Sashe 121
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta d’an tsorata, dan yanayinsa na yanzun yanayine na wanda yake cikin tsananin b’acin rai, capable of anything(a shirye wajen iya aikata komai ma).
sannan taga kamar furucin nata bai yi wani tasiri a kansa ba, amma sai ta dake!!
cikin sake son cin nasara a kansa tace”kwarai ma kuwa Yashjub! Na rantse da girman Allah, Wallahi, Tallah, billahilazim..idan har baka mayar da Kausar ba a yanzu a take to sai na tsine maka, ka bi duniya!!!.
Tun muna daga mu sai kai, tun kafin duniya ta ji!su Daddy su ji! ina so ka mayar da Kausar matsayinta na matarka. idan kuma ba haka ba to sai na yi maka Allah ya Isa nonona da ka sha!”.
A hankali Yasira wadda jikinta ya yi sanyi ta fara tsorata dan sam ba ta kawo abunda suka zo yi ba kenan,ta matso jiki ba kwari tace”Mommy kar ki yi haka, a nemo wata mafita amma banda wannan.”
Wani irin kallo Yashjub ya yi mata kamar zai yi magana, sai kuma ya kauda kai yace
“Mommy ni da kaina na tab’a kama Kausar da Yassir a side d’inmu, shiru kawai na yi muku ban fad’a ba!, shin ta ya kike so
In yi zaman aure da dadiron k’anina?…
A ganina Kausar ta haramta a gareni, dan Allah ki ma janye wannan maganar saboda anzo in da ba zan tab’a yin abunda kike so ba.”
Jinjina kai ta yi kafin tace
“ko da ace zan tsine maka ko?”
Cikin d’an d’aga murya yace
“Mommy are you not listening to me?…shin ba kya jinnabunda nake faɗa ne?…
Kama ta fa na yi on bed! red handed!! turmi da taɓarya ita da Yassir, ta ya zan rayu da ita a matsayin matata??”
“Allah na tuba kana Ina Wa(Yaya) yake sakin Mace k’ani ya aura?!ai ba wai ance haramun bane kawai Halak ake bari dan kunya.
Saboda haka dan ka ga Kausar da Yassir wannan tsakanin su ne su da Ubangijin su,kai kuma kai ne wanda duniya ta sani a matsayin Mijinta!
Dan haka wannan duk bai shafeka ba!!!!”
Mommy ta fad’i hakan tana huci.
Cikin d’aurewar Kai haushi, bak’in ciki da tsananin mamaki yace
“bai shafe ni ba idan Kausar ta kwanta da ƙanina???
bai shafeniba dan ta kasance karuwa??
Mommy wacce irin uwa ce ke!?
Da har kike k’ok’arin ignoring (kike ƙoƙarin share) duk waennan facts d’in (haƙiƙoƙin) saboda kawai ki farantawa Kausar.”
A hankali yana kallonta yace
“anya Mommy kin san ciwo na kuwa??
kin san zafi na kuwa?
wannan rashin adalci haka har ina?ko dai inada wata uwar daban ba ke ba??!!!”
A rikice ta d’ago tashi d’aya ta d’aukesa da wani gigitaccen Mari!
Sai kuma ta fashe da kuka…
Cikin kukan tace”Wata tara ciff ka d’auka a cikin cikina, bayan nauyinka na wata tara haka na kawo ka duniya bayan na sha tsananin wahalar nak’uda!
Na shayar da kai na tsawon shekaru biyu..
kashinka, fitsari, tumbid’i duk ni ce mai wankewa mai gyarawa.
Sai da ka yi watanni shidda a duniya tukunna ka fara baccin dare, wanda a ta dalilin hakan ne ya janyomini na kamu da ciwon hawan jini, tsabar rashin samun ishashshen bacci. Idan baka da lafiya in kwana a zaune, in wuni a zaune cikin damuwa har sai naga ka warke!ƙiriniyar k’uruciyarka babu kalar wadda ban gani ba, babu wadda ban sha ba amma yau ni ce nake gaya maka abu kana yi mini musu! Ina fad’a kana fad’a Yashjub har ta kaimu ga kana iya kallon cikin tsabar idanuna kana cewa ‘ba ni na haifeka ba!!’
Ka san yadda maganar nan ta sanya ni na ji kuwa?
Auren Kausar fa a k’arshe duk kai na ke k’ok’arin yi wa gata amma ka kasa fahimtata!”
Ta k’arashe maganar tata cikin fashewa da wani Irin kuka.”
Duk shiruu suka yi kafin su Yasira su fara rarrashinta..ganin yadda shima ya yi shiru kamar maganganunta sun yi tasiri akansa ne ya sanya ta goge hawayenta tace”tunda ka ce ban yi maka adalci ba, to ka saurara ka kasa kunne ka ji ga adalci nan zan yi maka…
ko dai ka saki Manubiya itama, ko kuma ka dawo da Kausar!
A cikin biyun nan ka zab’i d’aya ka aiwatar, na baka mintuna biyu kawai kacal idan kuma ba ka yi ko d’aya ba mintuna biyun nan suka cika Yashjub Allah ya Isa ban yafe maka ba!”
Runtse idanuwa Yashjub ya yi da mugun k’arfi, a take wasu hawaye suka zubo masa.
Ba tare da ya bud’e idanun nasa ba ya ce mata”ki yi hak’uri!!na dawo da Kausar.”
Cikin tarar numfashinsa tace”na gode!
Kuma inaso ka sani Muddin ka sake sakinta b’acin ran da za ka fuskanta sai ya fi na yau wallahi!!!”
