← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 152

Sashe 30

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yassir ya lura da yadda Yashjub yake kallonsa amma sam bai damu ba!
A ransa ya aiyyyana “to ai gwara ma ya kaishi
bangon, ya k’ular da shi ta yadda zai yi shirme a k’ofar gidan surukan nasa!
Oho! Shi kam dad’i ma zai ji”
Ya aiyyana hakan a ransa, sai kuma cikin son sake fusata shi a fili Yassir d’in ya ci gaba da cewa
“Har ga Allah ka fara kaini bango kark……”
Maganar tasa ce ta mak’ale sakamokon hango Siyama da ya yi tsaye a bakin k’auren gidan, tana magana da alamar akwai wani a ciki wanda take magana da,
‘Anya ba gamo na yi ba kuwa?’
Ya yi wa kansa tambayar a cikin ransa, yana mai jin wani sanyi yana ratsashi, bai gama
dawowa dai-dai ba
Jidda ta fito, tana hararar Siyaman wadda ta tare hanya ta hanata fitowa har sai da ta sauk’e mayafinta daga Kai tukunna ta bata hanya ta fito daga gidan, ahankali Yassir ya motsa Bakinshi ya ce “woow”
ba tare da sautin woow d’in ya fito ba.

Girgiza Kai sir Najeeb ya yi kawai, ya juya, dan ya san tabbas Maata Yassir ya gani….

Wani tashin hankalin takaici ne ya lullube sir Najeeb ɗin a sanda ya juya sakamokon had’a ido da sukayi da Siyama dan yana juyowa kamar ance ta d’ago, suka had’a ido…
Wato ita Yassir yake k’arewa kallo shine ya k’ame haka….

Dakyar ita kanta ta sunkuyar da kanta k’asa ta ci gaba da takawa inda suke tana jin yadda k’irjinta yake bugawa
ahankali ahankali…..

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 16*

Sai yanzu Jidda ta hangesu,
dan haka itama ta bi Siyaman suka jera suka nufesu.

Duk yadda Sir Najeeb ya so sam sai ya gagara d’auke Idanunsa daga kan Siyama….ya so yin hakan amman sam sai ya kasa…babu kwalliya a fuskarta dan ko kwalli ba su samu sun saka ba sakamakon saurin da suke ta yi, amman
ba k’aramin kyau ta yi masa ba, shiyasa ya shagala da kallonta yana mai zuba wani Irin murmushin da shi kanshi bai san yana yi ba.
Hatta Yashjub wanda juyowar sa kenan sai da ya lura ya kuma fahimci kalar kallon da Najeeb d’in ya ke yi wa Siyama, shiyasa kawai ya tsaya yana kallon shi da d’an mamaki kwance a kan fuskarshi.

Jidda ce ta samu ta ce mishi “ina wuni”
Dan gaba d’aya Siyama ta d’an rikice sakamokon yadda take jin idanuwanshi suna yawo a Jikinta….

Da kyar ya d’an kalli
Jidda yace mata “Alhamdulillah”sannan ya juya ya amsa gaisuwar Siyama wadda ta Isa har cikin zuciya, ruhi da kwakwalwarsa.

Ahankali sukace “Ya Yash ina wuni”
Wanda shi
Kuma sai da ya d’an yi murmushi tukunna ya ce “Alhamdulillah”
Daga haka suka yi masa Allah ya sanya alkhairi, ya amsa cike da fara’a kafin ya sake duban Najeeb wanda still yake ta satar kallon Siyama yana murmushi.

Dakyar jidda ta iya cewa Yassir “Ina wuni”
Siyama kuwa ko kallonsa ba ta yi ba dan kwata-kwata gayen bai mata ba.

Cike da fara’a Yassir d’in ya amsa kafin ya d’aura da ”ya taro?”

Girgiza Kai kawai Yashjub ya yi,
kafin ya kalli Siyama
wadda take cewa ”Ya Musbah yace mu shiga da ku wajen su inna, Manu ma ku take jira”
Sai a sannan Yashjub ya yi murmushi ya ce ”Lead the way”
Ya fad’i hakan yana nuna mata hanya.

