← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 152

Sashe 90

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu wani ragowar dalilin da ya rage wanda zai sanya Jidda ta d’aura laifi a kan Al’ameen, saidai ta san su Baba ba za su tab’a fahimtarsa kamar yadda ita ta fahimce sa ba, shiyasa kawai ta d’an ja da baya cikin sharar kwallah tace”ka yi hak’uri Ya Al’ameen, mu yi hak’uri kawai”
Ta fad’i hakan tana mai fashewa da kuka.
Da sauri ya sake matsowa yana mai cewa “noo Jidda kar ma ki fara cewa mu yi hak’uri, wallahi ba zan iya ba”
Ganin sa daff da ita ya sa ta yi sauri ta sake ja baya ita shaf ta ma manta da murhu da ruwan zafin da ta d’aura,shi kuma abunda ya hango kenan dan haka ya yi saurin ruk’ota zuwa jikinsa ganin za ta afka kan murhun yace”careful!wuta a bayanki”
Salatin Ya Yusuf wanda ya haske su tarr da fitilar wayarsa mai masifar haskd da kuma”Jidda”d’in da Baba yace ne ya fargar da su.
Da wani irin sauri ta ture Al’ameen shima da mugun sauri ya cikata ya matsa ya shiga ambaton”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
a cikin zuciyarsa.
Juyawa kawai Baba ya yi, ransa a mugun b’ace ya fice daga gidan, yayinda Yusuf ya yi kansu zuciyarsa tana wani kalar mahaukacin tafasa..kamar wani mahaukaci sabon kamu haka ya koma, yana zuwa ya rarumi wani k’atoton icce ya makawa Al’ameen a kai da mugun sauri wanda hakan ya yi sanadiyyar fad’uwarsa a wajen, gefen kansa ya shiga zub da jini.
Wata razananniyar k’ara Jidda ta saki, ta yunk’ura da niyyar yin kan Al’ameen d’in wandake nan kwance kamar gawa amma tashi d’aya itama Yusuf ya d’auketa da wani gigitaccen mari kafin ya shak’o ta da dukkannin k’arfinsa ya buga ta da jikin bango..dai dai nan su Anty Umma waenda k’arar Jidda ta Isar musu suka afko cikin kitchen d’in,da gudu anty Umma ta k’arasa ta shiga k’ok’arin kwatar Jidda wadda zuwa yanzu idanuwanta suka fara lullumshewa kafin duhu ya maye gurbin ganinta jikinta ya saki a take ta sume a wajen……

A hankali take bud’e idanunta da suka yi mata rauni..dishi-dishi ta ke gani kafin ta fara gani da kyau kad’an-kad’an..ba ta gama tantance a inda take ba…cikin fushi ta ji Baba wanda ta ga ya juya mata baya suna magana shi da Inna yana cewa”saboda su Uncle sun yi mini abu sai in d’aura karan tsana a kan Yusuf, in rufe idanunwana in k’i in bi bayan gaskiya?. Fad’a ni da su Uncle muka yi ba da Yusuf ba!
kuma suma su uncle d’in inshaaAllah wata rana za mu shirya, amma ki daina saka Yusuf a cikin fad’anmu, ke ko irin karar da ya yi mana ma ba kya gani?
wanne d’a ne kika tab’a gani ana fad’a da mahaifinsa amma ya rufe idanuwansa ya bi bayan k’anin mahaifinnasa da ake fad’an da shi?
Kuma fa saboda bugun da su musbah suka yi masa ne ma fa abun ya soma amma yaron nan ya rufe ido yana mutuntani da goyon bayana,
ki duba ki ga yadda ya dinga bin bayan mu a gaban Baba Habu har kusan marin sa fa ya yi, suka samu sab’ani, duk a ta dalilin mu, amma duk da haka ke Yusuf bai kwanta miki ba?…….a da gaskiya na sa a raina ba za ta auri Yusuf ba, amma kuma abunda idanuwana suka gane mini yau ya sanya na ga dacewar dole fa in yi abunda na ga ya kamata a matsayina na ubanta!!
ko so kike mu zuba mata ido Al’ameen d’in ya gama lalatata?

Bari ki ji abunda ba ki sani ba hatta makaranta wasu lokutan shi yake kai ta ya d’auko ta Yusuf ya dad’e da gaya mini hakan dama, ido kawai na zuba mata ina jiran ranar da zan kamata tana kulashi ashe abun nasu ma ya zarce misali!…”

Cikin kuka inna tace”yanzu zargin Jidda kake yi ba tare da ka tsaya ka ji bayanin ta ba??”
Cikin tarar numfashinta yace”tabbas!tabbas zargin ta nake yi..idan kuma za ki iya gaya mini uban me ta ke yi a ruk’umk’ume a jikinsa a kitchen da duhu cikin dare inda ba a tab’a tunanin ganin Al’ameen d’in ba to Ina sauraronki…”

Cikin d’an b’acin rai Inna tace”wallahi zan iya dafa Al’k’urani akan akasi aka samu,Haba Baba Jidda fa?
Ashe dama ba ka yi mata sanin da za ka iya shaidarta idan irin haka ta taso ba?
sannan kalli fa abunda Yusuf d’in ya yi wa Yarinyarnan har ta kaisa ga sumar da ita amma shine za ka d’auke ta ka aura masa ita? A ganinka hakan dai-dai ne?
Sannan idan kace Yusuf a bayan mu yake ka ji ka gani ya zama mijinta me za ka ce a kan baba habu surikinta, wanda hatta yau da ya san tashi za ka yi a kusa da su kuma saboda su bai tsaya kun yi rabuwar arzik’i ba?”

