Sashe 124
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallamar Junior ce ta katsewa Hajiya Mama tunanin da take yi,
A hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta kallesa tace”ba sa gidan ko?”
Jinjina kai ya yi ya zauna a gabanta tukunna yace”driver d’insa na samu yana tartare kayansa, shine ya ke ce min wai an sallameshi ne saboda Yash d’in yace masa ‘sun tashi daga gida’
Yau da asubah wai ya kaisu hotel, d’azu kuma ya je ya d’aukesu ya kaisu airport,yace bai san jirgin Ina suka bi ba.”
Ajiyar zuciya hajiya mama ta sauk’e bayan ya dire aya, tace masa”ba ni wayata”kawai.
Yana mik’a mata ta nemo number Daddy ta danna call ta kara a kunnenta.
Ko gaisuwarsa yanzun ma ba ta amsa ba tace
“Yashjub ya tafi ba ya nan,ya turo mini message ya gaya mini abunda Khadija ta je gidansa ta yi Jiya,yace min dan Allah kar a nemesa.
Dan haka Ina mai baku umarnin kar wanda ya bibiyesa kamar yadda ya buk’ata,
ku bar shi ya huta da bala’in Khadija da y’ay’anta.
Ka ja mata kunne ka jawa su Yasira kunne sannan ka gayawa d’an uwanka shima ya sani.”
Tana gama fad’in haka ta kashe wayar ta ajjiye a gefe zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Daga wajen Hajiya mama direct gida Yahanasu ta nufa, dan tana son magana da Mommy, yau kam!
ba za ta yi shiru ba!abun ya yi yawa.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 40*
A d’aki, side ɗin su Yadira ta same ta ita da su suna hira…
Tana shigowa duk suka d’ago suka kalleta, sai kuma suka d’auke Kai babu wanda yace mata ci kanki, hakanan suka ci gaba da hirar su.
Mommy tana shirin yi mata magana ita Yahanasun ta riga ta ta hanyar cewa”Ina so za mu yi magana!”
Sai da gaban Baba larai ya yanke ya fad’i, dan in ba da kyar ba a yadda ta ga Yahanasu yau kam tabbas za ta iya fasa mata kwai a wajen Mommy, kuma ta san Mommyn za ta ji haushinta.
Kallon Yahanasu Mommy ta yi kafin ta d’an kalli Baba larai sai kuma ta mik’e ta nufi Yahanasun ba tare da ta saurari
Yusra wadda take cewa”eh lallai rainin hankali ma kenan.”ba.
Duk idanu suka zuba musu Baki sake har suka fice daga d’akin.
Side d’in Mommy suka nufa, suna shiga Mommyn ta kalleta tace”ya aka yi ??Yahanasu”.
Har ga Allah ta san bai kamata ta dinga jin haka game da uwar da ta kawota duniya ba amma she can’t help it!
Wani Irin haushi da takaicin Mommy take ji, ba ma ta jin za ta iya tsayuwa su yi wata doguwar magana, dan haka cikin k’aguwa da son barin inda take ta d’an matso kusa da ita tana kallon cikin idanunta tace”ki cewa Yashjub kin janye maganar tsinuwa, sannan ki daina yi masa barazana da tsinuwa idan ba haka ba wallahi tallahi sai na gaya masa cewa ‘ba ke ce kika haife sa ba’!”.
Wani irin zabura Mommy ta yi, jikinta ya d’au karkarwa, gaba d’aya ta fice a haiyyacinta, tashi d’aya fuskarta ta yi jazur!!..
D’an k’ura mata ido Yahanasu ta yi kafin tace”kamar yadda na tsammata..ba ki san na sani ba ko?to kuwa wannan karon Baba larai ta munafurce ki.”
Hawayen da suka zubo mata ne suka sanya ta yin shiru, itama Mommyn hawaye ta ke yi sosai zuwa yanzu.
Da kyar Yahanasu ta tsayar da hawayenta ta goge fuskarta tukunna ta ce
“A ranar da kuka dawo daga makarantarmu!
A ranar da kuka je kuka had’a guiwa da principal d’inmu kuka saka ta shirgawa Mama k’arya kuka ce Daddy ne ya fad’a!
To a wannan ranar ne na ji komai.
….Tun lokacin da Mama ta fara zuwa wajena a makaranta, na so in fad’a muku ke da Daddy, amma sai ta ce mini ba ta so ku sani, wanda a lokacin laifinta na gani da ta nemi in b’oye muku amma da na ji abunda kuka yi kuka saka aka ce mata Daddyn yace! ne ya sanya na fahimci dalilinta na cewa in b’oye muku.
Tana zuwa wajena a kai a kai, har ta fara yi mini maganar ‘tana so za ta d’auke ni in zauna a wajenta, shin zan bita?!’
ni kuma na ce mata ‘eh’.
A wanchan lokacin shekaruna ba su haura takwas a duniya ba, amma sai na yi lissafin cewa ‘idan na b’oye muku wannan al’amari to
kamar na munafurceku ne’
dan haka na yanke shawarar gaya muku ke da Daddy saboda daga ke har shi kuna nuna min tsananin soyayya shiysa na ga rashin dacewar b’oye muku zancen.
Ina zuwa dai-dai k’ofar d’akinki na ji muyarki cikin fushi kina cewa
“Larai!!wannan yana d’aya daga cikin dalilan da suka sanya na ce miki kar mu fitar da Khadijah har ma da mallan lawal d’in, amma kika k’i yarda kika ce ba za ki iya bari su mutu ba!