Juyawa ta yi hakama Jidda daga haka suka yi gaba su kuma suka mara musu baya.

Najeeb ji yake kamar ya janyota ya sakata a bayansu shi kuma ya shige gaban Yassir,
Ya san yadda shi kansa ta d’au hankalinsa bashi da tantama Yassir ma k’are mata kallo
yake ta yi, shiyasa kwata-kwata ya ƙi yarda ya kalli Yassir d’in dan ya san idan har ya ga yana kalle masa ita to tsaf zai iya bige masa ido…
ba wai iyaka Yassir kad’ai ba hatta Yashjub wanda shi danna wayarsa ma yake yi sai da Najeeb ya ji kishin shi, yana mai jin takaicin dalilinta na rufa mayafi bayan ta san yau maza za su taru!…’

Yassir kuwa gaba d’aya lissafinshi ya kunce…yana ganin Munirat mai shape da kyau to ga iyayenta a shape da kyau da komai ma
Yara kamar aljanu!!.
Tabbas yanzu ya fahimci dalilin Yashjub na zuwa nan ɗin ya mak’ale….

A bakin k’ofar gidan me hoton da yaransu suka zauna dama, dan haka suna zuwa suka kutsa suka shige a tare gaba d’ayansu.
Har d’akin su Manubiya suka shiga,dukda d’akin yana da girma sosai amma da kyar su kansu angwayen suka samu wajen zama, masu video coverage da hotuna kuwa a waje suka tsaya suka yi y’ar dabara suka d’auki abunda ya sauwwak’a.….Yadda al’ada ta tanadar haka suka gaida iyaye Matan, su kuma suka sanya musu albarka, daga nan sukayi musu y’ar guntuwar nasiha suka basu amana….
Dubu d’ari huɗu su Yash suka ajjiyewa ko wacce uwa, daganan suka mik’e suka yi musu sallama suka fita, suka barsu cikin shock.
inna ta ji ba dad’i da ta ga su mama ba su samu shigowaba har aka gama…ba wai dan kud’in ba sai dan ita a ganinta a hidimar bikin nan ai mama da anty umma sune iyaye..matan d’akin kuwa suma sun yi kara dan sun lura da yadda su maman suke ta hada hada shiyasa aka had’a kud’in guri guda aka raba daidai har da su.

Sai da suka fito tukunna Yashjub ya lura da Yassir, dama kamar ya ji muryarsa a bayansa
yanata ‘Ameen Ameen’,
“Hmm” kawai yace daga haka suka mik’a, su Siyama suka kaisu har parlournsu inda Manubiya take.
Parlourn tas
da shi sai tashin k’amshi yakeyi, ba kowa daga Manubiyan sai Aisha wadda ta gama gyarawa Manubiya
kwalliyarta, dan duk ta chab’e saboda kuka….

Jidda ce ta gabatar musu da Aisha a matsayin sister d’insu itama.
Da kulawa suka gaisa da ita, ta yi musu Allah ya sanya alkhairi suka amsa da fara’a…

Ba a daɗe ba, da wani brother d’inta zai wuce ta basa ƴarta(Khairat), tace masa ya kaita wajen mamanta anjima idan za su taho sai su zo da ita, kuma dama Aishar bata yi kama da Matar aure ba dan duk wanda kalleta ma ba zai yi tunanin ta ma yi auren fari ba, shiyasa har ita(Aishar) bata tsira daga kallo da mugayen tunanin Yassir ba…

Kan Manubiya a lullub’e yake, yana cikin mayafinta har zuwa wannan lokacin amma yana iya ganin yanayinta kad’an-kad’an…shiyasa gaba d’aya Yassir ya sake
gigicewa,hatta k’afafuwansa karkarwa suka fara yi….
ya san ba zai yiu ya had’e su su duka hud’un ba amman wallahi shi dukkansu yake so…
Dan haka ya shiga lissafi….
……dukda bai ga fuskar Manubiya sosai ba
amman itama ta yi mishi.
Ya san ba shi da damuwa a case d’inta, he’ll find his way (zai nemawa kansa mafita) ko ta halin k’ak’a ne, tunda Matar yayansa ce dan haka kamar ma a gidansu take ai.

