta kwantarwa da Yash hankali bayan ta san tabbas ta fisa shiga damuwa dauriya ce kawai take yi…ta jima ta na kuka mara sauti mai cin rai kafin daga bisani ta goge fuskarta ta tashi ta shige cikin d’akin, a da ba ta ganin nisan watanni dan nan da nan indai aka saka rana sai ta ga lokaci har ya yi, amman tabbas a yanzu watanni ukunnan da aka k’ara jin su take yi kamar shekaru d’ari uku…..

*Bayan Wata Uku*

Kwanci tashi…..cikin hukuncin ubangiji watanni ukun da aka k’ara a kan bikin su Manubiya har sun cike cif cif….wasu suna cikin tsananin murna wasu kuma suna bak’in ciki yayinda waensu suka ji kunya….

Cikin nasara Yash ya je aka duba masa Hannusa, aka yi masa duk wasu abubuwan da suka kamata.
kafin wata biyu ya ware sosai shiyasa a lokacin har Hajiya Mama ta ce ko za’a d’aura kawai, amman sai su Daddy suka ce kar ma ta bari ya ji, kawai a jira dan dai wata d’aya da kwana 7 ai kamar yau ne….

yadda auren ya sake tahowa ne ya sanya su Mommy suka fara d’aga hankalinsu, sai da kowa a cikin gidan ya lura. Shiyasa Hajiya mama da dage ta tsaya tsayin daka a kan al’amuran gidan, dan Matar nan da ta kira ta yi musu feshi kwanakin baya yanzu kusan kullum sai ta zo, haka aka dage da addu’o’i a cikin gidan ba kama Hannun Yaro. Idan kuwa anayi Baaba Larai ji take kamar ta mutu, dan har ga Allah ba k’adan ba Hajiya Mama take b’ata mata aiki gashi ta kasa korar ta a gidan.

Kamar yadda Yash ya fad’a sau biyu ya je follow up a UK..a ranar daya gama da ganin Likita suka tarkota har da mom suka nufo Nigeria.

Suna zuwa aka shiga murna da oyoyo, Hajiya Mama tana ta tsokanar Yash tana cewa
“ba ga shi lokaci har ya yi ba, amman da har da kwallar sa da aka ce za’a d’aga auren, Itafa gaskiya tana kishin wannan kishiyar tata tun kafin ta zo, dan yadda yake wannan rawar k’afar ta san tana zuwa zai manta da ita”

Dariya duk akayi banda Mommy wadda take jin kamar zata mutu, cikin tafiyar tsofaffi Hajiya Mama ta nufi kitchen..yau dan rigima da kanta ta dafawa Yash jalof d’in taliya dan ta san yanaso, ba yadda Ummi ba ta yi da ita akan ta kawo ta yi ba amma ta ce “ta yanka mata albasa kawai”(shima saboda matsalar idon ta ne),
daganan ta girka abunta tsaf kuma ya yi dad’i sosai.

Mom da Ummi ne suka bi bayan Hajiya Mama yayinda Daddy da Abhi suka nufi waje dan suna da wajen zuwa, junior kuma ya bi bayan Yadira da ya ga ta nufi garden alamun waya take yi.

Yash yana zaune yana murmushi ya ji kawai an damk’i hannunsa yana d’agowa suka yi ido biyu da Mommy dan haka ya sauk’e ajiyar zuciya kawai yana kallonta…dan tun d’azu da ya shigo bayan ya je sun gaisa ko ‘ya hanya’ ba ta ce masa ba, kamar ma fushi ta ke yi da zuwan nasa,kuma a cikin watanni ukun nan ya lura kamar ma gudun sa take yi dan idan ya je k’ofar ta kullum a kulle. Yana cikin wannan tunanin ya ji tace “biyo ni, Inada magana da kai”
Daga haka ta juya ta nufi parlourn bak’i.

Sai da ya fesar da numfashi tukunna ya mik’e ya bi bayanta, yana wucewa su Yasira da Baaba larai suka yi sama dan kar ma a zo a tambayesu yana ina.
Chapter 20 · 0% Book details