← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 152

Sashe 45

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya mik’e ya zauna akan gadon gefenta, kusa da ita sosai!! Har cinyarsa tana gogar tata, kafin a hankali ya ɗan gyara ya fuskanceta sosai sannan ya sa hannayenshi biyu ya yi cupping fuskarta a cikin tafukan Hannayensa tukunna ya
shiga share hawayen nata da babban ɗan yatsanshi still yana rik’e da fuskar tata bai cika ba, yana kallonta yanajin wani sanyi yana ratsasa.

Maimakon kukan ya ragu sai yaga hawayen nata ma k’aruwa sukeyi dan haka kawai sai
ya janyota zuwa jikinsa ya rungumeta da kyau! Ta yadda hatta yanayin yadda zuciyarsa take bugawa tana iya ji.
Kamar zai fashe mata da kuka ya ce
“Dan Allah ki daina! bana
k’aunar ganin hawayenki, inshaaAllah babu kuka a gidana, ba zan baki dalilin yin kukan ba da yardar Allah, na dad’e da yi wa kaina alk’awarin ba za ki yi kuka a gidana ba! Zan baki dukkan farin ciki da jin dad’i!….
Dan haka kar ki fara karya min alk’awarina tun yau, pls, dan Allah ki daina kuka..”
Jin yadda yake ta had’ata da Allah itakuma ta gagara tsaida hawayen nata ne ya sanya ta d’ago a hankali ta d’aura Hannunta a kan Bakinsa, kafin ta shiga girgiza masa Kai, alamun ya yi shiru ya daina rok’onta, a lokaci guda kuma ta samu ta tsaida hawayen nata.

Shirun kuwa ya yi, ya shagala da kallonta yana mai shak’ar kamshin da itakanta ta ke yi da kuma d’umi da kamshin da hannun nata sukeyi..wanda tashi d’aya ya ji yanayinsa ya fara chanzawa.
Itanma dakyar ta iya d’auke idanunta a fuskarsa ta sunkuyar da kanta k’asa tukunna Ahankali tace “Ina wuni!” tana mai jinta kamar ta fi kowa zama safe a duniyarnan kasancewarta rungume a k’irjinsa.

Murmushi ya yi mai had’e da dariya, kafin ya lumshe idanunsa cike da shauk’i yayi kissing tafin hannunta wanda ke a kan bakinsa.

A hankali ta fara k’okarin zamiye hannun nata dan tashi d’aya sak’onsa ya dirar mata ya shiga ratsata ta ko Ina.

Ruk’o hannun ya yi da sauri, kafin ya samu ya bud’e idanunsa da suka fara chanja launi, tukunna yace”Lafiya Alhamdulillah amarya ta kuma uwargidana”

Sunkuyar da kanta kawai ta sake yi
tana murmushi k’asa k’asa….dai dai kunnenta ta ji ya ce”Tunanin me kikeyi ne haka bayan gani a gabanki?”
Ya fad’i hakan cikin d’an turo baki sannan yana mai sake ruk’umk’umeta…

Yanayin yadda ta ji k’irjinsa ya shiga bugawa fiyeda da ne ya sanya ta d’an d’ago a hankali tace”zan sha ruwa”

Dariya sosai ta basa amman sai ya dake, wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauk’e tukunna ya cikata da kyar dan wani irin shauk’i ne yake jansa….mik’ewa ya yi ya d’an daidaita kansa tukunna yace”muje!na had’a mana dinner a k’asa”kafin ya juya ya cire hularsa ya ajjiyeta a gefe tukunna ya mik’a mata hannunsa yace”Bismillah”
Ba kayan d’azu bane a jikinsa
amman shima wannan d’in fari ne k’al, jamfa, yanayin d’inkin mai masifar kyau.
Ahankali ta mik’e tsaye
ta shiga gyara zaman alkyabbar ta harda sake rufa hular…

Murmushi kawai ta ga yayi kafin ya matso ta sosai tukunna ya sa hannu a gaban rigar ya shiga b’alle bottons d’in alkyabbar, sai da yakai
har ciki inda bottons d’in suka tsaya tukunna ya sa hannunsa a bayanta yad’an turota jikinsa kafin ya ja alkyabbar k’asa ta tafi ta fad’i a wajen.

