Sashe 151
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya ta yi sosai tace”ka yi winning! Ka zab’i in kawo maka special ɗin yanzun kenan!
Inda ace ‘kai’ ka d’auka to da sai nan da dare tukunna zaka samu special d’in.”
Daga haka ta Mik’e, ta je ta d’auko disposable plate d’in ta dawo ta
koma
Inda take zaune nan kan cinyarsa ta zaune rik’e da plate ɗin, sannan tace masa “gashi”
Murmushi ya yi yana kallonta, tashi d’aya ya sa hannu ya bud’e ya kai idanunsa wajen.
….
Shiruuu ya yi yana kallon pt d’in dake nan ajjiye a kan tissue wanda yake nuna masa positive….
Yadda ya yi shiruun sannan ya k’ame ya sanya ta d’an d’ago ta kalli fuskarsa shima a dai dai nan ya kalleta da Idanunsa da suka yi jazir hawaye ya fara zirara bakinsa yana karkarwa yace”d-daaa g-ask-e??”
Jinjina masa kai ta yi ta kamo free hand d’insa ta d’aura a kan cikinta tukunna tace”Eh!!”
Bata Ida rufe bakinta ba a zafafe ya had’e bakinsu waje guda ya shiga kissing d’inta yana mai sake sakata a jikinsa kamar wanda zai mayar da ita cikin jikin nasa ne…..
………..
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, cike da zallar farinciki….
An saka ranar Yahanasu da Dr Engr Kamal haka Hadiza itama an bayar da ita a Ya Musbah har an saka rana suma.
Najeeb ya sauk’a, ya mayarwa da Yash gaba d’aya companies d’insa da businesses d’insa dan shima aiyyukansa sun yi masa yawa zuwa wannan lokacin dama kawai maneji yake yi…
Ummi da Mama kuwa shi kansa Daddy ya fad’a ya sake maimaitawa
‘ko a labari ko a film bai tab’a ganin kishiyoyin da suka had’e Kai suke shimfid’a rayuwar asalin zaman lafiya na tsakani da Allah da kwanciyar hankali ba! Kamarsu.’
Gashi sun rungumi su Yasira, ta ko wanne b’angare sun zame musu Uwar da sukayi rashin sa’arta, idan aka shigo cikin gidan in ba wai Mutum ya riga ya sani ba dama chan ko kuma an fad’a masa to ba wanda zai tab’a sanin mahaifiyarsu bata cikin gidan, dan su Ummi basu rage su da komai ba.
Hakanan suma su Yasirar suke girmama Ummin da Mama, sun d’aukesu iyaye, suna zaune da kowa tsakani da Allah.
Tsakanin su Yasira da Manubiya kuwa abun sai dai ace ‘Alhamdulillah!’, dan sosai suke nuna mata da gaske fa sun shiryu..sosai kuma suke kyautata mata suke mutuntata da nuna mata asalin k’auna da tsantsar tattali kuma har cikinn zuciyoyinsu babu mix a dukkan abubuwan da su ke yi mata ɗin…
A fannin Manubiya itama ta tashi sosai ta tsaya wajen jaansu ajikinta kamar ƴan uwanta!
Kwata kwata babu jirwaye ko mix itama a cikin ƙauna da kulawar da ta ke musu, dan tsakaninta da Allah sannan da zuciya ɗaya ta ke yi musu komai.
A fannin kuɗi dai Yash yana da shi dan haka komai in ya tashi ta kafa ta tsare tare take cewa a yi musu ita da kowa, amma opportunity kam idan ya zo ya zamana ba zai yiu a yi musu su duka ba to Manubiya ta kan hakura ta barwa su Yasira…Shiyasa a ko da yaushe suke sake jin regtret!…suna sake jin Zallar dana sani yana daɗa shigarsu saboda gashi Manubiyan da suke tunanin zata yi musu mugunta ko kuma za ta raba su da ɗan uwansu ita ce tsaye tsayiin daka wajen ganin sun haɗu kuma sun shaƙu da ɗan uwan nasu dukda shima Yash ɗin dama ya ɗau alƙawari kuma hakan ne burinsa amma da ace Manubiya bata so ba to da sun san abubuwa da yawa ba su kankama a tsakaninsu da Yash ɗin ba. A gaban kowa sannan a ko da yaushe za su iya tsayawa su bugi ƙirji su ce sister in law ɗinsu is the best!