Yanzu ai ga irinta nan, inda ace Daddy ne ya fara jin labarin zuwan da Khadija take yi wajen Yahanasu! Ya fahimci ta na raye har yanzu ai da mun shiga uku!!!.
Kuma yanzun dan mun cewa principal tace mata ga abunda Daddyn yace ke kina tunanin za ta hak’ura ta daina bibiyar y’arta ne?dan kawai ance za a tona mata asiri?
ina ce farrak’u kika ce kin yi mata da duk ahalin gidan nan sannan kin kafeta a duk inda take? To ya akayi ta fito?”
Sai da Yahanasu ta share hawayenta, tukunna ta kalli Mommyn ta ce
“Kai na ne ya d’aure a take a lokacin bayan na gama jin hakan, dan ban gama fahimtar me kike nufi ba, har sai da na ji batun Baba larai tukunna na fahimta,ta inda na je tana cewa”Kar ki damu akasi aka samu, amma zan gyara, sannan saboda Allah Mommy yanzu ace duk Irin taimakon da lawal ya yi mana sai mu barshi ya mutu??
ba dan shi ba ai da tuni Khadija har yanzu tana tare da Imam…”
A lokacin shekaruna takwas amma tashi d’aya na fahimci abunda kuka yi, na fahimci komai, saboda a ko da yaushe cewa ake yi gobara ne ya kashe mahaifiyata kuma na tuna yadda ko shekara ba a yi ba Daddy yace mana kar wanda ya sake kiran ko da sunanta, sannan akwai ranar da na ji yana kuka yana cewa Hajiya mama ‘da ya sani ya tsananta bincike, da ya sani bai kunna musu wuta ba.’
Shiyasa na fahimci komai, kuma na fahimci tabbas duk shirin ku ne ke da Baba larai.
So na yi in tona muku asiri amma sai na ji kina cewa”shikenan na yarda da ke, amma gaskiya ya kamata ki yi Abu mai k’arfi wannan karon a kansu, ki sake kafe ta a duk inda take, inda Hali ko makwabta kar ta dinga samun jin dad’in shiga!
saboda wallahi na tsorata matuk’a sannan inaga Larai gara kawai in fito in gayawa Yahanasu gaskiya, ina so ta san cewa ni ce na haifeta! na san za ta fahimceni!…
kalli fa yadda Khadija take zuwa wajenta a b’oye a matsayin Mahaifiyarta itama kuma ta b’oye mana!
A gaskiya abun ya fara damuna, kuma Ina tsoron kar ta girma abun nan da na yi kuma na yi shiru ya ya lalata alaƙa ta da ita”
Shiruu Yahanasu ta yi tana kaiwa nan, sai da ta jima tana ƙoƙari tukunna da kyar ta iya tsayar da hawayenta ta samu ta ci gaba da cewa
“Ban yarda da abunda kunnuwana suka jiye mini ba, sai da na ji Baba Larai ta katse ki itama tana cewa
“Khadija ki rufa mana asiri, kar ki ja mana,kar ki je garin soyayya da k’ulaficin y’arki ki je ki tarwatsamu!!Wallahi ko da wasa idan aka san Yahanasu ce y’arki ba Yashjub ba to komai ya lalace mana kenan..kar ki yi tunanin idan kika gaya mata maganar za ta b’uya, ni na san dole za ta fito, dan haka ki ja bakinki ki yi shiru, har mu samu mu cimma burinmu tukunna sai mu san abunyi!
As far as I know Yahanasu tana gabanki, za ki kula da abarki, sannan babu wanda zai cutar miki da ita, dan haka idan har zan baki shawara ki d’auka to ki ja bakinki ki yi shiru.
Sannan kuma! yadda kike yi a gaban Daddy ki d’an rage, har ma a gaban su Yasirar suma duk ki rage..jiya bakiga al’ajabi da mamakin da Daddy ya shiga ba da akace masa kin daki Yasira saboda Yahanasu, kuma itama Yasira suna cin abinci ina jinta tana cewa ‘Mommy ta fi son Yaha a kansu!!’
dan haka ki ja bakinki ki yi shiru sannan ki
Iya takunki tun kafin ki tonawa kanki asiri.”
..
Zuwa wannan lokacin har sheshsheƙa Yahanasu ta ke yi, a hankali ta sa Hannu ta goge hawayen da su ka ƙi tsaya mata, kafin ta ci gaba da cewa”Ina jinta tana ce miki kar ki damu ko nan da shekara nawa ne indai kika gaya mini ke ce mahaifiyata ta asali to ba zan guje ki ba, kuma ba zan ji haushin ki ba dan
za ta yi mini katanga da Mutane saboda gudun kar in yi k’awaye a gaba in fahimci duniya su zuga ni idanuna su waye in fahimci kin zalinci ni!
Sannan za ta rufe mini Baki saboda kar in gayawa kowa na ga Mama, sannan za ta rabani da Mama, ba zan nemeta ba ta inda za ta yi mini abunda ba iyaka Maman kad’ai ba ban Isa in sake shiga jikin wani har mu yi sirri da su in kasa fad’a miki ba!
Na k’arshen kuma tace
Za ta yi abunda ke kad’ai za ta bari a jikina, bayan ke babu wanda ya Isa ya shiga jikina har ya san cikina, komai kawai kika ce zan bi ki in karb’a hannu bibbiyu ba zan yi jayayya ba.!….
Saboda har abada ba za ki gayawa Daddy gaskiyar tsakanina da ke ba dan gudun matsala, dan haka idan kuka yi mini hakan to za ki gaya min ke mahaifiyata ce ni kuma zan amince in karb’eki
Hannu biyu, kuma ba zan gayawa kowa ba sannan ba zan kuma ji haushi ba!.