Sashe 8
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ya ce ’’Manu!
Ba zan tab’a bud’e k’ofar nan ba idan har ba ki gaya min abunda nake son ji ba, in ma bakya sona ne to ki fad’a min!.
Ni a ganina ke kika bari har aketa bugun nan, sannan ina so ki san cewa in har Doctor ne yake knocking d’innan to Mutane zai koma ya je ya tattaro a zo a b’alle k’ofar, tunda marar lafiya ne a cikin ɗakin dan haka in
su ka ji shiru yayi yawa za su yi tunanin ko wani abun ne ya sameni, gashi jiya na sanya sun zare cctv d’in d’akin nan, kinga ana zuwa ba ma Mutum d’aya ba mutum dayawa ne za su ganmu tsulum ɗin!
kuma Allah kad’ai ya san tunanin da kwakwalwar kowa za ta basa.
Dan haka komai yana a hannunki, ki yanke hukunci da wuri tun kafin a zo
a b’alla k’ofar nan saboda idan akwai abunda ya ke tabbatacce to shine ‘ni dai ba zan tab’a bud’ewa ba yau har sai na ji ishashshiya kuma gamsashshiyar kalma daga gareki’.’’
Ya k’arashe maganar yana murmushi k’asa k’asa yana kallonta
Dole ta ajjiye kunya a gefe
tun kafin ya janyo mata magana a cikin asibiti..
Dan haka ta runtse idanunta da k’arfi tukunna ta ce ’’i love you(ina son ka)”
A hankali Yash wanda tashi d’aya kasala ta rufar masa ya d’an matsa kusa da ita kad’an yana mai bin fuskanta da kallo,
ahankali kamar wanda baya so kowa ya ji ya ce ’’how much?(kamar adadin yawan yaya?)’’
Direct daga zuciyarta ta ce ’’so
very much(marar adadi)’’
Wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yance’’za mu yi auren mu nan kusa ko?’’
Jinjina kai ta yi still idanunta
a runtse tace ’’inshaaAllah’’
‘’Ki haifamin ya’ya masu kama da ke?’’
ahankali ta sake cewa ’’inshaaAllah’’
Wani bugun aka sake yi
wanda ya sanya Manubiya ta bud’e idanunta da suke ta kyalli dan a cike su ke taff da kwallah! Ta kalli k’ofar da sauri…
tabbas yau kam ta san babu yadda za’ayi ta iya had’a idanu da Yashjub dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa tukunna ta ce ’’plss ka bud’e, dan Allah’’
Lumshe idanunsa ya yi ya bud’e, yana mai sauƙe wata nannauya kuma zazzafar ajiyar zuciya, a ransa kuma yana mai ji kamar ya fita wajen ya je ya shak’e koma wanene a bakin k’ofar da yake ta yi musu wannan uban knocking haka, me shegen naci!!!! Tashi d’aya ya ji ya tsani knocking! Dole zai rubuta a cikin diary d’inshi shikam ‘ya tsani knocking, har abada!!’
This is the best moment of his life!, yana da buƙatar ya kaɗaice da ita
sannan ya samu yayi expressing kansa more and deep amman kawai an kama an zo an dame su, gashi ba ya so ya karya alk’awarin da yayi mata ta hanyar k’in bud’e k’ofar.
Da k’arfi aka sake yi dan haka Manu ta sake cewa ‘’dan Allah’’
A hankali ya juya ya zura makullin ya murd’a ya bud’e k’ofar yanajin kamar yana bud’ewa kawai ya fellawa wanda yake knocking d’in mari…………..
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 05*
Yana bud’ewa suka yi ido biyu da Yasmeen, a hankali ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin ya ce ’’ban yi tsammanin ganinki a nan ba”
Babu Mommy da Daddy a wajen ballantana ta yi rashin kunya, shiyasa ta yi shiruu ta d’an sunkuyar da kanta k’asa, kafin kuma ta d’an d’ago ta kallesa tukunna ta ce ’’Yau ce ranar da na ke shigowa aiki nan asibitin, shine na ce bari in lek’o in duba ka’’
‘’Nagode’’
kawai yace da ita, daga haka ya fara k’ok’arin maida k’ofar.
