← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 152

Sashe 19

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta zo shiga tukunna kuma sai ta fara kame-kame…
Ba k’aramin dad’i ta ji ba da bata ga Baba a d’akin ba, amma dukda haka sai da ta d’an ji nauyi dan kasa had’a
Ido ta yi da Inna, illa kawai sai
ta je ta durk’usa ta gaida ita daganan ta cewa Jidda ta zo ta tayata d’aukar kaya dan Muhsin yana shigowa ya fad’a toilet.

A hanya take tambayar Jidda ‘ko su Baba sun yi fad’an daren da ta yi?’ amman sai ta ji Jiddan ta ce mata a’a, besides ai ba ta yi dare sosai ba ma….
Sai a sannan ta sake, su ka kwashi kayan suka kai ciki.

Sai da Jidda ta je ta kira Siyama tukunna hankalinta ya kwanta, tare suka ware ledojin da komai,ita Manubiya sai da suka ware ma tukunna ta ga gift d’in Muhsin(agogo mai tsananin kyau na maza)da wayar da ya saka mata ba tare da saninta ba
iPhone mai kyau k’irar wadda ake yayi, shiyasa a take ta kirasa domin ta yi masa godiya…. har ga Allah gaba d’aya Yash ya sa ta fara jin wani iri dan gaskiya ita dai hidimar ta yi yawa..tana fara masa godiya kuwa ya chanza topic d’in dan dama yace mata ta daina yi masa godiya ba ya so!ba k’aramin dariya ya bata ba da ta ji ya ce ’’ta je aiki,ta na da report’’
da farko ta d’auka da wasa yake yi sai da taga ya dage tukunna ta tabbatar da gaske yake yi.
Aikuwa sai da ta yi da gaske ta ce ’’ga skul da za su koma soon”
dan ba’a ba su wani hutu mai tsayi ba, ‘ga kuma hidimar biki, dan Allah ya yi hak’uri ya bari ta tura masa kawai’’
tukunna da kyar ta samu ta shawo kansa ta lallab’asa ya d’aga mata k’afa amman da cewa ya yi sai ta je.

Daga nan ta ji ya yi shiruu kamar mai tunanin wani abun, dan haka ta shiga tambayar sa menene, sai da k’irjinta ya buga da ta ji ya ce ‘’Abbakar ya tab’a cewa yana son ki ne??’’

Sai da ya sake cewa’’umm???’’
Tukunna da iyaka gaskiyarta ta ce masa ’’A’a”

Numfashi ya fesar kafin yace “can I ask you a favor???”

Ahankali ta samu da kyar ta ce ’’E mana! anything’’
saboda yadda ta ji tashi d’aya muryarshi ta chanja sannan ranshi ya b’aci.

Cikin katse mata tunani ta ji
Ya ce ’’ko gaisawa ba na so ki sake yi da shi”

Sai da ya sake cewa “am I asking for too much?(ko hakan ya miki tsauri da yawa?)”
tukunna ahankali ta ce ”A’a”
sai kuma tace
“ba ma ya yi min magana fa,ya daina kulani”

cikin tarar numfashinta yace”saboda kishi ne ai yasa ya daina yi miki magana, saboda ya ji an fara maganar aurenmu, yanzu kuma ya ga za’a koma skul shine ya je ya karb’i transfer, yanzunnan Najeeb yake gayamin ya samu transfer, bakiga kalar wahala da kud’in da ya kashe ba amman haka ya bi a gaggauce ya yi transfer”

Shiruuu Manubiya ta yi, tana jin wani takaicin Abbakar yana taso mata…a tunaninta da kuma ganinta sam alk’awari bai ce haka ba, wato
ma gudun ta yake yi, a ranta tace”idan ma wani abun na yi mishi ai kamata ya yi ya neme ni da zancen mu sasanta ba wai ya yi irin wannan abu haka ba’’ dan ita kwata kwata ba ta yarda da maganar Yash da ya ce ‘saboda kishi ne ya sanya shi ya yi transfer ba….’
Ta fi yarda da ko dI wani abunsa sgi Abbakar ɗin ne ya sa ya yi hakan, ko kuma mahaifiyarsa….

Cikin son kawar da zancen Abbakar d’in Manubiya ta sako wata hirar, dan ya b’ata mata rai ba kad’an ba, da
kyar kuwa ta samu mood d’in Yash ya chanja, har yake bata labarin “ai Najeeb ma ya samu wani zazzafan appointment, dan haka zai bar skul d’in”.
Ta kuwa yi murna sosai dan ko ba komai sir Najeeb ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarta…..

Sai da Manu ta tabbatar Yash ya huce sosai tukunna suka yiwa juna sallama, kamar za su cinye juna don so haka nan su ka yi sallama ko wannen su cikin tsananin so da shauk’in d’an uwansa.

Tana gamawa su Siyama suka tisa ta a gaba da tsokana, abun mamaki har da Muhsin, ita sai a lokacin ma ta fara da na sanin yin wayar a gaban su.

Sai da Baba ya zo ta nuna mishi komai ya sanya albarka bayan ya gama fad’an hidimar ta yi yawa tukunna suka b’are wayar aka jonata a chargi

Dan jidda tace”tayi maza ta kwashe important abubuwanta ta cire layinta a tshohuwar wayar ta bata dan ta ma riga ta zama tata……

Har k’ofar side d’in su Siyama suka rakata dan lokacin da ta zo tafiya dare yayi sosai, tukunna suka koma nasu d’akin..
••
Yashjub yana gama waya da Manu dai-dai ya shiga bedroom d’inshi kenan kiran Daddy ya shigo wayarsa, yana d’auka ya ji muryar Daddy yana cewa”ka zo parlour na,Hajiya Maama na son magana da kai”

Yadda Yashjub ya ji muryar Daddy dama sai da gabansa ya yanke ya fad’i, shiyasa ko wanka ya gagara yi tashi d’aya ya juya ya nufi side d’in Daddyn yana jin yadda k’irjinsa ya ke bugawa akai-akai.

