Sashe 65
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rungumeta kawai ya yi shima yana mai sauk’e ajiyar zuciya a jejjere, yana bubbuga bayanta a hankali alamun rarrashi.
Sun jima a haka dan har ta yi shiru bata d’ago ba, ta yi lamo kawai tana sauraron bugun zuciyarsa.
Tukunna a hankali tace”Ina so zan koma d’akin naka, mu biyu kawai”
Murmushi ya yi kafin yace
“Whatever u say (duk yadda ki ka ce) love….hakan za a yi”
Daganan ya gyara musu position suka kwanta a kan gadon ya shiga rarrashinta kamar zai yi mata kuka……
Daman ba ta fara girki ba..kamar yadda Jidda ta gaya mata washegari da safe ta had’a kayanta har waenda ta rufe a jaka kaff ta kwashe, Yash ya tayata kaiwa d’akinsa, dan ta gama tsarawa akan ko sun dawo to ta bar d’akinta kenan muddin Yadira ta na gidan.
Tunda kuwa ta haye sama ba ta sauk’o ba dan hatta abinci delivery man yana kawowa idan ya bawa Yadira nata zai wuce da nasu sama…ba ta tashi sauk’owa ba sai bayan azahar lokacin da suka zo fita.
Ita a tunaninta ma tare za su fita da Yadirar amman sai ta ga sun tafi iyaka su biyu kawai.
Haka suka je suka kammala komai na shirye shiryen tafiyar su.
Sai dare wajajen k’arfe takwas tukunna suka dawo.
Suna shigowa suka tarar da Yadira da Yassir a zaune a parlourn shi yana waya ita kuma tana kallo
…..tabbas idan Yassir bai daina yi wa matarsa wannan d’an iskan kallon ba wallahi zai yi abun ban mamaki!! sai dai duk abunda zai faru ya faru!
tsabar Iskanci har wani lashe Baki yakeyi ƙasa ƙasa gashi ya k’ank’ance idanu yana kallonta tun daga sama har k’asa…
Tsabar takaici Yashjub ɗin bai san lokacin da yace mata “ta wuce ta tafi d’aki”ba
Sai a sannan Yassir ya yi murmushi ya mik’e tsaye ya k’arasa inda suke, Manubiya tana shirin wucewa ya sa hannu ya karb’i ledar hannunta wanda sai da ya had’a da hannnunta da ledar ya runtse ya murza tukunna ya k’arba ledar yana wani kalar murmushi sannan yace “barka da dare antynmu”
Da kyar tace “lafiya”
Har ga Allah ta tsani Yassir musamman ma yanzu da ta gama tabbatarwa d’an iska ne!! saboda kalar yadda ya runtse mata hannu ko ita Yarinya ce ta san kalar na y’an duniya ne, har wani murzawa fa ya yi..
Shi kam Yassir laushi da taushin hannun nata ne ma ya fi komai d’aga masa hankali, dakyar ya juya ga Yashjub wanda ya kafe sa da idanu yace “Ina wuni”
Yana wani killer smile.
Dakyar Yashjub ya iya danne fushin sa, dan ya kul’e sosai ba kad’an ba!! ya san case d’in Yadira ya Isa wajen Mommy da Daddy bashi da tantama dan Yahansu tace “tanada magana da shi idan ya zama free ya kira ta”
Shiyasa kawai ya danne kansa saboda gudun kar a kuma yin wani case d’in.
Cikin kawar da kai yace “lafiya”
Kafin ya d’an kalli Yadira itama yace mata “lafiya”wadda sai da ta bari Manubiya ta wuce tukunna ta gaida shi, daga haka ya juya yana mai bin bayan Manubiya wadda ta wuce sama da sauri da kallo, kafin ya maida dubansa ga Yassir..
da mamaki ya k’ura masa ido ya shiga k’are masa kallo dan idan idanuwansa ba k’arya suka yi masa ba tou kamar kayan bacci yake gani a jikinsa, shi sai yanzu ne ma ya lura sannan ya tuno bai ga motarsa a waje ba..
Cikin son fahimtar sa yace
“Banga motarka a waje ba,
ko dawowa za a yi a d’auke ka?”
Murmushi ya yi kafin yace
“Bello ne ya kawo ni ya koma,
wai zan kai ku airport ne da safe gobe, daganan sai mu wuce gida ni da Yadira”
Shiruu Yashjub ya yi a ransa yace ‘’a tak’aice dai kaima a nan ɗin za ka kwana!”
A fili kuma kawai sai ya jinjina kai ya sa Hannu yace “bani ledar”
Da sauri Yassir yace
“No,ga guda biyu masu nauyi a hannunka,bari kawai in kai muku d‘aki
Cikin d’an tsare gida Yashjub yace ‘’bani nan, sai da safe’’
Ya fad’i hakan yana sa hannu ya k’arba ledar…
Ba dan Yassir ya so ba ya basa,
daganan ya zura wayarsa a aljihu ya wuce d’akin bak’i na nan k’asan zuciyarsa tana turiri…so ya yi ya d’an fara k’addamar da shirin sa akan Manubiya tun yau! Ya so ace ya
bata ajiyar sak’o mai nauyi mai tsayawa a rai wanda har ta je honeymoon d’in ta dawo yana mata yawo a rai.
Ya san rik’e mata hannun da ya yi ma wani abu ne amman ya so ace ya yi wanda ya d’an fi haka…
Bai kamata ya dinga jin kishi ba tunda ba Kausar baceba amman har ga Allah haushi yakeji idan ya tuna Yashjub zai tafi honeymoon da ita wata uwa duniya!
Anya kuwa ba k’aunar Manubiya yakeyi ba kuwa!
dan yanzu haka ma da ya tuna da cewa tare za su kwana ita da Yash wani irin tafarfasa zuciyarsa takeyi….
