Sashe 71
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da kyar dai ta kawar da tunanin, suka k’arasa Ummi ta ja mata kujera ta zauna itama ta zauna.
Sai a lokacin tukunna Mommy ma ta zauna, tana mai jan
numfashi da kyar, dan ji takeyi gaba d’aya iskar parlourn ta yi mata k’adan!
Yanayin Manubiya da kalar cika da fresh d’in da ta ga ta yi dama a gaskiya indai idanuwanta ba gizo sukayi mata ba tou kuwa ciki ta hango d’anye ma kuwa, yanzu kuwa jirin da ya kwasheta ya sake tabbatar mata…amma taya? Ta san dama shi Yashjub ba kasafai abu yake kama sa ba ko ya kama sa ma to ba ya dad’ewa a jikinsa wannan gado ya yi a jininsa yake, sannan bata tab’a iya juya masa lissafi…to amman ita Manubiya fa??
taya akayi har ta bari wani abun ya shiga tsakanin ta da shi da har ta kai ga samun ciki!
Idan ma ta bari d’in to taya ciki zai iya zama a jikinta bayan ajiyar da akayi…
Anya ba gaskiya Yasira ta fad’a ba kuwa da tace ‘aikin Baba larai ya daina ci yanzu!’
Tunda gashi dai
tun farkon had’uwarsa da Yarinyar nan aka gagara rabasu, aka gagara lalata maganar auren,
suka gagara su hana d’aurin auren, suka gagara cireta a ransa da rayuwarsa,
yanzu gashi ciki yana neman b’ullowa kuma sun gagara cusa Kausar cikin gidan Yashjub.
Dan haka
Indai har Yarinyar nan ba waliyyiya baceba tou tabbas da gaske aiyyukan Baba larai sun daina ci.”
Mommy ta aiyyana hakan a cikin ranta.
Yasira ce ta zuzzuba mata duk abubuwan da suka dafa a plates ta tura mata gabanta tana mata wani kalar murmushi kafin tace “bismillah”
Ahankali Manubiya tace “thankyou”sannan ta sa Hannu ta d’an sake jan abincin gabanta.
Da kulawa Daddy yace
“In duk abincin ba su yi miki ba, akwai cooks ki fad’i abunda kike ra’ayi sai a dafa miki.
Ahankali Yassira tace
“Idan ma na waje kike so sai a siyo miki”
Dakyar Manubiya tace
‘’A’a zan ci wannan d’in ,nagode sosai ‘’
Tana mai jin dad’in yadda Daddy yake yi mata had’e da mamakin Yassira.
Sai da ta juya ta kalli
Inda Yashjub yake zaune a chan cikin parlour ya yi kicin-kicin da rai, tukunna ta juyo
ahankali ta d’auki lomar abincin da Yahansu ta zuba mata ta kai Baki…..ba don kar ta fito da shi waje su ji ba dad’i ba tou da tuni ta fiddo sa dan tashi d’aya ta ji wani irin amai ya yunk’uro mata dan haka ta yi sauri ta had’iye ta d’auka ruwa ta kora ta shiga k’ok’arin danne aman da yake ta so ya fito, a ranta kuma tana mamakin ‘wacce irin fever ce haka wadda bata tab’a yin irin ta ba mai amai’ dan har ga Allah kwata kwata lissafin ta bai kawo mata ciki ba.
Cike da k’arfin hali ta d’aura spoon d’in ta a plate d’in da Yassira ta turo mata gabanta
gudun kar Mommy ta ji ba dad’i idan ba ta ci nasu ba…a hankali ta deb’o ta yi bismillah a cikin ranta ta nufi bakinta da shi wanda hakan ya sa tun
daga kan Mommy har izuwa kan Yadira gaba d’ayansu suka tsaya da cin nasu abincin sukayi mata ‘k’uuurrr!’ da ido suna jira kawai su ga ta kai cikin bakinta.
Da mamaki Daddy ya saki Baki kawai yana kallon su…lura da hakan da Baaba larai ta yi ne yasa ta yi sauri ta zunguri Mommy cike da takaici, da sauri Mommy ta juya ta kalle ta, Baba laran tana shirin nuna mata yadda Daddy yake kallonsu suka ji Manubiya ta tura kujerar ta baya da sauri ta mik’e…
Ko gama juyawa ba ta yi ba amai ya kece shaaa……..
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 27*
Da wani irin sauri Yashjub ya taso ya k’araso inda suke, yana zuwa ya rik’eta da niyyar shigar da ita ko da d’akin Yahanasu ne amman hakan bai yiu ba!
Dan tashi d’aya ta shiga kwarara masa aman da ta ke yi ɗin a jikinsa ba ji ba gani…ganin yadda jikinta yake karkarwa ne ya sanya ya riketa sosai had’eda d’an tallafota,ahankali ahankali yana d’an bubbuga mata baya.
…
Sai da ta amayar da gaba d’aya abun da ke a cikinta tukunna ta d’an fara dawowa cikin haiyyacin ta…dukda yadda take cikin jin zafin abunda ya gama yi mata d’azu, sai ta tsinci kanta da jin tausayin sa da kuma rashin jin dad’i ganin yadda gaba d’aya ta b’ata masa jiki.