Dan abunda ta ke yi musu kamar itama ɗin tasu ce ba wai Yash ɗin shi kaɗai ne nasu ba.
Yadda take yi musu addu’a akan aure tsakaninta da Ubangiji kuwa, ko a kanta ne inda ace ba ta yi auren ba to iyakar addu’ar da za ta yi kenan, dan ta san abun yana damunsu kwarai da gaske.
Rayuwar gidan dai asalin jin dadi da farin ciki zallah, gashi arzik’in Daddy da Yash sai sake bunk’asa yake yi.
Manu kam wani zubin har kuka take yi…saboda indai farin ciki ne da tsantsar soyayya ta miji da dangin sa to itakam ta samu….tabbas Ubangiji ba yadda ba ya iyawa; ya kan chanja situation daga bak’ik’irin ya koma fari k’alll!!.
Bayan dangin miji da Miji ita kanta rayuwarta da rayuwar gidansu aya ce, dan zuwa yanzu cikin hukuncin Ubangiji rayuwarsu ta zam abar sha’awa ga kowa tabbas!!
Kusan za a ce sun samu komai su kam, Alhamdulillah.
Har islamiyya su Yasira suka koma saboda su samu su yi repenting da kyau sannan su koma ga Allah yadda ya kamata, dan da gaske sun shiryu shiryuwa ta tsakani da Allah, sun yi danasanin abubuwan da suka dinga yi a baya….Miji ne dai ko saurayi har yau shiru, dan bayaga Yaha wadda ta auri Kamal har zuwa wanan lokacin babu wadda take da mashinshini a kaff cikinsu.
Daddy ya so su Manu su tashi su yi gidansu a daban, dan shi gani yake yi kamar an takura musu, amma ita da su Yasira suka ce sun fi jin dad’in zaman taren, dan haka aka sake gyara mata side d’in Yash suka ci gaba da zama a nan.
…………
Bayan shekara bakwai.
Babu zancen Yusuf babu labarinsa har gobe, an gagara amsoshi.
Company da Businesses d’in da Yashjub ya so ya d’aura Yassir akai shi ya bawa Ya Musbah, kuma abun ya bunk’asa ya yi albarka fiye da tunanin mai
tunani….
Ya Musbahn ya kammala degree d’insa a buk, yayi masters d’insa a cairo duk a fannin business admin, gashi Allah ya dafa masa kasuwancinsa dan duk wanda ya tab’a to sai ya yi albarka, yanzu haka a kaff layin nasu babu wanda ya kaisa bud’i da arzik’i jama’a har maula suke zuwa wajen Ya Musbah, haka masu buk’atar taimako suma…Daga ya dawo daga tafiya za a fara layi a kofar gidan, kowa yana son ganinsa….
Ya sake gyara musu gidan gaba ɗayansa, ta inda ya mayar musu da gidajen duk
biyun masu bene, ya kyalkyalce su ta koina, dan ana shigowa cikin layin katangar da gate na gidan da kuma gidanjen guda biyu ne suke fara ɗaukar idanun mutane.
Shekaru uku baya da suka wuce su Baba Habu suka yi wata mummunar gobara!
babu dai wanda aka rasa duk an fitar dasu akan lokaci ammafa ko cokali basu samu sun d’auka ba, komai sai da ya k’one….a lokacin ya Musbah ya fara tashen arzik’insa shi ya kwashessu ya kama musu haya na shekara d’aya…a cikin watanni tara aka gina musu gidaje a cikin filin nasu masu bene hawa d’add’aya part uku Uncle Baba Habu har da anty umma, da babban parlourn kaka mallan….
