← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 152

Sashe 128

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kurum kwata-kwata sai na kasa d’aukar ciki.
Hankalina bai gama tashi ba sai da Imam ya kwashe dukiyarsa gaba d’aya ya damk’awa d’an cikin amaryarsa !!!
dama chan ba so nake yi Yaron ya zo duniya ba saboda Larai ta ce mini tabbas Namiji Amarya za ta haifa…dan haka Ina jin wannan batun na jajirce kuma na dinga yi wa Larai kuka har sai da ta tsaya tsayin daka ta taya ni muka kashe Yaron tun yana ciki! saboda ita Larai ta ce za ta yi komai amman banda kisan Kai, dan shi ya rabota daga garinsu ya kusan tona mata asiri, bayaga haka ita har ga Allah ba ta son yin kisa..to kukan da na dinga yi mata da kuma zancen raba dukiya da ta ji ne ya sanya ta biye mini a wanchan lokacin.

Tun daga nan muka k’ara k’aimi akan asirin da muke yi wa Khadija (amarya) akan ta bar gidan Imam, mu bata ta ci! mu ba ta sha! mu zuba mata a ruwan wanka amma sam abu ya k’i yin tasiri a kanta! kwata kwata ba ta ma da shirin tafiya, abun yana kama ta ba wai ba ya kama ta kwata-kwata ba kawai dai ba ya yin tasiri ne a kanta.

A kwana a tashi a haka har muka samu ciki a tare ni da ita…
Tunda muka samu ciikin Larai take aiki Akan ni in haifi Namiji ita kuma ta haihu babu rai, kamar yadda ta yi na farko…
cikin yana yin watanni biyar Larai ta fahimci Tabbas fa Khadija (amarya) sai ta haihu kuma Namiji za ta haifa, sannan Yaron mai tsananin albarka ne! Da sa’a! Dan dukkannin abunda ya saka a gaba sai ya cimm masa kuma attajiri ne mai masifar kud’i, sa’a da nasara ta ko wacce kusurwa ta rayuwarsa!.

Sai da na suma a tsaye!!
Bayan na gama jin wannan mummunan batu daga Larai, dan hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba, saboda a ranar ne na lab’e musu na ji Imam d’in yana sake damk’awa cikin jikin Khadija dukiyar sa kamar yadda ya yi a na farko, ita kuma tace ba zai you ba shine yace mata to a cikin mu ni da ita duk wadda ta haifi Namiji ita za a bawa…
shiyasa na nufi wajenta a hargitse dan na san idan muka yi kunnen doki to tsaff Imam zai yi son kai!
Dan haka na nufi wajen larai direct domin mu samu mu tattauna a nemo mafita to shine ita kuma ina shiga ta tare ni da mugun zancen….

Da kyar! Dan sai da Larai ta yayyafa mini ruwa tukunna na dawo haiyyacina da mugun kyar.
Ganin Ina shirin had’iyar zuciya in mutu ne ya sanya tace mini ‘’me zai hana mu musanya Yaran, ni in karb’i mai albarkar..’
tashi d’aya tun kafin ta k’arasa na k’i amincewa, na ce kawai a cigaba da aiki a kansa ta yadda ba zai yi albarka ba kuma ya yi rayuwa mara dad’i mara nasara ya mutu wulak’antacciyar mutuwa, tunda mun riga mun san sai fa ya zo duniya.

Wani babban tashin hankalin saida na yi scanning na tabbatar ni mace zan haifa!
saboda ban tab’a kawowa zan haifi mace ba duba da yadda muka dinga aiki akan in haifi Namiji.

A wannan lokacin ma Baba larai ce ta sake bani shawara kamar farko a kan mu musanya Yaran, inyaso bayan mun haihu an bayar da dukiyar idan ma kashe Yaron za mu yi sai mu yi tunda dai Yaro yana a hannunmu ai tsaf za mu iya yin kome muka ga dama sab’anin yanzu da yake a ciki.
Kuma kar in damu zata toshe duk wata hanya da za a zargemu ko da kuwa Yaron ya yo zubin uwarsa ne.
Tashi d’aya na amince dan a wannan karon kam na gamsu kuma na fahimta…tun a lokacin muka san yadda muka yi muka siye likitan da muke zuwa asibitin wajensa…ta hanyar yarda da shi da Baba Larai ta yi bayan ya fad’i mana shi hakan kawai yake da buk’ata daga garemu.

A ranar da na fara labour muka bata magani itama muka tayar mata da nata labour ɗin ta hanyar ba ta kwayar da ya bamu a ruwa ta sha ba tare da ta sani ba.
Tana shiga d’akin haihuwa gudun kar ta fahimci wani abun aka shak’a mata anesthesia aka yi mata cs!!

Kusan a tare muka haihu
Ita aka fito mata da Yashjub ni kuma na haifoki, Likitan da nurse d’in da Baba larai suka yi sauri suka sauya, aka fitar da ke a matsayin Y’ar da ta haifa, ni kuma bayan y’an mintuna aka fitar da Yashjub aka ce na haihu.

