← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 152

Sashe 148

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai kan Yashjub ya fara juyawa…Da kyar ya yi gyaran murya, dan haka duk suka kallesa, tukunna tiryan tiryan ya shiga zaiyyano musu yadda ya ga Mommy ta fito daga gidanta, da yadda ya bi bayanta har zuwa inda ya ganta a gaban rami ta saka Ya’ishan….
Sannan ya d’aura da cewa
“A gani na bai kamata a binneta a haka babu sutura ba, shiyasa bayan mommy ta tafi na ɗaukota, to kuma ina gama sakata a mota sai na ji labarin rasuwar Inna….”
Manubiya ya kalla wadda take kuka kamar ranta zai fita yace
“Ina zuwa gwaggo Suwaiba ta nemi ganina….tashi d’aya Ina shiga ta sanar da ni Inna fa ba mutuwa ta yi ba, amma ita kanta bata gama sanin mai ya faru da ita ba..saboda lokacin da suna yi mata wanka ta ga babbar yatsarta ta Hannun dama
ta yi motai alamun akwai rai a tare da ita amma kuma ba ta numfashi, kuma Likita ma ya tabbatar da ta mutu…a wannan lokacin ta ce mini bata so ta ce bata rasu ba ta sakawa su Manubiya rai, kuma a zo daga baya aga ta rasu d’in, saboda ta tabbatar mini aikin asiri ne ba na asibiti ba, to komai zai iya faruwa a gaba ta yiu ta tashi ta you kuma ta wuce…shiyasa tace mini za ta wuce da Inna k’auyensu, a taru a yi mata addu’a dan suna da manya manyan hafizai a k’auyen masu tsoron Ubangiji da sani, daga nan sai a ga abunda Ubangiji zai yi, Idan bata tashi ba to za su binne ta a chan, idan kuma ta tashi za su dawo da ita da izinin Allah….

Zannuwa da cottons kawai da kara muka had’a aka saka a makara aka je aka binne dan bama so kowa ya san maganar……inajin batun Gwaggwo Suwaiba tashi d’aya na fahimci komai sharrin Mommy ne, wani abun suka yi shiyasa take ta nuk’u nuk’u da rasuwar Ya’isha musamman ma da na tuna yadda na ji Ya’isha ta je gidansu Manu a day before, shiyasa na had’a har da Ya’isha aka kaisu k’auyen su Inna a tare da zummar ayi musu addu’ar tare dan itama na yi tunanin watak’il asirin ne ya shafeta, sai dai kuma ita Ya’isha suna zuwa aka tabbatar ta rasu dan har ta fara kumbura ma shiysa na je aka yi mata sutura aka binneta a chan ɗin……..”

Gaba d’aya parlourn kaurewa ya sake yi da koke koke…da kyar Manu ta k’araso gabansa ta tsaya jikinta yana karkarwa tace”inna fa?”
Murmushi ya yi yace,kwana talatin ta yi ta warke, yanzu haka ma suna hanyar dawowa, tun jiya gwaggo Suwaiba tace mini sammako zasu yi yau inshaaAllah, yanzu haka da ma da shirin muna gama abunda muka fita yi sai mu wuce……”

K’amewa Manubiya ta yi, ta kasa motsi, sai da su Yasira suka zo suna kuka suka rungumeta tukunna ta dawo cikin haiyyacinta…
Share mata hawaye Yasira ta yi ta fara k’ok’arin durk’usawa a gabanta…da sauri Manu ta tarota ta shiga girgiza mata kai tace”na ji na san me kuka yi…
Yasira tun Ina cikin mahaifiyata Allah ya k’addara hakan zata faru da ni ,idan na haihu Alhamdulillah idan ban haihu ba haka Allah ya tsara, kawai inaso ki san cewa kome kuka yi na yafe muku na rungumi k’addarata….let’s just start a fresh…..”
Rungumeta suka yi gaba d’ayansu har Yasmeen da Yahanasu suna wani Irin kuka….

