Sashe 32
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jinjina Kai Mommy ta yi kafin ta ce”na fahimceki,”
Sai kuma ta share kwallarta ta d’ago ta kalle ta kafin ta ce ”ki yi min alfarma guda d’aya
‘ku je ku d’auko ta banda ni, sannan duk runtsi kar ki bari a wani kawota nan a ce ta gaida ni’
dan muddin na yi ido biyu da Yarinyar nan yau tou tabbas zan iya mutuwa….”
Shiruu ta yi kafin ta fashe da wani irin kuka ta ce ”Larai na tsani Yarinyar nan!! Ban tab’a tsanar Mutum kamar yadda na tsane ta ba! A cikin watanni da basu wuce hud’u ba gaba d’aya ta ɗaga min hankali ta raba ni peace of mind d’ina(kwanciyar hankalina)……”
Cikin share hawayen da suka wanke mata fuska sosai ta ce “dan Allah Larai wannan karon ki dage sosai!!! Sannan a yi duk abunda ya kamata, dan ba zan karb’i wani uzurin daga gareki ba kuma du! zuciyata ba zata iya jurar Yarinyar nan na tsawon lokaci ba. Baya ga haka ma idan har ta dad’e na san kin fi kowa sanin abunda zai faru da mu….”
Murmushi Baba larai ta yi kafin tace “ki kwantar da hankalinki, inshaaAllah ba za ta yi dogon zango ba…sannan ina sake yi miki albishir ɗin ba za mu bari ta gauraya da zuriar gidan nan ba ta hanyar hana komai shiga tsakaninta da Yash!
Ba abunda zai shiga tsakaninsu ballantana har ta samu gindin zama a gidan, ko ta sake shiga ransa…ni na san me daa me na ke shirya mata, ki kwantar da hankalinki
kawai..”
Dai-dai nan Ya’isha, Yadira da Yusra suka shigo suka nemi guri suka zazzauna suma suna jiran dawowar Yasira da Yasmeen a samu a kama hanya da wuri, dan yanzun suka had’u da ita tace makullai za ta karb’o a wajen Yahanasu sai su wuce, shine Yasmeen ta bita su kuma suka yo nan.
Suna zuwa suka tarar da Yahanasu tana waya tana shiryawa da sauri da sauri…tana ganinsu dama ta san ba alkhairi ne ya kawo su ba, dan haka ta yi sallama da wanda suke wayar ta ajjiye wayar ta kalli Yasira ta ce “Yassira har kun shirya? Ai sai yamma tukunna za’a d’auko Amaryar”
Sai da Yasirar ta nemi waje ta zauna tukunna ta ce ”Am, Ina buk’atar keys ne, za mu kai gifts d’in da muka siyawa Ango
da amarya gidan, idan kinada abunda za’a tafi da shi kuma sai ki kawo mu yi miki gaba da shi, dan mu yanzunan za mu tafi.”
Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin ta ce ”keys ba sa Hannuna….inada sak’o, amma na bawa friends d’insa yanzunnan suka wuce da shi suma wai za su kai gifts ne, daga nan su biya su yi masa sallama saboda flight d’insu ya kusan d’agawa….”
Cikin tarar numfashinta Yasmeen tace “no wahala…ki bamu adress d’in gidan kawai sai mu wuce.”
Ta fad’i hakan tana mai k’arasa shigowa cikin d’akin, dan ita a bakin k’ofa ta chake ta tsaya tun d’azu.
Murmushi Yahanasu ta yi tukunna ta ce “Yasmeen nima ba sanin address d’in gidan na yi ba, shiyasa ma kika ji nace miki na bawa friends d’insa sak’ona sun tafi min da shi dan na ji sun ce su sunsan gidan wai sunje d’azu da safe….”
Tana gama fad’in haka ta d’auki makullin motarta sannan ta k’arasa inda Yasira take ta damk’a mata key d’in d’akin nata ta ce ”idan kun fita ki rufemin pls, Ina sauri ne.”