Manubiya tana jin muryar Yasmeen zuciyarta ta fara wani irin tuk’uk’i….yanayin conversation d’in su ba kad’an ba ya d’aure mata kai, gashi ta ji Yarinyar sai wani kashe murya takeyi tana wani lallaɓasa……
Da sauri Yasmeen ta sa Hannu
ta d’an tare k’ofar kafin ta ce
‘’Those are for you(waennan naka ne)”
Ta fad’i hakan tana mai nuna masa allurar Hannunta.
Wannan karon ɓata rai Yashjub ya yi, cikin d’an
fushi ya ce ‘’i’m fine, na warke. Idan kuma allurar mai mahimmanci ce to ki ji ki nemo Likita ya zo ya min.”
A ranshi yace ‘’lalle ma Yaran nan, rainin hankalin nasu ya yi yawa, su gama basa raini da attitude a gaban Mutane, shine yanzu kuma dan ta maida shi d’an cikinta za ta zo mishi, kuma ko bada hak’urin rashin kunyar da ta yi masa ma bata da shirin yi. Kamar ma bata yi komai bama’’
Ta ji zafi sosai amman sai ta
dake, ta d’an yi murmushi,
kafin a hankali ta ce ’’nima ai Likita ce, kuma shi ya shiga surgery, just let me (kawai ka bari in shigo) in i…..’’
Cikin fushi sosai ya ce
‘’Ke! Ina miki wasa??’’
Bai jira jin amsar ta ba ya ce ‘’b’ace min a gani, kafin in karya ki a wajen nan’’.
Dai-dai nan Jidda da Siyama suka k’araso wajen, dan basu
samu lemo da ayaban a kusa ba shine Ya Musbah ya karb’a suka tafi nema shi da Muhsin bayan ya balbalesu a titi kamar zai rufesu da duka.
A hankali Yasmeen ta d’an sunkuyar da Kanta ta fara k’ok’arin maida kwallar takaicin da take shirin yin nasarar zubo mata.
Sai da Jidda ta d’an rissinar da kanta
tukunna ta ce ’’Ya Yashjub, Ina wuni’’
Haka ma Siyama
Jinjina Kai ya yi kafin a hankali ya ce ‘’Alhamdulillah’’
Daganan ya juya ya shige, bayan ya bar musu k’ofar a bud’e.
Kamar ba za su kula Yasmeen ba, sai kuma jidda ta ce mata
‘’Sannu, Ina wuni’’
tunda ko da ace dai Likitarsa ce(dan sun ganta sanye da lap coat)
amma tare suka gansu suna magana de.
Da kyar ta iya d’agowa ta kallesu….kyawawan Mata ajin farko, masu ji da asalin kyau da k’uruciya, gashi sai wani kalar k’amshi sukeyi, su duka biyun. Sai dai tashi d’aya yanayin kayan jikinsu zai sanya a fahimci suna cikin yanayi na rayuwa…..sanye suke da dogayen rigunan Abaya bak’ak’e, amma
tsabar yadda kayan suka ji ruwa har bak’in ya d’an fara komawa kamar kalar dark ash!
Sannan rabin stones d’in jiki duk sun zube, tashi d’aya ta ji gabanta ya yanke ya fad’i!!!
Kallon
da taga suma sunayi mata ne
ya sanya kawai da kyar ta ce “fine’’a cikin zuciyarta tana tunanin ‘to wacece budurwar Yash d’in a cikinsu’………..
Sai da suka tura k’ofar suka
shige, tukunna ta samu damar yin ido biyu da Manubiya
wadda itanma Allah Allah dama takeyi a d’an bud’a k’ofar ta samu ta ga wacece take magana da Yash d’inta haka yake disga ta.
A bud’e su Jidda suka bar k’ofar dan a tunanin su shigowa za ta yi.
