← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 152

Sashe 41

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi tana so ta yi magana amma ta san idan ta yi magana abun sai ya fi haka zafi dan tanada tabbacin maganar da Siyama ta yi musu tun farko ne ya sanya su yin wannan haukar..

Ahankali Ahankali sheshek’ar kukan Manubiya yake tashi a cikin parlourn…cikin rarrashi Iya ramma ta ce ”ki yi shiru, ki yi hak’uri ki je ki gaidasu, ki tafi d’akin ki.
Aure fa ibada ne, dama haka abun yake sai kin yi hak’uri da duk wasu k’alubale da za ki fuskanta…
ki yi hak’uri, ki yi ta hak’uri, ki rungumi hak’uri dan yanzu kika fara hak’uri…Indai har zaman auren kike son yi kuma aljannah kike nema…”

Kamar Siyama za ta fashe da kuka tace”Iya ramma,ta Ina gaida su ya zama ibada??”.
Cikin fushi da d’an fad’a fad’a
Iya ramma tace “za kiyi shiru ko sai na hamb’are ki?”

Cikin kuka Manubiya ta cewa iya ramma “ba zan fa gaidasu ba, ku maida ni d’aki ka…”
Cikin katseta Iya ramma ta girgiza kai kafin tace
“Manu ki yi hak’uri, kar ki ce haka, dangin mijinki ne su..ki
kauda kai kawai kar ki biyesu”.

Dariya Ya’isha ta yi kafin ta matso tace
“Au wai itanma cewa ta yi A’a?.
Wow!
This is gonna be fun(al’amarin nan zai ƙayatar)…dan mu kam yau sai an yi Al’ada.
Bari ki ga ta kaina ma za ki fara”
Ta fad’i hakan tana mai matsawa
kusa da Manubiyan ta tsaya a daff da ita….

Kowa shiruu yayi kawai yana kallon ikon Allah…tabbas waennan sun tabbata dabbobi!
Wanne irin cin mutunci da cin fuska ne wannan haka a gaban mak’ofta da y’an unguwa saboda Allah…

Kuka ne ya tahowa Jidda, dama a high take, shiyasa ta yi sauri ta juya ta shige d’aki.

K’ok’arin juyawa itama Manubiyan ta fara yi…a hankali cikin tsananin mutuwar jiki Inna ta mik’e ta k’arasa inda take tace…………..

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 19*

K’ok’arin juyawa itama Manubiyan ta fara yi…a hankali cikin tsananin mutuwar jiki Inna ta mik’e, ta k’arasa inda take dai-dai ita kuma ta gama juyawa, sai da ta juyar da ita tukunna a hankali murya cike da rauni ta ce ”durk’usa!”

Shiruu Manubiya ta yi ta k’i motsi sai da Innaa ta sake cewa “durk’usa!”
Tukunna a hankali ta durk’usa a gaban Ya’isha tana wani irin kuka.

Jinjina kai Inna ta yi kafin tace
“Allah ya yi miki albarka”
Gaba d’aya parlourn a tare aka amsa da “Ameen” har su Yahanasu.
A hankali Innaa ta cika ta
ta kalli Iya ramma ta ce ”ki kaita ta gaida ragowar.”

Mik’ar da ita Iya ramma ta yi suka nufi Baba larai, suna
wucewa Inna ta yi sauri ta fice
daga parlourn. Tana fita ta saki
hawayen da take ta k’ok’arin rik’ewa….

Hatta Yadira sai da Manubiya ta je ta durk’usa a gabanta.

