← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 152

Sashe 123

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Abhi ya d’an ruk’o hannusa, alamun ya yi shiru, dan ya san Hajiya mama yau kam ta riga ta gama kaiwa high!!!!

Daddy yana ji yana gani haka Hajiya Mama ta had’a kayanta tsaf tsaff, ita da Junior suka tafi tsohon gidansa dan tace ‘ko Abhi d’in ma kar ya biyo ta, shima takaicinsa take ji! idan kuma taga d’aya a cikinsu a inda take kafin ta wuce uk to sai dai ta k’arashe kwanakinta a hotel har zuwa lokacin da za ta wuce uk ɗin’

Da Yamma Yashjub ya turo mata da message ta inda yake cewa”Jiya an d’aura masa aure da Kausar ba tare da yardarsaba.! A jiyan ya saki Kausar, to kuma a jiyan Mommy ta zo ta sanyashi ya mayar da ita…

Yana da babban dalilin da ya sanya ba zai
Iya zama da Kausar ba, sannan akwai abubuwa da dama a halin yanzu da suke damunsa waenda suka sanya ba zai iya ci gaba da zama a gari d’aya da su Mommy ba….dan haka yana da buk’atar sarari da lokaci, dan Allah kar su nemeshi…yanada buk’atar break daga fitinar family d’insa.”

Sai da Hajiya mama ta yi kuka a lokacin da ta karanta message d’in Yashjub, dan sosai ya tab’a mata zuciya!!!
Ace mutum shi da k’asarsa! shi da gidan Ubansa! amma fargaba da fitintinu sun hanasa ya sake ya rayu a wajen!!
wannan wanne irin abu ne haka!!
Allah ya Isa tsakaninta da Mommy wallahi!…
Junior ta kira tace
“ya je gidan ya duba mata..idan sun riga sun tafi to ko driver ne ya tambaya watak’il su gano inda suka nufa”
ba wai binsa ko fad’an inda yake za ta yi ba, kawai dai taana so ta san inda yake for her peace of mind (saboda hankalinta ya ɗan kwanta)..saboda itama ta goyi bayan tafiyar da zaiyi d’in d’ari bisa d’ari.

Har daren ranar Hajiya
Mama a fusace take, ta k’i
ta kula kowa ta k’i ta saurari kowa, kuma tace in banda Junior ba ta so ta ga kowa a inda take!!
hatta Yahanasu da ta je ba ta samu ganinta ba, dan ta rufe d’akin ma da take ciki abubuwa da tunani sun yi mata yawa.
…….Tun ranar da su Mommy suka haifi Yashjub da Yahanasu ta kasa gane abu guda d’aya game da Mommy;kwata-kwata ba ta d’aukarsa ya dad’e a hannunta, kullum tana mak’ale da Yahanasu.
A tunaninta (Hajiya Mama) kunyar Haihuwar fari ce ta sanya takeyi masa hakan amma sai ta lura kamar ma haushin Yaron Mommy take ji, tun ba ma da Hajiya Mama ta ga Mommyn ta ce a bashi madara ba, wai ‘ruwan nononta bai zo ba’ amma Likita yana zuwa da aka tilastata aka matso sai ga ruwan Nono fall yana zubowa…
Tun daga wannan lokacin ta saka mata ido dan tashi d’aya kwakwalwarta ta bata ‘ko dai saboda maganar dukiya da Imam ya yi ne ya sanya Khadija ta musanya y’arta da d’an kishiyarta!!’
Saboda a lokacin Yahanasu da take jaririya kamanninta sun yi shige da na Baba Larai, da ta fara girma ne dai ta koma kamannin Daddy.
Shi kuma Yashjub da Daddy yake kama da yana jariri amma yana fara yin wayo har kawo yanzu da Khadija amaryar Daddy yake kama, sam ba ya kama da Mommy.

Har kusan shekara d’aya zuwa biyu Hajiya mama ba ta gano wata hujja da zata sanya ta ce Yashjub ba d’an Mommy bane ba saboda yadda Mommyn take yi masa babu wanda ya Isa yace ba ita ta haife sa ba,kuma a wanchan lokacin ba ta san Mommy da mugayen halaye ba,shiyasa kawai ta kawar da komai ta cire shakku ta cigaba da addu’a, sannan ta mik’awa Ubangiji lamuranta ta barshi ya yi ikonsa, dan zuciyarta ta ƙi ta daina yi mata wasi wasin ‘anya Yashjub dan Mommy ne kuwa!!?’
Gashi ita Babba ce, ba zai yiu ta tada husuma akan wannan gagarumin al’amari haka ba, azo a yi bincike aga ba haka bane gashi Ubangiji da kansa yace “kar ka tsananta bincike”
Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru ta ci gaba da addu’a…
A lokacin ne kuma Mai gidanta ya rasu mahaifin su Daddy, dan haka zaman ta sai ya dawo Gidan Daddy tunda shine Babba.
Sai dai ko sati ba ta iya yi a gidan ba haka kurum ta ji komai ya fita a kanta, ta tsani gidan, ta tsani jama’ar gidan!!
Wanda hakan ya sanya ta koma Uk da zama. Dukda tana so ta d’an saka ido akan zaman Daddy da amaryarsa saboda a lokacin dukda Daddyn ba ya yiwa Amaryar tasa abubuwa a gaban Hajiya maman amma ta fahimci akwai matsala, sai dai kuma ba zata iya zama a gidan ba dan haka ta hak’ura ta tafi bayan ta had’a su su biyu Daddyn da Amaryartasa ta tambayesu Daddy yace mata babu komai ba fad’a suke yi ba,
Itama amaryar haka.

