Sashe 143
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A b’angaren Kausar kuwa, tana nan cikin tashin hankali dan ga Yash da Manu a cikin gidan kusa da ita amma kamar basa nan…..ba ta Isa ta je inda suke ba kuma tunda suka zo
ko ganinsu bata yi ba, Yasmeen dai tana zuwa wajensu har Yadira idan sunzo, amma shi kam saboda ita ko lek’owa bayayi itama Manu ya hanata shiga main cikin gidan kuma su Hajiya mama sun yarda da hakan, Daddy dai da asubah suke gaisawa Hajya mama kuma ta kan je musu da kanta…….
..
Tun daga kan Hajiya Mama har zuwa kan Yadira wadda suke yawan zuwa gidan….duk y’an gidan mamakin Kausar suke yi dan ta ma fi su energy. Kwata Kwata ba ta jin nauyin cikin jikinta, sannan babu alamun ciki ya d’auko tsufa a tartare da ita…….
Kwatsam!! yau suna zaune aka yi musu waya daga asibiti wai ‘Kausar ta haihu, ta haifi baby boy!’
Matarda Ba ma su san lokacin da ta fita dafa cikin gidan har ta tafi asibitin ba.
Ummi da Yasmeen ne kawai suka je asibitin…sai da Ummi ta firgita a lokacin da ta d’auki Yaron! sakamokon tsananin kamannin da suke yi ita da Yaron, hatta Yasmeen sai da ta lura da hakan, dan haka kanta ya sake d’aurewa tamau game da al’amarin Kausar da haihuwarta…
Basu dad’e da zuwa ba su Mommy suka k’araso, dan haka Su ummin suka yi mata sallama suka wuce gida kawai, hatta Yasmeen ma wadda Ummi ta yi tunanin zata d’an zauna da su mommuyn bata zauna ɗin ba, biyota kawai taga ta yi.
Su kansu su Mommy sun yi mamakin tsananin kamannin Yaron da Ummi, amma kawai sai suka bari akan watak’il saboda tana yawan kallon ummin kullum ne, shiyasa.
Mommy har da cewa”akwai wani d’an makwaftan su itama da ya tab’a yin kamanninta lokacin suna yawan shiga gidan!!”.
Daganan kuma suka hau murna, sannan aka fara zab’e zab’en suna aka zab’i ‘Alan’, ba kad’an ba sun ji matuk’ar dad’i da Yaron ya kasance Namiji dama tuntuni mommy take cewa ta yi scanning ita kuma tace bazata yi ba, gara kawai ta Haifa a gani.
Kausar ba ta b’oye musu abunda ta k’ullawa Manubiya ranar suna ba!
Su dai su Yasira basu ce komai ba, dan zuwa yanzu komai ya fita a kansu!
Mommy ce ta bada goyon baya, dama tana neman ta inda zata rage bak’in cikin Manubiya kafin a samu asirin ya kamata ta tafi forever…
Idan kuma ma ta mutu kafin ranar sunan to falillahilHamdu!!!
Daganan kuma suka shiga tattauna akan kud’in da zasu had’a bayan suna a samu Mommy ta ga likitan ido,dan suma zuwa yanzu al’amarin idon nata ya na tsorata su.
…
Bayan kwana d’aya aka kaiwa su Hajiya mama Yaron har gida ,Yash kuwa Ana ce masa za a kawo Yaron ya gani ya fita ya bar musu gidan sai dare tukunna ya dawo.
Wanda hakan ya kusa haukata Kausar a lokacin da mai aikin nata ta dawo mata da Yaron take bata labari, dan ita a tunaninta Yaron ne zai sanya ta samu kusanci da Yashjub daganan kuma ta sameshi yadda take so……….