Daddy ya bada rabin dukiya kamar yadda ya yi alk’awari, amma fa ba ni da burin mallakar wannan dukiya kamar yadda nake da burin kashe Yashjub saboda kwata kwata ko fuskarsa ba na son kalla, gashi aka tilasta mini hakanan Ina ji Ina gani na dinga shayar da shi.
Kwatsam!!ina ta shirye shiryen yadda za a yi in raba shi da duniya ba tare da kowa ya zargemu ba sai ga ciki a jikina, cikin y’an biyu..

Tun cikin yana da watanni hud’u Baba Larai ta fara mafarkai marasa dad’i game da Yaron da zan haifa..Tabbas mun fahimci Namiji ne kam wannan karon ammafa Yaron kwata-kwata bashi da albarka, ga kuma mutuwa da zai yi wulak’antacciya idan har bai yi arzik’i ba!!! sannan duk abunda ya soma to ba zai yi albarka ba…

Hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba, dan sai da jini na ya hau na kwanta a asibiti sau bakwai saboda wannan duba da Baba larai ta yi ta gano mini bala’i..sai da muka nutsu muka yi lissafi Sosai muka bincika tukunna muka gano Ashe ‘asirin da muka yi wa Yashjub tun kafin ya zo duniya ne ya fad’a a kan Yassir!’
tunda asirin an yi sa ne a d’an Khadija matar Imam kuma kinga nima sunana Khadija, sannan nan gidan imam aka jefa shi shiyasa duk daɗewar abun sai ya dawo ya faɗo nan ɗin.
Sannan ko bayan da muka fahimci abun bai kama Yashjub ba bamu damu mu yi wani abun a kai ba dan kwata kwata ba mu kawo cewa zai fad’a kan Yassir ba bayaga haka babu ma ta yadda za a yi mu karya abun saboda ba zamu iya nemosaba, dan a babban ruwa mai tafiya muka jefa dan haka kinga la shakkah ba ma ya cikin Nigeria, ya bi ruwa.

Babu abunda ba mu yi ba, babu kuma abunda bamu gwada ba amma idan muka yi aikin muka gwada in banda wasu sabbin masifu a kan na da babu abunda muke gani a tauraron Yassir, amma ita d’ayar Yarinyar lafiya lau dan zuwa wannan lokacin mun fahimci twins ne.

Kamar kullum a wanchan lokacin ma Baba larai ce ta sake kawo shawarar’mai zai hana mu yi hak’uri mu taushi zuciyoyinmu mu raini Yashjub! tunda shi zai yi albarka, in ya so idan ya girma ya gama tara abunda ya tara sai mu san yadda muka yi muka d’aura Yassir a kan dukiyarsa, shi kuma Yashjub mu kashesa!
Daga nan komai ya dawo hannunmu, in ya so sai Yassir ya kula da komai tunda ba Yassir d’in ne ya fara tarawa ba..dukiyar ba tasa bace ba dan haka in sha Allahu ta san komai zai tafi cikin sauk’i, abun zai yi albarka!
dan shi Yassir d’in abunda ya fara ne dakansa ba zai yi albarka ba. So inshaaAllah komai zai yi kyau.

Sannan idan hakan ta faru babu batun wulak’antacciyar mutuwa a Yassir tunda a yadda ta gani sai idan ya rasa komai ya rasa kowa ne tukunna wannan al’amarin
zai faru da shi.’

Ko kad’an ban yi mata jayayya ba, dan nima plan d’in ya yi mini d’ari bisa d’ari.
Dan haka muka tashi muka tsaya tsayin daka na danne zuciyata, na ja Yashjub a jikina, na kula da shi duk dan saboda y’ay’ana, sai dai kuma tun lokacin da Yashjub ya kai shekaru 4 a duniya na fahimci kamar ma ya tsane ni!
Sam ba ya son magana ma da ni, ba ya son shiga jikina, baya jan y’an uwansa a jiki…
Gashi duk cikinku mahaifinku ya fi son shi…
Daga k’arshe ma Hajiya mama ta d’aukesa gaba d’aya ya koma wajenta…na so ya dawo a wanchan lokacin amman a banza, dan yadda Hajiya mama ta ga na d’aga hankalina na san shiyasa ita kuma ta ce ba zai dawo ɗin ba.

Yashjub tun yana zuwa mana
hutu sau 2 a shekara, daga baya ya koma sau d’aya ko
bayan shekaru biyu, daga k’arshe ma ya daina..sai dai Daddy da su Yassir su je, ni kuma a lokacin mun yi kacha kacha da su Hajiya mama tace idan ta ganni a inda take sai ta yi mini abunda ban tab’a tsammani ba.

Tun Yashjub yana shekaru 17 na so ya fara saka su Yassir d’in a jikinsa, da suka girma suka yi wayo sosai nan ma na yi masa maganar ya fara saka shi a business d’insa amma ya k’i, na zo nace to ya bashi jari nan ma ya k’i, gashi a lokacin na fahimci son kan da Daddy ya kuma yi a lamarin yadda ya kasafta share na company d’insa.
shima
gashi (shi Yashjub d’in) ba ma ya nan ballantana in san yadda zan yi in yaudare sa ya ja d’an uwansa, gashi kuma asiri bai cika tasiri a kansa ba kamar Khadija(uwarsa).
Chapter 128 · 0% Book details