Daga haka ta sa Kai ta fice
da sauri dan ko hauka takeyi
ba za ta bari su Isa gidan nan ba tare da an riga an kai Manubiya ba….
Tana fita Yasmeen ta ce ”idan nace muku ku barni in ci uwar Matar nan ku ce ba haka ba, yanzu kalli! Gaba d’aya ta raina Mutane, gani take yi itama ta kai Mutum…”
Shiruuu Yassira ta yi tana lissafi kafin ta mik’e da sauri tana shirin bin bayanta ta jiyo tashin mota, sannan ta ji an wangale gate an fice da gudu. Ko ba’a fad’a mata ba ta san tashin motar Yahanasun ne shiyasa cikin b’acin rai ta yi wulli da makullin da ta bata akan gadon ta fice,
ranta a b’ace.
A yadda suka fita suka bar su Mommy a haka suka dawo suka tarar da su…suna shiga ko zama ba su yi ba
Baaba Larai ta ce ”ya aka yi? Ta baku?”
Ajiyar zuciya Yassira ta sauk’e
tukunna ta matsa kusa da ita ta ce “ta fice, da sauri! Bayan ta ce mana keys ba sa Hannunta, sannan wai bata san kwatancen gidan Yash ba saboda tsabar ta raina uwarta!”
Sai da ta sake sauk’e numfashi tukunna ta ce ”Inaga ta zargi wani abun ne……a ganina gara kawai mu hak’ura, kin san halinta mahaukaciya ce! Ina tsoron kar ta je ta gayawa Yashjub ko Daddy wani abun mu je ta taso mana da case.
“Ta fad’a d’in”
Mommy ta fad’i hakan tana mai k’arasowa inda suke, sannan ta sake cewa “dan Allah ta fad’a! Sai me?.
Ki kira Yashjub d’in yanzu ya yi miki kwatance, ku bi bayanta na san gidan ta nufa..idan kukaje ko a gaban ta ne ku yi abunda kukaje yi, ita ta sani, ta dad’e ba ta fad’a ba.”
Shiruuu Baaba Larai ta yi, sai da ta gama lissafi sannan ta kalli Yassira tace “ki kira Yashjub d’in…
Saboda wannan shine kad’ai damar da za mu iya samu dan haka ba za mu yi da sanyi sanyi ba!
saboda in dai har muka bari Manubiya ta shiga gidan a haka sakayau ba komai to munada gagarumar matsala.”
Shiruuu Yassira ta yi ta k’i cewa ko yin komai sai da Yasmeen ta ce mata “ko ni in kira shi ne?”
tukunna ta fita waje domin yin wayar….
mintuna biyu ta d’auka a waje kafin ta dawo….tana shigowa duk suka tsura mata idanu suna jiran amsa…..
Sai da ta zauna akan gado ta dan dafe kanta tukunna ta d’ago tace”Mommy dan Allah mu bar wannan idea d’in”
Sai kuma ta kallesu duka kafin tace “ba zan b’oye muku ba gaskiya ni tsoro nakeji….na san babu yadda za ayi Ya Yash ya bar gidansa babu cctv…haka kurum a hangomu muna yayyafe yayyafe da hayak’i da abubuwa…..
Inda ace cewa akayi idan mukayi ba za ta tare ba tou da zan biye muku ayi
komai ta fanjama fanjam, amman ba zan d’au wannan kasadar kawai saboda wani tushe ko ginshiƙin korartata da
mukeso mu gina ba, haka kurum muna zaman zaman mu kar ku janyo mu saka kanmu a case gaba d’aya.
Ni kam count me out (ku cire ni daga wannan) gaskiya!.
Yanzun da na fita na kira shi har sau uku bai d’auka ba, a na
hud’un kuma da ya ɗauka ya ce ‘mu bari kawai ba sai mun kai flasks d’in yanzu ba, mu saka a motocin mu, idan muka d’aukota anjima sai mu yi zuwa d’aya….k’arshe ma kashe wayar ya yi bayan yace min yana zuwa.’