D’inkin lace ne a jikinta…..ba k’aramin tafiya kuwa ta yi da imaninshi ba dan lace d’in da d’inkin da ita kanta gaba d’aya sunyi masifar yin kyau! Dama ita Allah ya yi mata sura mai kyau gashi d’inkin an yi sa ne style d’in fitted gown, yayinda d’ankwalinta ya d’an yi baya gashin gaban goshinta da rabin na kanta duk sun baiyyana a waje, sai
shek’i suke yi…..Shiyasa Yash ya ma kasa magana dan shi kam an tashi kansa, bai tab’a ganinta a irin yanayin nan ba, bai tab’a samu ya k’are mata kallo kamar hakan ba, gashi rigar kusan rabin k’irjin duk a net yake…
Ganin kallon yak’i k’arewa ne yasa ahankali tace”Muje” tana mai jinta gaba d’aya a takure ga wani kunya da fargaba da suka lulub’eta.

Hannayensa ya sark’e around her waist, cikin lumshe idanu da bud’esu ya ce”Anya dinner d’innan za ta yiu kuwa?? Na fara ganin dishi-dishi wallahi…”

Da sauri ta d’an ja baya, sai
kuma ta yi gaba ta wuce ta gefen sa da hanzari tana mai jin yadda k’irjinta yake dukan uku-uku.

Murmushi kawai yayi kafin ya juyo yana wani Irin kallonta, tukunna da kyar ya d’aga k’afa ya fara takawa nan inda take tsaye ta juya baya tana wasa da y’an yatsun hannunta……..

Ya zagaya k’asashen duniya daban daban amman zai iya
cewa bai tab’a ganin mace mai kyawun structure kamar Manubiya ba har ma fuska bai tab’a ganin mace mai yanayin irin kalar kyawunta ba….ya san kuma soul d’insu ne ya had’u saboda yanada tabbacin ko da ace ba hakan take ba looks ɗinta ba haka duke ba, dole dai zai kamu da sonta…bai san ya zai yi ba da ace bai sameta ba, shiyasa ya ke ta daɗa godiya ga Allah s w t da ya amsa Addu’o’insa ya bashi ita, kuma in sha Allahu sauƙa da sadaƙar da ya rarraba aka dinga yi tun lokacin da auren ya matso har kawo yau akan ‘Allah ya tabbatar masa da alkhairi, ya kuma kaɗe duk wata fitina!’
ba za a daina ba, zai yi ƙoƙari a ci gaba da yi, na ‘godiya ga Allah’, har zuwa wani lokaci, dan shi kam Ubangiji ya yi masa babbar kyautar da bai ma san yaddda zai fara godiya ba…

Tana tsayen, ta ji shi a bayanta,
kafin ta matsa ko ta yi yunƙurin yin wani abun ma ta ji ya yi sauri ya d’aura hannunsa akan flat tommy d’inta (shafaffen cikinta), kafin ahankali
ya ce ”da gaske fa
na daina jin yunwar”

Dasauri tace”Cikina har ciwo yake min tsabar yunwa”.

Dariya ta ji yayi wadda har
sai da d’umin numfashinsa ya addabi wuyanta, kafin a hankali ya yi kissing wuyan dan yadda d’ankwalin nata ya tunkushe ya zame both daga saman goshinta da kuma k’eyarta ya had’e da ribbon d’inta hakan ba k’aramin kyau yayi masa ba….a yadda yake tsaye a bayanta
ba k’aramin kyau sajen k’eyartata da bak’ak’irin d’in sumarta suka yi masa ba shiyasa ya kasa hana kansa appreciating moment ɗin, cikin sake shigewa cikin jikinta ya sake sakar mata wani passionate peck a wajen, ya san zata matsa dan haka ya yi saurin sake ruk’ota da kyau da dukkan hannuwansa biyu.

Yadda jikinta ya fara karkarwa shi kansa sai da yayi mamaki… dan ba kaɗan ba ta taɓu sakamokon abunda ta ji a jikinta wanda abubuwan da ya yi mata suka haifar, da kuma abubuwan da ta ji daga gareshi wanda ya janyo tsoron da ya bada gudummawa wajen kiɗimata.

