← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 152

Sashe 47

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita Yahanasu sai a wannan lokacin ne ma ta tuna cewa makullin d’akinta yana hannun Yassira!
Tashi d’aya ta san za su yi case idan ta shiga dan itama yadda take jin zuciyarta a yanzu kam wallahi kaff cikinsu babu wadda zata iya ragawa.

Tana yin parking Yassir ma yana fitowa daga cikin tasa motar.
Tun lokacin da suka taho dama
Munirat ta riga ta gama shawarar abunda za ta yi a cikin ranta, dan haka ta juya ta kalli Yahanasu tace”Bara in karb’i sak’o na, sai na shigo”.
Yahanasu ba ta kawo komai a ranta ba tace mata “to”
daga haka ta bud’e musu motar suka fito a tare, ita ta nufi main door Munirat kuma ta bi bayan Yassir wanda ya nufi b’angaren sa….tana ganin Yahanasu ta shige ta k’ara sauri..

Sarai ya ga lokacin da ta biyosa, amman ya yi banza da ita, yayi wucewarsa kamar bai ganta ba.
sai da ya zo shiga har ya zaro key ya ji tace
“Na san ka lura da ni”

Shiruu yayi kamr mai tunanin wani abun, kafin ya zura key d’in ya bud’e k’ofar tukunna ya juyo yace “Munirat a gajiye nake sosai!Make it fast pls..me ki ke sot?”
Matsowa kusa da shi tayi
tace “har haka muka zama?
Make it fast?baka ma da lokacin saurarona?
Okay ba komai shikenan!”

Ta fad’i hakan tana k’ok’arin juyawa…
rik’o hannunta ya yi, ya janyota garesa har sai da fad’a jikinsa kafin ya tallafe k’ugunta da hannunsa d’aya yace”Ke fa kika tura ni nesa da ke….wallahi har gobe Ina sonki Ina k’aunarki,
amman duk rintsi ba zan taɓa yi miki dolen ƙulla alaƙa da ni ba…..”

Gaba d’aya Munirat ɗin is uncomfortable, dan tunda take wani Namiji bai tab’a yi mata irin wannan ruk’on ba idan ba shi d’in ba
amman
kuma so take su shirya,kar ta
turesa ko kuma ta hanashi rik’eta ya zama ya fusata, sannan ga maganganunsa
na ‘yana sonta’
Da suka k’ara narkar mata da zuciya, shiyasa ta k’i motsi sam
tak’i cewa komai.

Hakan kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa Yassir ba, dan haka ya sake rungumeta da kyau kafin yaci gaba da gaya mata k’arya da k’arairayi har da cewa”har zazzab’i da rashin lafiya yayi kwanaki duk a ta dalilint,idan ya ganta kamar zai mutu haka yake ji gashi ba ta kulasa shiyaaasa za ta ga kamar gudun ta yake yi!”..
sannan ya fito k’iri k’iri ya ce mata ‘shi fa ba zai iya yin soyayyar y’an k’auyen da take so su yi ba, in dai har tana sonshi to ta sake da shi..ko ma me suka yi ai shi ɗin ne dai zai aureta a ƙarshe, dan haka ta daina wahalar da kanta tana wahalar da shi, indai har ta yarda da shi kuma shi takeson aura to a ganinsa ya kamata ta sake jiki da shi.!’

Ko da ta yi masa maganar Kausar ma, kanshi tsaye sannan ba kunya ba tsoron Allah yace mata “shi ba komai tsakanin sa da Kausar, ba sonta yake yi ba, kawai dai sun shak’u ne tun Yarinta”…..