Har Manubiya ta d’auke idanunta daga kanta amma
ita Yasmeen din ta kasa, kallonta kawai take yi tana sakewa….sanye take da dark army green ɗin jilbab har k’asa, yanayin yadda ta yi parking gashinta ta d’aure igiyoyin jilbab d’in ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba….…’’Hi Yasmeen’’ d’in da sir Najeeb ya ce mata ne ya dawo da ita daga duniyar k’arewa Manubiya kallo, da sauri ta kawar da kanta ta mayar gareshi kafin dakyar ta samu ta d’an k’ak’alo murmushi ta ce ’’Najeeb,
Ina wuni!’’
Ta fad’i hakan tana d’an murmushi.
D’an lek’awa ya yi, ya hango Yash suna gaisawa da su Jidda, bai ga fuskokinsu ba
dan sun bashi baya ne iyakar
gefen fuskar Manubiya ya samu ya gani.
Juyowa ya yi ya kalleta kafin ya ce ‘’ya na ganki a bakin k’ofa?’’
ya yi mata tambayar yana tsare ta da idanuwa.
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ce ‘’ko da na zo ma na kusan 20 minutes, tukunna da kyar aka bud’e min, ashe Madam ce a ciki shiyasa, Itace yayar tamu ko?’’
ta yi mishi tambayar tana kallon Manu.
Direction d’in inda ya ga tana kallo ya kalla shima, tukunna ya d’anyi murmushi ya juya ya kalli Yasmeen d’in sannan ya ce ’’Yeah itace!
Ba ku gaisa ba ne? Mu je cikin mana..’’
Girgiza Kai kawai ta yi kafin ta ce ‘’Yace ma in ban bar nan ba sai ya karya ni, ma gaisa wata rana, bara in wuce’’
Ta fad’i hakan tana d’an yin gaba, sai kuma ta juyo ta ce ‘’am…
d’azu, na ga miss calls d’inka, sorry ina driving ne, shine na saka wayar a silent’’
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce ‘’akan Ya’isha ne!
Kin dai san halinta…..
Anyways (mu bar zancen yanzu kawai), na ga kamar kina sauri, ki je za mu yi magana anjima’’
‘’Ok’’
kawai tace, kafin ta juya ta yi gaba….
Shiruu Najeeb ya yi ya ɗan bita da kallo har ta b’ace ma ganinsa, a ransa yana tunanin ‘menene yake damun Yash haka ne?’
Shi, shi kad’ai iyayenshi suka haifa, Yana yawan fatan inama ace yanada siblings (ƴan uwa),
shiyasa har gobe yake mamakin Yash, ya rasa dalilin da yasa baya appreciating kyautar da Ubangiji ya basa ta ‘siblings..’
Girgiza Kai kawai ya yi, kafin ya shige cikin d’akin Bakinshi d’auke da sallama.
A hankali
duk suka amsa, kafin Manubiya ta d’ago cikin girmamawa ta gaidashi
Murmushi ya yi, ya ce ‘’Lafiya, ya
gida, ya mai jiki?’’
‘’Alhamdulillah’’ ta ce,
daganan ta sunkuyar da kanta.
Kusa da Yash ya d’an matsa tukunna ya ce masa “Ya jiki?’’
Kamar ba zai amsa shi ba, sai kuma ya ce ‘’Alhamdulillah, ai
na d’auka ba za ka shigo ba’’
Murmushi Najeeb d’in ya yi
kawai ya girgiza Kai kafin ya mayar da idanunsa a kan su Jidda waenda suka ce masa ‘’ina kwana’’
A tare.
Sai da numfashinsa ya yi sama!
sakamakon ido biyu da sukayi shi da Siyama. Dakyar ya samu ya iya ce musu ‘’lafiya, Alhamdulillah’’
sannan ya yi sauri ya d’auke Idanunsa daga kan Siyama wadda ita bama ta san yana yi ba, dan suna had’a ido ta sunkuyar da kanta.
Manubiya ya kalla kafin ya ce ’’ya na ganku duk a tsaye? Ku zauna mana.
Itanma sistern ki ce?’’
Ta san sun had’u da Jidda ranar a asibiti, shiyasa ta fahimci Siyama yake nufi, dan haka ta ce ’’Eh,k’anwata ce, cousin
sister’’
A hankali ya ce ’’MashaaAllah’’,
Sai kuna ya sake cewa “ku zauna mana’’