Sannan gobe inshaaAllah za ta tare, ba ma buk’atar ka yi sabon gida ballanta ka tafka rashin adalci! a nan za ta zauna d’akinta kusa da na Manubiya, idan na ga kamun ludayinka daga nan zan yi deciding idan ware gida za a yi,ko kuma Babba za ku chanja wanda ya fi wannan….”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice su Yasira suka mara mata baya..Yasira jiki ba lakka Ya’isha kam abun ba k’aramin dad’i ya yi mata ba.
Har suka fita bai bud’e idanunsa ba, yana nan a yadda yake…..har Manu ta hawo saman bayan ta ga fitar su ta ta rufe k’ofa, yana nan bai motsa ba.
Yanayin yadda ta gansa kad’ai ta san ba lafiya ba.
Ta dai san ba sakinta ya yi ba, dan inda ace sakinta ya yi to da tuni su Ya’isha sun nemota a gidan sun yi mata tujara..amma in ba da kyar ba tanada tabbacin Mommy ta saka shi ya maido da Kausar ne.
A hankali cikin tsananin k’arfin hali ta k’arasa garesa, tana zuwa ta kamo hannayensa duka biyu ta ja shi…
Bai yi mata musu ba ya bita suka zauna a kan sofa, a hankali ta mtsa jikinsa ta rungumesa tukunna cikin son kwantar masa da hankali tace”all will be fine..(komai zai daidaita)wata rana sai dai labari..ka kwantar da hankalinka…”
Cikin tarar numfashinta yace”Mommy ta saka na mayar da Kausar,cewa tayi idan ban mayar da ita ba za ta tsine min.”
Tunda ya fara magana Manubiya ta fara hawaye..yana iya jin yadda jikinta yake vibrating, k’irjinta kuma yake bugawa sosai shiyasa tashi d’aya wani matsanancin tausayinsu ya lullub’esa.
Manubiya ji take yi kamar za ta mutu..kishi, tashin hankali da komai ma duk sun lullub’eta, amma kuma ba za ta biyewa son kanta ta je ta kai Mijin da take masifar kishin da so wuta ba!
Indai har tana son Yashjub da gaske to za ta so su rayu har a Aljannah a tare ba wai ta bashi kwarin guiwar da zai tafi wuta ba,dan haka ta tattaro duk wata jarumta da k’ok’arinta da juriya ta fara magana”Ya Yash na gaya maka duk abunda ka ga Allah ya tsara hakan shine mafi alkhairi, ni kam na hak’ura babu komai zan zauna da kishiyar..
Na gaya maka ai, koma menene indai a kanka ne to duk zan jure..ni da kai ba za a ji kanmu ba, dan haka ka kwantar da hankalinka kar ka damu ina tare da kai duk rintsi, we will survive this, together!.
dan Allah kar ka sake yin jayayyya da su Mommy, ba zan so ka tafi wuta ba….”
Wani irin kuka ne ya taho mata wanda ya katse mata maganar tata…dama tunda ta fara maganar muryarta ta shiga rawa tana kakkatsewa.
K’ank’ameta Yashjub ya yi, k’irjinsa yana wani irin mahaukacin gudu.
Sun jima a haka kafin yace”ki fara had’a kayanki”
Da farko ba ta fahimci inda zancen nasa ya dosa ba sai daga baya,dan haka tace”Ya Yash we can’t just pack up and leave..ko ba komai Kausar matarka ce akwai hakki…”
Cikin tsananin b’acin rai ya zuba mata jajayen idanunsa yace”idan kika sake cewa Kausar matata ce za ki ga b’acin raina”.
Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa wanda hakan ya sanya ya ruk’o hannunta duka biyu yace”Mannubiya muma fa mun chanchanci mu yi farin ciki…
Annabi Muhammad sallahu alaihiwasallam da kansa a lokacin da aka nuna ba a sonshi Hijara ya yi daga Mecca ya koma Madina!.
Ki duba fa kiga, Yassir raina ya ke nema!
Mommy tana so ta had’a ni dole in yi zaman aure da dadiron ƙanina!
sannan sisters d’ina suma bangama yarda masoya na bane ba!
Tsoro nake ji ma in duba abunda na ke son dubawa a kansu saboda na san kamasu zan yi da laifin.
Ki gaya mini abu guda d’aya! Dalili kwaya d’aya tak da zai sanya in ci gaba da zama a cikin Mutanen nan?
sun nuna ba sa so na ba sa sonki, so kike yi mu ci gaba da zama a haka har sai bak’in ciki ya kashe mu???”
Bai jira ta bashi amsa ba ya ce “we deserve to be happy..sannan I’m not suppose to make you cry baby, idan ban cika alƙawarin da na ɗaukarwa kaina na sakaki a ƙololuwar farin ciki ba to bai kamata in sakaki a cikin matsanancin tashin hankali ba.”
“Cikin kuka sosai kamar ranta zai fita tace”Rayuwarmu a nan take, bani da mafarki da burin zuwa k’asar wasu in yi rayuwa..
A nan muka had’u da kai Ya Yash ba ni da burin da ya wuce in rayu a nan in tsufa a nan…...”
A hankali ya yi cupping fuskarta a cikin tafukan Hannayensa sannan yace”Mannubiya idan akwai lokacin da nake buk’atar asalin zallar goyon bayanki to yau ne!
dan Allah dan Annabi kar ki yi mini turjiya.
Ba na buk’atar musu ko wani sabon Abu negative(korau), na riga na cika dayawa! Matakin ƙarfin juriyana ya kai k’arshe….ba zan iya sake jurar wata matsalar ba…dan Allah please ko me nace miki kawai ki ce mini ‘to’dan Allah”
Ya fad’i hakan hawaye suna masu zubo masa.
Wani irin kuka ta sake rushewa da shi, ta rungumesa ta na mai jinjina kanta alamun ‘to’.