← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 152

Sashe 3

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin duk sun fita kuma kamar Daddyn yanaso ya yi magana da su Yash d’in ne yasanya Ummi ta mik’e ta ce ’’akwai abunda kake sha’awar ci? Ko in dafa maka komai ma??’’

Murmushi yayi ya ce “
‘’Anything Ummi, tnx’’

Allah ya k’ara sauk’i suka yi mishi daga haka suka juya suka fita ita da Munirat.

Suna fita Daddy ya mik’e daga inda yake ya k’araso ya zauna akan kujerar da ta ke kusa da gadon, inda Yash yake kishingid’e Yahanasu kuma a zaune.

Shiruu duk suka yi kafin Daddy ya kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa “Yashjub, abunda Yassira ta fad’a gaskiya ne’’

Lumshe idanu Yash ya yi kafin ya bud’e a hankali ya ce ’’haba
Daddy, kana jin maganar tasu fa ka san kawai shirmen Mata ne’’

‘’Koma akwai shirmen Matan to gaskiya ta fi yawa a ciki’’
Daddy ya bashi amsa cikin katseshi kafin ya d’aura da cewa “ba ka kyauta ba!
From today onwards(daga yau har abada) bana son ka bada ƙofar da wata zata gane akwai banbanci tsakanin y’an uwanka, inaso ka nuna mata duk d’aya suke a wajen ka sanann ka nuna mata mahimmancin su da mu kanmu
a wajenka!!! Hakan shine dai-dai, kuma kamar yadda Yassira ta fad’a hakan ne zai sa ba zata samu damar shiga tsakanin ku ba’’

Kamar Yashjub zai yi kuka dan takaici cikin b’ata fuska ya ce
‘’Haba Daddy, you sound exactly like them(ya kaima ka ke magana kamar su), yanzu ta Ina Manubiya…’’

Cikin katseshi ya ce
‘’Bana son musu’’

A hankali Yahanasu ma ta ce
‘’Yashjub, ka yi abunda sukeso a samu a zauna lafiya’’

Cikin jin dad’in abunda ta ce ɗin Daddy ya ce ’’yauwwa y’ar albarka, kishi a tsakanin y’an uwa bashida dad’i sam kuma ba zan lamuntaba, dan haka kar ka bada ƙofar da za a soma shi!!!
Dan kar ka sha mamaki idan hakan da ka yi ya sanyawa ita Yahanasun bak’in jini.
Meyasa ka ji ana cewa iyaye kar su ke nuna wanda suka fi so a tsakanin y’ay’an su?’’
Bai jira jin amsar su ba
ya cigaba da cewa ‘’saboda irin haka!.

Kuma aure ya zo a k’urarren lokaci mahaifiyarka kanta bata sani ba ni kaina ina tunanin ta yadda za su d’auki abun ba tare da sun ji wani iri ba
sannan kuma kwatsam ka zo da wannan al’amari!?
Haba, dole a ji haushi mana Yashjub.

Umarni nake baka, daga yau bana so in sake jin komai, kana ji Ummi har ta fara cewa kun fi shak’uwa kai da Yahanasu
Ita da ta zo jiya jiya har ta fahimta, dan haka kamar yadda suka buk’ata ka gyara tun kafin itama ta zo ta fahimci wani abun azo ana samun matsala.

Sannan whatever it is (ko ma menene)
da yake going on a tsakaninka Kai da Mahaifiyarka
inaso ka gyara shi da wur wuri ku shirya, in dai har kana son albarka kuma kanaso nima mu shirya ni da kai!!!
uwa ba abar wasa bace ba!
sabuwar rayuwa za ka shiga!

Ka je ku shirya ka nemi albarkarta’’

A hankali Yashjub ya ce
‘’Tam, in sha Allah Daddy’’

Shiruu d’akin ya kuma yi kafin chan Daddy ya furzar da numfashi ya ce ’’sai maganar Yassir, his company…wallahi har bana so in yi tunanin abun, ban san Ina ya kai kuɗaɗen ba komai ya tsaya chak!
Sannan contract d’in ma da ya d’an samu shima abun ya ƙi ya yiu kuma laifinsa ne dan sam bai d’auki abun da mahimmanci ba.

Da farko da nace zan zuba masa ido ne kawai in kyale shi amma duk yadda na so yin hakan na gagara, he is still my son(Saboda shi ɗin ɗana ne)’’
Daddy ya k’arashe maganar tasa a hankali yana mai fesar da iska kafin ya cigaba da cewa’’ni dai na riga na gama sakawa araina ba zan sake bashi jari ba, tunda bai san ciwon kanshi ba, amman kai za ka iya idan ka ga dama ba wai tilasss nakeyi maka ba sai
In ka ga dama.’’

Ajiyar zuciya Yashjub ya sauk’e kafin ya ce ’’akwai abunda nake shirya mishi, aikin da nake yi d’azu da safe ma kenan shiyasa na zauna a doguwar kujerar baya…..’’

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 02*

Shiruu ya yi kafin chan ya fesar da iska ya ce ’’sabon company ne na bud’e masa, na riga na gama registerring da CAC tun-tuni, na biya komai na karb’a har certificate.
Dama wani d’an information suka bid’a kuma shima na tura a d’azun. Na bud’e masa company d’in ne domin ya samu ya dinga shigo da k’ofofi windows bulbs da duk wasu kayan gine-gine dai nake ganin dacewar ya fara karɓar kwangilar su, naga abun it’s easier (yafi sauƙi) kuma in a fancy way tunda za’a dinga yawan tafiye-tafiye wanda na san abunda ya fi so ɗin kenan, gashi kuma babu wahala…
In sha Allah ni da Uncle ɗin Najeeb za mu harhaɗa shi da Mutane da zarar ya fara, zai samu alkairi a ciki sosai in sha Allah kuma kaga yanada ilimin architect so in yanada wayo zai iya cin moriyar hakan ya dinga samun riba biyu, tunda wannan aikin dai ba zai dinga cinye masa lokaci da strength ɗinsa ba, kuma dama na san wahalar ce baya so.