A hankali ya durk’usa, ya d’ago k’afafunta ya tallafota, kai tsaye ya d’auke ta gabad’yanta in a bridal style..wanda hakan ya sanya ta runtse idanunta sannan ta yi saurin zagaye hannayenta a wuyansa, a haka ya nufi k’ofar ya fita da ita daga cikin ɗakin, gwanin ban sha’awa.

Har suka nufi stairs bai ajjiye ta ba kuma bashi da niyyar ajjiyetan, dan haka tace
“Inada nauyi fa”
Kallon d’an mitsitsin bakin nata yayi da idanunta waenda suke a lumshe har yanzun kafin
Ya yi murmushi ya ce
“Ni kuma Inada k’arfi..”

Bai ajjiyetaba sai da suka shiga cikin kitchen tukunna ya ajjiyeta a hankali.
Da kyar ta d’an zame hannayenta da ta sak’ale wuyansa da su, suna masu shak’ar numfashin juna…
sai da ta daidaita tsayuwar ta, tukunna ta fara k’ok’arin bud’e idanunta.

Facing juna sukeyi itada shi,
shiyasa tana bud’e idanun nata suka had’a ido yana yi mata murmushi kafin ya ce ”I made it for you(na haɗa ne domin ki)”

A hankali ta fara juyawa…tun kafin ta gama juyawa ta fuskanci mini dining table d’in
ta fara murmushi..
Ba wani uban
decoration yayi mai yawa ba, just simple amma mai kyau gwanin burgewa sannan a take ya yi masifar tafiya da imaninta…….flower bouquet ne mai asalin kyau a ajjiye a kan dining d’in da card a ciki, sai ballon guda d’aya babba da aka sak’ale ta sak’k’o kan dining d’in da rose’s masu kyau
zub’e a k’asa, da kuma kan dining d’in sai abincn da ya jera a kai ‘drinks da chicken’ sai
candles da ya kunna y’an kad’an a kan dining tabble d’in.

A hankali ta ji ya rungumeta ta baya
kafin yace “da fatan ya burge ki”
Murmushi tayi ahankali ta jinjina masa kanta alamun ‘yes!’

Ajiyar zuciya ya fesar yace
“Alhamdulillah”

Kafin ya sake kwarin ruk’on da yayi mata yana mai sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere.

A hakan suka tsaya kowannen su yayi shiruu kawai.

Ita ta fara kawo k’arshen shirun sakomakon yadda ta ji yanayin tsayuwar tasu da komai ma yana shirin chanjawa, shiyasa ta d’an muskuta. numfashi ya fesar , kafin yace”Oh sorry..
Mu je ki ci abincin ko?”.
..
Ahankali ta sa Hannu ta fara d’aukar note d’in jikin flower ta shiga karantawa, ai kuwa har da y’ar kwallarta dan ba kad’an ba kalaman soyayyar da ya rurrubuta suka shige ta suka ratsata…cikin jan hanci ta juyo ta ce ”Thankyou, I love it and I love you more..”
Wani irin blushing (murmushin) ya shiga yi tukunna suka rungume juna a wajen suna ji kamar su cinye juna dan so, sun jima a hakan kafin ya ruk’o hannunta suka k’arasa kan kujerar dining table ɗin suka zauna…Sam Manu ba ta ji dad’in cin abincin ba kuwa dan a kan cinyarsa ya d’aura ta kuma shi ya dinga bata a baki, tana ci yana bata labarai kala kala
Childhood d’insa da schools d’in da ya yi, sai da ya ga ta d’an sake kuma ta ci sosai
tukunna yace “suje su yi sallah”…..Loma d’aya kawai ya iya yi shikam kuma hakan ma dan ta tilasta masa ne saboda sam shi kam ba zai iya wani cin abinci ba, ba wai baya jin yunwa bane kawai dai ya riga ya san bakinsa ba zai iya d’aukar taste d’in komai ba a halin yanzu.

Ganin kamar zai yi mata kuka ne yasa ta hak’ura ta tsaya kallon ikon Allah
Babba yana shagwab’a!
Chapter 45 · 0% Book details