Sashe 56
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk dariya sukayi, kafin su fara mik’ewa da niyyar tafiya…
da sauri yace”Au wai dama da gaske kuke? tafiya haka da wurwuri kamar ana korar ku?”
Wayarsa ce ta d’auki k’ara, dan haka ya yi excusing kansa ya matsa gefe domin amsa kiran Mommy…
Yana wucewa Manubiya ta d’ago Kai ta kalli Aisha wadda har yanzu bata zauna sosai ba ta ce ”Wai da gaske tafiya zakuyi haba mana”
Ta fad’i hakan kamar zata fashe da kuka.
Murmushi Aisha ta yi tana shirin yin magana muryar Ya Musbah tq katseta ta inda ya ke cewa”Manu, kuka kikayi ne?”
Saida ta sunkuyar ta kanta k’asa na d’an lokaci, tukunna ta d’ago ta kalle sa tace “A’a”
Sai kuma hawaye sharr suka b’alle mata a take kamar an kunna famfoo.
Cikin rashin jin dad’i Aisha tace
“Kinga dalilin da ya sa mukeson tafiya da wurin kenan!..
Yanzu dan Allah idan ya dawo ai sai yayi tunanin mu muka ce wani abun ko.
Taya zaki sa kuka haka?
So kike ki janyo mana bak’in jini?”.
Zuwa yanzu Ya Musbah ya tamke fuska tamau tsabar takaici!…
Duk rashin hak’urin Baraka sai da ta yi wata goma sha d’aya a gidansa tukunna ta fara kuka a ranar sunan mai sunan baba, saboda ba’a yanka mata rago da tunkiya ba instead an yanka iyaka rago.
Amman shi kalli k’anwarsa ko sati d’aya ba ta yi a gidan miji ba amma har ta fara kuka!
Ba ma hawaye ba…
A hankali ya mik’e ya k’arasa inda take ya zauna a gefenta,
yana jin tsananin tausayin ta yana ratsashi, cikin nutsuwa ya bud’e Bakinsa ya fara magana
“Manu ko ma menene ya faru ki yi hak’uri kinji ko?
ki daina kuka,
haka auren yake sai hak’uri..”
Ajiyar zuciya Ya Nafi’u wanda ya ke shirin tsaida Ya Musbahn ya sauk’e, dan a tunanninsa tambayar ta Ya Musbahn zai kuma yi akan ‘mai akayi mata’
amman sai yaga yayi lissafin manya, dan haka ya d’an ji
sanyi aranshi saboda shima ba kad’an ba ya ji ba dad’i game da yanayin da suka tadda Manu d’in a ciki.”
Dakyar Ya Musbah ya sake cewa”Mun so mu d’an zauna amman kukan nan naki ya koremu”
Da sauri ta dag’o kanta ta shiga goge hawayen nata tana cewa “Allah na daina”
Murmushi yayi yana mai jin inama ace yanada ikon da zai iya goge mata koma wanne irin takaici ne yake addabar zuciyarta haka.
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ”nan gaba idan mun zo, sai ki yi k’ok’arin k’in yin kuka ko?idan har ba ki yin ba sai mu zauna,kin ji?”
Ya fad’i hakan cikin d’aga mata gira d’aya.
Dai dai nan Yashjub ya k’araso wajen, tun d’azu ya gama waya da Mommy amman ya kasa komawa wajen su..tunda yake bai tab’a jin kunya da nauyi irin wannan ba, dan tun d’azu tunda ya d’ago ya ga Manubiya tana kuka ya ji wata kalar kunyar ta da nauyin su Ya Musbah sun yi masa kawanya.
Sam bai kamata ace ya bari hawayenta su zuba ta silarshi ba, ever!.
Yana k’arasowa Ya Musbah ya mik’e ya k’arasa inda yake ya mik’a masa Hannu, da kyar
duk su biyun suka k’ak’alo murmushi kafin Ya Musbah yace “Kayan suna varender anan muka jere su ,mun so mu shishshigo da su har kitchen mu d’an zauna to amman wannan shagwab’abb’iyar matar taka ta kore mu…daga
ganin mu ta hau kuka.
Bara mu wuce
Allah ya sanya alkahairi.”
Wani abune ya tokare k’irjin Manubiya ganin yadda duk cikinsu babu wanda ya damu ma ya tambaye ta me akayi mata, sannan kuma bama za su tsaya ma ta gansu sosai su yi hira ta d’an ji sanyi ba, har zasu tafi..ga kuma kishin Kausar wanda zuwa yanzu haka kurum ta ji ya sake turnik’e ta,
dan haka kawai sai ta mik’e da kyar ta je ta yi hugging su Siyama tace “na gode”
daga haka ta wuce sama da sauri mai kamar d’an gudu dan
bataso ta sake sakin wani kukan a gaban su kar su ce sun fasa dawowa next time d’in ma gaba d’aya.
Tun kafin ta kai ga k’arasawa d’akin nata ta saki kuka.
Yashjub ne ya rakasu har mota yana ta musu sannu da godiya da basu sak’on gaisuwa a Baba da Inna, dauriya ce kawai yake yi dan gaba d’aya jin sa yake wani iri duk ba da’di.
Sai da ya ga fitarsu tukunna ya kira masu gadi yace su shigar da komai ciki.
Kasa tsayawa ya yi har su gama, hakanan ya barsu anan k’asan ya nufi d’akin Manubiya ransa duk a jagule…ya lura bayan cin fuskar da su Yassira suka yi wa Manubiya da kuma zancen Kausar tabbas akwai shagwab’a da tab’ara a lamarin nata, ya san sai ya yi rarrashin da gaske tukunna za ta sak’k’o…gashi Mommy ta kira shi tace “ya zo shi da Manubiya yanzun nan!…..”