Dai dai nan Gwaggo da wata mai aikinsu suka fito, cikin sunkuyar da kai ta ƙaraso wajen tukunna tace”itama tanada magana!”

Ashe ranar da Mommy ta yi magana ita da Yahansu a ɗakin Yahanasun, Gwaggo ta ji komai, har ta yi recording ma, dan haka tana ɗan ɗari-ɗari tace
“tanata so ta kunnawa Daddy amma bata san ta Ina zata fara ba….”
nan kuwa ta kunna musu, kowa ya ji muryar Mommy tarr tana bayani dalla dalla, kamar yadda ta yiwa Yahanasu a wachchar rana……

Hajiya Mama ita dai k’arshe k’afafuwanta kasa d’aukarta suka yi, dan haka ta nemi guri ta zauna a naan kan kujerar.

Kowa kuka yake yi a parlour..suna gama jin recording d’in Gwaggo ta cewa Yashjub “a wachchar ranar ma
tana gani kamar Kausar Abu ta zuba masa, dukda dai bata tabbatar ba amma ta lura da ita da yanayinta..”
nan ta zaiyyane masa yadda suka yi da kausar ɗin a ranar…..

Numfashi Yashjub ya fesar, ya share hawayensa, ya nemi guri ya zauna yana mai jinsa kamar wani sabuwar halitta….kasancewar sa ba d’an Mommy ba yana daga cikin abubuwa mafi dad’i da ya tab’a faruwa da shi a tarihin rayuwarsa, shiyasa wani sanyi nutsuwa annashuwa suka mamaye sa……
Da kyar ya iya bud’e Bakinsa ya cewa gwaggwo
“yanzu kam babu batun Kausar, ta bar cikin rayuwarmu har abada….halinta ya bita.”
Duk parlourn “Ameen” suka ce, kafin Daddy ya kalli Yaha yace mata
“Maiyasa kika yi shiru, wannan gagarumin al’amari haka Yaha???”

Sabon kuka ta fashe da shi, tana kukan ta k’arasa ta ruk’o Hannun Yashjub tace”I’m so sorry….”
Dan ta fi jinsa ta san ta fi yi masa laifi akan Daddy tabbas!…
Rinannun idanunsa ya d’ago, ya zuba mata,,kafin yace
“Yaha ba zan b’oye miki ba! Sam ban ji dad’in yadda kika yi shiru game da wannan al’amarin mai matuk’ar mahimmanci a rayuwata da ke ba, har iyau kuma na fahimceki kuma na fahimci uzurinki, dan haka karki damu, komai ya wuce..”

Su Yasira ya kalla waenda suka matso garesa suma, ya ce ”kuma abunda kuka yi mini ba komai, ba zan ce na manta da shi kamar bai faru ba, amma kar ku d’au hakan ku saka a ranku dan inshaaAllah ba zai zamo silar shiga tsakani na da ku ba..rashin walwala da shak’uwata da ku ya sanya Mommy ta samu damar shiga tsakanina daku, ta yi poisoning mind d’inku against me, har ta kai kuka yarda cewa bana sonku, wanda ni hakan nature d’ina ne kuma kasancewarku mata da kuma yanayin rawar kan Yassir ya sanya na ga dacewar in sake zama mai tsauri a kanku saboda kyautuwar tarbiyyarku, amma inshaaAllah daga yau zan gyara! na gane kuskurena..in sha Allahu zan jaku a jikina mu zamto abu d’aya! Abokan juna, ta yadda babu wanda zai sake iya shiga tsakaninmu…kasancewata step brother a gareku ba wai yana nufin zumuncinmu zai samu rauni ba sai dai ma ya k’ara k’arfi InshaaAllah…”
Rungumesa gaba d’ayansu suka yi a lokaci guda har ba a iya hangoshi ma, cikin kuka suka shiga ce masa “kar ma ya sake cewa shi step brother d’insu ne, har abada za su zama d’aya, babu y’an ubanci a tsakaninsu inshaaAllah…..”

