Sashe 119
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yashjub Yana fita gida ya nufa…har yanzu kwakwalwarshi ta k’i ta bashi kwakkwaran dalili kwaya d’aya wanda ya sanya su Daddy suke tunanin ya kamata ya auri Kausar saboda shi duk wannan bayanin da Daddy ya yi sam baiga ta inda hakan ya zamo hujja akan ya auri Kausar ba.
Zai iya kula da ita da ‘danta ba tare da ya kalli inda take bama,
Idan kuma tafiya takeso ta yi to
ta na iya wucewa, ta tafi duk inda takeso ita ta sani!Abu d’aya da ya ke da tabbacinsa shine idan ta riga ta haihu duk inda take indai a cikin duniyar nan ne to zai nemo ta kuma ya karb’o d’ansa, daganan kuma ita da shi har abada wallahi.
Maganar b’ata suna kuma ta je ta yayata ɗin, dan shikam tunda har ya sab’awa Ubangiji sannan Iyayenshi y’an uwanshi da Manubiya kowa ya san abunda ya aikata to tsoro ko kunyar ubanwa kuma zai ji??
Wallahi ba ya shakkar ta d’auki loudspeaker ta hau helicopter ta yi Yekuwaaa! sam hakan ba zai damesa ba,bai damu da mutane da abunda za su ce ba…kawai dai ya san duk shekarunsa da k’arfin tunaninsa bai Isa ya hango abunda su Ddaddy suka hango ba, shiysa ya yi putting maganar tasu into consideration.
Tunda ya taho yake addu’a Allah Ubangiji ya sa kar Manubiya ta amince, dan wallahi ba ya jin zai iya shak’ar numfashi muddin akace Kausar ta zama matarsa…ya ma san manu ba za ta yarda a yi mata kishiya ba, ta na son shi ba zata amince ya auri wata ba duk runtsi
,kuma zai yi ta nuna mata hujjoji har ya yi convincing d’inta.
Tunda ya taho, ya ke jin yadda wayarsa wadda ke a aljihu take ta faman vibrating…
Ganin an jera masa misscalls sama da ashirin ne yasa ya hak’ura ya zaro wayar zai amsa shi a tunaninsa ma daga gida ne amma sai ya ga bak’uwar number…tana katsewa ya fara shirin mayar da wayar aljihu saboda driving yake yi bayaso ya rik’e wayar a Hannu gudun samun distraction, kamar gizo haka yaga message ta notification bar an rubuta”ka duba watsapp, an turo maka shaidu akan wanda ya saka aka kaiwa Estate d’inka hari duk dan a kashe ka.”
Sai da sitiyarin motar ya kufcewa Yashjub, da mugun sauri ya rik’e! Allah ya rufa asiri bai bugu ba bai bige kowa ba, dan haka ya yi sauri ya yi parking a gefen kwalta yana jin yadda k’irjinsa yake bugawa zuciyarsa tana tsinkewa kansa kuma yana juyawa.
Wata zuciyar tana hanasa bud’ewa dan bai san mai zai gani ba sannan wa zai gani ba! Yayinda wata zuciyar take azalzalarsa akan ya hau ya gani.
Sai da ya yi addu’o’i ya ce ‘Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi’ tukunna ya danne zuciyar da ta ke hanasa bud’ewa..tashi d’aya ya kunna data ya hau Online k’irjinsa yana wani tafarfasa a lokaci guda kuma yana tunanin to waye wannan mai turo evidence haka ko dai tsokanarsa ake yi ana so a raina masa wayo….
to amma ai ba kowa bane ma ya san a na binciken.
Sai da messages suka gama shigowa tukunna ya hango number da ta kirasa d’in a ta chan k’asa ga kuma video nan alamun an turo tun d’azu, da messages wajen ashirin a cikin chat d’in.
Yanzun ma sai da ya yi da gaske tukunna ya shiga chat d’in ya yi scrolling chan sama ya fara daga farko inda aka turo abubuwa har wajen guda biyar aka goge,kafin a sake turo bayanai da pictures da videos.
