← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 152

Sashe 139

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sama-sama take jin muryar Ya Musbah shima yana kuka yana
yayyafa mata ruwa yana kiran sunanta!
A hankali ta shiga k’ok’arin bud’e idanunta kanta yana wani irin mahaukacin sarawa…dishi-dishi ta fara gani kafin ta samu idanunta suka ware tarr,,tana iya kallon fuskar ya Musbah shab’e-shab’e da hawaye wanda hakan ya sake tabbatar mata tabbas Inna ta rasu!!!

Mik’ewa ta yi ta zauna ta shiga k’are musu kallo, kowa ya hallara har da mai sunan Baba ya Nafi’u da Aisha da Likita yana duba Inna.

Fashewa ta yi da wani irin kuka kanta yana wani kalar mahaukacin sarawa ta samu ta mik’e daga kan sofar dake a d’akin(inda suka d’aurata)
da mugun kyar ta wuce Ya Musbah ta k’arasa inda Likitan yake duba Inna tana shirin yin magana dai dai shi kuma ya d’ago ya kalleta tukunna ya kalli su Baba cikin karyewar zuciya yace”rai ya yi halinsa!sai dai mu yi mata addua!!..i’m so sorry…..”
Gaba d’ayansu har mai sunan Baba da Khairat fashewa suka yi da kuka! Yayinda ita kuma Manubiya ta nemi nata kukan ta rasa hawayen idanunta suka k’afe k’aff saboda tsabar masifa da tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki wanda ba ta tab’a jin kwatankwacinsa ba tunda Inna ta kawo ta duniya!!

Tabbas zafi rad’ad’i zugi da d’acin rashin Mahaifiya daban yake! Ta yi going through hell a rayuwarta dan masifa kusan kaɗan ne za ta ce bata ɗanɗana azabarsu ba amma ba ta tab’a jin kalar bala’in da ta ke jinta a ciki a halin yanzu ba.!

Ita ba ta fad’i ba ita ba ta zauna ba hakanan ta tsaya musu k’ememe ta k’ame kamar gunki dan haka gwaggo Suwaiba ta ja ta ta kaita kan kujerar da ta taso ta zaunar da ita ta rungumeta tana wani irin kuka kira take”Mannubiya ki yi kuka,dan Allah ki yi kukan nan ko kya rage zugi da zafin zuciya……..”
Dai dai nan Baraka ta shigo d’akin d’ankwalinta rik’e a Hannu….haka kurum d’azu suka ga ta fita a rikice yanzu kuma gata ta dawo a hargitse!!!!…
Ba ta ita suke ba, shiyasa babu wanda ya ko sake kallonta ma har ta Isa ta je ta bintik’e Manubiya daga jikin Gwaggo Suwaiba ta mik’ar da ita cikin tsananin tashin hankali tace”Manu ya ake ciki?”

Girgiza kai Manubiya ta yi cikin rauni ta durk’ushe a wajen tana k’ok’arin janyo kuka amma sam ya k’i zuwa!
Sake mik’ar da ita Baraka ta yi tace”ta mutu kenan yanzu shikenan??”
Cikin fara jin haushinta gwaggo Suwaiba tace”ta rasu zaki ce Baraka ba wai ta mutu ba, kuma addu’a za ki yi mata ba hauka ba!”
D’amara Baraka ta yi da d’ankwalin Hannunta tace”ki gaya mini tsakaninki da Allah..shin
A tsakankanin jiya da muka rabu da ku zuwa yau shin ta bi ta kan k’ofar band’akinta ta wuce? bi ma’ana ta shiga b’andakin ta kafin ta mutu!???”

Cikin k’unci Ya Musbah yace”Baraka bar nan!!”