Still layi ya ga tana yi
Bayaga hakan wannan uban aman da ta shek’a dama dole ta zama bata da k’arfi a Jikinta, dan haka ya durk’usa bai damu da wai a gaban su Daddy yake ba kawai ya kinkimeta ya nufi d’akin Yahansu da ita.
Da sauri Kausar ta goge hawayen da suka silalo mata, sai kuma ta juya ta nufi sama da gudu. Kallon ta kawai Yassir ya yi, saida ta b’acewa ganin sa tukunna ya juya ya kalli su Yashjub da suke shiga d’akin Yahanasu kusan a tare da shi da su Ummi da Munirat da Yahanasun.
Sai da ya kaita cikin shower glass tukunna ya dire ta.
Sai a sannan itama ta bud’e idanunta.
Gaba d’aya fanfunan dake a jikin shower d’in ya ware musu
wanda hakan yasa ta sauk’e wata k’ak’k’arfar ajiyar zuciya.
Ganin yana shirin fara zuge mata zip d’in rigar tata ne ya sa da sauri ta ce”Dan Allah A’a, su Yahanasu fa suna waje!
Idan muka gama wankan ta ya za mu fita??”
Murmushi kawai ya yi yana kallon ta yace”Kar ki damu, kafin mu gama mu fita na san za su fita su,
ba za su zauna a d’akin ba.”
Ya fad’i hakan yana sake k’ok’arin ruk’ota yana mai jin wani so da k’auna da kuma tausayin ta suna ratsashi
Add’ua kawai yake yi Allah Ubangiji ya sa tunaninsa ya zamo gaskiya.
Turo Baki ta yi ta d’an ja baya da dukkan ragowar k’arfin da take ji kafin tace
‘’A’a ni dai,kuma Allah ka daina d’aukata a gaban su Daddy dan ni yanzu ban san ma ta Ina zan fara kallon su ba”
Shiruu kawai ya yi yana kallon ta yana wani irin murmushi
kafin a hanakali ya matsa yace
“Sorry!ki yi hak’uri akan abunda ya faru ɗazu, amma dan Allah kar ki sake,
Har yanzu zuciyata zafi take yi.”
Ta fahimci mai yake nufi dan haka ta had’e rai tace
‘’A tunanin ka na fad’a jikinsa da gangan ne?‘’
Shiruu yai yana kallon ta, dan shi sai yanzu ma ya yi wannan lissafin…a hankali ya fesar da iska ya matso ya yi cupping face nata a cikin tafukan hannunsa sannan yace
‘’Mu bar maganar pls, na ji na yi laifi, rashin fahimta ne aka samu, kuma bai kamata in yi miki hakan sannan a gaban Mutane ba, ki yi hak’uri ki yafewa Babyn ki, um…..”
Ya yi maganar yana mai lankwasar da Kai.
Cikin d’aura hannayenta a kan nasa tana k’ok’arin kwatar fuskarta tace
‘’Kai d’in Babba da kai ai ba Baby bane, sai dai in kwace mini suna kake son yi…
Kalli fa yadda ka fini tsayi”
Murmushi ya yi yana mai farin cikin yadda ta huce nan da nan, a hankali yana kallon kyakkyawar fuskarta ta cikin ruwan da yake rushing a ta koina na jikin su yace
‘’Ok, bari mu tantance waye ne Babyn……’’
…
Kamar yadda ya fad’a, ko da suka fito daga wankan ba kowa a d’akin sai akwatunan su.
Murmushi kawai ya yi, ya bud’e ya d’auki towel ya cire vail dinta da ya rufa ya d’aura kafin Ita ma ya d’aukar mata towel ya nufi toilet d’in.
Kamar za ta fashe da kuka haka ta fito, ita kam bata san da wanne ido za ta ke kallon y’an gidan ba…d’azu ya d’auke ta yanzu kuma ya sa su Yahansu sun fita sun bar musu d’akin….
Jiri take ji sosai shiyasa ta nemi waje ta zauna a kan gado tana ganin uku-uku.
Da kyar da taimakon sa ta shirya cikin wata English dress har k’asa mai dogon hannu,sama sama ya yi mata drying gashinta ya saka mata hula daga nan ya durk’usa a gaban ta yace
‘’za mu je asibiti ne, ko a kira doctor gida?’’
A hankali tace
‘’Ba na jin dad’i, jiri nake yi, kuma inaso in kwanta”
“Ok” kawai yace
Daga nan ya mik’e ya k’arasa ya d’auko wayarsa ya danna kiran family doctor d’insu…
Suna gama wayar ya koma inda take ya saka ta a jikinsa kafin yace
‘’Me kike so? Me kike sha’awar ci in je in nemo miki??”
Girgiza kai kawai ta yi tana jin zuciyarta tana tashi
dan sunan abinci kawai da ya ambato gaba d’aya sai ta ji kamar za ta yi amai.
Sake rungumota ya yi tsan tsan kafin yace
‘’Ki fad’i ko menene zan nemo, ba zai yiu ki zauna a haka ba.”
Ahankali tace
‘’Allah ba na son cin komai ni dai’’
Yana shirin yin magana wayarsa ta d’auki k’ara..ganin sunan Yahanasu ne yasa ya d’auka ya kara a kunnensa….