Tukunna Yassira tace “Alhamdulillah, muna iya wucewa da Amarya yanzu tunda ta nuna zatayi biyayya.
Once again, sorry fa! Idan na b’atawa wasunku rai, Al’ada ce ta zo da hakan.”
Daga haka ta mik’e ta kalli Ummi tace “za ku iya fitowa da ita, ni na gama nawa.”
Tana gama fad’in haka ta d’auke d’ankwalinta wanda ta shimfid’a ta zauna a kai ta yi gaba, a take Yasmeen da Baaba Larai suka mik’e suma suka bi bayanta. Suna fita su Yadira ma suka fice.
Za’a fara maganganu da gulmace gulmace
Iya ramma ta yi sauri ta mik’ar da Manubiya ta nufi k’ofa da ita, ganin haka yasa Umman su Siyama ma ta mik’e haka ma
su Yahanasu.

Su Maman Baraka sun shiga
wajen Amaryar uncle basanan akayi show d’in, labari kuma yana zuwa musu da suka fito lokacin suka tarrar har an fito da Manubiya, sun so sun tarar sun ganewa idanunsu…..
sallama suka yi wa Amaryar uncle suka bi bayan y’an kai Amarya, gudun kar a yi shima babu su.

Babu yadda Manubiya bata yi ba amman haka tanaji tana gani suka hanata shiga wurin Inna wadda tun d’azu ta lura ta fita daga parlourn,

ba tare da sun barta ta shiga d’akin nasu ba aka yi waje da ita aka saka ta a mota tanata kuka kamar ranta zai fita, Mata kuma sunata rangad’a gud’a!.

Yahanasu tana fitowa daga gidan su Manubiya ta d’au waya ta kira Yashjub….duk abunda su Yassira suka yi sai da ta kwashe kaff ta gaya masa komai har abubuwan da suka faffad’a akan gadon Manubiyan d’azu da rana duk sai da ta fad’a masa.

Ran Yashjub idan yayi dubu tou yau ya b’aci, shiyasa ko gama sauraronta ma bai iya yi ba ya kashe ya kira Yasira ransa a masifar b’ace yace mata ”kar ta kuskura ko da wasa ta k’arasa masa gida!Tunda mahaukaciya ce ita to ta kad’a kan ragowar mahaukatan su wuce gida!
Idan kuma suka kuskura suka je masa gida to wallahi sai ya ba su mamaki.
Iyakar b’arnar da suka yi masa ya Isa haka, kuma hakan ma su jira zuwansa gobe zai samesu, they will answer to him…”

Tabbas yau mai rabata da Yahanasu sai Allah, dan tashi d’aya ta san itace ta gaya ma Yash!

Abunda basa so ɗin kenan
gashi kuwa tun yanzu ya fara korarsu yana cewa ‘kar aje masa gida’.

Sun kusan Isa gidan lokacin da ya kirata, haka nan tana ji tana gani ta kira Yasmeen da Ya’isha ta zaiyyane musu tukunna ta ce ”su juya akalar motocinsu su nufi gida, Idan suka isa gidan sai a tattauna”

Sai da kuwa suka yi wa Ya’isha da gaske tukunna ta yarda ta juya ɗin dan da farko cewa ta yi ‘wallahi sai ta je,’.
Haka nan dai ta hak’ura, ta nufi gida tana jin kamar ta kama da wuta dan bala’i…..

Guiwa a mugun sace sannan Zuciyoyinsu fal takaici da bak’in ciki suka k’arasa gida, Yasira tana ji tana gani matakinsu da su ka shirya na gaba ya tafi a banza, dan akwai abunda ta kuma shiryawa za su yi a gidan Amaryar……
…….
Maman Siyama da Iya ramma ne a gefe da gefen Manubiya, sai Maman
Aisha a gaba.

Kukan da takeyi sai da ta bawa kowa tausayi, Yassir kam wanda shine ya d’auki Amaryar ba k’aramin mamakinta yake ta yi ba, dan shi bai yi tunanin Amare suna kuka har haka ba bayaga hakan ma ita da za ayi mata gata!…Ita da za a
d’auketa daga wannan garbage d’in a kaita aljannar duniya, ga kuma mijinta miji kamar Yashjub ta samu amma
shine take wannan kukan!…..
shiyasa gaba d’aya mamakinta ya rufe sa ya shiga
tunani da kuma san ya nemo
‘ko dai akwai wani dalilin da ya sanyata kukan….’