Kansa ta nufa tana zuwa ta tsaya a gabansa tace”Amsa d’aya za ku bani sai in tafi!!
Shin kafin Inna ta mutu ta bi ta kan k’ofar band’akinta? ‘eh’ ko ‘A’a’?
Dan Allah ku bani amsa in san makomata saboda idan ba ta wuce ta shiga band’akinta ba to akwai matsala fa!! wallahi akwai matsala!!!!”.
Sai kuma ta nufi Inna tana zuwa ta fara k’ok’arin ruk’ota tana cewa “Allah yau sai kin tashi kin fad’a mini shin kin bi ta kai ko baki bi ba, ki tashi idan ba ki
bi ba to ki bi yanzu a gabn idanuna in gani…..”
Dai dai na Ya Musbah ya k’araso ya juyo da ita ya d’auketa da wani kalar rikitaccen mari.
Kuka ta fashe da shi tace”ba ta haukace ba ta mutu ni kuma na haukace!!!saboda Allah in banda mugunta irin tata ta ya zata kwanta ta mutu ba tare da ta bi ta kan abunda na zuba mata ba?
salon ta jaza mini bala’i!!!!” sai kuma ta fincike ribbom d’in kanta ta hau barbaza gashin kanta ta fara tsalle tana dira tana cewa
“ai ku barshi ba sai kun fad’a mini komai ba ma, yadda na fara ji a jikin nan nawa na san ba ta bi ba ni kuma asirina ya dawo kaina, Innalillahi wa inna ilaihirrajiun mun tafi ba zamu dawo ba, da ni da Inna mun tafi inda ba a dawo wa!! ita ta tafi garin matattu ni kuma na tafi garin mahaukata daga ni har ita ba zamu tab’a dawowa ba!!…
Bokan yace mini asirin baya karyewa ba a tab’a iya k’aryawa…”
Daga haka ta juya ta kinkimi takalmin da ta gani a k’ofar band’akin ta rungume ta fice da wani irin mahaukacin
gudu tana kurma uban ihu!!!…
…
Iyaka maganganun Baraka sun isa su faiyyace musu komai!!! shiyasa kawai duk suka bita da ido kowa yana Allah wadai!!!.
Halin da suke a ciki bai sanya kowa ya sake bi ta kan Baraka ba..tana wucewa suka ci gaba da koke kokensu.

Kafin awa d’aya gidan ya cika taff da jama’a, har da matan su Uncle da Mama kowa ya hallara, har Najeeb da Siyama su Jidda suma sun ce suna airport.

A nan parlourn Baba mai k’ofa ta baya, Gwaggo Suwaiba da Mama suka yi wa Inna wanka amma da ikon Allah ana gama yi mata wankan Gwaggo Suwaiba ta hana a yi mata sutura, har kawo yanzu, kawai dai sun rufa mata zani sunata yi mata addu’a, ita kuma Gwaggo suwaiba ta k’ura mata idanu tana ta kallonta.
…….
Najeeb da Manubiya sun kira Yash amma bai d’aga ba, kuma bai biyo kiran ba shiyasa Najeeb yace bari ya je gidan ya dubosa.

Tun cikin dare Yash ya kasa barci sakamokon mummunan mawuyacin halin da ya dinga ganin Mommy da Ya’isha a ciki a mafarki…shiyasa ya kasa hak’ura duk da yadda Mommy ta ja masa kunne kar ya je inda suke! k’arfe bakwai ta na yi ya fita ya nufi gidan saboda zuwa wannan lokacin ko rufe idanunsa ne in ya yi to kamar Irin a cikin gobara haka yake ganinsu, shiysa ma ya yi tunanin ko gobara ce ta kama a gidan gashi duk d’insu babu mai d’aukar wayarsa.

Yasira,da! ta yi fushi, tace Wallahi Hatta office d’in ma ta daina zuwa, amma sai Mommy da Y’aisha suka yi mata magana jiya da daddare suka ce “ta je, ai bazasu zuba masa ido su kyalesa hakanan ba, kuma idan ba ta je ɗin ba to tsaf zai iya d’aura Ummi a kan komai tunda Yash bai gama resumin aiki ba”…dan haka ta shirya saboda dama yau ta san da zuwan manya manyan bak’i.