Sai da su Baba Habu suka yi da gaske tukunna kunya danasani da nauyin Baba suka barsu suka zo gidan suka yi godiya!. suna kuka sosai suka nemi yafiyar Baba bisa ga abunda suka dinga yi masa!!….murmushi kawai Baba ya yi ya ce musu “‘komai ya wuce, burinsa kawai shi a yanzu a yi zumunci, bai rik’e kowa a cikinsu a rai ba!’
A rayuwa kowa ya kan yi kuskure, amma abunda ake so shine mutum ya gane kuskurensa kuma ya gyara, shi kuma wanda aka yi wa laifin ya yi k’ok’ari ya yi hak’uri kar ya ce zai rama, ta hakan ne za a ga dai dai sannan komai ya tafi bisa tsari.”
Ai kuwa Baba ya ga zumunci ganin idanunsa, kuma yana kan ganin zumunci saboda a halin da ake ciki Hatta d’inki tare Baba Habu da Uncle suke yi da shi! komai iri d’aya, wani zubin har agogo iri d’aya suke sakawa, gidansa kuwa suna yawan zuwa, wanda kasancewarsa k’aramin cikinsu ya sanya shima yake zuwa nasu gidajen sosai domin ya hutashshesu.
Anty Umma kuwa tunda akayi gobarar da ta dawo gidan Baba har yau su Inna sun ce kawai ta zauna tare da su…Gwaggo Suwaiba itama tana yawan zuwa, Mijinta har yau yana nan amma fa ciwo ya ci ya cinyesa ko tafiya ma ba ya iya yi, haka nan take fama da jinya.
Kaka mallan shima tun shekaru shidda baya ko bakin maganar ma babu, yanzu kuwa ba ma ya sanin waye a kansa.ciwo ya ci ya cinyesa sosai.
…….
Hannun Ya Musbah a bud’e yake sosai, shiyasa yake dad’a samun bud’i, kwata kwata bashi da rowa bashi da kyashi…Ya Nafi’u shima ya samu chanjin aiki, yanzu yana da rufin asirinsa amma duk da haka Ya Musbah sai da ya siya masa gida ya chanja masa mota tukunna hankalinsa ya kwanta, sannan har gobe kayan abinci! kayan sakawa nasa da na Yaransa biyu mace da Namiji da na matarsa kullum ya Musbahn ne yake siya! k’iri-k’iri ya hana Ya Nafiu yin duk wata hidima, ya d’auke masa komai, dan idan duniya da alk’awari ba zai tab’a mantawa da Nafi’u ba.!
Duk wani business da yake yi sai ya san yadda ya yi ya sako Nafi’u a ciki shima ya samu abunda ya samu.
Sosai rayuwa ta chanja tables suka juya!
Yaransa uku a halin yanzu duk maza dan Hadiza ta Haifa masa Yashjub da Naf’iu.
A ko da yaushe Ya Musbah idan ya samu hali da dama ya kan yi ƙoƙarin wajen ganin ya sanar sannan ya fahimtar da Mutane cewa ‘duk yadda tsanani ya kai tsanani duk yadda hanyar ta kai ga ƙullewa toshewa sannan duk yadda komai ya rufe koina ya yi duhu, har ta kaiga Bawa yake ganin no way out! Babu mafita kwata-kwata! To bawan Allah kar ya taɓa fidda rai daga rahamar Ubangiji!
Sannan wayo dabara ko kwarewar Mutum ba ita ta kaisa zuwa ga nasara ba rahamar Ubangijice.
Kuma a duk yadda ka ga Mutum a yau kar ka taɓa rainasa saboda baka san wayene shi ɗin ba a gobe.
Jidda itama suna zaune cikin Jin dad’i dukiya da daula da tsananin k’aunar juna, suna son juna ita da Ammi ma Sosai suke zamansu lafiya….Yaranta uku, biyu mata d’aya Namiji, ta kammala karatunta a northwest, yanzu haka tana businesss.