Sai da Yassir ya tabbata ya gama zurma ta ta kamu tukunna ya d’aura da cewa”I love you so so much,ke kaɗai nake so Munirat”
Har cikin zuciya da jininta kuwa ta ji wannan kalmar tana yawo…… sai da ta lumshe ido ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace”I love you too”ta fad’i hakan tana k’ok’arin zamewa jin yadda ya sake mannata a jikinsa,kallon fuskarta ya yi kamar bai fahimci son zamewa take yi ba yace “mun shirya ko?”
Jinjina masa kai ta yi tana murmushi,ahankali yace”bari in tabbatar to”bata ankara ba ta ji ya fara kissing lips d’inta.
Bata biye sa ba saboda shock da
tsoro gashi kuma bata saba ba.
Ya kai 1 minute tukunna ya rabu da ita yana mayar da numfashi tukunna ahankali yace”haka na ke so…”
Ya fad’i hakan yana murmushi yana shafa kumatunta.

Ya lura da yadda jikinta ya d’au karkarwa tun d’azun har yanzu,sannan sam ta k’i magana ta ƙi ma ta yarda su haɗa idanu.

Ahankali yace
“Munirat,ko na b’ata miki rai ne?”
Ya fad’i hakan yana lek’en fuskarta.

Dakyar ta iya cewa
“A ‘a”

Murmushi yayi….

Ya na buƙatar hutu kuma ya lura ba abunda za ta iya yi masa yanzu dan ya ga yadda ta shiga shock daga iya ka kiss kawai.
shiyasa cikin son sallamar ta yace
“Muje in raka ki,kema ki samu
ki huta ko?”
Ahankali tace
“Okay”
Gaba d’aya jikinta a sanyaye…..rik’e hannunta yayi, daganan ya d’an janyo k’ofar entrance na side d’innasa
suka fara takawa yana d’an janta da hira amman ita daga ‘um’sai ‘um um’.

Sai da ya kaita kan kwanar da za ta sadata da main door d’insu tukunna ya d’ago hannunta yayi kissing yace mata”good nyt, zan kiraki”
Ahankali ta d’anyi murmushi tace “Sweet dreams”
daga haka ya yi waving d’inta suka rabu.

Sai da ya b’acewa ganinta tukunna ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya….ta san yin hakan babu kyau sam bai dace ba! amman ba ta jin zata iya hak’ura da Yassir gaskiya!
Dan haka za ta biye masa,
kuma inshaaAllah zata nuna masa rashin dacewar hakan a hankali a hankali in tafiya ta yi nisa, ta san Yassir yana sonta dan haka idan ta sake ɗaukar hankalinsa ta samu ya sake dulmiyawa a cikin kogin sonta to ta san za ta iya hana sa abubuwan da yake yi mata kuma ya hanu! Inyaso daga nan sai su yi tsaftataccen relationship d’insu, su yi aurensu in ya so sai ta sallama masa komai ta kula da shi yadda ya kamata su samu happy ending.
A ganinta hakan shine mafita
akan dai ace ta rabu da shi
bayan suna son juna, ba za ta iya zuba ido tana kallonsa ba, dan yadda ta ga ya fara nuna intrest akan Jidda ta san in ta bari aka tafi a haka shikenan sunanta sorry.
Ba ta da mai bata shawara su Ummi tun kwanaki da ta ganta da Yassir sam suka daina sake mata, ko hira Ummi da Yayarta sun daina yi da ita sun nace akan ta fito da miji kawai faka faka ta yi aure, ba dan haka ba da ko yayarta ta tuntub’a da maganar amman ta san sam ba za ta fahimceta ba wani sabon case d’in ne ma zai taso,shiyasa ta yanke decision d’in ta da kanta,ta yi abunda ta ga shine dai dai…
A gaba, In lokacin yayi kuma aka samu suka ɗan huce sannan su ka ga Yassir ɗin da gasken gaske ya shiryama aurenta, to ta san dole za su haƙura su yarda da shi suma.

Da wannan tunanin ta k’arasa bakin main door na mansion d’in ta danna, ganin a bud’e ne ma yasa ta tura zundumemiyar bullet proof door d’in ta shiga….