Maganar farko da idanunsa suka fara yin tozali da ita itace”K’aninka jininka Yassir Imam kura shine ya haye mu ya bamu hotonka ya bada bayanan ka ya tsara mana yadda komai zai tafi a tsari domin mu samu mu kasheka.
A k’asa idan ka yi downloading za ka ga komai za ka ga yadda ya bamu kud’i da duk wani shiri da muka yi tare da shi.”
Wani irin jifa Yashjub ya yi da wayar jikinsa yana wani irin karkarwa!!ba dan kan kujerar mai zaman banza wayar ta fad’a ba da tuni ta tarwatse!!!!
Wani irin karkarwa da huci ya shiga yi yana jin yadda numfashinsa yake shirin d’aukewa!
Da kyar a hankali a fili ya shiga cewa”innalillah wa inna ilaihirrajiun, ya Allah kasa hakan ba gaskiya bane ba!”.
Ba shi da wani zaɓin da ya wuce ya sake lalumo wayar ya yi downloading ya bud’e ya kalla videos ɗin saboda yadda aka taso masa da tashin hankalin nan idan ba ganin ya yi ba ya tabbatar ko kuma akasin hakan tou ya san tsaf nan da y’an mintuna zai iya samun heart attack……..
Hakanan ya lalumo wayar ya bud’e ya shiga downloading hannayensa suna wani irin mugun karkarwa…
da kyar ya danna play, yana addu’ar Ubangiji ya sa kar ya ga Yassir amma sai dai kash!videon yana fara tafiya fuskar Yassir ce farkon abunda ya fara gani ya kuma fahimta,tare da mutumin da yake custody d’insu da wasu guda biyar!!
Yassir d’in ya na yi musu bayani dalla dalla yana jaddada musu kar fa a samu matsala su tabbata ya mutu.
D’ayan videon kuma inda yake basu mak’udan kud’ad’e ne sai ragowar kuma call recoding ne wanda ya k’unshi yadda suka dinga communicating, har wayar da suka yi d’azu yace su goge suka yi negotiating akan zai basu 3m duk sai da suka tura da receipt d’in 2 da 1m d’in da ya turo daga baya……..
So yake yi ya yi kuka, hawaye su zubo daga cikin idanunsa amma k’aff!!yau kam babu hawayen sun k’afe sun k’are…
Wani Irin jaa!idanunsa suka yi, jijiyoyin kansa duk suka baiyyana…so yake ya k’aryata amma babu hanya dan idan ya ce fuskar Yassir aka saka bai Isa ya ce muryar ma sakawa aka yi da yanayin maganarsa ba…..
Ya fi awa biyu a cikin motar, dan har sai da Manubiya ta fara waya sakamokon daren da ta ga yayi,tukunna ya kira driver d’insa ya kwatanta masa inda yake.
ya zo ya d’auke sa suka nufi gida dan kwata kwata ba zai iya yin driver d’in ba.
Shi kansa driver d’in sai da yanayin Yash ya bashi tsoro!Kamar wani zombie d’in robot haka ya zama, da kyar ma ya chanja waje ya koma mazaunin mai zaman banza.
Ko da suka isa gida ma bai sani ba har driver d’in ya zagayo ya bud’e masa ya ce masa”mun iso” har sau hud’u tukunna ya yi firgigit ya d’an kallesa kafin kusan bayan mintunan uku ya samu da mugun kyar ya motsa ya fito ya nufi k’ofar entrance.
Ba zai iya komawa ya d’auko key a cikin mota ba dan haka ya tsaya yana danna doorbell..
Lokacin da ya dawo Manubiya tana kitchen tana k’arasa soya wainar fulawar da suke yi ita da Siyama kafin su Ya Nafi’u su zo su d’auketa ta tafi.….jin door bell ya sa ta yi tunanin ko dai su Siyaman ne suka dawo maybe sun yi mantuwa dan basu dad’e da tafiya ba.