Tare suka fita ita da Yusra, wadda zata ga invigilator d’inta a yau,ta sauk’e Yusran ita kuma ta wuce office……

Sosai yau Mommy take jinta a sama, ta dad’e bata samu soundsleep (bacci mai daɗi) kamar na jiya ba, saboda ta riga ta san yau zata ji labarin mutuwar Manubiya….:

Tun a jiyan da suka gama magana da Ya’isha ta yi musu sai da safe ta shige d’aki, har suka gama breakfast su Yasira suka fice sam Mommy ba ta ji motsinta ba, dan haka ta lek’a d’akin da yake mallakinta..
Da wani irin mahaukacin gudu ta k’arasa cikin d’akin sakamokon hango Ya’isha da ta yi wanwarr a k’asa a yashe…..
Tana zuwa ta d’agota ta d’aurata a kan cinyarta ta shiga kiran sunanta amma ko gezau!!
Duddubata ta hau yi amma sam ba ta ga alamun rai a tartare da Ya’ishan ba, ga idanunta sun k’afe suna kallon sama wanda hakan ya sanya tashi d’aya Mommyn ta fashe da wani irin kuka ta rungumeta da k’arfi a jikinta cikin kuka ta shiga cewa “I’m so sorry Ya’isha, Innalillahi wa Innailaihirrajiun….”
Sai kuma ta mik’e zumbur ta fita waje….

Sai da Mommy tabbatar ta kulle ko’ina, sannan babu kowa a gidan tukunna ta koma ta d’auko makullin mota da Hijabi ta zo ta bud’e boot d’in motar gudun kar a kamata dan motarta babu tint.

Tana wani irin kuka ta je ta kinkimo Ya’isha da kyar ta sakata a booth, hakanan tana ji tana gani ta rufe y’ar tata a booth a ranta tana k’iyasta yadda zata yi da su Yashjub muddin ta samu Ya’isha ta farfad’o dan wannan duk laifinsu ne!!! tunda uwarsa ta shigo rayuwar Daddy har yau ba ta samu kwanciyar hankali ba, gashi yanzu saboda shi da Manubiya ta zo wannan flat house d’in d’an mitsitsi ta zauna sannan kalli a booth ta saka y’arta yo
Idan bata ga bayan su Manu ba ma ai ba ta cika sunanta Khadija ba wallahi…..
Sannan ad’uarta d’aya ‘Allah dai ya sa ba aikin bane ya lalace, Allah ya sa dai abun ya kama Manu’ dan tabbas jiya Ya’isha tace mata bata yi mistake ba, to amma kuma mai ya faru!!!? Me yasa abun ya tab’a mata y’a!!!!?
Hakanan tana ta sak’e sak’e hankalinta a masifar tashe ta je ta zuge gate d’in tana wani irin kuka…tana gama zugewa ta koma ta fitar da motar ta fito ta mayar da gate d’in ta rufe, sannan ta koma ta ja motar ta nufi gidan tsohon jiya dan ta san shi kad’ai ne zai iya farfad’o mata da Ya’isha………

Sosai tun d’azu Yashjub wanda sam ba ta lura da shi ba ya ke tsaye yana kallonta yana mamakin yadda take kuka…….sannan yadda ta zuge gate da kanta ta fita da asussubah, tabbas hakan abun mamaki ne.

Sai da ta Isa k’ofar gidan tsohon, tukunna ta tuna ba ma ta d’auko wayarta ba, ballantana ta kirasa ya bud’e mata, dan haka kawai ta fito ta Isa bakin k’ofar gidan nasa ta hau bugu.

Ba ta wani dad’e tana bugawa ba tsohon ya zo ya bud’e mata k’ofar, dan dama daga shi sai
dabbobi ne a gidan.
Chapter 139 · 0% Book details