Ya na shigewa Yadira ta girgiza kai a ranta tace
‘’Ya Yassir kenan!”
Shiyasa fa ta k’i yarda da Junior saboda duk kusan halinsu d’aya da shi da Ya Yassir, sai dai Ya Yassir ya fisa sosai dan nasa kam ya fara zama disorder….babban dalilin da ya sa bataji haushin Kausar a lokacin da ta yi futun futun tace ba ta son Yassir ba shine
ta san shima ba ita kad’ai yake kulawa ba kuma duk macen da take son zaman lafiya da kwanciyar hankali da ruhi to ba za ta tab’a zab’ar Yassir a matsayin Mijin aure ba…
Saboda idan aka bincika Ya Yassir tou tabbas za a tarar yanada matsala ko dai psychological ko kuma asiri aka yi masa da Mata!
Dan ita dai tunda take bata tab’a ganin confused d’an iska kamar Ya Yassir ba….za ta iya cewa indai Mace sunan ta Mace tou Ya Yassir yanaso..
Ta san Kausar yakeso da aure amman fa y’an matan da yake so da lalata sam ba za su k’irgu ba! kuma shi sam babu ruwan sa da class ko wani abu makamancin hakan…
Yanzu haka a iyaka cikin gidan su kawai ta lura akwai abu a tsakanin sa da Munirat ga Kausar yanzu kuma yadda ta ga tun d’azu da ya zo yana ta faman tambayar ta Manubiya ta fahimci akwai matsala ta nan ɗin ma, dama tun jiya yadda ta ga yana ta shishshige mata ta san da walakin.
Bata san mai yake damun sa ba, bata tab’a ganin Namijin da bashi da tsayayyen zaɓi da ra’ayi irin Yassir ba, wani zubin tana lura da shi idan ya ga Mata jikinsa har karkarwa yakeyi, gashi yanzu tsabar idanunsa sun rufe Matar yayansa yake shirin farmawa!”ashe kuwa za’ayi kisan kai! Indai ya Yash ne”
ta fad’i hakan a chan k’asan ranta kafin kuma ta tab’e Baki ta mik’e, tanajin haushin Manubiya yana ratsata…
a hankali a fili tace ‘’su suka sani’’
daganan ta nufi sama d’akinta…….
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 26*
Dukda Manubiya a k’ule take da Yassir, amman sam sai ta k’i yi wa Yashjub maganar sa, dan kamar yadda Jidda ta gaya mata inshaaAllah ba za ta sake basu k’ofa su zamo silar b’acin ranta ko na mijinta a rayuwar aurensu ba, sannan ba za ta sake da su ba….addu’a kuwa tun a jiya ta duk’ufa da yi dan ko shiru ta yi to a zuciyarta addu’a takeyi….
Shima Yash d’in bai yi mata maganar Yassir ba,
shiyasa ita bama ta san a gidan zai kwana ba.
Hira kad’an suka tab’a daganan sukayi nafila suka tofa addu’o’i ko wanne ya bi gado.
Tun k’arfe uku ta tashi ta yi wanka ta fara shiri, har breakfast yau ta d’an had’a musu ta ajjiye wa Yadira nata a k’asa, nata ita da Yash kuma ta hau sama da shi ta ajjiye a d’akin…
Yassir kuwa wanda yake ik’irarin ya zo kai su airport ne, sai da Yashjub ya zo tafiya sallah tukunna ya tashe sa da kyar…
Doguwar rigar abaya ta saka bak’a ta yafa mayafin..babu kwalliya ko k’adan a fuskarta amma ba k’aramin kyau ta yi ba.
Ahankali Yashjub wanda dawowar sa daga masallaci kenan ya k’araso ya tsaya a gabanta cikin kasala ya amsa gaisuwar ta, kafin ya yi shiruu kawai ya shiga kallonta, sai da ya gama k’are mata kallo tukunna yayi cupping face d’inta a cikin tafukan hannunsa yace‘’I’ll forever love you!a ko da yaushe inaso ki yi ruk’o da wannan kalmar dan daga zuciyata da ruhina ta taho babu hijabi’’
ya karashe maganar tasa yana mai sakar mata light kiss a saman lab’b’anta.
A hankali Manubiya ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya, dan kamar yadda yace mata maganar ta taho daga zuci da ruhinsa to itama haka maganar ta shiga cikin zuciyarta ta samu mazauni dan har kwalla sai da suka d’an taru a idanunta.
Cikin nutsuwa ya d’auke lips d’insa ya mannna mata wani light peck a kumatunta da forehead kafin yayi hugging nata yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, sun d’an jima a haka tukunna
ya cikata dakyar ya d’an gyara tsayuwar tasu ya koma gefenta ya sak’ale hannunsa na dama a cikin na hagun ta yace “shall we?’’
Yayi mata tambayar yana mai d’aga mata gira sama.
Murmushi ta yi tana jin tsananin son mijin nata da k’aunarsa suna ratsata dan har wani irin kallo Yash ya ga tana yi masa mai tafiya da imani da zuciyar wanda akeyi ma wa.Ahankali ya ce
‘’Baby wannan kallon fa?so kike ki sumar da ni?’’
Ahankali itama yadda yayi mata maganar kamar mai rad’a tace
“Ka yi kyau yau sosai, sosai!!’’
Ta fad’i maganar cik’e da shauk’i.
Wani irin blushing Yashjub ya shiga yi mai had’e da dariya
yana jin sa a sama……
“Mu wuce ko’’?
Muryar Yassir ta katse musu dogon kallon kallon da suke yi wa juna suna masu murmushi,mai cike da shauk’i da sak’onni.