Kamar d’azu yanzun ma a zaune ya same ta a bakin gado,
tana kuka.
A hankali ya k’arasa inda take ya durk’usa a gaban ta….shi fa bai iya rarrashi ba wallahi bai ma san ta Ina zai fara ba!.
Tun lokacin da ya durk’usa a gaban ta gaba d’aya sai ta ji ba dad’i!
Dan duk lalacewa, komin takaicin da take ji bai kamata ta bar shi ya d’urkusa haka da sunan bata hak’uri ba, dan ta san hak’urin zai bayar.
A hankali cikin sharar hawaye tace”Ka tashi,ba kuka nake yi ba”
Murmushi yayi kafin ya ruk’o k’afafunta ahankali yace “Dan Allah ki yi hak’uri…”
Da sauri ta zamo daga kan gadon, ta fara k’okarin kwace k’afafun nata tana cewa”Ni dai dan Allah ka daina!babu kyau.”
Y’ar guntuwar dariya ya yi yana kallonta yace
‘’babu kyau miji ya bawa matarsa hak’uri?’’
Cikin tarar numfashinsa tace
‘’A’a, babu kyau ka durk’usa kamar haka, dan Allah ka daina, kana sakawa Ina jin ba dad’i”
Ta fad’i hakan tana mai goge ragowar hawayen da sukayi saura a fuskar tata.
Cikin kwabe fuska tare da kwaikwayar muryar ta yace
“To ke ba ki san babu kyau ki yi ta kuka kina d’aga min hankali ba?”
Sannan ya ɗaura da cewa
“sannan kalli fa a yadda su Siyama suka tafi, na san duk hankalin su a tashe yake, za ayi tunanin ko har na fara cutar da ke ne tunda daga ni sai ke a gidan. Ni addua ta d’aya ma kar su gayawa su Baba”.
Shiruu ta yi tana sauraron sa,
ganin hakan yasa ya matso kusa da ita sosai ya tallafo fuskarta a tafin hannunsa yace “Hawayen ki tsada gare su, dan Allah dan Allah Baby ki daina saurin zubar min da su.
kalla idanunki gaba d’aya kin wahalar min da kanki ba tare da kin tsaya kin ji kan zancen ba ma.”
Shiruu ta yi kawai ta kasa cewa komai, haka shima yayi shiru ya zubawa kyakkyawar fuskarta ido…kad’an kad’an ta ji yana matso da fuskarta garesa yana d’an murza gefen kumatunta, ta san inda ya nufa shiysa ta yi saurin mik’ewa ta juya masa baya tana kallon gadon tana mai gyara d’aurin dankwalinta.
Lumshe ido ya yi, ya bud’e kafin ya mik’e tsaye ya na kallonta, lokaci d’aya ya saka hannu ya yi hugging nata tsantsan ta baya, a hankali ya d’aura kansa a kan dokin wuyanta yana mai shak’ar k’amshin jikinta mai sanyaya zuciya had’i da ɗimauta shi a ko da yaushe.
Cikin tsananin mutuwar jiki ya ce “ki yi hak’uri ban gaya miki asalin maganata da Kausar ba,
dalili kuwa shine a lokacin da na ji maganar sam ban dauk’i abun serious ba, shiyasa kikaga ban saka shi a fannin da yake da mahimmanci na rayuwata ba.
Dukkannin abunda na gaya miki kika sani game da ni tou shine mai mahimmanci duk abunda kika ga ban gaya miki ba tou bashi da mahimmanci da amfani shiyasa, amma naga kamar rashin gaya miki maganar Kausar d’in yana neman janyo wani labule a tsakanin mu wanda ba zan bada k’ofar hakan ba.”
A hankali ya juyo da ita yana facing d’inta rik’e da k’ugunta ya fara zaiyyano mata yadda ranar ya ji Kausar tana gayawa Mommy ‘tana sonshi’
sannan ya d’aura da cewa”Wallahi Wallahi apart from Kausar d’in da Mommy sai kuma Yahanasu da ya gayawa sam shi bai ma san wani a ciikin su Yassira ya san da zancen ba, bai san maganar ta je kunnuwansu ba ta yadda har suke tunanin zai aureta, shi a mazaunin shirme da rashin tunani ma ya d’auki maganar tata shiyasa bai bawa abun mahimmanci ba.
Amman yana so ta yi masa alfarma d’aya!’ta manta da komai da kowa
ta yarda da shi akan abunda zai fad’a mata yanzu
‘Tun yana Yaro shi tsarin mace d’aya garesa, kuma Kausar ita ce Mace ta ƙarshe da zai iya aura,
saboda kwata kwata jininsa bai d’auke ta ba tun yarinta,
ko da ace su biyu ne kad’ai suka rage a duniya ba ya jin zai iya rayuwa da Kausar a matsayin matarsa’….’’
A hankali Manu ta sunkuyar da kanta tana jin wani sanyi da nutsuwa yana lullub’eta, dan tabbas maganganunsa sun rufe kusan kaso arba’in na damuwarta, zuwa yanzu ta fahimci ba b’oye mata yayi ba.
Dukda tana fargaba da kuma kishin yadda Kausar d’in take son Mijinta amman still ta d’an ji sauk’i da ya fito ya gaya mata komai, sannan daga yanzu ta zaɓi ta yarda da shi akan lamarin,kamar yadda ya buk’ata.