A zaune ya same ta, ita da Daddy da Ummi da mom da Abhi.
Sai da ya gaishesu one by one suka amsa tukunna ya nemi guri ya zauna.
Yana zama Hajiya Mama ta yi gyaran murya tukunna cikin rarrashi tace”Yash! da ni da iyayenka gasunan mun yanke shawarar za’a d’aga aurenka, za’a k’ara wata uku a kai. sakamokon matsalar gocewar k’ashi da ka samu.

kar ka yi gaggawa, ka bi komai a hankali, a je a samu a duba ka sosai dan a gaskiya ban gama yarda da gyaran da suka yi maka a nan ɗin ba, ka yi hak’uri ka bari a d’aga bikin, lafiyarka ta fi komai.

ka warke garau tukunna sai a yi komai cikin nutsuwa da kwanciyan hankali, ka ji d’an albarka”
Hajiya Mama ta k’arashe maganar cikin tsananin lallami.

Tunda ta fara magana idanun Yash suka cicciko da hawaye.
Kamar wani d’an Yaro haka ya d’aga kai ya kalli Abhi da Daddy Irin ‘ku sa baki mana’ d’innan..

ajiyar zuciya Abhi ya sauk’e kafin yace‘’Yash it’s for your own good (domin lafiyarka ne).
in banda kai da abunka ma ina kai ina yin aure a haka saboda Allah fa, tunda har mukazo aka yi tambaya aka yi komai aka baka Yarinyar nan to a ganina dan an k’ara wata uku ba komai bane, kamar yau ne.

ka yi hak’uri ka bi Junior da mom d’inku, ku je a duba maka hannun sosai ka warke garau! In yaso sai ayi auren…
I promise you, zan tsaya maka ka auri Manubiya under any circumstances (ko da ta halin ƙaƙa)
Ina nan har 3 months da ni da Hajiya Mama inshaaAllah sai an yi auren an kai maka amaryarka tukunna za mu koma.”

Cikin bashi assurance (tabbaci) Daddy da Hajiya Mama ma suka mishi alk’awarin duk rintsi inshaaAllah za su tsaya masa ya auri Manu, haka ma su Ummi.

Zuwa yanzu Yash har wani dishi-dishi yake gani tsabar tsaka mai wuyar da ya shiga….
manya sun sakashi a tsakiya suna so a d’aga for his own good sannan sun yi masa alk’awarin tsaya masa duk rintsi a yi auren,on the other hand kuma (a wani ɓangarem kuma ) gani yakeyi kamar idan aka d’aga wani abun ka iya faruwa, bayaga hakan ma kwata kwata baya k’aunar abunda zai janyo a d’aga auren nan.

Ahankali Hajiya Mama tace’’ka yi hak’uri, ka kwantar da hankalinka, ka samu lafiya tukunna.
fiancé d’inka (matar da zaka auran) tananan tana jiranka babu inda za ta je, kana dawowa za’ayi auren, ka ji ko?”

Cikin son jin amsar da za ta fito
daga bakinsa Abhi yace”kai muke jira Yash,a matsayinmu na iyayenka ga abunda muka ga ya dace,na yi magana da friend d’ina tuni, za a yi
maka booking appointment dan haka ya kamata ku tafi da wuri a je a dubaka da wuri, ko?’’

Da kyar Yash ya d’ago rinannun idanunsa….
da kyar muryarsa har wani karkarwa take yi yace”…….”

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 11*

Da kyar Yash ya d’ago rinannun idanunsa…

da kyar muryarsa har wani karkarwa take yi ya iya cewa ”duk yadda kuka ce Abhi Allah ya sa hakanne ya fi alkhairi.”

Ba k’aramin dad’i suka ji ba kuwa, dan haka suka shiga saka masa albarka tare da fatan alkhairi.

Ganin yana shirin fashewa da kuka a gabansu ne yasanya ya mik’e har wani jiri-jiri yake ji ya ce musu”sai da safe”
daga haka ya sa Kai ya fice, yana mai ji kamar ya kurma uban ihu!!
So yake ma ya yi kuka amma sam ya kasa, shiyasa ya nufi side d’insa ya na zuwa ya shige d’aki ko bi ta kan Junior bai yi ba ya shige ya rufe kanshi ya kashe wayoyinsa…….

Sai washegari da safe tukunna Manubiya ta ji labari, duk yadda take ta cewa ita dai 2weeks ya yi kad’an a d’aga amman sai ta ji ba dad’i, musamman ma da Yash ya kira ta ta ji kamar kuka ma yake shirin yi mata…gaba d’aya sai ta sake gigicewa.

Suna kashe wayar itama ta nemi fashewa da kuka, sai da Jidda ta d’an kwantar mata da hankali ta had’a da tsokanarta tana cewa
“au dan an d’aga aurenta shine za ta yi kuka?”
Tukunna ta wayance ta fake da borin kunya.

Dukda su Mommy sun ji, kuma sun san d’agawa kawai aka yi ba wai fasawa gaba d’aya ba, amman hakan bai hanasu shiga cikin tsananin farin ciki ba, ji suke yi kamar su zuba ruwa a k’asa su sha dan Baba Larai ta ce ’’d’agawan da aka yi hakan ma nasara ne, kuma za su samu isashshen lokacin da za su tarwatsa maganar inshaaAllah.
dan watanni uku kam is more than enough for them (ya ishesu) su yi abunda ya dace,”
Chapter 19 · 0% Book details