“Mu je”
Muryar Iya ramma ta katse masa tunani.
Jinjina kai kawai ya yi daga haka ya kunna motar ya danna double signal, ragowar na gabansa da bayansa suna ganin haka suma suka tashi motocinsu da suka cika taff da jama’a, suka sanya double signal, suka fara k’ok’arin barin layin…..

Komawa ciki Siyama ta yi domin ta je ta taho da su Jidda dan ta lura ba su fito ba.

Sir Najeeb sam bai yadda ya bud’e motarsa a kowa ba, ba ya so Siyama ta hango shi ta k’i shiga kuma ba ya so a cika motar dan bai shirya d’aukar kowa ba sai su d’in, shiyasa ya ji dad’i sosai da ya ga har an fara tafiya su basu riga sun tafi ba. Dan haka ya gyara zaman motar tasa a dai-dai k’ofar gidan.
Babu irin neman da Ya’isha ba ta yi masa ba….shi kam ya ganta sarai amma ya manna mata!..
Dan tana d’aya daga cikin dalilan ma da ya d’auko mota mai tint, kuma da ya zo d’in ya sake jin takaicinta dan tun daga farkon zuwan su har kawo yanzu da aka fito duk yana kallonsu, ba k’aramin haushi ta sake basa ba da yaga kalar shigarta! Kayan Jikinta da kuma yadda ta rufa mayafinta a iyaka Kai ba kaɗan ba ya bashi takaici….dan gaba d’aya jikinta a bud’e, gashi ta yi wa lace mai mugun tsada d’inkin fitted gown matsattse sosai kuma har da tsaga a baya!
A rayuwarsa ko bai san Mace ba sam ba ya so ya ga ta yi irin wannan shigar….

Yana cikin wannan tunanin ya ga su Siyama sun fito ita da Jidda har da Munirat. Tsayawa kawai ya yi yana kallon yanayin shigar ta simple and cute, so breathtaking!.
Yana kallonsu suka bud’e har motoci biyu amma babu guri.

Haka kawai dama Siyama ta ji motar datake fake a k’ofar gidan bata burgeta ba, ganin ana shirin wucewa a barsu
yasa ta ja hannun Jidda suka nufi motar….
Sai a lokacin ya sauk’e ajiyar zuciya.
Bai ji dad’i ba da Munirat ta bud’e gaba ta shiga, ya so Siyaman ce ta zauna a gaba…tana shiga tace “laa!Ya Najeeb Ina wuni.”

“Alhamdulillah” kawai ya ce a hankali ba tare da ya kalleta ba dan baya so Siyama wadda take shigowa yanzun ta fahimci shi d’in ne.
Tana shiga ta rufe ta juya ta kalli Jidda ta ce “Da ikon Allah motar kuma empty ma”
Yana jin ta rufe k’ofar ya sa lock ya kunna motar dai-dai itama ta fahimci ashe shi d’in ne dan gefen fuskarshi kawai ta kalla ta gane shi.
Da sauri ya kunna motar ya bi bayan convoy d’in.
Yana ganin ta tana ta k’ok’arin bud’e k’ofar amman ta kasa, dariya ta basa dan yadda ya ga ta had’e rai ba kad’an ba ta burgesa, abunda ya kasa fahimta guda d’aya shine ‘idan ta samu ta bud’e k’ofar motar shin fita za ta yi kenan a haka yana cikin tafiyar ko yaya?’…..
Murmushi ne ya sub’uce masa wanda duk saida suka ji, daga nan ba wanda ya yi magana haka suka d’au hanya motar shiruu
a haka har suka k’arasa gidan amarya Manubiya, dan tuni Yassira ta sa Yassir ya gayawa ragowar ‘ba sai an je gidan Mommy an gaida ita ba, direct kawai a wuce gidan amarya.’
Chapter 41 · 0% Book details