Da wannan tunanin ta fita dan sam ba ta kawo Yash bane da kansa ya tsaya yana danna bell maimakon ya bud’e kawai ya shigo.
Manubiya tana bud’e k’ofar suka yi ido biyu da shi a hargitse..dan fuskarsa ta yi jaaa idanunsa ma haka, jijiyoyin kansa sun fito sannan gaba d’aya babu nutsuwa a tattare da shi.
Yana ganinta sai ya sake karaya tashi d’aya ya zama emotional cikin tsananin damuwa da neman agaji ya fad’a mata a jikinta ya fashe da kukan da ya nema ya rasa d’azu!jikinsa yana wani irin karkarwa har abun tsoro.
Duk k’ok’arinta kasa rik’esa ta yi dan ya yi mata nauyi…a wajen suka zube nan bakin k’ofar ko rufewa ba su yi ba….tsoro da al’ajabi ne suka sanyata fashewa da kukan itama tana yi tana tambayarsa “me ya faru??”
Shiruuu, bai ce komai ba, dan ya kasa magana, ya kasa cewa komai kawai ya k’ank’ameta yana kuka bilhakk’i da gaskiya.
Sun jima a wajen sosai, kafin ta ji ya shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere yana wani irin numfashi….
Cikin sake fashewa da kuka tace”Ya Yash dan Allah ka fad’a mini koma menene, kana dad’a tsoratani fa!”
Ahanakali ya d’an cikata har yanzu jikinsa bai daina karkarwa ba…da kyar suka mik’e da taimakon juna,ya tura k’ofar ta rufu tukunna suka k’arasa cikin parlourn suka zauna ya ruk’o hannuwanta duka biyu ya runtse su a cikin nasa…..
Sau biyar yana bud’e Baki da niyyar yin magana amma sam sai ya kasa.
Ajiyar zuciya ta sauk’e k’irjinta yana dukan uku uku tace “duk runtsi, sannan a ko da yaushe zan tsaya maka kuma zan goyi bayanka akan dukkan komai!
Da ni da kai ba za a ji kanmu ba! Dan haka
Ka yi mini magana Mijina, dan Allah ka fad’a min ko ma menene.Mu nemo mafita mu magance matsalar tare.”
Da kyar ya samu ya iya bud’e Baki ya shiga yi mata bayani daki daki a kan case d’in Kausar, komi abunda ya faru yau sai da ya zaiyyane mata.
Kafin yace”duk abunda kika ce hakan za a yi, amma dan Allah dan Annabi kar ki ce in aureta,wallahi ba zan iya rayuwar aure da ita ba!”
Manubiya ba ta iya cewa uffan ba tsabar matsanancin tashin hankalin da ta shiga…shin wannan ɗin mafarkine take yi??
Da gaske wata ce take d’auke da cikin Mijinta a jikinta!kuma ake shirin aura masa ita?!!
Yashjub d’inta fa!inaa!!!duk kawaicin ta ba zata iya ba wallahi ba za ta iya ba!!!!
Ashe dama haka mata suke ji idan za a yi musu kishiya?ashe kwanakin baya da ta ji kishi da haushin Kausar duk wasa ne!!
Dan sai yanzu ne ta san menene kishi! ta kuma san zafin sa ta san yadda ake ji…wani irin feeling take ji feeling d’in da ko mak’iyin ta ba za ta so ace
ya ji ba!
Ji take yi kamar ta yi hauka!!!
ji take kamar za ta mutu!!
Hatta b’argo da tsokar dake a jikinta yau kam tabbas sun san tana cikin masifa….
Yanayin da ta shiga ya isa ya sanya Yashjub ya fahimci amsar ta ‘a’a’ ce, dan haka cikin tsananin farin ciki ya rungumota yace”na ji dad’in wannan decision d’in naki,na ji dad’i….”