← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 152

Sashe 135

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai-dai nan Yassir da Yasira suka shigo, da sauri suka k’araso suka rik’eta, Yasira itama cikin kuka tace
“addu’a za ki yi mata Mommy, dan Allah ki yi salati ki daina ihu…”
Sai a lokacin Mommy ta shiga ambaton ‘innalillahi wa inna ilaihirrajiun’ ba k’akk’autawa a gigice tana wani irin kuka jikinta yana karkarwa.

Shiruu duk suka yi, suna kuka kafin Ya’isha tace”an baku ita?”
Jinjina kai Yassir ya yi yace”Tana mortuary, sun yi saurin saka ta a k’ank’arar saboda ta kumbura gawar ta fara wari! zuwa gobe da safe inshaaAllah sai a yi mata wanka a binne ta!”

Wani irin kuka mai k’arfin gaske Mommy ta fashe da shi..
Haka suma su Ya’isha, babu mai rararahin wani, kowa kawai kuka yake yi gaba d’aya d’akin ya birkice, dan ko kusa da d’akin aka zo a wannan dare to sai an fahimci an yi musu rasuwa.
A tsaye ranar suka kwana babu wanda ya runtsa.
Washegari da sassafe suka nemi sallama aka sallami Mommyn daga nan suka d’auki Larai suka wuce da ita gida domin su yi mata wanka a mik’ata gidanta na gaskiya!!!.

Kamar yadda su Yasira suka ci karo da labarin gidan tsafin da jami’an tsaro suka binciko a garin kano tare da hotunan victims d’in ta watsapp hakanan yau suma su Daddy suka gani har da Kausar…Hankalinsu ba k’aramin tashi ya yi ba..Yashjub ma yana idar da sallar asubah ya gani..
Daddy ya so ya hanashi zuwa inda suke, amma kawai sai ya rabu da shi ya tafi, Hajiya Mama kuma ta kira Yusra da Yasira ta yi musu gaisuwa tace su mik’a gaisuwarta zuwa ga su Ya’isha.

Motocin su Yasira suna gama yinparking a k’ofar gidan Momy wanda ke a tudun yola dai-dai nan Yash ma yana k’arasowa kamar had’in baki, da ma ya san nan d’in suka nufa.

Mommy tana hangosa ta fito a fusace, ko ta kan su Yasira da suke ce mata “ta tsaya su shiga ciki tukunna sai a yi” ba ta bi ba, hakanan ta nufi Yashjub tana zuwa ba ta yi wata wata ba ta zabga masa wani Irin rikitaccen mari……….

Da mamaki ya dafe wajen yana kallonta kawai, ya ma kasa magana.
Ita kanta sai da ta mareshin ta d’an ji sanyi a cikin ranta tukunna ta yi tunanin duba da yadda Yassir fa da kashe sa ya so yi bai kamata ace ta maresa ba, dan haka tace”tsabar kai dak’ik’i ne Yashjub! ace a had’a video da voice d’in d’an uwanka amma ka gagara gane k’arya ne aka shirga? ina karatunkka da ilimin ka suke?

sannan ka je ka wani tartaro mini su Hajiya mama ka sako su cikin case d’in nan saboda baka san ciwon kanka ba?”
Ba ta jira jin ta bakinsa ba ta d’aura da cewa
“To bari ka ji, ba ni ka wulak’antaba wallahi kanka ka wulak’anta, kuma inaso ka sani wallahi tallahi muddin baka je ka wanke d’an uwanka ka shiryasa da mahaifinka ka gyara abunda ka lalata ba to ni da kai har abada!!
Ka b’ace mini daga gani duk ranar da ka gyara b’arnar da ka yi sai ka zo gareni!”
Tana gama fad’in haka ta juya fuuu ta wuce ciki ta shiga ta gate d’in da su Yasira suka bud’e suke ta k’ok’arin shiga da motocin.