Na san kuma wataƙila zai yi wa Yahanasu maganar, ita kuma
Allah kad’ai ya san me za ta ce masa ta yadda na san tashi d’aya zai
fahimci gidan kawai muke so mu je.”
Cikin fushi da fad’a Ya’isha ta ce “ya fahimta mana sai me?
Gidan d’an uwanmu ne fa!…kina wasa!! Idan ban kwashe kayana na koma chan da zama ba ki chanja mini suna!”
Cikin sako wani sabon issue ɗin Yasmeen ta kalli Mommy ta ce “Ya’isha ta yi magana anan fa Mommy, mu muna nan su suna chan abun fa ba zai yiu ba, ya kamata ace ko
Yadira ta je gidan ta zauna da su.“
Mikewa tsaye Yassira ta yi a fusace kafin ta ce ”wai ba ki da lisssafi ne?me yasa bakwason bin komai a hankali? Ya ana neman toshe wannan ke kuma kina neman b’ullo da sabon abunda zai d’agawa kowa hankali??….Ki yi shiru da wannan zancen dan Allah ki bari ayi komai at once (ɗaya bayan ɗaya).”
Cikin son su fahimce ta Yasirar ta ci gaba da cewa ”idan har zan bada shawara a bi, to kar wanda ya janyo fad’a ko case da Yash..dan haka yanzu kawai mu hak’ura….dan Allah a bar batun zuwa gidan yanzu a nemi wani madadin.
Haba mana!!! Ku ko ta Kausar ma bakwayi?
Sannan idan fa muka bi komai a sannu muka samu Kausar ta shiga gidan na tabbatar Manubiya ba ta Isa ta k’ara ko da sati a cikin gidan ba, ai kunsan wacece Kausar!
Kunsan ita kad’ai ta ishi Yarinyar riga da wando wallahi!
Ba zata barta ba, kunga wannan ma ai wani madadin, gara shi akan zuwan da mu ke son yi yanzu dan ya fi sauƙi…amman gaba d’aya kun k’i ku nutsu ku bi komai a sannu kun dage sai kun bankad’a komai a idanun kowa an gani…..”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga cikin d’akin.”
Tana fita Baaba Larai ta sauk’e ajiyar zuciya…..tabbas ta
san Yassira tana da gaskiya..gaskiya ta faɗa!!
Sai dai kuma indai ba abunda ta shirya akayi kafin Manubiya ta shiga cikin gidan nan ba to kwata kwata bata
hango rabuwa tsakaninta da Yashjub ba!.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta ce ”Larai, manta da zancen Yassira ba zata fahimta ba,
Yarinyar nan ba alkairi bace ba, rayuwarta a matsayin Matar Yash hatsari ne garemu, dan haka kar ki biyewa Yasira,
kar mu ɗauki duk wani abu da ya shafi Yarinyar nan lightly(da wasa)…”.
Ajiyar zuciya Yusra ta sauk’e kafin ta ce ”Mommy bana son Yarinyar nan tun farko.”
Cikin tarar numfashinta Yadira ta ce “tunda aka fara zancenta babu zaman lafiya a cikin gidan nan, gashi sai sake raba kanmu takeyi mu da Ya Yash..”
“Bata Isa ba kuwa, Allah ya fi ta”
Cewar Baaba Larai, kafin ta kalli Ya’isha ta ce ”ki kira Najeeb, ki tambayeshi location d’in gidan, idan zai yiu kar ki bari ya san zuwa za mu yi.
……………
Tuni, an sallami masu hotuna, shiyasa suna fita suka kama gabansu. …
Su Jidda su kuma, Aisha suka tsaya jira wadda ta shiga gida domin ta sanar da su Inna sun wuce.
A gefen Jidda Yassir ya d’an
tsaya kafin ya ce “Bismillah, ku jira ta a mota mana, akwai rana”.