Aisha kuma bata kai su Jidda
kyau ba, dan haka zai yi hak’uri ya cire ta a lissafi ba dan yana so ba…

A yanzun matsalarsa itace ta yadda zai samu both Jidda da Siyama dan har ga Allah bai ga ta yarwa a cikinsu ba……

Dariyar Najeeb ce ta katse masa tunani….cikin sigar tsokana Najeeb d’in ya cewa Yash “ya dai? Ko kawai mu ce a
bamu Amaryar mu tafi da ita tun yanzu mu da kanmu?”

Sai a sannan hankalin Yashjub ya ɗan dawo Jikinsa, a hankali
ya yi murmushi yana mai jin wani farin ciki mara misaltuwa yana sake lulub’esa, tukunna cikin nutsuwa ya taka ya k’arasa inda take zaune,
ya yi bismillah sannan ya zauna a daff da ita kamar zai shige cikin jikinta!
A tare daga shi har itan suka sauk’e b’oyayyiyar ajiyar zuciya, kafin ya sunkuyar da kanshi yana wani irin murmushi…..

Su Jidda har ma da masu hoto, suna nan tsaye suna jira ya bud’e mata fuska a yiyyi hotuna amman sai suka ga ya d’ago ya kallesu ya ce ”Bismillah, ku zo a yi hoton.
Jidda bismillah”
Ya ƙarasa faɗin hakan yana mai nuna mata gefen Manubiya alamun ta zo ta zauna.

Mai hoton ne ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce ”Am…
ranka ya dad’e, ai sai ka yaye mayafin nata tukunna za’a fara ɗaɗɗauka…haka na ga ana yi a duk lokacin da na je d’aukar hoto”

“Haka ka yi wa taka kenan??”
Yashjub ya yi masa tambayar ba tare da ya kalle shi ba dan
zuwa wannan lokacin hanakalinsa ya tafi zuwa ga y’an yatsun Hannunta waenda take
wasa da vail d’inta da su….
tun ranar da ya rik’e mata Hannu a office d’insa yake muradin ranar da zai sake samu ya rik’e, shiyasa without thinking twice (ba tare da ɗaukar lokaci ba) ya ruk’o Hannun nata cikin nasa duka biyu.

A tare duk su biyun suka sauk’e ajiyar zuciya wanda duk sai da sukaji, sai kuma ta yi sauri ta sunkuyar da kanta k’asa….jin shiru ba a fara d’aukar hotunan bane yasanya Yash ya d’ago da kyar, ya zubawa me hoton lumsassun idanuwansa.

Najeeb mai hoton ya kalla wanda ya ce masa “ka d’auke su a hakan mana” tukunna ya matsa ya fara saita camera…..
wajen kalar biyar zuwa shida aka yi musu, me hoton yanata mamaki dan shi kam yau ya ga amarya mai lullub’i.

Sai da aka gama yi musu su biyu, tukunna su Jidda ma suka shiga, Yassir kuwa har da zama kusa da ita, aka yi musu su uku…wanda zaman da yayi a kusa da itan saida ya sanya Yashjub ya ji kamar ana zare masa numfashi.
Najeeb kam ya san halin kayansa shiyasa ya tsaya a tsaye a gefenshi akayi musu.

Zuwa yanzu hatta masu hoton sun lura da yadda Najeeb yake ta kallon Siyama wadda gaba d’aya ita kuma take a takure da shi, shi kuwa sai wani nan nan yake da ita abun har mamaki ma yake bata…shiyasa ita da Jidda harma da Aisha suka d’an fara fahimtar inda Mutumin ya dosa .

Masu hoto suna fita Aisha tace
“Yauwa mu zamu wuce, muna d’an sauri saboda akwai kayan jere da za mu kai gidan nata”
Chapter 30 · 0% Book details