Har suka gama shigewa Yash yana nan yadda yake ya ma kasa motsi..
‘shin da gaske Mommy ta yarda da cewar sharri aka yi wa Yassir, kokodai son Yassir ne ya sanya ta yi masa wannan borin??’
Ya yi wa kansa tambayar a cikin ransa..Saboda ya tabbatar ko k’aramin Yaro idan ya ga video d’innan da voice da shaidu ya san ba had’awa aka yi ba.

Juyawa kawai ya yi, ya shige cikin motarsa ya kunna ya wuce, yana tafiya ya turawa Yasira mesaage ya yi mata gaisuwar rashin da suka yi, dan Mommy tana shiga ya ga ta fito za ta zo wajensa shi kuma ba zai iya sake ci gaba da tsayuwa a k’ofar gidan ba zuciyarsa za ta iya tarwatsewa
..Tabbas Mommy ta tsaneshi!!!

Sai da Yasira ta bari Yassir da su Yusra sun shige ciki tukunna ta yi saurin ruk’o hannun Mommy k’asa k’asa tace”Mommy videos d’innan da gaske ne fa!! Yassir da kansa jiya ya yi mini confessing, ya tabbatar min bai ƙaryata ba…….da kin sani ba ki yi wa Ya Yash haka ba gaskiya, jiya dai na ji haushinsa da bai zo ya ganki ba amma yau ai da mun tsaya mun sauraresa tunda ya zo ɗin.”

Shiruuuu ta ga Mommyn ta yi..ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta tubure kawai tace sharri aka yiwa Yassir dan haka ta cewa Yasirar
“rikicewa Yassir ya yi jiya, shiyasa yace miki shine, amma tabbas ni na san sharri ne aka yi masa……’
Rabuwa da ita kawai Yasira ta yi, ta bari akan sai an kai Baba Larai, zafin mutuwar da komai ma ya fara raguwar mata tukunna sai su yi magana da ita ta fahimtar juna.
….
Gaba d’ayansu kashe wayoyinsu suka yi, saboda Mommy tace ba ta son y’an gaisuwa su san tana nan, bama ta buk’atar ganin kowa a halin yanzu…da kyar da mugun kyar suka samo matan da suka yarda suka yiwa Baba larai wanka dan a k’ank’arar da aka sakata jiya ya sanya yanzu kuma duk sai ta lagwab’e da k’ank’arar ta narke, dan ko jikin nata kana tab’awa sai ka ji kamar zai biyoka ga uban wari!
Suma Matan dai daga k’arshen wankan kawai ruwa suka yayyafa mata aka yi mata sutura…..
Sai la’asar tukunna suka samu aka sallaci Baba Larai aka kaita makwancinta…

Ana dawowa daga kaita
Mommy ta cewa Kausar ta tafi, ita tsoranta d’aya kar itama Kausar d’in Daddy ya koreta dan tabbas suna da buk’atar ta a cikin gidan…tare suka tafi ita da Junior Yasmeen da Yadira…..
Suna tafiya Yassir shima yace musu”zai wuce za su ci gaba da zama da wani Abokinsa kafin komai ya yi settling”
Mommy ta so ta tsayar da shi gudun kar wani abun ya same sa, amma da ta fahimci video d’in a iyaka family ne ya zagaya aka gaggani hukuma ba su riga sun gani ba sai kawai ta rabu da shi ya tafi….ba ta kuma yi masa maganar ba saboda ta lura kamar ba ya son zancen!
Har ga Allah ita she’s proud of Yassir saboda ya yi yunk’urin kawar mata da matsalar ta
(Dama ita tun a wajen da abun ya faru ta so ta fahimci shine, ta kuma fusata da Yash d’in bai mutu da gaske ba)
dan haka ta bisa da kyawawan addu’o’i da fatan alkhairi, su Yasira kuma ta ci gaba da yi musu borin ai sharrin aka yi wa Yassir d’in.