A tsattsaye ta samu kowa,
Mommy da Kausar ne kawai babu sai Daddy, amman har Ummi tana k’asan, amsa sallamar ta Ummi tayi kafin tace”Daga ina kike??”
Cikin tarrar numfashin Ummin Munirat ɗin tace”Waya na tsaya yi ne”

Kallonta Yahanasu ta yi ta d’an yi shiru sai kuma tace “Mu je d’akinki, in kwana achan”.
Daga haka ta juya ta kalli Yassira tace “Ki dafa key d’in ki cinye dan Allah!”
Ta fad’i hakan tana k’ok’arin wuce ta.

Fincikota Yassirar ta yi ta dawo da ita gabanta ta tsayar tukunna tace “Inaga baki fahimceni ba Yahanasu!
bacci ne kwata-kwata yau baki Isa yi a cikin gidan nan ba!
Dan wallahi yadda kika shiga tsakanin mu da d’an uwanmu
ki ka d’aga mana hankali to kuwa kema ba ki isa kin runtsa ba!.”

Cikin fushi Ummi tace “baki da hankali ashe Yassira?”

Kafin Yassira wadda ta juyo a fusace ta yi magana tuni Ya’isha ta amshe cikin tsiwa ta fara cewa “Haba ke kuwa! Wai
ashe kwata kwata kwakwalwarki bata d’aukar lissafi ke!.
Magana ake ta y’an uwa!
Tun d’azu sai ce miki ake yi ki
wuce ki tafi d’akinki amman
kin nace sai da kika ji komai,
kuma hakan ma bai ishe ki ba, tsabbar shishigi kin wani tsomowa mutane Baki..
Ina ce Daddy dakansa yace
‘ki fita harkar kowa, kuma idan family suna magana ki daina saka Baki’.?”

Cike da kwarin guiwa sannan ba tare da shayin komai ba Munirat ta taho tace “Ya’isha! Tou ai ni a ganina idan aka bar family d’in za su yi b’arna da shirme ne, tunda basu san abunda ya dace ba,
shiyasa Ummin take saka muku baki dan idan aka barki Allah kad’ai ya san kalar dak’ik’ancin da za ku yi”

Da sauri Ummi ta damk’o Hannun Munirat ta tura ta tace “wuce ki tafi d’akinki kafin na makeki”
Dan yadda ta ga Yusra da Ya’isha sun yo kan Munirat ɗin a harzuƙe ta san idan bata yi wani abun ba to tsaf za su rufeta da duka.

Za ta yi magana Ummin ta daka mata tsawa tace “wuce!! Nace ki wuce!”

Da sauri Yasmeen tace
“ai sai ta wuce d’in mu gani idan saman ubanta ne ya gina!.Kun je kun gama yi wa Mutane shishshigi kun k’ulla k’ullalliya shine yanzu zaku ce za ku
kwana lafiya?
Ai ba ku taki zaman lafiya ba, dan haka bacci bai ganku ba, masifa da tashin hankali ne suka ganku!”

Cikin fushi Munirat tace
“Okay!….
Sai yanzu na gane matsalar ku,
ko kuma ince matsalolinku!…
Na farko baku samu yadda kuke so ba!
Na biyu kuma Ya Yash ya fatatttake ku, shine kuka zo zaku d’aga mana hankali zaku hana mutane bacci! saboda tsabar bak’in ciki da k’unci…
kun rasa Ina zaku sa ranku shine kuke so ku huce a kanmu, ko?.

Ai ba mu muka ce ku zama bad people ba….kuma da ace kuna da kirkin sannan kuna yi wa Mutane kirki to da duk hakan bata faru da ku ba.

Kuma abunda ban gane ba, shin idan mun tsaya d’in mai hakan zai k’are ku da? kawai kar mu yi bacci shine burinku ko me??
kuna jin abunda kukeyi kuwa?
kowa fa ya na jin hakan ya san kawai kuna neman inda za ku sauƙe fushi da ɓacin ranku ne, haba mana!
Ku gyara abun naku ta hanyar yin wani abun mai ma’ana wanda hankali zai ɗan ɗauka ba wai wannan ba!”
Chapter 47 · 0% Book details