Cikin tsananin fushi Baba yace”na riga fa na gama magana!
babu wani abunda ya Isa ya sakani in chanja ra’ayina, na tabbata inda ace Musbahu ne ya ganta a yadda Yusuf ya gansu ita da Al’ameen da shima abunda zai aikata a gareta kenan tunda hakan ne dai dai…to shi Musbahu ya gudu ya yaye kansa da kansa dan hakan idan Yusuf ya hukunta Jidda a matsayinsa na yayanta hakan bai zama laifi ba….”

Cikin kuka inna tace”ta ya sumar da Jidda ya zama ba laifi ba?”
Da mugun k’arfi Baba yace”Aminatu!!!!!”
Cikin fushi ya d’aura da cewa”ba na son jayayya, ki barni in ji da abubuwan da suke damuna…ba na so in sake fuskantar tirjiya daga gareki,ina umartar ki da ki yi mini biyayya a yi auren nan a gobe a kaita d’akinta idan ba haka ba wallahi wallahi wallahi za mu samu gagarumin sab’ani da ni da ke!”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fice…

A hankali Jidda ta mayar da idanunta ta rufe…tana jinta kamar ba a duniyar ba…tunda take ba ta tab’a jin Baba ya d’agawa Inna murya ba sai yau duk a ta dalilin ta…ta na son Ya Al’ameen sannan ta san idan ta auri Ya Yusuf tabbas bak’in ciki ne ajalinta, amma kuma inshaaAllah ko alamun tashin hankali ko kuma yunk’urin kare kanta ba za ta yi ba…ta fahimci inna ta yarda da ita ta yi trusting d’inta Manu ma ta san za ta yarda da ita Baba kuma za ta barsa ya aurar ta a Ya Yusuf d’in indai hakan zai sa ya huce,inda rabon wanke kanta wata rana shima zai fahimci ba wani abun suke yi da Ya Al’ameen ba….za ta yi masa biyayya inshaaAllah, dan tunda ta fara tirjiya a Ya Yusuf ta nuna Ya Al’Ameen take so babu abunda alaƙarta da Ya Al’Ameen d’in take ta haifarwa Ahalinta sai masifa………..

Siyama ba ta so kwana a gidan Manu ba, amma haka suka tursasa mata akan sai ta kwana abun mamaki har su Yasira waenda suka yi musu k’abe k’abe ko motsi in suka yi idanunsu a kansu yake ….su dai su Manubiya kawai sun zuba musu ido ne suna kallon ikon Allah da kuma rashin wayonsu, dan wannan rashin wayo ne, saboda yadda suke yi kowa ya riga ya san akwai wani abunda suke son cimmawa, shiysa daga Manubiya har Siyama suke ta addu’o’i da neman tsari daga sharrin su…dukda kuwa d’azu Yasira ta bawa Manubiya hak’uri ta ce “ta yi hak’uri akan abubuwan da suka yi mata, duk sharrin shaidan ne, kuma sun fahimci itace zab’in yayansu, ta yi hak’uri inshaaAllah hakan ba za ta sake faruwa ba, su na so su faro komai saboda da ita, daga fako.”amma hakan bai sa Manubiya ta yarda da su ba…kawai dai ta bita da murmushi tace mata “komai ya wuce”

Dukda gwaggwo ta zo, hakan bai sa sun yi shirin tafiya ba..shima kuma Yashjub bai ce musu komai ba ya rabu da su amma dukda haka idanunsa a kansu yake.
Ko da dare ya yi su da kansu suka tsara cewa’Siyama ta kwana a d’akin Manubiya na da,su kuma za su zauna a d’akin da Yadira ta zauna’.Gwaggo kuma dama tana k’asa d’akin bak’i.

Murmushin yak’e Siyama ta yi dan ta yi tunanin a wajen kwanan ma za su nanik’e musu ne…Yasirar ma gudun kar su ga suna ta manne musu ne ya sanya wannan karon tace a yi hakan.

Sun mik’e kenan kowa za ta tafi ta kwanta wayar Manu ta fara haske a karo na biyar daga zaman su zuwa yanzu,duk tsura mata idanu suka yi, a hankali ta yi musu murmushi tace”sai da safe”daga haka ta juya ta nufi sama, tukunna suma suka wuce d’aki.

Suna shigewa Manubiya ta dawo da sauri ta Isa gaban Siyama wadda ke k’ok’arin shiga d’aki itama tace”Siyama dan Allah ya ake yin blocking mutum,na kasa”
Kallonta ta yi kafin tace”ki duba goggle”kamar ba za ta tambaya ba sai kuma tace”wa za ki yi blocking haka jikinki har yana rawa”
“Abbakar”Manubiya ta bata amsa a tak’aice tana mai daddana wayar hannunta kafin ta d’aura da cewa “ya ishe ni da kira,wai dan Allah yana buk’atar taimakona. Kin san shi kuma Ya Yash ya ce ba ya so ko gaisawa ne in yi da shi”
Ta faiyyace mata hakan a lokaci guda tana k’ok’arin blocking Abbakar dan har ta gano yadda za ta yin.

Shiruu Siyama ta yi tana tunanin”ko dai ta gaya mata Mahaifiyarsa ce a kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, ta san shi yasa yake ta kiranta.
Ko kuma kawai ta rabu da ita inyaso ita da Jidda sai su san yadda za su yi su karb’i kud’in a hannunta su basa dan ta san kud’i yake so.”
“Done!”
D’in da Manubiya tace ne tana haki kamar wadda ta yi y’ar tsere ya katsewa Siyama tunani.Daga haka Manubiyan tace mata sai da safe ta juya ta haye chan sama.
Chapter 90 · 0% Book details