Bayan shekara biyu ta zo hutu,a wannan lokacin ne ta ci karo da layu da abubuwan ban mamaki a d’akin Mommy, k’asan gadonta.
lokacin Yashjub yana wasa ya tura Abun wasan nasa a k’asan gadon, ya isheta sai da ta zo ta duba ta d’auko masa dan su Khadijan duk basa nan sun fita kitso…
Hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba, saboda har da tsaka mai rai a cikin kwalba da abubuwa na tsafi kala kala ta gani a k’asan gadon Yarinyar da kusan rainon ta ma ita ta yi.
A lokacin Mahaifiyar Mommy itama ta rasu, kasancewar Hajiya Mama babbar k’awa ga mahaifiyar Mommy kafin rasuwar ta ya sanya ta ga ba laifi bane ba idan ta kirata ta zaunar ta yi mata magana ta kub’utar da ita daga kan Hanyar b’ata da halakar da ta d’auka wanda ba ya b’ullewa.
Dan haka suna dawowa ta nemi ganinta, sai da suka keb’e iyaka su biyu kawai tukunna tace mata“ta ga abubuwan da ta ajjiye a d’akinta a k’asan gado”….nasiha sosai Hajiya mama ta yi mata sannan ta jaddada mata “ ta rik’e Allah da addu’a, shi zai sa Imam ya so ta ba wai tsafi ba..a duk lokacin da ka yiwa mutum tsafi ya so ka to fa idan abun ya karye tsanar da zai yi maka sai ta fi ta farko….”

Kan Mommy a k’asa lokaci da Hajiya mama take yi mata nasihar kuma daga ‘to’ sai ‘inshaaAllah’ kawai take ta cewa amma tana ji Daddy ya shigo tashi d’aya kawai sai ta fashe da kuka! kuma ya yi tambayr duniyar nan ta k’i magana, ita kanta Hajiya mama kasa magana ta yi tsabar mamaki da al’ajabi. Sai daga baya tukunna da kyar ta bud’e baki ta gayawa Imam d’in cewa “nasiha take yi mata akan biye biyen malamai”ita ba ma tace masa ta ga abu a k’asan gadon Mommyn ba!,
Ita Mommyn ce da kanta tace”ai Hajiya maman tace ta ga kaza ta ga kaza a k’asan gadonta waye waye…”
Har da abunda Hajiya Mama bata ce mata ta gani ba duk sai da ta lissafo kaff abubuwan da suke a k’asan gadon nata da kanta…
Tana magana tana kuka! kukan da duk wanda ya gani sai ya tausaya mata.
A take Hajiya mama ta ga alamun b’acin rai a fuskar Imam amma dai bai ce komai ba ya yi shiru,ganin Yarinya tana shirin shiga tsakaninta da d’anta ne yasa tace “to a je a duba”
A take cike da kwarin guiwa Mommy ma tace “ta yarda a je a duba”
Tun daga nan jikin Hajiya mama ya yi sanyi dan sai a lokacin ta tuna ‘ba ta gyara katifar sosai ba’ dan ba zata iya ba ta yi nauyi, dan haka wataƙil Mommy ta gani sun gane an duba wajen dan haka sun kwashe….ai kuwa hakan ne dan ana zuwa in banda k’ura da akwatuna babu abunda aka gani a k’asan gadon Mommy.

Daddy bai ce mata komai ba,sai bayan kwana hud’u Allah kad’ai ya san mai da mai Mommy ta yi masa ta kuma fad’a masa tsabar an shanyesa hakanan ya zo yana ce mata wai”akwai wani Likita da za su je ta gani, idan mutum yana hallucination (yana gane gane) shi ake gani, a kaff garin Kano he’s the best”
a lokacin kacha kacha ta yi masa ta koresa, amma tundaga ranar daga ta ga k’adangare a d’akinta, sai ta ga maciji!!
kuma idan ta je ta tattaro mutane aka zo aka duba ba’a ganin komai! Hakanan za ayi ta kallonta ana mata kallon tab’abb’iya.
Ganin Mommy tana shirin haukatata ne ya sanya ta tattara kayanta ta d’auki Yashjub tace zai je ya yi musu hutu ta tafi da shi,dan abunda Mommy ta yi mata ya sanya ta fahimci tabbas za ta iya aikata fiye da chanjin Yaro ma.Tun daga lokacin ta san yadda ta yi ta d’auke Yashjub gaba d’aya daga gabanta, dan indai harshashenta daidai ne to kuwa ta san tsaff Mommy zata iya cutar da shi ko ma ta kashe sa,tunda indai saboda dukiya ne ta musanya Yaran to kuwa bata ga dalilin da zai sanya mommyn ta barshi a raye ba! Tunda yanzu kam dukiya ta dawo hannunta, ita da su Yassir………

Yanzu kuma da Mommy ta tura su Yasira suka zubarwa da Manubiya ciki hakan ya sake assasa zarginta ta fahimci komai,shiysa ta cewa Daddy ya barta a gidan su yi bincike a kanta sosai saboda tana so ta gano gaskiyar lamari da kuma duk wasu abubuwan da ta aikata a b’oye, su samu su tara shaida a kanta ta yadda za su fi hukuntata da hujja, dan tabbas ta san Mommy ta dad’e tana cutarsu ba tare da sun sani ba..to shi kuma Daddy gashi yanzu ya sake k’ak’abawa Yashjub Kausar.
Ta san ba laifin su bane ba, amma kuma ta kasa hana kanta fusata!! dole ta fusata saboda abun ya tab’ata sosai.Dan Auren Kausar da Yashjub kamar an sake kafe Mommy a cikin zuriarta ne….
Chapter 123 · 0% Book details