Already yanada building d’inshi, dan haka sai ya fara anan ginin ɗin dan adress na wajen ma na saka.
Tunda yanzu ya fara na san wajen zai ishe sa kafin mu ga abunda gaba za ta haifar.

Amman Daddy ka yi hak’uri ka yi mishi magana, ka ja mishi Kunne.
Ka ga dai yadda ya mayar da wanchan campany d’in zane-zanen nasa,
na san wannan babu wani wahala kowa ma zai iya
But it’s Yassir that we are talking about here (amma magana ce mu ke yi akan Yassir) dan haka
sai an ja masa kunne akan ya maida hankali.’’

A hankali Daddy yana jin tsananin k’aunar Yash d’in tana sake ratsa shi ya ce ‘’inshaaAllah Yash, zan ja masa Kunne sosai’’ kasa hak’ura ya yi sai da ya ce ‘’na ji dad’i sosai da ka damu da d’an uwanka har haka..
Allah ya yi maka albarka, Allah ya sake had’a min kanku.
Amman naga kamar har yanzu bakwa shiri da shi tun abun nan da ya faru ranar chan a gida’’

Murmushi Yashjub ya yi kafin ya ce ’’eh!baya min magana, he’s still mad at me (har yanzu yana fushi da ni) shiyasa dama na bari akan sai na gama komai sai in had’a a lokaci guda in basa takardun tare da sabuwar motar da na siya masa ta neman sulhu.

Murmushi Daddy yayi kafin yace’’Allah ya muku albarka’’
Yana mai jin wani irin farin ciki yana ratsashi.

A tare duk suka had’a Baki
suka ce ‘’Ameen’’
Daganan suka shiga tattaunawa akan yadda auren Yashjub d’in zai kasance…da farko Daddy cewa ya yi ko za a d’an k’ara lokaci tunda bashi da lafiya amma kalar zaburar da Yash d’in ya yi saida ya sakasu dariya
shikuma ya sa kanshi a kunya
dan haka ya ja Bakinshi ya yi gum! bai sake cewa komai ba, a ransa kuma yana mamakin yadda Manubiya ta maida shi.

Daddy dama ya san maganar gida ba shi ne zai yi ba tunda abun na masu yi ne, aikuwa ilai yana yin maganar Yashjub ya ce “ya gama da wannan ma.”

Sun tattauna sosai tukunna
Daddy ya tafi bayan Yashjub ya yi mishi alk’awarin shiryawa da Mommy da zarar ya koma gida InshaaAllah, dan tuni dama ya ji ya d’an fara hucewa akan abunda ta yi masa, ga kuma maganar da suka yi da Manubiya kuma yanzu kam tunda har Daddy ma ya sa Baki inshaaAllah zai je su shirya ya bata hak’uri dukda kuwa itace mai laifi.

Sai da Daddy ya fita tukunna Yashjub ya sanar da Yahanasu cewa ’kunce masa tayoyin mota fa akayi’
Dan sam baya so kowa ya sani ba tare da ya gama sanin abun yi ba.

Hankalin Yahanasu ba k’aramin tashi ya yi ba gashi ya ce mata ‘’ta yi shiru ta tsaya tukunna kar a fara bincike har sai ya gama deciding akan ‘zai d’au mataki ko ba zai d’auka ba’ tukunna ’’.

Sai da yayi da gaske tukunna ya kawar da batun yana dana sanin gaya mata dan in da ace ya san haka zata d’aga hankalinta to da shiru zai yi…..
Cikin son kawar mata da tunanin ya sake sako maganar auren nasa, ta fahimci abunda yake son yi shiyasa kawai itama ta d’an sake ta biye masa ba wai dan fargaba, tashin hankali tare da tunanin abun sun barta ba.

Cikin sanyin jiki Yashjub ya fesar da numfashi ya shiga tunani…
‘abu ya kankama sai shirye-shirye ake yi amma shi damuwarsa d’aya
bai san ya za su kaya da shi da amaryar tashi ba dan a cikin kwana biyun nan ya lura gaba d’aya a k’ule take da shi
jiya kamar za ta yi masa kuka wai kaff su Ya Musbah da Inna gani akeyi kamar auren takeso da wuri shiyasa ta ce a kira Ya Musbah da wurwuri
ita dai gaskiya in b….!.’

‘’Inaga gara mu ci gaba da had’a kayan ni da su Ummi ko?’’
Muryar Yahanasu ta katsewa Yashjub tunani.

Girgiza Kai kawai Yashjub ya yi
kafin ya ce ‘’kar ki damu, suma za su yi wani abun important, had’a lefe aikinki ne ke kad’ai…’’
har ya d’an lumshe idanunsa ya sake kishingid’ewa sai kuma ya bud’e ya kalleta ya ce ’’Yaha! A tunaninki Kausar za ta iya kasheni??’’

Shiruuu ta yi, ta dad’e tana nazari kafin ta sauk’e ajiyar zuciya ta ce ’’gaskiya a’a!.
Amma mai yasa ka yi tunanin hakan?”
Ta basa amsa tare da jeho masa tata tambayar.

Ajiyar a zuciya ya sauk’e kafin yace
“kawai dai…kin san na fad’a
miki maganar da na ji itada Mommy suna yi a wachchar ranar
da kuma abubuwa da yadda ta ke ta yi min.
Chapter 3 · 0% Book details