Itadai Yasmeen har gobe gaba d’aya mamakin lamarin haihuwar Kausar take yi, ta lura kowa ma hakan take a wajenaa, amma kawai ba a son yin maganar ne…kwata kwata jikin Kausar bai nuna alamun jego ba, kuma duk girman Yaron ance bata samu tear ba, sannan har zuwa ranar suna ruwan nono bai zowa Kausar ba hakanan ake ta d’urawa Yaron madara.
Gagarumin suna aka had’a na gani na fad’a suka gaiyyaci Mannubiya…ita Manubiya da farko cewa ma ta yi bazata je ba, shima Yashjub yace “ta huta kawai”
Saboda yau ɗin za su je gida, jibi arba’in d’in inna, amma sai su Anty Umma sukace “ta je kawai tunda sunan da yamma ne kuma ma har sun gama shirye shiryen sadakar da za a yi jibi…
saboda idan bata je ba kowa mummunar fassaara zai yi mata, tunda har sun gaiyyace ta to ta je kawai.”
Dan haka ta tashi ta fara shiri….
Bata jima da fara shirin ba Yash ya yi mata waya ya ce ya taho dan haka ta ƙara sauri…. tana cikin shiri kiran Abbakar ya shigo wayarta a karo na ba adadi…..tun d’azu basu zauna ba, shiyasa bata samu ta saka wayar tata a charji ba, dan haka yana kira wayar ta katse ta mutu gaba d’aya!
Tabbas ta san zai ga kamar kashewa ta yi, kuma Abbakar bai chanchanci wulak’anci daga gareta ba, ko ba komai yadda ya dinga d’awainiya da Inna da Baba bai kamata ace ita ta banzatar da al’amarin tasa mahaifiyar ba..har harbinsa aka yi a ranar da akayi case d’in black snake duk saboda ita da ahalinta…..tana cikin wannan tunanin Muhsin ya shigo cikin d’akin kamar ba zata yi komai ba sai
kuma kawai ta karb’a wayar hannunsa mai tochila ta saka sim d’inta a ciki ta kira asalin layin Abbakar….
ga mamakinta bayan ya amsa sai ji ta yi ya ce mata “dan Allah ta fito,
dama ya zo
ganinta ne, yana neman alfarma a wajenta.”
So ta yi tace ya shigo, amma ta san su Aisha ma sai sun yi mata magana muddin suka gansu tare shiyasa kawai ta fita tanata jero istighfari….A nan wajen ta samesa zaune a kan machine d’insa, yana hangota ya mik’e ya nufota wanda hakan ya sanya jikinta sake d’aukar karkarwa….
Gaisawa kawai suka yi daga haka ta fito masa k’iri k’iri
tace “dan Allah ya daina yawan kiranta, Mijinta baya son mu’amalarsu, ya yi hak’uri kar ya janyo mata matsala….”
Sosai ya nuna mata ya fahimta yace
“ta yi hak’uri dama godiyar kud’in da ta tura masa ya zo yi mata, sannan ta k’ara hak’uri da shi amma kud’in basu kai ba..aiki za a yi wa Mahaifiyar tasa a zuciya, yanzu haka dai cikin kud’ad’en da yake ta tarawa saura dubu d’ari biyu…..”
A take ta sake tura masa kud’in ya cika, tace “ya yi
hak’uri ta san yayi mata halaccin da bazata iya k’irgawa ba, amma dole ta yanke alak’arsu har abada, ta yi saving aurenta, idan yana buk’atar wani abun ya gayawa Muhsin shi kuma zai gaya mata”
Hakanan suka rabu yanata jera mata godiya, zuciyarsa k’all dan chan ya hango Yashjub ya danno kan motarsa tun d’azu amma da ya gansu sai ya tsaya ya ja ya yi parking, ita kuma Manu sam ba ta lura da shi ba.
Tunda ta fito yake ta addu’a Yashjub ya zo dan Kausar tace masa mai gadin yace
“tun d’azu ya fito……”
Tun a jiya ya tura masa mesaage ta inda yake cewa
“a tunaninka sharri na yiwa matarka ko?to yanzu haka halinda ake ciki kud’i take bani nake tarawa zan siya mana gida,mu ja jari kafin ta rabu da kai.