Da kyar suka iya had’a ido da Yahanasu, suka nemi gafarar ta, they really can’t believe wai ‘Yaha cikinsu d’aya!’ kuma suka dinga yi mata wulak’anci, ta yi shiru, sannan itama Mommy ta sani amma ta yi shiru! duk dan cikar burinta, tabbas Allah ne kad’ai zai yiwa Mommy hisabin da ya fi dacewa da ita….

Hajiya Mama ma tun d’azu ta fara hawaye, fad’i take”Alhamdulillah Alhamdulillah”
Ta godewa Ubangiji da ya bata Aron rai ta ga wannan rana…Alhamdulillah da ya fallasa rub’abb’en irin gidan Imam a gabn idanun kowa, matsalar gidansa ta zo k’arshe.

Cikin sharar hawaye Yash yace”hak’ik’a yau tana daga cikin ranakun da suka kai k’ololuwar dad’i da farin ciki a cikin ranakun rayuwata…Hak’ik’a Ubangiji mai kun faya kun ne!
Ya kan yaye damuwa ya chanja al’amari ya kawar da matsala mai girman gaske a cikin k’ank’ani lokaci…
Mu dai kawai abunda ya kamata mu yi a ko da yaushe shine mu yi trusting d’insa mu saka gaba d’aya fate d’inmu akansa sannan mu mik’a dukkannin al’amuranmu garesa, daga nan komai zai yi falling into place cikin sauk’i…..in da Rabbana ba wahala….

Alhinina d’aya a halin yanzu
‘rasuwar Ya’isha, da mahifiyata wadda bama ta san tanada ni ba…..”
Ya fad’i haka cikin zubar hawaye..

Cikin sharar hawaye shima Daddy yace”Tabbas Khadija ta dad’e tana zaluntata tun asalin farko…da ace Ubangiji zai bani dama to da na koma baya na janye abunda na yiwa Mahaifiyarka Yash…da na gaya mata cewa ‘na yarda da ita d’ari bisa d’ari kuma na san sharri ne akayi mata…dan ko ba a gaya min ba na yarda na san sharrin ne.”

Inama ace Khadija (mahaifiyarka) bata rasu da bak’in cikina da takaicin na ƙi yarda da ita ba…inama ace tana raye da na sauk’e wannan nauyin, na nemi gafararta…..”

Yahanasu ta san ta yiwa Mama alk’awari, amma kuma an riga an linke Daddy ta baibai! Ta yadda ba zai tab’a fahimtar Mama tanada rai ba muddin ba nuna masa ita akayi ba….dan haka ta goge hawayenta tace
“tanaso kowa ya biyota, tanada surprise d’in da takeso zata nuna musu, kar wanda ya tambayeta
menene, kawai kowa ya biyota…”
Daga haka ta shiga d’aki ta kwaso key sannan ta Kira Mama tace mata”tana Ina?”
Maman tace”Tana gidansu Manu, tun jiya Gwaggo Suwaiba ta kirata tace su had’u a gidan da sassafe gasunan yanzu haka ita da su Ammi suna shiga gidan….”

Yahanasu tana fitowa suka taru suka tsara akan ‘za a d’auko y’an sanda, su tafi da Mommy, su mik’ata kotu a yanke mata hukunci…’

Daga nan suka nufi gidansu Manubiya akan sai sun gama da nan d’in, tukunna za su je a tafi da Mommy, dan bayan Inna dake hanya Yaha tace musu nata surprise d’inma yana gidansu Manu.
•••
Kausar bata tarar da su Yasira a gidan Mommy ba, dan ko da ta yi knocking ma Mommyn ce ta zo ta bud’e mata da kanta, wanda ganin Kausar ɗin a yadda ta je mata ya yi matuk’ar d’aga mata hankali dan haka ko shiga bata bari sun yi ba tana gama rufe gate ta shiga tambayar ta “mai ya faru?!.”

Sosai Kausar ta zama emotional, dan haka ta fashe da kuka cikin kukan ta shiga zaiyyane mata abunda ya faru…
Chapter 148 · 0% Book details