Sai da Yash ya je ya ga Manu, tukunna ya fara haramar wucewa gida shi kaɗai, saboda dama tun jiya take rok’ansa akan ‘ya barta ta yi kwana uku’ tunda gida ma za su chanja, ai kuwa da ya barta ɗin ta ji dad’i kwarai, amma kuma yanayinsa da ta gani wanda ya sanya ta fahimci akwai matsala ne ya ɗan ɓata mood ɗin nata, dannhaka ta hau tambayarsa…..

bai b’oye mata ba, ya gaya mata cewa”Daddy ya kori Yassir, kuma k’arshen abun bai yi dad’i ba, dan har da Mommy itama sai da ta bar gidan”
,sosai Manu ta tab’u daga jin zancen, da kyar ta taushi kanta sannan ta yi namijin k’ok’ari wajen kwantarwa da Mijin nata hankali, tukunna suka rabu shi ya wuce gidan Daddy shi da Najeeb wanda ya zo bada jimawa ba, har da Siyama.

Ita Manubiya ba ma ta yi tunanin da Siyaman aka zo ba, dan basu dad’e da yin waya da ita ba, kuma bata gaya mata ba..
sai da su Yash d’in suka wuce tana shiga parlourn nasu daga parlourn Baba kawai ta ganta a zaune, ai kuwa nan suka hau murna har da hawayen farin ciki.

Sai da su Yash suka kama hanya tukunna ya tuna bai sanarwa su Manubiya rasuwar Baba Larai ba,dan haka ya bari a kan sai zuwa anjima sai ya gayamata, ya san dole za ta kirasu ko ma ta je har gidan ta yi musu gaisuwa…addu’arsa d’aya ‘Allah ya sa kar Mommy ta yi mata abunda ta yi masa itama’
Tunda da ma gashi ba ta sonta.

A b’angaren Kausar kuwa, zuwa yanzu ta gama tsarawa da sanin abunyi, dan haka jimamin Baba Larai yana d’an sakinta ta kira Ya’isha tace”tana so ta had’ata da Abbakar, akwai abunda zai yi mata”
Da kyar Ya’ishan ta had’ata da shi kuwa!
Saboda last time Abbakar d’in ce mata ya yi “kowa kawai ya yi ta kansa daga yanzu!
dan plan d’in da suka had’a last time ɗin bai yi masa ba, gashi ba su yi nasara ba sannan kuma sai da yayi watanni uku a asibiti…”
Hakanan dai ita Kausar ta nace sai da aka had’ata da shi tukunna hankalinta ya kwanta, saboda shi ne kawai ta ga niyyar su ta zo d’aya tunda yana son Manu itakuma tana son Yash dan haka za su taimaki juna bilhaƙƙi da gaskiya, dan ta zauna ta yi tunani sam ba za ta wani biyewa Mommy ba wallahi!
Ba za ta iya hak’ura da Yashjub ba…kowa kawai ya yi ta kansa……….

Ita dai Yasira tana jinsu suna wayar da Ya’isha..har aka tura number tana mamakinsu a ranta tace”wato dai wanda ya mutu ya riga ya tafi!duniya kuma kowa sai ya ci gaba da abunda ya saka a gaba.
Kalli yadda suka ci gaba da k’ulle k’ullensu kamar ba yanzunnan aka dawo daga kai Baba Larai kabari ba.”

Ita ma Yusra lissafin da take yi kenan.
Ita sam ba ta yi tunanin Kausar d’in ta san da issue d’in Abbakar d’in ba ma, wataƙila sai dai in ko Ya’ishan ce ta fad’a mata.

Su Yassir suna gama tafiya, Mommy ta cewa su Yasira su zo su raka ta…su sun yi tunanin ma kayan abinci da abubuwan buk’ata za su sissiyo, sai da suka ga ta d’auki hanyar inda za su je tukunna suka fahimci inda suka nufa…
Chapter 135 · 0% Book details