Manubiya ni take so ba Kai ba za ta iya yin komai saboda ni….idan Baka yarda da maganata ba ka duba alert a wayarta.”
Shiyasa tunda Manu ta fito yake ta addu’ar Yash d’in ya zo saboda ya samu ya sake k’ulleta idan Yash d’in ya gansu tare.
A b’angaren Yash kuwa kwata kwata bai yarda da maganar Abbakar ba! Haba mana!! Abu kamar na wasan Yara, amma fa da ya gansu tare ya kusan suma a cikin motar dan ko last week sai da yace mata ba dai ta kula Abbakar ba ya fakewa da zuwa musu gaisuwa ko? ita kuma tace masa “eh”
Sai gashi yau ya gansu tare a tsaye a waje ba ma a cikin gida ba, kamar wasu masu zance!!!
Su Siyama sun tafi Umrah, Jidda kuma bata da lafiya, shi kuma Muhsin da shi ake aikin kimtsa gida ga aike, shiyasa ba ta samu me rakata ba…Bata dad’e da komawa cikin gidan ba Yash ya kirata yace”ta fito ya zo!”
Peach colour lace ne a jikinta da white vail takalmi da y’an kunne da agogo…Bata yi kwalliyar komai ba, amma sosai ta yi kyau, shiyasa da ta fito ya tuna a haka fa ta ga Abbakar ya ji zuciyarsa kamar zata fashe….
Tana fitowa ta bud’e motar ta shiga suka gaisa sama-sama ya kunna motar ya ja suka yi gaba fuskar nan a tamke kamar bai tab’a yin dariya ba, wanda hakan ya d’aure mata kai matuk’a! Dan ya kan yi shiru ya yi ta tunani amma bai cika had’e rai kamar hakan ba..
Duk da alhinin rasuwa da take a ciki haka nan ta daure ta dinga yi masa magana..wanda daga um sai um um kawai ya dinga binta da shi…..
A haka har suka k’arasa wajen..
iPhone d’inta ta zaro ta jona a jikin motar tasa dan ta ga bashi da niyyar shiga, ita kuma ta d’auki purse d’inta ta fara k’ok’arin fita bayan tace masa ta gode,
Kamar daga sama ta ji yace
“muga wayarki!”
A hankali tace
“gata nan tana charji, wanna kuma ta Muhsin ce na saka layina a ciki”
Ta yi maganar tana mik’a masa wayar”
Karb’a ya yi kanshi tsaye ya shiga message ya duba.
Yadda ya mik’o
Mata wayar sai da ta tsorata tana karb’a yace mata”jeki!!”
da d’an k’arfi!
A ransa yana ji inama bai duba ba…shiyasa fa tun d’azu yake ta tausar kansa amma zuciya ta tunzurashi sai da ya duba!!!
Ya san maganar Abbakar k’arya ne da ya ce tana basa zai siya musu gida, to amma kuma meyasa ta tura masa kud’i ba tare da ta tambayesa ba, sannan meyasa ta fita waje wajensa……
iPhone d’inta da ta kawo haske ya shiga ya duba nan ma yaga ta tura masa..
‘Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!
me yasa manubiya zata yi masa haka??”
Ba shi da mai basa amsa, a take kawai ya ji hawaye sun b’alle masa, dama ga masifar dayake a ciki tun kwanaki talatin da bakwai baya yanzu kuma ga kishin da yake shirin tarwatsa masa zuciya da kwakwalwa. shiyasa kawai ya kafa kansa a kan sitiyarin motar ya fashe da wani irin kuka.
Ya jima yana kuka kafin ya shiga jero istighfari, yq ɗago ya goge fuskarsa yana maida numfashi, dai-dai nan ya ji ana knocking masa gilashin motar tasa….